Free chapter ยท Read without an account

Episode 13&14

by Babybintuu ยท FARAR MACE KO MAYYA CE

๐Ÿ‚ *FARAR MACE* ๐Ÿ‚


        *BY*


 *Ummu Sumayya*

```Vote me on wattpad ```

    *#Bintubaby*


*ELEGANT ONLINE WRITER'S*



         *PAGE SAVEN*


Sauri sauri tashirya cikin atamfa holland mai zanen ja da ba'ki ko kwalliya batayi ba tad'auki car key tafito tashiga d'akin Mom,

Cike da mamaki take kallon ta kafun tace wani abu Samraat d'in tariga ta dacewa 

"Uhmm am fine Mom zamu futa da Murfat ne naga gari please"

Cikin farin ciki Mom tace "masha Allah adawo lafiya saura kidawo kikuma kwanciya kiga yanda zanyi dake"

Dariya tayi sannan tajuya tafuta da sassarfa kamar ba ita bace akwance kwanaki shida dasuka wuce,

Tafiya sukai sosai harsun fara barin cikin abuja Murfat tad'auki hanyar wani k'auye dake kusa da Wuse sosai suka kutsa cikin daji saida suka iso wajen wasu duwatsu sannan ta Parker kasantuwar dama ita ke tukin tunda ita tasan wuri,

Dukkan su fitowa sukai suka d'auki wata hanyar da k'afa kuma Samraat da duk tsoro yagama cika ta takalli Murfat tace "wai har yanzu bamu k'araso ba ? Naga mun kuma d'aukan wata hanyar?"

Wata shegiyar dariya Murfat ta k'yalk'yale da ita kafun takalli Samraat she'ke'ke tace "kina tunanin komai cikin sau'ki zaki same shi biyan bu'katar kice ba tawa ba niban nuna gajiya ta ba saike hmmm munkusa k'arisawa KO mu koma ne?"

Cikin sauri tace "no muje am sorry ba da wata manufar namiki tambaya ba"

Baki tad'an tab'e tana cigaba da tauna chewing gum k'as k'as alamun ko ajikin ta,

Saida suka shafe mintuna talatin suna tafiya kafun su iso wata y'ar bukka da akai mata ado da jan k'yalle ga wuta a k'ananan kasko yanata ci bal bal kuma babu kowa awajen shiru,

Gaba d'aya Samraat tagama tsorata gani take kamar wajen y'an cire kai Murfat takawo ta tsinkayar muryar ta tayi tana fad'in,

"Gafaran ka dai Durwanu tsinanne d'an tsinanniya munzo gareka da bu'katar mu katai maka mana" (wa iyazu billah)

Daga cikin bukkan suka ji wata mashahuriyar dariya tana tashi kafun yabayyana b'igit agaban su,

Wani irin fitsari ne ya kufce ma Samraat saboda tsaban tsoron dataji itako Murfat ko ajikinta saima sujjada da tai mai tanajan Samraat itama tazube sukai sujjada atare,

Kansu yadafa yana fad'in "bu'katun ku zasu biya amma ak'arshe abun akwai gagarumar matsala idan kun amince kud'in aikin ku dubu d'ari biyar ne kuma sai aiki yaci zaki kawo kud'in amma kafun nan aljanin dazaiyi aikin yana bu'katan jini zaki yanka shanuwa d'aya ba'ka sannan ki binne rago d'an shekara d'aya ba'ki da ranshi"

Gaba d'aya Samraat tagama tsorata banda kyarma babu abunda jikinta keyi ga uban zufa data gama jik'a ta, Murfat ne tace 

"Mun amince Durwanu d'an matsafi jikan matsafa tsafi da sihiri gaskiya ne ba'ai matsafi kamar ka ba bakuma za'a ta'ba yiba har abada"

Wata shegiyar dariya y'a k'yalk'yale da ita kafun yace "Kutashi kutafi asararru nan da sati d'aya ku dawo inkun aikata abunda nasaku b'at yasake b'ace wa sai dariyar sa"

