Free chapter · Read without an account

007

by Jamila A Bello · DANGINMU NE SILA

_*DANGINMU NE SILAR KOMAI*_


    Na


JAMEEY❣️


*MANAZARTA WRITER'S ASSOC.*


_*BISSIMILLAHIR-RAHAMANIRRAHIM.*_

____________________


   _Free Page 7_

_Follow me AREWABOOK dan samun sabon update cikin lokaci_ https://arewabooks.com/chapter?id=62d034a2f9d9563d0158345d username Jameey123.



"Ki kasan ce mai yawan tausayi da jinkai kinga ban lafiya bai dace kitafi ki barni ba."a marairai ce Nizam yai maganar,yana dafe marar shi kamar mai ciwon cikin gaske.Sauke idon ta tayi daga kallan shi tace."Ya Nizam bacci nikeji faaa."yanda taja karshen maganar saida tsikar jikin shi ta mike wani irin bakon yanayi ya saukar mashi a lokaci guda."Am so sorry beb,ba zakijima belive me."langabar da kanta tayi tana kokarin kwace hannunta daga rikon da yai mata,duk yanda taso ta zame takasa cikin wani irin salo na daban yace."Heart beat ki yarda dani mana idan kika koma ɗaki wazai kula dani kinsan yanda ciwon ciki ke katsa mani."kamar mai raɗa ya ida maganar yai baya baya kamar zai faɗi ƙaaa da sauri ta riko hannun shi gam tafara cikiniyar janyo shi jikinta da karfi hakan yasa dawo saman ta,sake rumgume ta yayi bisa kaffaɗan kirjin shi daga shi har ita sauke ajiyar zuciya sukeyi suna jan numfarfashi kamar wa'anda sukayi dambe,ita tsoro taji ganin zai fadi,yayin dayake jin wani irin masifafan dadi ya ratsa mashi kohon zuciya a hankali ya shiga sinsinar dogon wuyanta yana shakar dadddan kamshin turaren jikin ta,a hankali ya lumshe manyan idanun shi yana sake yi mata muhalli a kirjin shi sun kai minti biyar a haka a hankali suka dago fuskokin su suna kallan junan su kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar shi,ko kaftawa baiyi haka yake kallan kwaryar idanun ta yana tabbatar da soyayar shi a cikin su,jikin ta yai masifar sanyi a susuce tafara yin karfin halin turashi,shima yagama shagala da kallan ta duk tsikar jikinta tafara zubawa yarrr jin idanun sa akanta duk sai taɗan ta kure jikin ta cikeda karfin hali race."Abban Sadiq saida safe nagaji."juyawa tayi zata shige dakinta cikeda gafin nama ya sake rikota"Ummin Sadiq help me pls muje ɗakina saiki kwana kinji yar aljanna."samun kanta tayi da gyaɗa mashi kai ga wani irin kwarjini da yaimata bataji zata iya yi mashi musu.a hankali ya haɗe hannayen su batai mashi musu ba suka bufi ɗakin shi.suna shiga tahau gyara mashi gadon saida ta gama gyara shi tsaf ta kalleshi tana kwabe fuska cikeda shagoba"Ya Nizam zo ka kwanta."zuba mata idanin sa yayi ganin yanda takara yi masa kyau musamman yanda take sarrafa labban ta wajen yin magana da shagwabar ta komai mata yana kara burge shi...ganin yanda ya kafeta da ido yasata kara langwabewa kamar zatayi kuka baisan sanda yace.Kefa ina zaki kwanta."?batareda ta kuma cewa komai tafara tafiya a hankali harta isa saman tree seater ta kwanta akai sannan ta rufe da bargo ta juya mashi baya tana cinno karamin bakin ta,shidai da ido ya rakata a hankali yake tako harya isa kusa da ita ya duka a sifar magiya da lallashi yace."Heart beattt."ya kirata cikeda salon da baisan yayi amfani da shiba ita kanta saida taji voice din har cikin brain dinta zuwa zuciyar ta."uhmm."ta amsa shi cikeda kasala."common muje ki kwanta a bed kinji tawan."immm immm."tace tana ɗage kafaɗa alamun bata zuwa."plss haba sweet heart." a hankali ta juyo da fuskar ta face din su na facing juna tace."Allah ka ƙara damuna yanzun nan zan tafi ɗakina."Sorry."yace ya mike a sanyaye ya kashe light sannan ya saka masu dump light yakoma kan bed ya kwanta,shiru ne ya gauraye ɗakin kowa da abinda yake ayyana a zukatan su,sai juye juye yake ya kasa bacci, a hankali ya fara jiyo saukan numfashin ta alamun tafara bacci har tsawon 20mint jin shirun yayi yawa sosai hakan yasa shi duba agogon dake bisa bangon dakin yaga gar 12:30 da gani tayi nisa a cikin bacci,a hankali ya mike kamar mai sanɗa yake taku gudun kada taji motsi ta farka har ya isa wajen ta ya duka ya ɗauko ta cak kamar ƴar baby ya maida ta saman gadon shi ya kwantar da ita,a hankali ya hau bisa bed din ya kwanta yana rungume ta sannan yasa hannu ya kashe dum light din a hankali ya jamasu duvet ya rufe su yana cusa kanshi tsakanin wuyanta zuwa kirjinta yana shinshinar ta wani irin sanyin dadi da farin ciki ya rufe Nizam yanajin dumin jikinta na ratsa shi ba kaɗan yai missing komai na taba,a hankali yake shafata yana wasa da sassan jikinta gently yanda bazai tada taba,ga wani irin daɗi da ya mamaye mashi zuciyar,banda juyi ba abinda takeyi,shima a haka amintaccen bacci mai daɗin gaske yai awan gaba da shi...... 

