Free chapter · Read without an account
Labarin Yaya da ƙanwa
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*TASBIWUL DANE*
_(CARBIN ƘWAI)_
👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨👩❤️👨
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* 🤜🤛
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ 📖🖊️
Hohoho! Ina masoya kuma makaranta litattafan hausa novel? Yau ma ga jarumar ta ku ta dawo a cikin sabon littafin ta mai taken *CARBIN ƘWAI*, Littafin *CARBIN ƘWAI* Ma'ana *TASBIWUL DANE* littafine da ya k'unshi wata irin cakwakiyar sark'ak'iya da kuma ban al'ajabi gami da zazzafar soyayya, zai fad'akar ya nishad'antar da masu karatu, domin samun na ki da wuri ki/ka hanzarta biya dan karatu cikin salama, ka da ki bari a baki labari maza hanzar ta ki nemi naki akan farashi mai rahusa. Ga mutanenmu na Niger zaku biya katin Airtel ko Moov na dala dari Cfa zaku tura akan lamba kamar haka *94-98-56-52*,
ga mtanen mu na Nigeria kuma zaku tura Naira 300 ta wannan account d'in 0002517237 lubabatu shehu Taj bank, bayan kun tura sai ku tura shaidar biyanku ta wannan lambar, ko kuma ku tura Kati a kan wannan lambar *94-98-56-52*
Mun gode sai kun zo.
_Bismillahir rahamanir rahim_
_1_
Ƙarfe 02:30 na dare ya shigo ɗakin baccin nashi, kaya ya fara cirewa zai shiga wanka, ƙofar banɗakin daya buɗe ne yasa ta farkawa a baccinta da ya jima da yin nisa, juyawa tayi ta kalleshi ta tashi zaune, ƙasa da sama ta kalleshi tana murza idanu tace "Alhaji sai yanzu ne ka shigo? Duba fa ka ga agogo ƙarfe nwa...?"
Ta faɗa tana kallon agogon itama dake fuskantarta, shima kallon agogon yayi tare da shafa tumbinshi yace "E, yau na fara shigowa warhaka ne da zai dameki?"
Taɓe baki tayi tana rumgume hannaye a ƙirji tace "Hummm! Na sani, kawai na yi magana ne dan naga sai ranar kwanana kake wannan cika daren."
Dakatawa yayi daga shirin buɗe banɗakin ya kalleta yace "Me kike nufi ne *Saratu*?"
Turo baki tayi gaba tana sake haɗe fuska tace "Ga abu a zahiri, saboda ni ba ƙaunata kake ba shiyasa."
Dogon tsaki yayi tare da shigewa banɗakin, ranta ne ya sake ɓaci ta bishi da kallo sai kuma ta tashi tare da ɗaukar hijabinta ta sa ta fice a ɗakin tana ayyana "Aikin banza, ni za ka wulakanta har ka dinga min tsaki?"
Bai jima a banɗakin ba yana fitowa ya samu wayam bata nan, bai damu ba sai ma goge ruwan jikinshi da yayi ya d'an shafa turaren hamata sannan ya aje towel d'in ya dauko wayoyinshi babba ɗaya da kanana biyu ya kwanta yana sauke sauƙaƙƙen numfashi.
Lumshe idanu yayi yana neman bacci ido rufe, da sauri kuma ya buɗe tare da waiwaina idanunshi yana ayyana "Anya kuwa ya sa hannu a takardar kayan nan da aka ɗauka a mangazar kaya?"
Sai kuma wata zuciyar ke raya masa "Ai takardun na hannunka, gobe da safe sai ka saka."
Ajiyar zuciya ya sauke tare da sake rufe idanunshi, wani lissafin ne ya ƙara zuwa mishi a kai ya fara tunanin "Kuɗin da na ba Nasiru anya kuwa sun cika daidai? Da alama kuma..."
Sai kuma ya share zancen sa'ilin da zuciyarshi ta raya mishi "Fatana dai kayan nan su zo lafiya lau, mutane dayawa ke jiran kayan nan."