Murfat ne tami'ke sannan tad'aga Samraat data zama kamar butum butumi taja ta suka tafi baya baya harsuka daina hango bukkar sannan suka dawo tafiya daidai sai asanna Samraat tasaki ajiyar zuciya,

Har suka kai mota babu mai magana acikin su yanzun ma Murfat ne take driving hankalin ta kwance tana bin wa'kar jeboy mai taken am in luv harsuka isa cikin gari sannan takalli Samraat da idanun ta yake alumshe kamar me barci nan KO fargaba da rud'ani ne fal cikin zuciyar ta datake ta bugun famfalak'i kamar zata faso k'irjin ta,

Baki Murfat tata'be tace "ina kince akan Fahad babu abunda bazaki yi ba and why daga zuwan mu duk kin canza inbazaki iyaba nakira shi awaya nagaya mai"

Cikin sauri tasauke ajiyar zuciya tace "bafa bazan iya bane kawai na tsorata da yanda yabayya na ne amma ni KO mutun yace na kashe indai zan samu Fahad wallahi saina kashe"

"That's good girl yanzu gobe kifito makaranta da wuri sai mu biya muyi abunda yakamata dan da zafi zafi ake dukan k'arfe" ta'karisa maganar daidai tana parking k'ofar gidan su 

"Hakane na gode Murfat Allah bar zumunci kigaida Mom"

"Amin zataji zaki iya driving d'in kona kira bros yazo yatafi dake dan wallahi nagaji dayawa ban iya xuwa gidan ku nakuma dawowa"

"No karki damu saimun had'u goben" tafad'a tana weaving d'inta bayan tafita a motar sannan taja tabar unguwar kasan tuwar basu da nisa ma su Murfat suna pape junction su kuma suna maitama cikin wani irin farin ciki dawata daddad'ar iska dake shigan ta ta'karisa gidan tanayin parking tafito saiga Muneef dataga ya wani rame kamar bashi ba yana tafiya ahankali kamar mejin tausayin k'asa ya nufi side d'in Mom da mamaki d'aga murya tace 

"Hi"

D'an waigo wa yayi ganin ta yayi murmushi yace 

"Daga ina kike da yamman nan?"

Baki tad'an turo batare data bashi amsa ba tace "uhm Bros baka da lafiya ne kai wannan ramar haka?"

Kanshi yashafa yace "ina tambayan ki kina tambaya na bazaki ban am......."

Wani irin tari ne yasark'e shi saka makon hango Fahad da Mufeeda sunfito daga sit room sai murmushi suke zuba ma juna,

Cikin sauri Samraat tace "sannu Bros are you ok?"

Kai kawai yajin jina batare daya daina kallon su ba,

Inda taga yana kallo itama tamaida hankali take taga abunda yakusan sa azuciyar ta tabuga wani uban ihu tasaki wanda yajanyo reaction d'in su duka,

Fad'i tayi a'kasa kamar wani abune yasame ta tana kuka had'e da dafe k'irjin ta, 

Dasauri Muneef yayi kanta haka Fahad da Mufeeda ma da d'an sassarfa suka k'araso suka rufu akanta gaba d'aya sun rud'e barin ma Muneef dayanzu suke magana dashi,

Cak Muneef yad'auke ta yanufa palourn su da ita take suma suka rufa mai baya direct sama ya haura da ita yakwantar da ita akan kujera yana mata sannu ganin yanda take hawaye,

Cirko cirko sukai kafun Fahad ya'kariso inda take kwance yad'an rankwafo yace 

"Meyake miki ciwo ko k'afar kice?"

