Free chapter · Read without an account

Part 12

by Safiyya Haruna · Rumasa'u

RUMASA'U.


BY SAFIYYA.


Page 12.


"Tana da juna biyu d'an s...


" Wani irin juna biyu Doctor!? " Alhaji Ahmad ya katse shi.


" Alhaji juna biyu dai ma'ana ciki na haihuwa d'an sati tara da kwana shida, yashiga watanni na uku kenan"


"Innalillahi wa inna ilaihin raji'un, Hasbunallahu wal ni'imal wakil, Lahawla wala k'uwwata illa billahil aliyul azim!". Alhaji Ahmad ya ambata cikin dafe goshinsa.


Kuka hajiya Aminatu ta k'ara fashewa ta shi ta zube saman kneel nata tare da d'aga hannu sama ta ce "Allah kai ne Allah sarki d'aya tilo wanda baka da tamka, kai ne mai cikakken iko ga dikkan komi, masanin dikkan lamura fili da b'oye, kai ne mai saukarwa bayi da lamura masu dad'i da kishiyarsu dik domin cikar ikonka. Ya Allahu ya rabbil arshil azim, ya auwalu ya ahiru ya zahiru ya bad'inu, domin cikar zatinka tare da sunayenka tsarka-ka kawowa wannan baiwa taka d'auki abisa wannan ifti'i da ke kewaye da rayuwarta, lamuran su yi sauk'i gareta domin alfamar Manzon Allah S.A.W." Ta shafa a fuskanta tare da tashi ta zauna tanajin nauyin da k'irjinta ya yi na raguwa a sannu.


"Amin ya rabbi, Amin Aminatu, Allah ya amsa wannan addu'a taki ya sa ta isa fadar Allah batare da hijabi ba." 


"Amin ya Allah." Likitan ya amsa cikin goge kwarmin idanunsa da tissue.


Motsawa Likitan ya kuma yi cikin fargaba har ya bud'e baki sai kuma ya kulle ya d'auki Biro ya cigaba da rubutu tsawon wasu mitoci sannan ya d'ago yana shafar fuskansa.


"Please doctor fad'i maganarka insha Allah yamu d'auka da sauk'i sabida mu bayi ne masu neman taimakon Allah a dik kan lamuranmu."


"Very good Alhaji hakan na alamtamin da yarinyar ta yi dace da iyaye na gari wanda zasu share mata hawaye batare da kyama ba."


"Tabbas muna shirye da d'aukan ragamarta Likita." Hajiya Aminatu ta amsa cikin tabbatarwa.


"Hakan abin alfahari ne Hajiya. Yanzu zanyi muku bayanin dikkan abinda ke tartare da yarinyar."


"Muna sauraren ka." Alhaji ya fad'a cikin ambaton sunar Allah a ransa.


"Bayan Hawan jini da juna biyu yanzu haka ta yi loosing memory nata, rayuwar da ta yi abaya dik ya shafe."


"Ya Salam." Hajiya Aminatu ta ambata cikin k'aramar murya.


"Sorry Hajiya haka Allah ya rubuto mata ba wanda ya isa ta goge su."


Gyad'a kai ta yi tare da k'an-k'ame hannun mijinta dake saman shoulder nata.


"Bincike ya nuna zata dawo tunaninta na baya idan ta kuma ganin kwatan-kwacin lamarin da ya jefata cikin yanayin in kuma hakan bai afku ba to zuwa wani lokacin zai iya dawo a hankali sannan game da cikin jikinta kada kuyi yunk'urin ciresa sabida k'ananun shekarun ta dan yin haka had'ari ne ga rayuwarka zai yiwu ta sami matsala a mahaifarta wanda bama fatarsa, idan kuma tazo haihuwa wajibi ne aji mata cs dan shima barinta ta yi labour zai iya sanyawa ta kamu da cutar zubar fitsari sabida haka sai akiyaye kuma akula da ita sosai dan yanzu komi sai ta koya abinda taga kunayi shi ne zai soma zama a brain d'inta kafin nan gaba tasoma ganewa."


"Mungode Doctor insha Allah zamu kiyaye."


"Alright yanzu zan rik'eta zuwa nan da sati d'aya sabida ayi maganin k'ananun ciwukan dake ciki da wajen fatarta, kamar maleria da typhoid da kuma nasarar saukar da hawan jinin"


"Shi kenan Doctor sai kayi mana list d'in kud'ad'en da kuma abinda ake buk'ata musiya."