   Washe gari da safe misalin karfe 8:00 ya dawo daga masallaci yana shigowa yafara."Heart beat wake up good morning...turus yayi ganin batanan ji yayi kamar ya bita,amma ya hakura,shiri ya farayi zai tafi office wayar shi tahau ringing da ido yabi screen din ganin Sectary kamar bazaiyi picking ba sai kuma ya ɗaga."Sir good morning."morning."ya amsa yana daura agogon hannun shi."you have a meeting by 10."Okay but zan biya ta hospital kafin time yayi hope ba wani abu."?.."Yes sir."bai kuma cewa komai ba ya aje wayar yaci gaba da shirin sa,saida ya dauki one hour yana shiri banda kamshi ba abinda yake bazawa cikin black suite and black shoe yai kyau masha Allah,bashi ya shirya ba sai 9am yana fitowa ya kalli kofan apartment din Nazima dayake suna facing dana juna kamar zai shiga sai kuma ya fasa a nutse yake footing step kamar bai son saukkowa zuciyar shi nasan taga masoyiyar shi before ya bar gidan dagowar da zaiyi idanun shi sukayi tozali da Nazima tasha gayun ta cikin wani dakkken maroon less dinta daya dace da farta jikinta bakaramin kyau tayi mashi.Cikin kankanin lokaci zuciyar shi tafara racing ganinta tareda lawyern ta yana mata tambayoyi tana bashi amsa ga gyalen data yafa akanta sai daukar ido stones din jikin shi yakeyi,wani mugun kishine ya turnike Nizam take yaji bakin ciki ya taso mashi ko motsi ya kasayi."insha Allah Barrister."tace tana sakin murmushi dagani taji dadin zuwan shi.

  A kufule Nizam ya iso inda suke yana facing din Barr Mukhtar ya hade girar kasa data sama,wani irin bugu ta tsinci zuciyar ta tayi jin sanyayyan kamshin turaren da taji ya sanar mata da fitowar Ya Nizam juyowar da zatayi idanun su suka sarke dana juna take gaban ta ya faɗi daganin yanda yanayin shi ya sauya.a sanyaye barister ya tashi yana mikama shi hannu yace."Morning Doctor."kamar bazai bashi hannu ba sai kuma ya cije,shikanshi Barister yakasa sakin jikin shi dan dole ya kwashi tarkacen littafin da yake jotting yai mata sallama ko amsawa ta kasayi ya fita.