Kai tagirgiza kafun tad'auki hannun ta tasa asetin zuciyar ta tace "zuciya tace take min ciwo kawai naji jiri ya kwashe ni nafad'i"

Gaba d'aya zuba mata idanu sukai cike da mamaki musamman Mom data fito tagan su kuma tsaf taji abunda Samraat d'in tace,

Ajiyar zuciya yasauke yace "innalillahi tun yaushe yafara miki hakan and hope kinje kinga Dr"

Lumshe idanun ta tayi tanajin saukar KO wace kalma acikin zuciyar ta take kuma zuciyar tafara washe wa tanajin kamar su dawwama ahaka amma takasa bashi amsa jitake kamar su kwana ahaka,

Shiko Fahad ganin tai shiru ne yasa yakalli Muneef yace "Dr wannan b'angaren kane hope zaka d'aura ta akan magungunan dasuka dace sannan kazauna da ita kafahimci menene damuwar ta dan alamu sun nuna tana cikin damuwa kuma zuciyar ta tana iya bugawa ako wani lokaci"

Baki Muneef yata'be yana kallon Mufeeda da ta'ki kallon inda yake shiko kamar maye yakafe ta da idanu kuma yakasa gane sha'awarta yake ko sonta gaba d'aya a kwanakin dabai ganta ba ba'karamin tashin hankali yashiga ba da dare tunanin ta yahana shi barci amma wai sai yadangan ta hakan da sha'awar ta datake d'awainiya dashi,

Gyaran murya Mom tayi wanda hakan yadawo dashi daga duniyar tunanin daya fad'a Dr Fahad har ya wuce zama yayi agefen kujera yana sosa kai,

Wata uwar harara Mom ta wurga mai kafun tace 

"Lafiya ka kafe Mufeeda da ido Fahad na maka magana kai banza dashi har ya wuce?"

B'ata rai yayi yace "kai Mom waye nakafe da ido ni kawai abubuwa nake lissafawa ba wani kallon ta danakeyi tome ma zan kalla ajikin ba'kar mace? Kuma k'waila"

K'wafa Mom tayi sannan takalli Samraat tace "kaidai kasani ita kuma wannan menene yasame ta"

"Muna tsaye kawai naga ta gurd'e tafad'i tana ta ihu so nayi tunanin ko k'afar ne ke ciwo sai kuma naji tana cema Dr Fahad zuciyar tace sannan tana ganin jiri kiduba yarinyar nan babu irin tambayar daban mata ba amma saidai tasa min kuka haka kema amma wai Fahad yatambaye ta tabashi amsa saiki gaya min menene ba'a miki agidan nan da har zuciyar ki takamu da ciwo?"

Cikin b'acin rai ta'karisa maganar

Kallon shi Mom tayi sannan takalli Samraat d'in data fara hawaye amma still idonta arufe tace "rabu da ita kawai kowa yayi nagari baran me shine"

K'wafa yayi sannan yafuta,

Jikin Mufeeda asanyaye tace "Aunty Samraat sannu Allah yasa kaffara ne"

Wani shegen tsaki taja kafun tami'ke tashige d'akin ta,

Da mamaki Mom tabita da ido gaba d'aya tarasa gane kan Samraat kwanakin nan kallon Mufeeda tayi tace 

"Kiyita ha'kuri da halin Samraat da Yayan ta tunda nanesa ma ai tazo kusa dukkanin ku rana d'aya zan aurar daku nahuta ke kungama daidaita wa da Fahad d'in?"

Kanta a'kasa tace "eh"

"To Allah yamiki albarka d'azun mukai waya da Mom d'in shi tace k'arshen satin nan yayyen babanshi zasu kawo kud'in komai da komai inda matsala kiyi magana"

Still kanta a'kasa tace "Mom nidai ta wajena babu matsala duk yanda kuka yanke daidai ne"

"Shikenan Allah yamiki albarka kinji"

"Amin Mom bara naje nai sallah naji anata kira"

"To nima tashi zanyi".


Cike da farin ciki tashiga d'akin ta k'asan zuciyar ta kuma wani k'unci ne yake taso mata tarasa dalili Addu'ah kawai tayi tashiga toilet tad'auro al-wala.


