Free chapter · Read without an account

Part 9

by Safiyya Haruna · Rumasa'u

RUMASA'U (The innocent girl).

By Mrsjmoon


Page 09.


Cikin natsuwa Muhsin ya fito jin an dafashi yasa shi zabura cike da tsoro domin bai lura da isowar Alhaji Ahmad ba. K'irjinsa ne ya harba ganin fuskan wanda ke gabansa domin shima atake ya hasko inda ya sanshi.


"Assalamu Alaikum. " Alhaji Ahmad ya furta tare da mik'a masa hannu, amsa sallaman ya yi batare da ya mik'a masa nasa hannun ba.


"Affuwan d'an uwa ba nufi baka tsoro ba." Ya ambatawa Muhsin cike da murmushi.


"No bakomi Alhaji." Ya amsa cikin dakiya.


"Thanks."


"You're welcome."


"Dama in bazaka damu ba ina son yima wata tambayace amma ina had'aka da girman Allah da Manzonsa in na tambayeka ka fad'amin gaskiya."


"In sha Allah."


"Good" Ya ambata cikin kallon gogon da ke d'aure a tsin-tsiyar hannun Muhsin a ta ke Muhsin d'in ya k'ara rikicewayi, a tak'aice Alhaji Ahmad ya ke k'are masa kallo ganin yarda k'irjinsa ke harbawa sai ya tako ya cike tazarar da ke tsakanin su ya kamo kafad'unsa da dika hannayensa ya girgiza kad'an "Be a calm my friend I just asks you, amsa kad'ai zaka bani bisa gaskiya amma banzo gareka dan nacutar da kai ba dan haka ka cire tsoron komi ni ba macuci ba ne dik kan lamurata na kanyisa ne bisa adalci in har na fahimci abokin mu'amalar tawa adali ne." 


Gyad'a kai Muhsin ya yi cikin sauke numfashi yana mai jin natsuwa na sauka cikin ruhinsa.


"Very good." Alhaji Ahmad ya kuma furtawa tare da janye jikinsa ya tura hannu cikin aljihu ya fiddo da agogo exactly irin na Muhsin ya mik'a masa nok'e hannu ya yi k'i amsa.


"Abokina shin wa ka sa ni mamallakin wannan a gogon kuma me kasani game da samunsa a inda akayiwa yarinyar fyad'e?" "


"Da farko sadda naga ogogon cewa na yi na d'an uwana Abid ne sannan bansan komi a game da samunsa da akayi a wurin ba." Ya amsa kai tsaye.


"Fahimtar da ni yarda zan gane dan sam ban fahimci zantukanka ba."


Jingina da jikin motarsa ya yi ya koro masa bayanin yarda suka yi da Abid d'in da kuma mahaifiyar su.


"Yanzu yana ina Abid d'in?" 


"Makaranta amma ina mai kuma tabbatar maka bashi ne mamallakin agogon ba domin na gamsu da bayanan mahaifiyarmu dan ni d'in shaidane na ganin agogon a d'akinta, yanzu haka in zaka iya jirana zanje na d'auko maka dan ka shaida."


"Kana son wanke sa kenan kamar yarda mahaifiyarku ta yi?"


"Ko d'aya ba haka ne manufarmu, Umma mai gaskiya ce ni kuma ina kok'arin sanar maka da gaskiyar ce kamar yarda rok'eni."


"Haka ne amma zan so ganin shi Abid d'in ido da ido sabida ina da tambayoyi da zanyi masa."


"Bani card d'inka ko digit insha Allah har office ko gida zamu zo tare da shi dan cikin satin nan zai shigo."


Mik'a masa card d'in ya yi tare da sa ke bashi hannu danyin musabaha wanna karan ya amsa sukayi sallama cikin mutunci. A cikin Mora Alhaji Ahmad ya zurfafa cikin tunanin akan dalilin da yasa suke son taimakawa mahaukaciya da d'iyarta alhalin basu san inda zasu gano su ba.