Kanta kasa takasa kallan fuskar shi tace."Ina kwana."kululun bakin ciki ya haɗe yana watsa mata wani irin kallo hakanan yaji haushinta marar misaltuwa a ranshi jin yayi shiru baice komai ta dago kanta ta saci kallan shi karaf idanin su suka sarke dana juna ya dalla mata wani bahaggon kallon dayasa ta rasa duk wani sukuni da natsuwar zuciya tasan kishin sa ne ya motsa sanin waye mijinta."Ya..Ya Nizam kayi...daga mata hannu yayi alamun dakatarwa dan baisan mizaice mata baisan sadda yasa kai ya fitaba yana bugo kafar dakin da karfin tsiya har saida ta rufe idanun ta zuciyar ta na halbawa da karfi,dafe kanta tayi ta fada bisa kushin tana sakin kukan data rasa dalilin yinsa.banda gudu ba abinda yakeyi har bai ganin gaban shi tsoron shi ɗaya kada akara zuga mashi mata,wani uban cintaya yayi yai parking yana hade kai d stiari kamar zautacce yace."zan koya maka hankali Barrister Mukhtar.Daukar wayar shi yayi har zai dailing number shi sai kuma yafasa ya aje girgiza kanshi yahau yi sai kuma ya dauki wayar ya kira number shi,Barrister dake zaune office yana sauke ajiyar zuciya yaji wayar shi na ringing wani irin faduwar gaba ta kama shi yakasa dagawa harta tsinke sai a kira na biyu yai karfin halin dauka yakara a kunnen shi."waya baka ikon ganawa da matata."?fesar da iskar bakin shi yayi yace."look Dr bawai wani abu na tattauna da ita akan case dinmu ne..."Keep quite harka isa kayi magana da matata a gidana kenan kaike hore mata kunne ko."?"No dr Nizam ka fahimceni...."Silence."ya daka mashi tsawa har saida Barr ya rufe idanuwan sa yace."daga yau nasake ganin ka tareda matata kuma agidana sainayi kararka kabari idan kun hadu tsiyar Kotun ku saikayi duk iskancin da zakayi amma ba agidana ba understand."Nizam..."i said understand or not."?a tsawace yake tambayar."Okay but.."me?har har kana da abinda zakace mani iyeh Barr? shame on you da hankalin ka kake bada gaggarumar gudunmuwa wajen lalata sunar ma'aiki kaji kunya idan kasanta."Kayi hakuri Nizam bansan bata nemi izini daga wajen ka."A sanyaye Barister ya ida maganar duk jikin sa yayi sanyi ,bakin cikine ya turnike Nizam baisan sadda ya daka mashi irin rikirkitartar tsawa harda yan cikin shi suka kaɗa tsabar razana yace."Kada kamanta kayi magana da matata without of my permission dan haka ka tanadi hujjar da zaka kare kanta."a rude Barr yafara ba Nizam hakuri."Sorry Dr ka saurari uzurina pls...datse kiran yayi yana wurga wayar bisa kujerar mai zaman banza ya maida kanshi bisa kujera yana maida numfashi mai zafi babban bakin cikin shi yanda Nazima ta zauna gaban kato tasha kwalliya yana mata tambayoyin iska!wani duka yakaima sitiary sannan yaima mita key a slow yake driving garya isa office banda tunani ba abinda yakeyi yakasa komai,ko meeting din da zasuyi saida ya tura mataimakin shi ya wakilce shi,haka ya yini ko uffan baicewa sai tunanin kalaman Nazima yakeyi yanda take cema Barr tana son zaman da zasuyi zuwa jibi mijinta ya saketa..."wannan kalmomi sukema Nizam yawo a cikin kwakwalwa tun yana ganin ƙiyayyar da Nazima ke mashi kamar wasa har abin yafi karfin tunanin sa,ganin tunani bayi mashi zaiba shiyasa ya fito daga office din ya hau motar shi ba inda ya sauka sai gidan Grannyn sa,wajen kakar su wadda ta haifi mahaifin shi Hajiya Hafsat Maikaba.