Ire-iren haka tunani ya cika masa ƙwaƙwalwa har aka fara kiran sallah asuba ba tare da ya rintsa na minti talatin ba sai lissafe lissafen harkokinshi, yana kwance har aka gama kiran sallah aka tayar da sallah aka idar bai motsa ba, baccin da ya fara fizgarshi ne yasa shi miƙewa zaune a gajiye kafin ya sauka daga kan gadon ya shiga banɗaki, alwala ya dauro ya fito ya zura doguwar riga ya shinfiɗa sallaya ya kabbara sallah, yana gamawa ya koma kan gadon ko rigar bai cire ba da tunanin ya samu baccin ko awa ɗaya kafin gari ya k'ara haske sai ya fita.
Tunda tayi sallah asuba take zaune falon idanunta akan ƙofar shiga da fita na d'akin mai gidan nasu, ta gaji da zaman har kamar ta yi ihu, ita dai ta san duka matan gidan suna da sabon fitowa da asuba su shiga madafa dan gaggauta d'ora masa abinda zai ci kasancewarsa mai sammakon fita a gida, amma sai ta rasa me ya tsayar da Saratu yau da har yanzu ba ta fito ba? Bubbuga k'afarta ta fara yi k'asa tana girgiza kai sai tsaki take ja.
Daga kusurwar d'akuansu ta ji ana fitowa, juyawa tayi dan ganin waye, wacce ta yi tozali da ita ne yasa ta jan tsaki ta sake dawo da dubanta gabanta tace "Mtsssss! Ku kenan mutane sai gulmar sababi, ba damar ka yi niyyar yin abu daga kai sai mijinka sai an saka maka idanu."
Kallonta kawai *Hawa'u* tayi ta tab'e baki ta nufi hanyar madafa dan yin abinda ya fito da ita, ganin bata kulata ba yasa ta jinjina kai tace" Na so ki tanka min wallahi da yau dqke zan karya a gidan nan."
"Saboda ita ce marainiyar wayonki ko?" Saratu ta fad'a tana fitowa daga d'akinta, da sauri *Falmata* dake tunanin ganin fitowar Saratu ta gaba sai ta ganta ta bayanta ta juya tare da mik'ewa tsaye, saida ta dalla mata harara sama da ƙasa kafin tace "E d'in, ina ruwanki?"
Takowa tayi gabanta tana fad'in "Da ruwana, zaman me kike nan?"
Ta faɗa tana dafe k'ugunta, da yanayin tijara tace "Ban gane ba? Kenan ban da ikon zama a inda nake so saida izninki?"
Ita ma da yanayin masifa tace "E d'in, dan nasan ba alkairi yasa ki zama a nan ba, ba don kina son saka min ido ba ai da baki tashi da sassafe haka ba."
Cikin ɗaga murya Falmata tace "Me kike nufi? Ina abun saka idon a nan? Har kin kai mace ne da zan saka miki ido?"
Sama da ƙasa ta harareta tace "Gashi kuwa, tunda har kin alamunki ya nuna zaman gulma kike a nan."
Da yatsa Falmata ta nuna tace "Idan kika sake cewa ina gulma sai na tsinke fuskarki da mari."
Dafa ƙirjinta tayi tace "Ni d'in? Yanzu Falmata rashin kunyarki ya kai ki ce za ki mareni? To dan Allah jaraba ki gani..."
Ta faɗa tana matsawa daf da ita har numfashinsu na gauraya tare da sake faɗin "Na da ɗin zaman gulma kike, ki mareni na gani marar kunya kawai."
Ja baya Falmata tayi tace "Kinsan dai idan na yi niyya sai na tsinke fuskar taki da mari kula ba abindddd..."
Ganin ita surutun ne ba cika aiki yasa Saratu ɗauke fuskar Falmata da marin da ya sata ja baya ta dafe kunci tana zaro idanu tace "Kai kai kai kai! Kika maren..."
Rarumarta Saratu tayi suka kacame da kokawa tamkar yan dambe, wannan hayaniya ita ta fito da dattijuwar mai kamala ta fito daga d'akinta, ganin wannan tashin hankali yasa ta girgiza kai cikin sanyin jiki tace "Yanzu fisabilillah ba zaku bari garin ya k'arasa wayewa ba?"
