Free chapter · Read without an account

DANGINMU NE SILA 003

by Jamila A Bello · DANGINMU NE SILA

_*DANGINMU NE SILAR KOMAI*_


   Na


YAR MUTAN KANKIA❣️


*MANAZARTA WRITER'S ASSOC.*


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM*_

--------------------

*It's 500 via Acct no 0777512438 Access Bank jamila abubakar bello and show ur evidence via ****



**** domin magna da marubuciyar kai tsaye*



   Free Page 3



★★★

"Heart beat,kuka kuma."?cikeda damuwa ya tambaye ta,dukar da kanta tayi tana kokarin tsaida hawayen dake ziraro mata wanda yake daidai da bugun zuciyar shi ba kadan kukan ta ke azabtar da shi ba."Wai me akaima mata."?ya tambayi Salma ba alamun wasa a saman fuskar sa."A sanyaye Salma ta faɗa mashi komai,mikewa yayi yana fesar da iska mai zafin gaske, ya kalli Amina duk tagama daburcewa."Amina duk yanda na gyargyaɗe ki bakiji ba kenan?miyasa zaki biye tasu,maza kibar wajen nan tunkan ranki yai mummunan baci sarkacin banza dana wofi."fita Amina tayi tana sumburar baki tana."yaya ai laifin sune ba kaga abinda sukaima Anty ba." "Koda laifin sune miyasa zaki biye su."?.."yaya ai...ganin yayi kanta yasa Amina ta fita da gudu tabar gidan."heart beat ki daina wannan kukan yana azabtar dani dayawa zubar hawayen ki yana azabtar da zuciya ta,ki daina wannan kukan kinji tawan ina sonki keece bugun zuciya ta kece farin cikina dan Allah kiyi hakuri,indai su Hafsat ne sai na ɗauki mataki akan duk wanda yake son ya wulakanta ki Ummin Sadiq kidaina yimani asarar hawayen ki kinji matatan."duk yanda Nazima takejin zafin abinda kannen Nizam sukayi mata saida taji dadin kalaman sa har kasan zuciyar ta,a hankali ta Fisge hannun ta daga rikon da yai mata,tafara magana a zafafe ga zuciyar ta nama ta ƙuna"Karabu dani Abban Sadiq!miye a ciki dan kana sona dan Allah ka sararaman nace ban son ka kuma wlh sai ka sakni."mikewa yayi tsaye kamar marar kuzari yanajin dacin kalaman ta gashi baki daya soyayar Nazima ta gama zauta shi,duk lokacin da zatace ta tsane shi,haka yake kara jin kaunar ta na kara fisgar shi.cikin sanyin murya da sifar kwantar mata da hankali yace."Dan Allah heart beat ki tausayaman kidaina furta munanan kalaman nan akaina ina son ki Nazma ki soni koda rabin son da nike maki ne,why zaki daina sona sabanin Da?miyasa bazaki soni ba kodan Sadiq,kiji tausayina kodan dangantakar dake tsakanin mu, ki soni kada ki rabu dani dan Allah."kamar wani gele haka yake bata hakuri cikin kankanin lokaci idanun shi ya sauya kala ga tsananin bugu da zuciyar shi ke mashi."Kayi kuskure daka haɗani da danganta ka kodan DANGINMU naƙika Abban Sadiq."A sanyaye ya sake rike hannun ta,yana karajin son ta"miyasa kika fiye son kanki dayawa?why not bazaki gane halin da nike ciki ba,kema kinsan bazan iya rayuwa babu keba Haba Nazma kiji tausayina!" zame hannun ta tayi ta shige ɗakin da sauri ya bita saidai kafin ya iso harta rufe ɗakin,ta saki uban kuka mai sosa rai duk abubuwa sun sha mata kai."Miyasa zaku tsane ni?wai mi nayi maku baku sona kawai saboda ɗan uwan ku zaku takura mani kuna dangina miyasa bakuda tausayi."Kukan ta kuma saki mai karfin gaske tana dafe kanta da takeji kamar zai rabe gida biyu.