   Koda ya isa saida ya gaishe da tsaffin gidan da yake baki daya kakanin su a gida ɗaya suke wani irin katon gida ne,wanda yafi kowa ne girma a cikin Maikaba Estate,yana da part kala kala a cikin shi,yana fitowa ya wuce wajen kakar tashi Koda ya shiga samunta yayi tana shan fura da nono,washe baki tayi ganin jikan nata tagau tsokanar shi"Haba yaya babba,sai yau nike ganin ka ko?taho kahau cinyar tsohuwa in maka tausa sannan in baka fura a baki kaha."baisan sanda murmushi ya subuce masa ba yace."Wai yar tsohuwar nan sai yaushe zaki iya fadin Nizam ne?kinga kibar wannan furar taki indai ba Ummin Sadiq ta dama taba ba kowa bai iya ba."yaka rashe maganar da sifar zolaya,itama da wasan tace."Wato dayake ni karaina aida'ace agaban Abban kune Abdulhamid da baka ce haka ba shima bai jima da fita ba."a zuciyar shi ko ji yake dama ya tadda shi dan ya kusa zuwa ya sanar dashi case dinshi Nazima,duk da yasan mahaifin ta akwai shi da daukar zafi shiyasa yake kin zuwa wajen shi, danko Abban shi baisan wainar da ake toyawa ba duk da jibi zai dawo daga England(UK)....a zahiri kuwa murmushi yayi yana mata tausa ita kuma tana bashi labari wani irin dadi yaji har yaji ya rage zugi da zuciyar shi ke mashi,da wasa wasa yafara shan furar kuma yaji dadinta bashi yabar gidan ba sai gab da magarib koda ya tafi masallaci ya dawo gida bai bari sun haɗu da Nazima ba har ya kwanta duk daren nan bai bacci ba tashi yayi yai sallah yakaima Allah kukan shi...


Itama anata bangaren saita shiga damuwa sodai duk da tana bukatar saki daga mijin ta amman ganin halin da ya fita sai takasa kwanciya har 12am tana jiran shigowar shi saida ta leko ta window amman bataji shigowar shi ba ganin dare yayi yasa ta tafi ɗaki duk ta gama shiga damuwa da haka taita juye juye karshe bacci ɓarawo yayi awan gaba da ita..

  Bayan kwana biyu ya kama yau ake komawa Kotu tunda ya tashi ya iske text massage din Barr Nafi'u Hassan Nakowa ya sake tunatar dashi yau ake cigaba da shari'a.ɗan guntun tsaki yaja jikisanyaye ya shiga bathroom yayi wanka dakyal yasha black tea sannan ya saka wani black yard ya fita zuwa falo nan ya iske Salma ta shirya gaida shi tayi ya amsa ta a takaice dai-dai Nazima ta sauko daga upstairs tasha ash din Abaya tayi rolling kana ganin ta saika sake kallan ta tsabar kyaun da tayi wani irin wawan kallo ya watsa mata saida ta sauke kanta asanyaye takasa ko motsin kirki magana yayi cikeda gadara yace."Kada ki kuskura kije Kotu a haka kuma na haramta maki wannan kwalliyar matsawar zaki fita waje kije ki shareta umurni nike baki ba shawara ba."baijira cewar taba ya fita a fusace, Salma ce ta maye mashi baya suka shiga mota suka tafi saida suka biya ta wajen mahaifiyar su dan ya gaidata a cikin bedroom din ta ya isketa ta gama shiryawa itama cikeda ladabi ya gaida ta, ta amsa a takaice...itako Nazima kamar tayi kuka haka taji ta mirrow ta kalli dressing dinta cikeda ɓacin rai tace."Wane hukunci zakai man da ya wuce saki daman shi nike bukatar saime wlh badan a gaban Salma kaiman wannan maganar ba Allah da ban goge kwalliyata..."Sumburar baki tayi ta bude Press dinta ta dako atamfa ta saka blue and pink color sai hijab mai hannun sannan ta fita ganin ta kusan makara.