Maganar Hajia *Umma* ce tasa Hawa'u dake tafasa shayin da ta saba sha da safe ta lek'o tana fad'in "Hajian sama (sunan da suke kiranta da shi kenan) da ma baki ba kanki wahala ba, tunda ya zama sabansu ki barsu kawai, tunda mai gidan na nan ai ya tsawatar musu."
Taɓe baki Hajia Umma tayi ta juya ta koma d'akinta bayan tace "Allah ya sawaƙe." Ita ma madafar ta koma ta ci gaba da aikinta.
Cizon da Falmata ta yankawa Saratu ne yasa Saratu fashewa da ihu tana faɗin "Kai kai! Inna lillahi! Ta kasheni, hannuna hannuna..."
Ihun ta ne yasa yaran gidan da basu da nauyin bacci fara fitowa daga ɗakunansu daga ciki har da samari da ɗakinsu ke sama, wani tangaren dake kan teburin tsakiyar d'akin Falmata ta d'auka da wahala ta kai mata saboda zaman kujera da Saratu ta mata tana shirin buga mata a kai yasa matashin da bai wuce shekara sha bakwai ba ruguwo da gudu ya riƙe hannun Falmatar yana fad'in "A'a aunty..."
Cikin dubara ya samu Saratu ta ɗagata tana huci da fad'in "Dan ubanki, gobe ma ki k'ara shiga sabgata."
Matashiyar da ta kama Falmata ta tashi tsaye ne ta harari Saratun tace "Gaskiya bana son wannan abun, sai ka ce wata jaka aka kawo miki, wannan ai cin zali ne."
Cike da gargaɗi Saratu ta nunata da yatsa tace "Ke *Safna* fita a harkata, uwarki ma..."
Wata kyakyawar matashiya da za ta kai shekara sha biyar ce ta matso tana fad'in "A'a Mama barni da ita, ai ba ke ce sa'anta ba ni ce nan."
Sai kuma ta kalli Safna tace "Wallahi kisan me zaki dinga fadawa mahaifiyata, idan ba haka na yanzun nan kema zan yi ƙasa-ƙasa dake, ƙarshe ambulance ce za ta kwasheku ke da uwar ta ki."
A zafafe Falmata tayi kan *Surayya* tace "In ban ci ubanki a nan ba ki tsine min albarka..."
Tareta Saratu tayi tana fad'in "Ni ce daidai dake ba ƴata ba."
*Mubin* da *Mubina* da basu fi shekara shida ba ne suka fara tafi a bayansu suna tsale suna fad'in "Yawwa ku casu mata ku casu, ku casu ba mai rabaku, ku casu mata ku casu, ku casu ba mai rabaku..."
*Ameera* ma tayasu tayi suna ta tsalle da waƙarsu, wannan hayaniyar uta ce ta hana mai gidan bacci har ya taso ranshi a matuƙar ɓace ya nufo falon, yana buɗe ƙofar d'akinshi kowa ya yi shiru inda yaran suka zuba a guje suka koma dakunansu.
Safna da Surayya ya tsura ma idanu da suka yi alamar za su dambatu suma akan iyayen nasu, sai kuma ya daka musu tsawa da "Muza ku wuce ku bani wuri."
Da sauri suka kama hanyar komawa ɗakinsu kowace na hararen ƴar uwarta, Saratu ce ta fara sadda kanta ƙasa tana shafa hannunta da har yayi ɗan jini saboda cizon da ta mata tana yatsina fuska saboda sai yanzu take jin raɗaɗin na ratsata.
Daga inda ba tare da ya matso kusansu ba yaa hassale sosai ya shiga nunosu da hannu yana fad'in "Har abada ku ba za ku yi hankali ba, kullum girma kuke kuna cin ƙasa, ku kenan kullum a masifa kuke, a waje na wuni ina fafutuka da mutane da lebarori, da dare zuwa safiya ɓacin ranku ya nemi kasheni, da wane kuke so na ji? Da matsalolin dake gabana ko da bak'ar masifarku?"
Da sauri Falmata ta nuna Saratu kamar za ta yi kuka tace "Ita ce fa Alhaji daga s..."
A mugun tsawace yace "Dallah yi min shiru, sam baku san kunyi hankali ba, da yaranku da komai amma kuna abu kamar yau aka haifeku, ku ko kunya ma ba kwa ji gaban ƴaƴanku kuna irin wannan?"