"Kawai tausayi ne." Ya ambata cikin sosa forehead nasa. Gyara kwanciya ya yi ya kafe k'ofar gate d'in gidan da ido sai ko ga Hajiya Aminatu ta fito cike da wal-wala ganin motarsa yasa ta ware idanu hannu ya d'aga mata ta iso ta zauna gefensa "Kai Dadyn Hamid anya wannan k'unatar taka ba mutuwa na kusayi ba kuwa?"


Harara ya cilla mata ya kunna mortar suka bar wurin batare da ya amsa ba.


"Uhm Hubby Allah lokuta da dama ina shiga cikin tsoro na kulawan da kake bani sai na yi ta sak'e-sak'e mara kyau like mutuwa ko rabuwa."


"Huwa Auwalin wa Ahirin wa Zahirin wa bad'inin wa huwa bi kulli shai'in Alim. Shi ne addu'ar samun waraka daga zancen zucci mara kyau dan haka sai ki yawaita yinsa dan samun natsuwar ruhi."


"Jazakillah."


"Amin."


"Abban Hamid mudawo kan maganarmu ta k'arin aure."


"Ya kika sami Hajiyar dafatan tana lafiya." Ya kauda zancen sabida bashi ne a gabansa ba.


"Lafiyalau ta ce na gaisheka kuma tana nan zuwa ganika tunda baka son ladar sada zumunta."


Dariya ya sanya batare da ya ce komi ba. Cikin hira mai cike da fahimtar juna suka k'arasa cikin unguwar, a hankali ya ke driving har suka iso inda yaso ganin Mahaukaciyar ya ja numfashi "Dear kinga inda na ganta cikin neman taimako."


"Allah sarki, Allah ya karemana su a dik inda suke."


"Amin ya rabbi."


Saida suka soma zuwa gidan Baba Liman suka gaisa sannan suka isa gidan aminin nasa Alhaji Bala wanda k'arara d'abi'unsu ya ke da bambanci. Kyawu hali da ki shiyarta ne ke had'e wuri d'aya lamarin da ke bawa al'umma mamaki matuk'a, domin Alhaji Ahmad mai kirki ne ya yin da Alhaji Bala ke da akasin haka, shi yasa har yanzu matarsa da Hajiya Aminatu k'awancensu sama-sama ne.


*

Iya kacin k'arfinta ta ke jijjiga Maman nata tana fad'in "Ki tashi mu gudu Mamana sunzo kashemu ne!." Amma bata da niyyar motsi kuka ta fashe da shi cikin waige-waigen hanyar tsira.


Ihun kuru-ruwan su ya tashi Maman ya yin da hakan ya firgita d'iyar itama ta k'wala ihu, a zabura ta yunk'ura zata fice daga kangon d'iyar ta rik'eta gam cikin fizgan numfashi mai nuna da tsananin tsoro ta ce "Mamana masu yankan kai ne sunzo kashemu wayyo Allah ina zamu b'oye?"


K'ara zabura ta yi sabida ihun nasu sai k'aruwa ya keyi cikin neman d'auki. Kafin d'iyar ta ankara har Maman ta fice a juye sai ta rufa mata baya amma ganin abinda ke faruwa yasa suka dawo da baya suka k'an-k'ame juna cikin firgici.


Wani kalan halittar abu ne mai dogon bindi keta zane su Malam Jauro da mutanen nan da sukazo dan illata Mahaukaciya da d'iyar ta. Jin gurnanin ya nufo inda su ke sannan ihun da su Malam Jauro keyi ya d'auke yasa d'iyar fizgan hannun Maman suka fito a guje daga lungun da suka b'oye dai-dai lokacin kuma da halittan ya iso bakin wurin ihu suka k'wala ganin ya d'aga bindinsa ya laftawa Mamanta a ciki ta zube k'asa tana mulmula cikin ihu.


"Na shiga uku ya kashemin Mama!." D'iyar ta ambata da k'arfi.