 Shiko Nizam kamar andasa shi jikin sa yai bala'in sanyi yana jin zafin abinda kannen sa ke masa,yarasa abinda ke masa dadi komai ya dagule mashi,da haka ya fita ya shiga mota ba inda ya sauka sai gidan su duk da kasancewar Estate daya ne amman akwai ɗan nisa ba laifi

 Yana parking,bai wata wata ba ya shiga cikin katafaren falon su wanda yagaji da kayan alatu na more rayuwar yau da kullun.dayake mahaifin Nizam mashahurin attajiri ne na faɗi da busa,daman can dangin su yan gadon arziƙi ne,amma yafi kowa kuɗi a cikin yan uwan nashi.

yana shiga cikin falon ya fara artaba da Rukayya batasan da shigowar shi ba,kamshin daya karaɗe falon yasa yan hanjin ta yamutsawa, tasan Ya Nizam ne a sanyaye ta duƙa ta gaida shi, kallan da yake watsama ta shi ya bata amsar abinda suka shuka,a ɗarare ta miƙe zata shiga ɗaki taji ya kirata da ƙausassar murya saida taji kamar tayi fitsari tsabar tsorata da tayi,gashi Momy bata nan bare ta kwace ta daga hannun Ya Nizam jiki sage ta isa wajen shi."Gani Yaya."ta ida maganar tana kokarin dukawa,tunkan guiwowin ta sukai ƙasa ya wanke ta da mari har saida ta kwalla ihu mai rikidarwa da gudu Goggo mai aikin gidan su tayo falor tafara bashi hakuri,ƙafa yasa ya halbata itako sai zunduma ihu takeyi tana neman ɗauki,duk ta gama firgita da lamarin Ya Nizam,ya sake ɗaga hannu zai mazgeta Goggo ta iso wajen shi tafara bashi hakuri."Alhaji dan Allah kayi hakuri kayafe mata."duk yanda ranshi ya ɓaci saida ya fasa dukan ta,saboda shi mutun ne wanda ke girmama mutane musamman naga ba dashi,sannan yana daraja Goggo sosai shiyasa ya kyale Rukayya duk tayi zufa sai kuka take harda majina,wani mugun kallo ya watsa mata hakan yasa ta haɗe sauran kukan da takeyi,so take ta tafi ɗaki saidai tsoron sa ya hanata saboda bai bata damar tafiya ba, itako Hafsat dake ɗaki tunda tajiyo ihun Rukayya ta sakawa room din key ta rufe,sai kuka take tunkan ya iso kanta,jikin ta na rawa ta ɗaukar waya ta kira Momy wajen five miscall amman batai picking ba."Ke ina Hafsat."bakin ta na rawa tace."ɗaki." ɗakin ta ya tafi yafara buga kofar,tanajin yana kiran sunan ta da sauri ta rufe bakin ta da tafin hannun ta tana kwalalo idanuwa waje tasan kashin ta ya bushe,take saida tayi nadamar zuwa gidan shi"Hafsat idan kika bari na sake ambatar sunan ki,baki bude dakin nan ba saina taka maki ruwan ciki."batasan sadda ta iso bakin kofar ba ta bude,sai kyakkyawar take ta kasa fitowa waje tsabar tsoron kalar hukuncin da zaiyi mata.Hakuri ta fara bashi tana kuka,tsaye yayi bakin kofar ya harde hannayen sa yace."bazaki fito ba."Ya Nizam kayi hakuri natuba wlh nadaina zuwa gidan ka ma."a tsorace ta ida maganar duk ta raina gaskiar ta."fito falo nace maki."dukawa tayi tahau yi mashi magiya ba kadan ta vata mashi rai amba da bayi niyar dukan taba,ganin tana bata mashi lokaci baisan sanda ya faske ta da mari ba ai da gudu Hafsat ta iso falo ta zauna kusa da Rukayya kamar ya'yan mage haka suka rakuɓe sai kuka sukeyi suna bashi hakuri."Ku buɗe kunnuwan ku da kyau ku saurari abinda zance maku."toh Yaya Allah munajin ka."Na rantse da Allah daga yau idan nakara jin wata daga cikin ku,taje gidana ko ta faɗama matata baƙar magana,wlh sai kunyi mamaki sai na ɓallaku kuna jina."?Da sauri suka ce "eh munji bazamu kara zuwa dan Allah kada ka dake mu kayi hakuri."Wannan damuwar ku ce,nadai faɗama ku ina Aishar take."?..."ta raka Momy shoping."

(Bayin Allah duk sun gama tsurewa kamar basu suka gama rashin kunya ba,maganin marar kunya kenan😂)


kwafa yayi yace."idan ta dawo ta sameni gida kuce mata ina neman ta ."?.."Toh zataji."fita yayi yana bugo kofa,koda ya isa lot mota ya shiga yai mata key yabar gidan yana driving hankalin sa nakan Nazima fatansa ya samu ya shawo kanta komai ya cakude mashi.