Gunguni Falmata ta dinga yi tana sadda kanta da satar hararan Saratu da ita dai ta ja baki tayi shiru dan ta fi Falmata saninshi tunda ita ta fara zuwa gidan kafin Hawa'u ma sannan Falmatar.
Maida kallonshi yayi ga Saratu da jin haushi yace" Ke ma babbar banza, da baki damu da miji ba, haka jiya kika baroni a d'akin saboda ke an miki ba daidai ba, yanzu wace tsiyar kika tanadar min to?"
Cike da danne abinda ke ranta ta d'an kalleshi tace" Alhaji me ye to na sai kayi wannan maganar a gabanta? Kuma fa fitowata kenan zan je na haɗa maka abun karin kumallo wannan matar ta tareni da masifa."
Sama da ƙasa ya harareta sannan ya juya ya shigr d'akin ya rufo k'ofarshi, ta gaban Falmata ta je bi tare da bangajeta har saida tayi baya kamar za ta faɗi tare da jan tsaki, Falmata kam murmushi tayi tace" Uhummm! Ashe ma ba'a d'akin mijin aka kwana ba, an rako mata duniya dai da ba'a san yadda za'a yi a tarairayi miji ba, mtsssss!"
Ta ja tsaki tare da nufa nata d'akin tana jin ba ma yau za ta je su yi maganar da take son su yi ba sai ranar kwananta za ta yi kissa ta karb'i kud'ad'en a hannunshi.
Da ɗan sauri ya fito yana amsa wayar dake kunnenshi da cewa" Shikenan Nasiru gani nan zuwa, ina zuwa ynzu su jirani, ka buɗe musu wurin su zauna kafin na zo."
D'akin uwar gidansa ya fara shiga da sallama ta amsa mishi tana mik'ewa tsaye, da yanayi na gaggawa yace" Da fatan dai kun tashi lafiya?"
Kallonshi tayi tace" Lafiya lau Alhaji, ka zauna mana."
Maɓallin rigarshi ya fara ɓallawa yace" A'a ina sauri ne, akwai wani abu ne?"
A nutse ta ci gaba da kallonshi tace" Ba komai, Allah ya tsare ya bada sa'a."
" Ameen." Ya fad'a yana juyawa zai fita, a hankali tace" Sai dai kuma..."
Juyowa yayi yana kaiwa bakin k'ofar yace" Sai dai kuma me? Ina ce kin ce ba komai? Kin san fa sauri nake baki ne suke jirana a mall."
Ganin kamar za ta takura masa ƙarshe ta fad'a masa abinda ke damunta ya gaza fahimta su tashi baram-baram ko kuma ma ya ma abun d'aukar sakaina kashi yasa tace" To shikenan, a dawo lafiya, idan ka dawo ma yi maganar."
"To." Ya faɗa yana ficewa a d'akin, d'akin Hawa'u ya bud'a sai dai ganin yaranta ƙanana ne ke bacci ita bata d'akin yasa ya mayar ya rufe ya nufi hanyar fita, sam ba zai shiga d'akin Falmata ba dan kuwa sun hassalashi a safiyar nan, dan haka ba zai kulasu ba.
Yana daf da fita daga falon Hawa'u da ta fito rike da flask d'in ta tace "Alhaji."
Juyowa yayi suna had'a idanu yace "Oh! Ashe kina nan? Na d'auka kin fita ai."
Murmushi tayi tana matsawa kusanshi tace "A'a Alhaji, tunda safe haka?"
Taɓe baki yayi dan shi dai ya san idan ta tashi yawonta wane lokaci ne bata fita? Tunda ya ga sun fara aron wata ɗabi'a ta satar hanya su fita a gidan bai sani ba ya ba kowace damar fita ta je ko babu izininshi indai abinda ya shafi rasuwa ko dubiya ne, amma sai ya zamana kullum cikin ce wa suke sun tafi gaisuwa da dubiya asibiti ko gida.
Hawa'u dake kallonshi da mamaki tace "Amma Alhaji za ka fita baka karya ba?"
Yatsina baki yayi kad'an ya shafi tumbinshi da ya fito ba dan ya k'oshi ba sai dan haka yake yanzun yace "Idan na fita na ci, ina da baki ne dake jirana."
