Free chapter ยท Read without an account
Episode 3&4
๐๐ *FARAR MACE...*๐๐
*Sabon Taku*
*Oum Sumayya*
BabybintuuY
Wannan littafin na kud'i ne akan farashi me sauk'i 500 via 4210014214 lawal shamsiyya eco bank sai atura shaidar biya ta *** masu tura kati mtn ko airtel numbobi kawai bana son vtu zasu tura ta *** idan baki/ka shirya ba please tsaya kashirya karmu b'ata ma juna lokaci sannan dan Allah banda kira only WhatsApp!
*PAGE THREE AND FOUR*
.Afusace yace "Said again!"
Kallon shi tayi dakyau tana basarwa ganin yanda yake huci tace "ba buk'atar na maimaita tunda nasan kaji koda shike nasan wannan bak'ar kake adana ma kanka hakan kuma yayi"
Wani irin hankad'ata yayi tafad'a saman gadon kafun ya wani pointing d'in ta da yatsa yace "you have to be careful akan abunda bakin ki yake fad'a" yana fad'in haka yasauka akan gadon yafad'a toilet yawani bugo k'ofar da mugun k'arfi,
Da wata uwar harara tabishi kamun taja tsaki tasauka agadon tewol d'in data yar tad'aura tana wani yatsina fuska tajanyo hand bag d'in ta kamun takoma bakin gadon tad'auko wayarta k'irar Samsung danne danne tafara na wasu y'an mintuna kafun takara wayar akunnen ta da alama kira tayi ring d'aya biyu uku tad'an kalli k'ofar bayin saita ce "Aunty babu wani cigaba fa mutumin nan yanda kika san waliyyi har tsirara nake agaban shi amma ko alamun wata sha'awa bana gani atattare dashi at the end ma yanxu yace kano zamu taho shirin mu na gaf da lalacewa wallaho kaina nikam ya kulle"
D'an jim tayi saikuma tace "tom shikenan Aunty zanyi duk me yiwwuwa domin yau itace dama ta tak'arshe idan ta kubce dukkanin shirin mu yalalace"
Shiru tasake yi for some minutes kamun tace "yes that's the solution thank you so much saikin jini"
Kashe wayar tayi tana gyara d'aurin tewol d'in cikin nazari saikuma tasaki wani irin shu'umin murmushi tamik'e dasauri wardrobe tabud'e tad'auki wata gown tazura batare datasa bra ba rigar royal blue ce tayi matuk'ar amsar fatar jikinta gashi roba ce ta matuk'ar bin jikinta siiririn mayafi tad'auka tayafa kamun tajuya da niyyar barin room d'in taganshi abayan ta yayi folding hannayen shi yana kallon ta da alama yajima awajen ayamutse ta kalleshi tarab'a shi zata wuce yawani ruk'o kafad'an ta da tattausan palm d'in shi murya can k'asa kamar wanda akaima dole yaayi maganar yace "ina zaki"
D'an duban shi tayi tana d'an turo baki cike da shagwab'a tace "wajen da zan samu natsuwa mana tunda kai baka buk'atata"
Hanci yad'an lakace mata kamun yace "Koya zan ganar dake bazaki gane ba narasa yanda akai kike nema ki lalace Halisa bakya son muyi tsaftataccen aure ne?"