Harbin da akayi ya sa halittan juyawa inda yajiyo sautin wannan shi ya bawa uwa da d'iyar nasarar tsira daga halaka suka d'iba a guje suka fice wajen kangon. Gudu sukeyi rik'e da hannun juna batare da lura cewa titi suka iso ba suka fad'a tsakiyarsa kai tsaye, Allah yasa babban titin babu motoci sabida dare ne amma da tabbas labarinsu ya zamo tarihi. 


'Yan banga ne masu sintiri cikin unguwa da gefen titina suka jiyo ihun su Malam Jauro shi ne suka iso wurin, ganin gawarwakin muatane hud'u zube tare da jiyo sautin ihu yasa sukayi harbi cikin rashin sanin abinda ke faruwa, suna ganin fitar mahaukaciya da d'iyarta suma suka d'iba a guje halittan ya rufa musu baya, bisa rashin sanin inda suka dosa suka nausa cikin kangon tamkar b'eraye haka suka rik'a tsalle suna dira bayan kangon ta window, dik wanda ya samu ya jisa a waje sai ya kwasa a guje cikin kuru-ruwan neman agaji, tuni sun zubda makamansu burinsu kawai tsira da rayuwarsu. Halitta ganin sun fice sai ta dawo ta koma makwancinta dama hayak'in tabar wuiwui da su Malam Jauro suka zo da shi ne ya tasota, amma din tsawon zaman mahaukaciya da d'iyarta bata tab'a fitowa ba.

Kango ne mai tsohon tarihi mutane basu tab'a jin abu mara dad'i ga me da shi ba sai fa wannan karan inda wayewar garin suka sami gawarwakin su Malam Jauro a ciki tare da makaman 'yan banga an rasa mai isa wurinsu sabida tsoron abinda zai biyo baya. Sai d'aukansu bidiyo da hotuna mutane keyi daga nesa, kowa ka hango cike da tsoro ya ke amma sabida ganin k'wam sun kasa barin wurin, jiniyar motar police yasa suka koma gefe wanda 'yan banga nan da suka tsira suka kai masu rahoto. kwashe gawarwakin sukayi suka nufi asibiti da su wa su kuma suka tsaya d'aukan rahoto amma shigarsu ciki dan yin binciken dalilin faruwar lamarin suka dawo a guje, kafin ace kobo kowa ya watse domin ance bakin rijiya ba wurin wasar makaho ba ne.


*

Cike da galabaita suka zube jikin wata primary bayan sunyi hutu fiye da biyar cikin gudun ceton rai. Yanzu gari ya waye haske ya wadaci ko ina, wasu bayin Allah ne sukazo wucewa suka gansu cikin mugun hali suka taima masu da ruwa bayan sun sha sun soma dawowa hayyacinsu sai mutanen sukayi tafiyarsu dan fahimtar da sukayi mahaukata ne dan ba wanda zaiga d'iyar batare da ya kirata itama da mahaukaciya ba sabida yarda ta yi butun-butun ga gudun da suka sha ya taimaka wurin fitar da ita kamannin masu hankali.


"Mamana wannan wani kalan rayuwa ce? Wallahi na gaji da ita, dama ace halittan can ya kashemu mun huta da garari." Ta ambata cikin zubar hawaye. Tashi Maman ta yi dafe da cikinta ta haye saman dakalin makarantar ta kwana zuwa can kuma ta tashi ta yi ta kwara aman jini hankalin d'iyar ya tashi matuk'a ta rik'eta cikin kuka batare da ta san taimakon da zata bata ba.


"RUMASA'U." Ta tsinkayo muryan Maman ta ambata. Kafeta da idanu ta yi domin gasgata abinda kunnuwanta ya jiyo mata.


"RUMASA'U." Ta kuma kira cikin sanyin murya."


"Mamana magana kike yi?"


Motsa kai ta yi cikin cije baki.


Alhamdulillahi! wayyo Allah dad'i kasheni, a she da rabon zanji muryan Mamana."


"RUMASA'U d'iyar albarka." Maman ta kuma furta tare da zamewa ta kwanta idanunta kulle.