        *WAI WAYE*


Alhaji Omar fatee haifaffen garin katsina ne kuma asalin su fulani ne gaba da bayan su, su biyu ne ad'akin su Omar da Abubakar, Abubakar ne babba sai Omar dake bimai, sum taso marayu ba uwa ba uba domin tun suna yara iyayen su suka rasu dangin uban su suka handame gadon da mahaifin su yabar musu mahaifun su maharbi ne shiyasa ma akece mai Fatee amma asalin sunan shi Abdul-Aziz sai fatee yabishi asalin sunan ya'bace inba kasanshi ba sosai bazaka san asalin sunan shi ba,

Sunyi karatu tundaga primary har zuwa secondary school a makarantar gomnati kasantuwar Abubakar yanada k'ok'ari yaci mock da akeyi sai aka biya mishi waec da neco kuma cikin sa'a yaci aiko take wani d'an majalisa yad'auki nauyin karatun shi kasantuwar unguwa d'aya suke kuma suna bashi tausayi shida d'an uwan shi uwa uba Abubakar yana mai aiki agidan shi sosai domin su basu dogara da kowa ba ahaka Abubakar yasamu yatafi B.U.K kano inda zai karanci Business yakuma fara karatun shi cikin sa'a yakan zo yaga Omar dake Ss1 duk wasu y'an bu'katun yau da kullum d'an majalisan nan Alhaji kabir yad'auke mai dan haka sosai yake kula da k'anin nashi ahaka har yakammala karatun shi Alhaji kabir yasamar mai aiki a companyn shi mai zaman kanshi kafun kace me tuni arziki yabud'e tako ina ga nauyin karatun Omar daya d'auka inda Omar yakaranci Pilot sai gashi y'an uwan baban su sunfara janyo su ajiki kowa naso yazo ya auri y'ar sa amma ya'ki yanuna kawai ayi zumunci, kwatsam Alhaji kabir yabud'e company a Abuja dan haka yamaida Abubakar can yakuma bashi manager

Bayan wani lokaci arzikin shi sai hab'aka yake kuma komai yana tafiya normal tsakanin shi da uban gidan shi Alhaji kabir kwatsam yad'auki y'ar sa Mubarakatu yahad'a da Abubakar yamusu aure duk dacewa Abubakar ba son Mubarakatu yake ba amma saboda halaccin mahaifin ta yazauna da ita cikin lumana ahaka har Omar yakamalla karatun shi yasamu aiki da aric airline sosai shima yake damawa inda bada jimawa ba yahad'u da Mom wato (Khadija) sukai auren su na soyayya duk kanin su a Abuja suka aje matan nasu saidai insun samu hutun aiki sukanje katsina suga y'an uwa ahaka har Mom tasamu ciki zokaga murna wajen su suduka kamar sujanyo rananr haihu Mubarakatu kuwa sosai tanuna ba'kin cikin ta akan cikin inda hankalin ta yatashi tace ma Abubakar lallai suje suga Dr aduba aga waye bai haihuwa dan ita haihuwa take so to bayan sunje anduba sune dukkanin su result yafito nanfa asirin Mubarakatu yatono domin Dr yatabbatar da cewar tazubar da kwayoyin haihuwar ta arariya dan haka itada haihuwa har abada,

Sosai hankalin ta yatashi jin asirinta na b'oye yabayyana haka suka dawo Abubakar baice mata uhm uhm ba illa kawai yasamu d'an uwanshi yagaya mai halin dayake ciki inda shikuma yabashi shawara akan ya'kara aure yace zaiyi tunani,

Abubakar yajima yana nazari gani yake kamar inya ma Mubarakatu kishiya tamkar yama ubanta butulci ne haka yaita sa'ke sa'ke tsayin lokaci yaci gaba da neman zab'in Allah,

A shekarar da aka haifi Abdul-Aziz da yaci sunan mahaifin su suna kiran shi da (Muneef) ne sukaje aikin hajji gaba d'ayan su wanda Omar ne yabiya musu to bayan sun dawo ne fa Alhaji Abubakar yafara neman aure inda yahad'u da Zulaikha a gwarinfa suka daidaita iyayen ta ba wasu masu k'arfi bane amma sunyi bincike sosai akanshi kafun akai auren cikeda sam barka,

Mubarakatu kuwa shiru tayi kamar bata damu da auren ba koda aka kawo amarya haka tatarbe su faran faran babu wanda bai yaba da halinta ba amma me tunda akai aure Alhaji Abubakar bai ta'ba kwana ad'akin amarya ba atak'aice ma bai zuwa inda take amma kullum suna tare da Mubarakatu tun Zulaikha na murna irin gudun nan da amare keyi har abu yazo yafara damun ta amma bata ta'ba gaya ma kowa ba harta shekara agidan watara na saiga Mom (Khadija) tazo gidan dake tasu tafi zuwa d'aya da Zulaikha yasa kota zo d'akin ta take sauka wani lokacin ma Mubarakatu takan bar musu gidan gaba d'aya sai dare takan dawo to yauma haka takasance tana ganin Mom tazo tabar gidan suna ta fira Muneef dake da shekara biyar yana zaune yana buga game sukuma suna firar su nanfa take tsokanan Zulaikha "Amarya any'a ba ciki gareki ba irin wannan fresh haka" 

Yak'e kawai tamata tace "Aunty banda komai nikam"

D'an shiru Mom tayi dan tafahimci basa zaman dad'i da miji sai da kishiya ahankali takalleta tace 

"Kodai planing Mubarakatu tasaki yi?"