Akaikace takalla shi kamun ta kauda kaii cikin takaici tace "idan kajure ni bazan iyaba koko ni dutse ce dazan kwana da gwarzon namiji ingarma kamar ka amma na kauda kai? Yes da ba haka nake ba amma cikin kwanaki uku nacanza saboda kaine kafara kwad'aitar min da son kasancewa dakai ko cemaka akayi bani da isashshen lafiya ne just once zamuyi abunnan aure zamuyi babu wanda zai gane daga ni sai kai fa please kaima nasan kana buk'ata dan Allah"Afusace yad'aga hannun shi daga jikinta kafun yajuya mata baya yana d'an tatttauna lips d'in shi batare da yace mata komai ba yazauna yana dafe kanshi kusan mintuna biyu yaji k'arar k'ofa alamun tafuta tabbas yana son Halisa kuma kwarai yanajin matsananciyar sha'awarta komai nata yamishi saboda kasancewar ta *FARR MACE* amma kuma shiba mazina ci bane hasali ma bai tab'a aikata dukkanin abunda ake tunanin yanayi ba shi kanshi yana mamakin yanda ko yaushe sha'awar shi zata tashi amma dayaje ga mace sai bananar shi ta kwanta yarasa dalili yaga likitoci ak'asa mabanbanta amma amsa d'aya ce lafiyar shi k'alau wannan dalilin ne yasa yake tsoron yin aure saboda shiga hakk'in matar shi sai gashi kwatsam Halisa tashigo rayuwar shi irin macen daya jima yan mafarkin samu *FARAR MACE* me class coca cola shape tabbas Halisa takaii mace tako ina bata da makusa da ita yashirya rayuwa da ita yatsara komai nashi kwatsam kuma sai k'addara tajuyo kanshi lokaci d'aya komai yab'aci wata zazzafar iska yafurzar kamun ahankali yasilale yakwanta cike da kewar Ammin shi.
***
Koda ta koma gida gaba d'aya barci ya k'aurace ma idanun ta tausayin Junaiha ne gaba d'aya ya addabe ta tabbas idan tabar wannan auren taci amanar Falmata shin dawani ido zata kalleta aranar dasuka had'u taci amanar ta kenan dole tayi duk me yiwwuwa na ganin ta kwatar ma Junaiha y'an cin ta dole tasan yanda zatai awannan karon ko ita ko *MODIBBO FAMILIES* cikin biyu dole ayi d'aya siririn numfashi taja kamun tamik'e tashiga bedroom kayan jikinta tarage tafad'a wanka cike da tunanin mafita da tunanin ta inda zata fara domin tasan tako ina sunfita k'arfi amma kuma bazata yarda da wannan nukufurcin ba.
******
Koda ta iso gida ababban d'akin taro ta iske dukkanin wani ahalin na gidan kowa na zaune akan rug yayin da wata kyakkyawar farar dattijiya da hutu dajin dad'i suka b'oye ainihin shekaru da tsufanta tana zaune akan wata kujera me kama data sarakai idanun ta sanye da farin glass tana kallon su d'aya bayan d'aya yaranta maza uku mata biyu Aliyu shine babba sai mai bi mishi mace Sarah sai Kamal,Mudassir sai auta Aisha dukkanin su sunyi aure matan na gidan mazajen su su kuma mazan kowanne yana cikin estate d'in da matan shi Aliyu matan shi uku Kamal matan shi biyu haka Mudassir shima biyu kowanne yana da yara amma dukkanin su y'ay'an su mata ne Aliyu ne kawai yake da d'a d'aya kwalli d'aya da dukkanin families d'in suka d'aura son duniya akanshi amma lokaci d'aya yakarya musu tsinke atakashi, cikin d'an b'acin rai tayi gyaran murya tana kallon agogon dake nuna shabiyu saura na dare ahankali tafara cewa "Duk naji koken ku akan wannan aure na Omar da takwara ta Kausar amsa d'aya nake buk'ata agareku shin Omar shine ya haifi kansa da har zai nuna bamu san abunda yadace dashi ba ko tsoron shi mukeji da har yake abu gaba gad'i ban tab'a yanke hukunci wani yak'etare shiba sai shi dana d'auki son duniya na d'aura mishi kasantuwar shi na jikan fari namiji acikin ahalin nan amma saii gashi lokaci d'aya yayi watsi da komi yanuna min iyakata ba komai mutuwa taja min da MODIBBO na raye babu wanda zai tab'a kawo mai togaciya amma dake ni mace ne yaran nawa ma ba ganin mituncina suke ba tunda har d'a d'aya kwalli d'aya zai gagaresu ba komai haka rayuwar take" tak'arisa maganar tana fyace hanci sai kuma tafara kuka tana goge hawaye tana fad'in "MODIBBO inama zaka dawo duniya daka ga abun mamaki da ban...."