"Mamana sunana kenan RUMASA'U?"


Bud'e ido ta yi ta shafo kanta batare da ta amsa ba.


"Mamana waye Banana?"


Murmushin da ke fuskan ta ne ya d'auke ta juya mata baya ta saki kuka mai k'arfi a gigice d'iyar ta rungume bayarta itama tana kuka.


"Mamana bana da Baba ko?"


"Kaini inyi wanka RUMASA'U."


"To Mamana tashi mu koma inda gidan wanka ya ke amma bazan kaiki wurinsa da wani yaso tab'amin nan." Ta nuna k'asanta.


Idanu Maman ta zare hawaye na zibowa.


"Mamana nasha wuya sadda wani ya tab'amin kuma har yanzu ina jin ciwo a gefen nan." Ta nuna gefen maranta cikin yamuca fuska. "


"Kai ni na yi wanka RUMASA'U sai ki bani labarin abinda ya faru nima zan sanar sa ke komi nawa amma kafin nan ina son ki kasance mai hak'uri tare da neman shawara musanman akan rayuwarki, kada ki sa ke kiga abinda zai cutar da ke kiyi shiru ko da kuwa fad'ar zai iya janyo miki matsala ne."


"To Mamana." Ta amsa cikin murna batare da ta fahimci inda zantukan suka dosa ba.


"Allah ya yi miki albarka ya rabaki da bak'in cikin rayuwa."


"Amin Mamana."


Barin wurin sukayi dik inda suka wuce jama'a su rakasu da idanu lamarin da ya kuma muzanta Maman ganin a halin da ta ke cikin datti bakomi ke kai kawo a ranta ba illa son had'uwa da Munir.


"Mamana tun yaushe kika dawo cikin hankalinki?"


"RUMASA'U bazan iya tunowa ba amma nasan wani zubin ina jin maganar ki kuma ina son taimaka miki amma bana iyawa banma sanin inda na ke sai bayan wasu lokuta shima dana soma gane lamura zan manta inda na ke nasan tabbas ina rayuwa cikin gushewar hankali dan na kan tsinkayi maganar mutane na kirata mahaukaciya kuma ban iya musawa sabida nauyin da bakina ya ke yi wurin fitar magana. RUMASA'U ina sonki so mara iyaka wallahi ina k'aunarki takwarata." Takai k'arshen maganar cikin cije lips zufa na tsats-tsafowa a gaban goshinta.


"Mamana nima ina sonki sosai sannan kema sunarki kenan RUMASA'U?"


Bata amsa mata ba sai dank'e hannunta da ta yi cikin d'aga kai sama.


"To a wani gari mu ke?"


"Kai ni nayi wanka RUMASA'U k'yan-k'yamin jikina na ke ji." Ta furta da kyar.


"To Mamana."


Rungume d'iyar nata ta yi a gefen jikinta dai-dai wurin da halittan nan ya bujeta, a haka suka cigaba da tafiya tana numfar-fashi yayin da d'iyar keta zabga mata surutu batare da ta lura da halin da ta ke ciki ba, suna isa bakin kasuwa a nan ta gaza cigaba da tafiyar ta sunkuya k'asa dafe da cikinta.


"Mamana tashi mun kusa isa wurin kin hangosa can gabanmu kad'an, nasan tunda naga ana wanke motoci ba zamu rasa wurin wanka ba" Shiru bata motsa ba, ta sunkuya gabanta ta d'ago fuskanta idanunta kulle tsira ma fatar idanunta ido ta yi ganin yana motsi sai ta girgizata "Mamana ki kalleni dan Allah."


Bud'e ido ta yi tana shirin magana tari ya turnik'eta sai ka tasoma yunk'urin amai sai ga jini na fita guda-guda. Kuka d'iyar ta fashe da shi Maman ta janyota jikinta abin mamaki bakinta ya kuma kullewa ta kasa iya furta kalma d'aya, k'an-k'ame Rumasa'u ta yi ta sa ki kuka mai ban tausayi.


*Mrs j moon.*


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.