Murmushi tayia b'oye dan tana hango sabon bala'in da Saratu za ta surfa idan ta ji labarin ya fita, bayan ta barota a madafar tana ta tashin hankali d'anyen k'wai tana soyawa da bredi, dariyar ƙetar da take ce ta sa har ya ficewarshi ba ta ma sani ba, saida ta ankara ne sannan ta d'aga muryarta don Saratu ta ji tace "To Alhajina a dawo lafiya, Allah ya tsare min ya dawo min da kai lafi..."
Fitowar Saratu da gudu gudu yasa suka had'a idanu sai kuma ta kalli flask d'in ta tana kara riketa jim a hannunta ta wucewa tana fad'in "Alhaji kenan, kullum kai da kawo duk don mu, Allah dai ya biyaka."
Da yanayi na raini da rashin bata darajarta ta mutum Saratu ta bita da wani kallo tace "Ke ya fita ne?"
A hankali Hawa'u ta juyo ta kalleta sama da ƙasa sannan tace "Ki tambayi wacce kika aje."
Juyawa tayi ta cigaba da tafyarta, ƙwafa Saratu tayi tace "Zan kamaki ne munafukar banza."
Tana shigewa d'akinta Falmata da ta ita ma sallamar da Hawa'u tayi ce tasa ta leƙowa, ganin Saratu na kumbura za ga koma madafa yasa ta yo mata gwalo ta fashe da dariya tace "Wuuuuu! Ba kwanan d'akin miji kuma bai ci abincin ba, sai ki ci kayan..."
Ganin Saratu ta yi kanta da gudu yasa ta rufe d'akinta tana k'yalk'yala dariya, haushi kam kamar za ta fashe, komawa madafar tayi ta kashe gas d'in tana fad'in "Sai dai uban kowa ya wuni da yunwa, wallahi kai da nake zaune dominka ba ka ci ba dan haka ba wanda zan b'ata lokacina wajen girma su ci."
*Gidan Alhaji Mudassir kenan*
_______________
A ƙalla awa ɗaya da rabi kenan yana tsaye bakin k'ofar band'akin riƙe da towel, a karo na ba adadi ya sake k'wank'wasawa a matuƙar sanyaye cike da ladabi yace "Mama am, dan Allah ki fito hakanan, za ku makara da cin abinci."
Har yanzu dai k'arar saukar ruwa ke tashi a band'akin, a hankali ya ɗora goshinshi a jikin k'ofar yana sauke numfashi a hankali, " *buppppp!*" Ƙarar faɗuwar robar shampoo d'in da ya ji yasa shi zabura daga tsaye ya k'urawa band'akin idanu, dafe saitin zuciyarshi ya yi ya k'ara maida goshinshi a k'ofar yace "Mama am, dan Allah ki fito, idan ba zaki fito ba ki saka tufafinki ni sai na shigo."
Sai yanzu kadai daga cikin band'akin wata murya k'asa k'asa aka dinga wasu maganganu da duk da yana ji amma bai san me take fad'a ba, juyawa ya yi da nufin zaunawa bakin gadon ya ci gaba da jira, sai kuma wayarshi da ke aljihu ta fara zittttt! Ziiiiit! A nutse ya ciro wayar yana dubawa ya danna ok ya d'ora a kunne tare da fad'in "Assalama alaika."
Daga can b'angaren aka amsa da "Wa'alaika salam, yallab'ai..." Sai kuma ya yi shiru, dafe k'ugunshi yayi da hannun dake riƙe da towel yace "Ina jinka *Muzaffar*."
Cikin ladabi yace "Yallab'ai dama akan baƙin nan ne da suka zo, har sun fara k'osawa wallahi suna cewa za su tafi, shine na ce su d'an dakata na sake kira."
Ajiyar zuciya ya sauke ya juya ya kalli k'ofar band'akin yace "Muzaffar, Mama am ce a band'akin daga wanka har yanzu ba ta fito ba, ina ta magana amma ta shareni, ina tsoron kar a ce hushi take dani, saboda jiya na mata alk'awarin zan kaita k'auye..."