Cikin sauri d'aya daga cikin su yanufe ta yana fad'in "Haba Hajiya meyasa kike fad'in haka inace burin ki ad'aura auren toba and'au....."
Afusace takatse shi da fad'in "Kamaluddin! Maganata tak'arshe agareku shine kunemo min duk inda Omar yake zuwa safiyar gobe idan ba hakaba bana son sake ganin fuskokin ku"
Tana kaiwa nan amaganarta tamik'e tad'auki sandarta tabar d'akin taron,
Gaba d'aya jikinsu yayi sanyi babu wanda ya iya kwakk'waran motsi har saida ta idasa futa daga d'akin sannan wata tamik'e tana yamutsa fuska takalli wacce ke kusa da ita tace ayatsine "Allah astagfirullah ni Jamila wai inace mace ce take gudu idan za'ai mata auren dole? Ohmn karo na farko naga namijin daya gudu dan za'ai mai auren dole abun itace zata gudu saboda mummunan GAMIN GAMBIZAN da aka kwafsa anhad'ata aure da mashayin giya kuma manemin mat..."
Agigice tadafe kumatun ta tana kallon shi kafun ta wartsake yanuna mata k'ofa yace "get out" cikin firgici tayi hanyar k'ofa da mamakin Alhaji Aliyu karo na farko daya tab'a kai hannun shi jikinta da sunan duka lallai akwai matsala,
Cikin takaici Alhaji Kamal yace "bai kamata kana kai hannun ka jikin mace da sunan duka ba sai hak'uri Yaya adinga k'ok'arin sarrafa fushi dan Allah"
Tsaki yaja bare kawai batare daya sake furta komai ba yafuta afusace,
Cikin sharar hawaye tace "Daya rabu da ita kome tafad'i shi yajama kanshi Allah yasani nayi iya bakin k'ok'ari na naganin nabashi tarbiyya amma ya watsar waye sila shine silar komai shi yanuna maii gata shi yanuna mai kome yanema zai samu ak'arshe abunda nake gudu shi ya afku"
Cikin b'acin rai Aunty Hannah take share mata hawayen fuskarta kamun takama mata hannu suka bar d'akin taron,
Haka kowa yadinga mik'ewa d'aya bayan d'aya yana barin wajen masu kwand'e baki da k'ana nan maganganu nayi masu Allah kyauta nayi.
*****
Sosai ta girgiza dajin kalaman Hajiya Malika wani iriin sabon tashin hankali tashiga takalli babbbar y'arta Sopiyya data kasa cewa komai kanta tadafe kawai tadawo da duban ta ga Aunty Zee dake ta trying wata number amma isn't reachable ajiyar zuciya tasaki kamun tazauna agefen gado cikin wani irin yanayi tace "Omar yabani kunya yacutar dani yagama b'ata min dukkanin wata martaba ta awajen sirika ta sannan ya fitar da lago na acikin kishiyoyina yaja min abun tsegumi amma duk abunda zai faru bazan tab'a bari auren nan yamutu ba domin ayanzu hakan shine burin dukkanin mak'iyan mu mukuma tabbatuwar auren shine zai dawo da dukkanin farin cikin mu inason duk yanda za'ai kutabbatar kun janyo Junaiha jikinku tayanda dukkanin motsin Hajiya Malika zai kasance mun sani"
Cikin nazari Hannah takalli Ammin nasu tace "Hakan ma mafita ce amma kuma wani hanzari ba gudu ba da akwai masu zagon k'asa acikin gidan nan saimun k'ara sa idanu sosai zamu fahimci komaii domin nasan Omar yana dajin magana amma lokaci d'aya yabirkice duk wani halin shi nagari yakauce baki tunanin komai agame da hakan?"