Koda suka tabbatar da yabar gidan sai suka fara masifa."Wlh Anty Rukayya sai mun koyama Anty Nazima hankali harta isa ta haɗa mu da Yayan mu."Hmm kedai bari Hafsat jibi yanda yaketa hakilo akan matar shi,ni wlh na rasa wane so Ya Nizam kema Nazima."Ji wani zancen asirce shi tayi,kuma wlh sai mun rura mata wutar da bata iya kashe ta."Wlh kuwa har nakosa Momy ta dawo komai yai mana sai mun gaya mata."Rufe nakin Hafsar keda wuya Momy tashigo ita da masu aiki dauke da kaya niƙi niƙi,da gudu Rukayya ta faɗa saman ta tana kuka, duk tsoro ya kamata tayi juyin duniya sunki magana da kyal suka faɗa mata abinda ya faru,girgiza kai tayi cikeda takaici tana sakin murmushi mai ciwo tace."Ku rabu da Nizam indai nice uwar sa kuma na amsa sunana Zaituna Buhari wlh sai nayi maganin wannan ballagazar yarinyar makira mai hali irin na uwar ta yan gadon asiri yarinyar kankanuwa amman ta shanye mani ɗana,duk family ya rasa wadda zai nacema wa sai ƴar mace mai mugun hali yar gadan gado."cikeda bacin rai ta kuma cewa."mikoman waya ta Humaira."Aisha da sakon Nizam ya isa wajen ta ta mikoma Momyn su wayar jikin ta duk yai sanyi kiran Nizam tayi lokacin yana cikin ɗakin Nazima yana ta lallashin ta,kiran wayar Momyn shi tasa shi ɗauka,ya gaishe ta cikeda girmamawa."masifa tafaratace. "ina fatan kanajina idan kai zuciyar ka ta mutu ko kaza ta sace ni Zaituna Buhari nasan kishin kaina Kaji kunya Nizam dan haka duk abinda kake yi kazo ka sameni yanzun yazun."bata jira amsar saba ta kashe wayar.Wani irin sarawa kan Nizam yayi da kallo yabi screen din wayar yana fidda numfashi mai zafi,itako Nazima kallan sa kawai takeyi duk da bataji me tace mashi ba, ammn tasan ba lfy saidai hakan ba damuwar ta bace,fatan ta ya sauwake mata taji da bala'i irin na Dangin su,a hankali yake kallan kwayar idanun ta yace. Heart beat dan Allah ki kara hakuri akan abinda sukai maki kinji."baijira cewar taba ya fita daga gidan a kafa ya tafi yana isa harabar gidan su,mai gadi ya gaida shi kai tsaye falo ya shiga da sallama a bakin shi ya iske kannen shi da Momy zaune kowa baida wani sukuni,zama yayi gefen mahaifiyar shi ya ya gaida ta cikeda ladabi,kauda kanta tayi gefe hakan ya sosa ma Nizam rai ya tsani fushin Momyn sa akan sa.

  A ɗarare suka gaida Yayan nasu itako Aisha ko haɗa ido ta kasayi dashi,Jiki mace suka wuce dakin su.Kamar jira take subar falorn ta haushi da faɗa."Ashe baka da hankali ban sani ba wai mike damun ka Nizam?Yanzun ko kunya bakaji ace akan wannan ficiciyar yarina shashahar kua auraka zaka dinga yima yan uwan ka ihuhar dukan su,Ohni Zaituna Buhari na shiga ukkuna an shanye mani ɗa,billahil azmin matukar ina numfashi saina wulakanta Nazim,kai in baccin kana sakarai marar zuciya dayake da kasha nono na tunbiɗi kayi taya za'ace wannan ficiciyar yarinyar sa'ar Salma ta dinga wahalar da kai iyeh ka ɗauki son duniya ka daura mata,ka iyama ka Saketa amma ka kasa dayake baka da zuciya har Kotu saida ta kaika,to bari kaji daga yau matuae nasake jin makaman cin haka ta sake faruwa wlh sai na saba maka Nizam!In banda abun kama Yar gadan gado zaka zauce mawa kaicona nayi da nasanin biyewa ra'ayin ka dana mahaifin ka har ka auri Nazima ga ya'yan dangi nan cike da gari kowa yana son ka amman ka nacema Nazima inbanda kadara ina kudan yake bare roman sa kabani kunya kuma ka sani na tsane ta ban kaunar ta."da sauri ya dago kanshi dake sarawa mashi ya kalli mahaifiyar shi jin kalaman da dakeyi y....


_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka  fara amfani da  maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


_*infection*_

_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

_***_

_____________

*Sdeendtm*

 I'm sell data to all Nigeria network


Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I'm

 selling MTN data with this cheap price* 


*MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.

 *Validity 1 month* 


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.* 

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp ***


 _Yar Mutan Kankia ce❣️_ 



Share

Pls

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.