Free chapter ยท Read without an account

Episode 7&8

by Babybintuu ยท FARAR MACE KO MAYYA CE

: ๐Ÿ‚ *FARAR MACE* ๐Ÿ‚


             By
Ummu sumayya
   *(Babybintu)*
     Vote me on wattpad
#Bintubaby

*Elegant Online Writer's*


   *PAGE FOUR*

____________________"Tabbas nasan Alhaji Omar fate kai masha Allah a ina kuka had'u?"
Yajefo mata tambayar yana kallon ta,
Murmushi tayi tana kallon shi tace "Dad lokacin da yaxo school d'in mu wata ziyarar baxata ne shine muka had'u"
"Masha Allah, Allah yasanya alkhairi sai yafad'a miki rananar da zasu zo KO dannima nasanar ma y'an uwa na"
"To Dad  daya sanar dani zan gaya maka"
"Shike nan Allah yayi albarka"
Akunyace ta amsa da "Amin Dad"
Tana gama fad'in haka takoma d'akin ta tafad'a kan bed d'in ta tana rungume pillow cike da farin ciki.
Bayan fitar ta Mom takaalli Dad tace "Kai masha Allah shalelena zatayi aure bara nazo nafara shiryata Dubai zanje siyayya KO?"
Dariya Dad yayi yace "lallai to ai duk saurin unguwar zoma tajira ahaihu ko kibari suzo idan muka tsaida magana insha Allah sai afara maganar zuwa kowace k'asa ce ma!"
D'an fari da Ido tayi tace "Alhaji ai mai kwarmin ido dawuri yake fara kuka nasan baza aja lokaci ba insha Allah"
Ajiyar zuciya Dad yasauke yace "Allah yazab'a mana mafi alkhairi kawai"
Jikinta yad'an yi sanyi tace "Amin ya Allah" Mik'ewa tayi tanufa kitchen don duba masu aiki kosun d'aura diner.
_________********________
Gaba d'aya tunda yad'aura idanu akanta yarasa natsuwar zuciyar shi soyayyar ta mai k'arfi ne tashige shi tundaga kallo d'aya tabbas shikam yasamu matar aure murmushi yayi yasake juyi atangamemen royal bed d'in shi ganin tunani bazai mai bane yami'ke yanufa main palour babu kowa sai TV daketa aiki shi kad'ai bedroom d'in Mom d'in shi yanufa tana zaune tana lazimi kyakkyawar dattijuwa dabazata haura shekara hamsin da biyu ba aduniya zama yayi yana gaishe ta cikin kulawa ta amsa tana k'are mai kallo shafa Addu'ah tayi tace "Son tasamu kenan wannan farin cikin haka bani nasha"
Cikin du'kar dakai yace "ummm Ammina bafa wani abu kawai dama" saikuma yafara sosa kai,
Murmushin manyance tayi tace "dama me? Kodai son yafara soyayya ne yanason aure?" Ta'karisa maganar cikin barkwanci,
K'asa yayi da kanshi yana sosawa yace "That's my Ammi the best in the world"
Mik'ewa tayi tana nannad'e prayer mat tace "nida nasan d'ana ciki da waje y'ar waye? KO ince a ina take?"
"Ammi nifa ban gaya mata inason taba d'azun naje gidan su Muneef zan duba shi kawai naganta agidan ina tunanin causing sis d'in shine dan Mom d'in shi ke ru'kon ta"
"Kai masha Allah ashe y'ar gida cema nad'auka Samraat ce ashe tanada wata mace datake ri'ko to any way dai zan kirata muyi magana karkaji komai indai ba'a mata mijiba kamar kasame ta ka gama"
Wani irin mik'ewa yayi cikin farin ciki yayi hugging Ammi yamanna mata kiss a forehead d'inta sannan yafara jera mata godiya kamar ma har yasamu Mufeedan,
Zama sukai gaba d'aya suna fira jefi jefi akan harkokin kasuwan cin Ammin.
__________ ******* __________
Saida taje tashaida ma Mom tadawo sannan tanufa d'akin ta cike da gajiya tayi sallah tad'an jingina da bango tana azkar duk da tanajin barci amma sai bata kwanta ba sabida tasan barcin bayan la'asr bashi da amfani wani irin banko k'ofar d'akin akayi wanda hakan yayi sanadiyyar d'agowar ta afirgice takalli k'ofar ganin Samraat ne yasa taduk'ar dakai cikin girmamawa tace 
"Barka da yam...."
"Mtssss ba wannan yakawo ni ba big bros yace kije kigyara mai side d'in shi yanzu yanzu" tana gama maganar tajuya abunta batare da tajira Mufeeda tace komai ba,
Sosai zuciyar ta take bugawa tafara maimata naganar "gyaran d'aki yau kuma innalillahi wa-enna ilaihirraji'un ya Allah help me" wasu hawaye ne suka silalo mata dasauri tagoge tami'ke cikin sassarfa tanufa side d'in nashi zuciyar ta na bugawa kamar zata fito daga k'irjin ta ahaka ta'karisa side d'in babu kowa sai sanyin ac da k'amshin air freshener daya cika palourn tsintsiya da moper data d'auko a store ta aje cikin sauri tafara aikin bayan tacire hijab d'inta sanye take da wata spaghetti gown peach color data bi jikinta takwanta gaba d'aya asalin shape d'inta yabayyana musamman hips d'inta daya kasance me rawa koya ta motsa jikinta shima sai ya motsa,
Saida ta kakkab'e sofa d'in sannan ta kakkab'e carpet d'in tashare tayi mopping cikin sauri take aikin sai gashi nan da nan tagama da palourn tasake fesa air freshener saida takulle k'ofan gudun kar yadawo yashigo,
Direct bedroom tanufa tafara wanke toilet sannan tagyara gadon tafara shara.