Shiru duk sukayi kamun Zee tace "Tabbas ina zargin akwai wata mak'ark'ashiya da makircin da aka jima ana k'ulla shi kuma zargina yatafi ga Aunty amarya da wannan sister nata"
Wani irin kallon su Ammi tayi zatai magana kenan sukaji k'arar fashewar abu daga awaje kallon kallo sukayi ma juna kafun Hannah takalli agogon dake manne ajikin bango fast 1am ahankali tamik'e tanufa k'ofar, batare dawani tsoro ba duk suma suka mik'e suka rufa mata baya
****
Ajiyar zuciya yasauke aranshi yace "Am so sorry Ammi na ina kewar ki amma kun lalata min dukkanin farin cikina ne that's why am so sory dasauri yatashi zaune kamar wanda aka tsikara ya janyo laptop d'in shi dake side drawer a ijiye kunnata yayi kafun yasaka wani sabon layi a modem d'in shi data yakunna take sak'onni suka fara shigowa ta gmail d'in shi idanun shi ya lumshe yana sake maimaita sak'on Ammin shi dayaci karo dashi ayanxu sossai ya tayar mai da hankali wani sabon b'acin raine yasake turnik'e shi kusan mintuna ashirin yaji alamun wani sak'on dasauri yabud'e idanun shi wani wawan tsaki yaja ganin picture d'in abunda yafi tsana aduniya ana dan ganta ta da matar shi k'aran k'ofa yaji hakan yasa yad'aga kanshi Halisa yagani d'auke kanshi yayi yana rufe laptop d'in afusace kamun yad'an jingina da fuskan gadon yana tunani akan furucin Ammin shi *_Ga matar ka Junaiha nabaka amanar ta ko bayan raina muddun kacutar da ita bazan tab'a yafe maka ba ina so kazame mata uwa kuma uba sannan kabata dukkanin farin cikin da miji yake bama matar sa bana son ganin b'acin rai afuskar ta Omar zakai alfahari da wannan had'in komu dad'e komu juma ko muna raye kobama raye inafatan zaka gaggauta dawowa garemu domin komai ya kammala agame da auren ka saika amshi wannan d'in amatsayin kaddara nikuma namaka alk'awari zan yafe maka sannan bazamu tab'a hanaka auren kowacece ba ayanzu Allah yamaka albarka namijin duniya Allah yakare ka aduk inda zaka kasance ka kula da kanka!_*
Wata zazzafar iska yafesar yana d'an jujjuya kanshi afili yafurta "tabbas kowa zaimin dariya matuk'ar akaji na auri bak'ar fata bak'ar fatar ma illiterate bak'auyiya ya Allah why why abun is too much for me bak'ar mace ohhhh" yaja wani zazzafar iska yafesar kafun yawani kaima iska duka yana fad'in "tunda tayi kuskuren shiga rayuwa ta wallahi saita gane shayi ruwa ne saina zamar mata kadangaren baki tulu saita gwammace rayuwar datayi ada saina shayar da ita ruwan bak'in ciki tabbas dakanta zata buk'aci raba auren nan saina mata dabaibayin da ko mai suna Farooq taji anfad'a saita firgice cikin ruwan sanyi zata gane kuskuren yimin kutse acikin rayuwata" yak'arisa maganar yana wani irin huci,
Halisa dake gefe da goran wani jus tana d'an girgiza shi tasaki wani irin shu'umin murmushi tana wani kad'a many'a idanun ta dasuke k'ara mata kyau tad'auki k'aramin cup tanufe shi cikin rangwad'a da kissa tana fad'in "Haba my Lion king cool your temper please ga jus kasha bai kamata kana b'ata ranka abanza awofi akan wata kucakar da cikin mintuna idan mukaso zamu b'atar da itaba don't worry about this just handle the case for me i will do anything inga tafuta cikin rayuwar mu sha wannan tukunna"
Kamar wani gaula haka ya amsa cup d'in yakai bakin shi idanun shi dasuka koma jajaye kamaar gauta k'ur akanta saida yasha fiye da rabi sannan yacire cup d'in abakin shi yana wani lumshe idanun shi jingina yayi da gadon wani irin shauk'i ne yafara koran wancan yanayin nashi,
Wani irin murmushi tasaki tana jujjuya idanun ta kamun ahankali tawani d'aura tattausan hannayen ta duka asaman tewol d'in shi tana murza shi zuwa k'asa tana fad'in........โ๐ผ
It's 500 via 4210014214 lawal shamsiyya Eco bank and send the evidence of payment via ***