"Wannan ba abin damuwa ba ne nima ina son ladar, za ku biya rabin kud'in rabin kuwa zan biya."


"Allah ya k'ara d'auka ka, ya kuma bata lafiya."


"Amin Alhaji, Allah ya yi muku alkhairi fiye da wanda kuka yiwa wad'an nan mutanen."


"Amin."


Yana fad'in kud'in da zasu biya atake Alhaji Ahmad ya ya yi masa transfer. Koda suka dawo d'akin Hajiya Binta ta wuce domin Muhsin yazo d'aukanta, Umma da Mahmud suka samu.


"Oh ni Mahmud nagama ganin abinda ya isheni."


"Me ya faru Mahmudu?" Umma ta tambayesa.


"Yanzu Umma bakiga abinda su Dady suka jajibowa kansu ba?"


"Na me fa?"


"D'orawa kai laluran wasu ba dangin iya ba na baba, wallahi kiyi musu magana tun wuri da su sallami mahaukaciyar yarinyan nan ta kama gabanta kada su kawo mana ita gida."


"Ikon Allah sai kallo, yanzu Mahmud rashin imanin naka har ya kai haka?"


"Kyakeshi Aminatu ai barewa ba zatayi gudu d'anta ya yi rarrafe ba."


"Me kike nufi da kalamanki Hajiya Umma?" Ya tambayeta cikin rashin kunya.


"Uwarka ta ke nufi sakarai kawai wanda sam baida hankali, get out! Ko ranka yafi mad'aci d'aci."


"Relax Aminatu ki...


" Barta Ahmadu tacimin ubansa tunda shaye-shayensa yasa bai ganin kowa da gashi wanda yayo gadon fitsara to wallahi kasani dik abinda zakayi baza ka tab'a kamo Yusufa ba."


"Ummana please."


"Affuwan Aminatu ba nufi na ci miki fuska ba ina dai son sanarwa da futsararren can shi d'in banza ne kuma wofi akan rashin imani da tantiranci."


"Umma kiyi shiru kinsan ba'a sonki da yawan damuwa."


"Ahmadu ka hanzarta kai Mahmudu gidan mari wata k'ila zai dawo natsuwarsa."


"Natuba Umma dan Allah Momy, Dady ku sa baki Umma ta janye kalamanta, wallahi in aka kaini gidan mari ajina yagama zubewa, kai Allah ya kiyaye ni tab'ewa."


"Fice a d'akin nan Mahmud ko in wanke ka da maruka."


"I'm sorry Sahibar Dady." Ya furta kamar mara hankali.


Ware ido Umma da Momyn sukayi baki bud'e.


Jan hannunsa Alhaji Ahmad ya yi suka fice dai-dai lokacin yarinyar ta motsa ta k'walla ihu "Mamana!" Ta furta da k'arfi, aguje Doctor ya shiga wanda ke kallo farkowar nata a computer. Cikin mintoci goma ya yi nasarar dai-daita bugun numfashinta ta d'aina fizge-fizge. Idanunta biyu sai bin d'akin da kallo ta keyi ta sauke dubanta kan Umma ta ce "Mamana." Likita ya dubi Hajiya Aminatu ya yi mata alamar ta matso ta k'arisa gaban gadon idanunta jajur.


"Mamana." Ta kuma ambata.


"Na'am Daughter kintashi?."


"Daughter kin tashi." Ta mai-maita cikin zare ido.


Murmushi Hajiya Aminatu ta yi sai itama ta maida mata da martanin murmushin.


"Hajiya abinda ta rik'e kenan kalmar Mamana dan haka yanzu komi kikayi shizata rik'a kwai-kwaya kafin zuwa nan gaba tasoma fahimtar dik abinda aka fad'a mata kuma tana aikatawa."


"Ok doctor na fahimta."


"Good sai kinyi hak'uri dan aiki ne mai wuya."


"Bakomi, ni dai burina ta sami lafiya."


"Lafiya." Ta ambata a hankali."


Murmushi doctor ya yi "Da alama tana da kaifin basira baza tayi wuyar gane lamura ba."


"Gane lamura." Ya kuma ambata tana kallon Doctor.


"Eh Baby."


"Baby."


Haka dai sukayi ta biye mata dik in sunyi magana sai ta ambaci kalmar k'arshe.


Umma saida ta zubda hawaye sadda taji lalurorin da ya sami yarinyar.


"Inaga Aminatu kubani ita na kula da ita a gidana."