Cikin jin kunyar ta tace "A'ah nifa bama tare muke kwana dashi ba"

Cikin mamaki tace "kamar ya?"

Shiru tamata dan batasan yazata ce mata ba,

Take khadija tafahimci shirin Mubarakatu na farraqa tsakanin Abubakar da Zulaikha bata sake cewa komai ba harta bar gidan,

Haka suka ci gaba da zama tsawon two years Abubakar bai zuwa inda Zulaikha take ko ita tazo sai yabar wajen atak'aice dai baya son ganinta komai take so saita gayama Mubarakatu ita zata mata,

To yau da gobe ba wasa ba sosai Zulaikha tashiga damuwa amma tarasa wazata gayama damuwar ta taji dad'i awannan yanayin mahaifiyar ta takwanta rashin lafiya tamutu wanda tsakani da mahaifinta babu nisa shima yayi mutuwar farat d'aya moto ta kad'e shi KO shura wa bai yiba tashiga tashin hankali maras misaltuwa ga dangin iyayen ta babu wanda yadamu da ita sosai take tausayin kanta ganin bata da wata gata, amma Mubarakatu taita kwantar mata da hankali ahaka harta dangana ita aganin ta Mubarakatu bazata ta'ba cutar da ita ba,

Khadija (Mom) kuwa ro'kon Allah da saukan alkur'ani tasa akai tayi akan lamarin domin tasa anyi istikhara ankuma tabbatar da matsala wasu ruwan rubutu na karya sihiri aka bata akace takawo ma Zulaikha tadinga sha tana wanka dashi har sati d'aya,

Koda takawo mata tabata takuma mata gargad'i mai k'arfi akan karta kuskura tagaya ma Mubarakatu kawai tai amfani dashi, to tafara amfani dashi aranan data gama fa saiga Alhaji Abubakar yashigo d'akin ta cikin dare,

Tana barci taji ana shafa mata jikinta ad'an firgice tafarka sanin bamai shigo mata d'aki ahankali cikin rad'a yace 

"Shish nine am sorry natada ke a barci ko ha'kkina nazo amsa please"

Sosai abun yamata wani banbarak'wai taso mai gaddama aiko yamatse ta yayi da k'arfi domin amtse yake Mubarakatu duk sanda yaje tadinga mai yanga kenan wataran ma tahana shi sai yabata kud'i masu yawa, to yau kusan wata d'aya kenan tahana shi yayi shikuma yaji kamar zai mutu kawai yaji bara yaxo wajen Zulaikha aiko sunsha dambe kafun yasamu yaci k'arfin ta tana ihu tana komai yarabata da budurcin ta ba'karamin wahala yabata ba dan yanda yake bi da ita kamar yasamu babbar mace 

Ihunta ne yafarkar da Mubarakatu aiko a birkice tafito daga side d'in ta tanufo inda takejin ihun data tabbatar na Zulaikha ne magana tadinga ji k'asa k'asa acikin d'akin dakuma kukan Zulaikha aiko cikin tashin hankali tabankad'a d'akin tashiga duk da duhun d'akin hakan bai hana idanun ta mummunan ganin Zulaikha ak'irjin mijinta tana zuba mai shagwa'ba ba wani uban ashar ta zun duma da yasa duka suka juyo ad'an firgice...............โœ๐Ÿป




*cai this Mata wai mijinta ๐Ÿคฃ๐Ÿค”*



*_How to subscribe ๐Ÿ‘‡๐Ÿป_* 

_200 for normal paid post once a day 400 for VIP group post twince a day, 4210014214 lawal Shamsiyya Eco bank and send the evidence of payment via *** or mtn card with this number ***_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.