  Koda Hajia Zaituna Buhari,tagama waya da aminiyar ta kuma kanwar Na'ima kallan Nizam tayi daka ganshi kaga mai damuwa,gutun tsoki tayi tace"Naji rashin kunyar da kaima yar uwa ta kuma da kanwar ka akan wannan sakaryar yarinyar dai ko?toh bari kaji muddin mukaje Kotu ka nuna ka mutu akan son yarinyar har kaƙi sakin ta wlh ranka ne zai mugun ɓaci! kajini da kyau ni Zaituna Buhari ƴa ga Hajia Aisha Maikaba kaf zuriyar ɗakin mu bamu da raggo dan haka ni bazan haifi raggo ba dafatan ka fahimta.?"

  Rasa abin cewa yayi banda gyaɗa kai da yayi alamar eh,awani sashen na zuciyar shi yana tunanin sanar da mahaifin shi halin da ake ciki dan baiji zai iya rabuwa da matar shi, dahaka yai mata sallama itama tashi tayi suka shiga mota tashi nagaba suna biye dashi har zuwa katuwar Spreme Court din atare duk sukayi parking daidai nan Nazima da kannen ta suma sunyi parking, atare suka gaida Hajia Zaituna amman ko kallan arziki basu isheta ba,shiko kallan matar tashi yayi yaga tabi umurnin shi kuma yaji daɗn hakan saidai yana ganin bata kyauta mashi ba da take neman takardar saki har takawo shi Kotu, a gaban idanun shi Fadila da Hafsat suka ingije Nazima,su Amina ne suka tareta saura kaɗan ta faɗi buɗe baki yayi zaiyi magana aiko Hajia Zaituna ta wurga mashi wani irin matsiyacin kallo,ba shiri ya haɗe kalaman shi da haka suka shiga Kotun kowa ya hallara Alkali kawai ake jira,basu jimaba ya shigo kowa ya mike bayan ya zauna kowa ya zauna Court din tayi tsit kamar an mutu Alkali ya maida kallan shi wajen magatakardan Kotu yaba shi izini karanta case din da za'ayi shara akan sa yace......


_________

_Danginmu ne Silar Komai labari ne daya kunshi tarin sadaukarwa ta wasu masoya da_ _sukema junan su sahihin so.Nizamuddeen da Nazima masoya ne da suka fito a cikin wani irin dangi masu yawan son zuciya da zamba cikin aminci dangine da tarin yan ubanci yayi gaba a cikin zuriyar ta_ _Maikaba.ta zabi mijinta ya saketa saboda Dangin su ta zabi ta rabu da duk wani farin ciki da jin dadin rayuwar da suka gina cikin tsantsar so da kaunar juna,ta zabi tabar uban ɗanta badan komai ba sai saboda Danginsu!miyasa ta zabi ta rabu da kowa nata duk akan_ _dangin su,wa'anne irin Dangi ne?minene Silar da zaisa ta nemi takardar saki a wajen mijin ta duk da irin son da sukema junan su.zata samu abinda take nema wajen mijinta?Wannan kaɗan daga cikin shimfidar Danginmu ne Silar_ _Komai...ko minene Silar?duk wannan amsoshin bazasu samu ba saikin biyoni a cikin wannan labarin mai dinbin darasi da nishadantarwa._ 

 _Yar uwa,garzayo kada ayi babu ke maza ki mallaki naki danjin dadin karatu cikin jin dadi da aminci akan farashi mai rahusa da arha #500 two post in a day.Via acct no 0777512438 Access_ _Bank Jamila Abubakar Bello show ur evidence via ***._ 


 _*Thank you🥰*_


★★★

*Sdeendtm*

 I'm sell data to all Nigeria network


Thank you for contacting Sdeendtm! *BUY DATA


 FROM THE AFFORDABLE PRICE*


*I'm

 selling MTN data with this cheap price* 


*MTN DATA PACKAGE*

500MB@===200

1GB@=====300

2GB@=====600

3GB@====900

5GB@====1,500


Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance.

 *Validity 1 month* 


*Airtel,9mobile and Glo* *also available.* 

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills* *Whatsapp ***

_____________

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka  fara amfani da  maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_


_*infection*_

_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_

_***_



 _Yar Mutan Kankia ce❣️_ 



Share

Pls

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.