"Umma ina son ta har cikin raina jinta na keyi tankar RUMASA'U na." Ta yi maganar kanta a k'asa.


"To shi kenan Aminatu Allah ya tayaki rik'o."


"Amin."


"To wani suna zaku kirata da shi? Tunda bata cikin hankalinta balle atambayeta sunarta."


"RUMASA'U na ke son a kirata da shi Umma sabida a baya ta sanarmin cewa bata san sunarta ba amma in kuma Dadyn Hamid ya sanja mata shi kenan."


"Na gamsu kuma sunarta kenan RUMASA'U koda ta dawo hayyacinta sabida dole ta yi muku biyayyar amincewa sa sunar."


Murmushi Hajiya Aminatu ta sa ki cike da jin dad'i ta koma bakin gadon ta shafi fuskanta zuwa fatar idanunta wanda ke cike da zara-zaren eyelashes.


"Umma yarinyar nan kamar jinin larabawa dan fatarta ta yi daban da ta Fulani."


"Aminatu hoo tun ba'a wanke dattin jikinta ba har kin gano da jinsin da ta yi maka?"


"Allah Umma ta yi kama da shuwa Arab, ki dubeta da kyau. Tun wancan ganin danayi mata na gano hakan."


Dariya Umma ta yi tare da shige wa toilet da ke d'akin dan d'auro alwallan sallar la'asar.


*

"Mahmud me yasa bakajin magana? Kai dai kullum in ba ayimaka sababi ba bakajin dad'i".


"Kayi hak'uri Dady na daina."


"Kullum haka kake fad'a amma kafin gari ya waye ka sa ke aikatawa, anya kana son gamawa lafiya kuwa?"


"Na ce kayi hak'uri bazan sa ke ba."


"Inaga gidan marin zan kaika kaga sai arik'a kiranta k'ato a cikin yara."


"Kai Dady kaima bayan Umman zakabi?"


"Shi ne alamun d'a na gari mai jin maganar manyansa, kaga kenan dan na marawa Umma baya ban fad'i ba."


"Natuba Dady."


"Na mazuru ko na har cikin ruhinka?"


"Na gaskiya."


"Ka yi alk'awari?"


"Eh."


"Kasan girman alk'awari kuwa?"


"Yes wanda ya karya ya zamo munafuki shi kuma munafuki dan wuta ne."


"Da kyau Mahmudu."


Murmushi ya yi wanda hakan ya kuma baiyana kamanninsa da Hajiya Aminatu ainun.


"Kaga ne abinda na ke so da kai."


"Sai ka fad'a Dady."


"So ni ke ka daina shan komi hatta sigari ka barta ni kuma nayi ma alk'awarin baka manager a company na tare da sabuwar mota fitowar zamani wanda 'yan gata ke hawa."


"Dady a hakan takarduna kammala karatu na basu fito ba?"


"Yes zan baka dik abinda na lissafa kuma da kadawo service alk'awarin zai tabbata."


"Wayyo dad'i ka sheni nima na kusa kece sa'a ko Momy ta daina yimin gani-gani."


"Kagani ba tun ba a kai ko ina ba ka kuma tafka shirmen, wannan shi ne illar shaye-shayen da akeyima fad'a akai."


"Yi hak'uri Dady zan bari ai."


"Zaka bari ko ka bari?"


"Zan bari."


"Ok ya yi inka barin sai mu d'ora daga inda muka tsaya"


"Dady na bari Allah." Ya ambata cikin rawar jiki.


"Shi kenan in ka dawo service sai mu shirya yarda zaka soma aikin amma ka-ka me bakinka kada Aminatu taji."


"Na kame gam wallahi Dady." Ya kulle bakin da hannunsa girgiza kai kawai Alhaji Ahmad ya yi batare da ya sa ke magana ba.


"Dady yaushe d'an Momy zai dawo?"


"Ka kirawoshi ka tambaye shi."


"Allah ya kyauta na kira wannan d'an rainnin hankalin, ai wallahi halinsa tsaf irin na Momy ce shi yasa suke k'aunar juna ake wareni dan rashin adalci."


"Allah ya shirya mana kai Mahmud."


"Amin tare da kowa." Ya amsa cikin d'aure fuskan.


Da ido Alhaji Ahmad ya raka shi har ya fice daga asibitin wanda ya tabbata majalisa zaije inda ya ke k'aro rashin kunya.


*Mrs j moon.*


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.