Girgiza kai yayi cike da damuwa ya d'auke hannunshi ya shafi gemunshi yace" Sai ta fito na mata duk abinda na saba yi sannan zan fito, idan ba zasu iya jira ba su tafi kawai, Allah ya kawo mana halalinmu har inda muke."
Da ɗan ɗaga sauti Muzaffar yace" Me? Yallab'ai ka kuwa san irin asarar da hakan zai janyo mana?"
Shima ɗan d'aga muryar yayi dan ya fargar dashi ta hanyar fad'in" Muzaffar."
Da sauri Muzaffar yace" Ka gafarceni yallab'ai, kada mu bari mu yi asarar kasuwanci da mutanen nan, a k'alla fa suna son carton na top bond sama da guda d'ari biyar, kuma mu suke so mu kawo musu, sannan..."
A tsorace tare da zazzaro idanu ya juya ya kalli band'akin ya furta" Muzaffar Mama am, ina zuwa..."
Da gudu ya nufi band'akin ya kama hannun k'ofar ya lumshe idanu, a zuciyarshi ya ambaci" Mama am ki gafarceni."
Tura k'ofar yayi tare da wara idanunshi yana son ganin fashewar madubinda ya ji yanzun, a hanzarce ya k'arasa gabanta ya durƙusa tare da warware towel ɗin ya rufa mata a jiki dan babu komai a jikinta, saida ya gama rufa mata sannan ya yatsina fuskarshi hawaye na cicciko masa idanu, kallon fuskarta yayi ita ma kallon k'afarta take yi da take zubar da jini daga saman saboda madubin daya yanketa.
Duƙar da kanshi ya sake yi sosai ya matso hawayen da suke ta tururuwar fitowa daga idanunshi ya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!"
Sai kuma ya sake kallon dattijuwar yana rik'o kafar ta ta yace "Mama am laifina ne, ki gafarceni dan Allah, sakaci na ne, me yasa zan saka madubi a wurin wankanki? Mama am ki yafe min."
Sai kuma ya ja majina ya miƙe tsaye da sauri ya kamata cike da kulawa yace "Muje mama am, muje asibiti."
Tirjewa tayi tare da banka masa harara ta cinno bakinta gabanta tace "Sakeni."
Girgiza kai yayi tamkar k'aramin yaron da za'a k'wacewa alawa yana sako da wasu hawayen yace "Um um! Mama am, muje dan Allah."
Ba ta sake tirjewa ba sai binshi da tayi tana wasu surutai, bakin gado ya zaunar da ita ya nufi wajen wata drower ya ɗauko akwatin magani ya dawo ya durƙusa gabanta, a nutse ya kamo k'afarta ya d'ora a kan cinyarshi dake rufe da wando kalar ruwan k'asa na yadi mai santsi, buɗe akwatin yayi ya d'auki kaɗa da alcol yq ɗan ɗiga a kaɗar sannan ya kalli fuskarta yadda ta kafe fuskarshi da idanu, murmushi ya sakar mata yace "Yawwa Mama am, ki ci gaba da kallon fuskata haka."
A hankali ya shiga goge mata ciwon da alcol amma ba ta nuna jin zafi ba sai dai tana ɗan mitsika k'afar ta ta dake kan cinyarshi, yana gamawa ya sake duban ciwon, yanka ne sai dai ba wani babba ba, a haka ya naɗe mata shi da bandeji sannan ya sauke k'afar a hankali ya ɗauko ruwa ya dawo kusanta.
Ibuprofen ya ɓalla guda biyu ya bata ba musu ta bud'a bakinta ta karɓa sannan ya miƙa mata ruwa tasha, d'auke kayan yayi ya mayar sannan da sauri ya ɗauko mata wani rantsatsen leshe kalar fari da kore, doguwar riga ce kamar dai yadda ya fi son d'inkinta ya kasance saboda larurar rashin lafiyarta, saida ya fara taimaka mata ta saka dogon wandon yadi mai taushi daga ciki fari sannan ya zura mata rigar, wani irin ɗaurin d'an kwali ya mata mai sauk'i wanda zai dace da saka hijabi sannan ya saka mata hijabin fari, takalmi masu kyau ya aje mata ta saka sannan ya feshe mata jikinta da turare suka fita.
*Alhamdulillah.*