Zaune yake agaban Abba yana shaida mai yanason aje aneman mai auren Khalisat  a Kano
Cikin d'an farin ciki yayi murmushi irin nasu na many'a yace 
"Masha Allah yaushe kake so aje"
Cikin sake du'kar dakai  yace "duk sanda kasamu lokaci babu matsala amma inason ayi abun da wuri saboda nakusa komawa banaso natafi babu mata"
Kai Abba yajinjina yace "Masha Allah dama inda gaf dayi maka magana sai gashi ka magantu to Alhamdulillah insha Allah k'arshen satin nan zamuje saika sanar ma many'an yarinyar kuma akwai bu'katan agudanar da binci ke akan ita yarinyar duk da ubunta sananne ne"
Ajiyar zuciya Muneef yasauke yace "Duk yanda kayi daidai ne Abba nizan koma"
"To Allah yashi albarka kaji ka gaida Mommy taku kace gobe ina nan b'ullowa"
Kanshi yashafa yana fad'in "Amin Abba zataji ga wannan kasha ruwa" ya ajema Abba bandir d'in d'ari biyar biyar 
Albarka yasake samai sannan suka futo tare
Har compound yarako shi yahau mota body guys d'in shi yaja suka nufa gida,
Ajiyar zuciya yasauke cike da farin ciki zai auri muradin ranshi kuma *FARAR MACE* tabbas shikan shi yasan Khalisat one in town ne musamman many'an idanun ta masu matu'kar d'aukan hankali murmushin tama kawai abun kallo ne balle uwa uba intana shagwa'ba, murmushi yasake yi haka yayita tunane tunane harsuka isa gida aka bud'e mai yasauka yashiga gidan dan yanason yad'an watsa ruwa kafun ayi magrib murd'a k'ofan yayi yajita akulle d'an tsaki yaja yazaro key ahannun shi yabud'e Allah ma yasa yanada spare danshi shaf yamanta yace agyara mai side dan haka bai kawo komai ba aranshi yana shiga yaji wani sanyi da k'amshi sun daki fuskar shi yanayin daya tilasta shi lumshe idanu take wani irin shauki yakama shi dan yana bala'en son sanyi arayuwar shi shiyasa baya shiri da zafi,
Direct bedroom yanufa yana d'an warware boturan gaban rigan shi zuciyar shine tawani irin bugawa saka makon sake ganin abubuwan dasuka hargitsa mai kwanya jikin shine yafara karkarwa kamar mazari ga wani abu kamar magnet dake janshi zuwa gareta,
Tana duk'e tana shimfid'a bedsheet gaba d'aya many'an boob's d'inta sun turo kamar zasu fad'o kasantuwar rigar datasa mai babban wuya ne kwata kwata bataji shigowar shi ba domin tayi nisa a aikinta kawai jitayi anyi hugging d'inta ta baya anzagayo da hannu ta gaba anmatse mata boobs,
Afirgice ta kwantsama wani uban ihu..........โœ๐Ÿป


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.