Free chapter · Read without an account
Remark
by Hawwa__B__Kumo · MAKTOUB!
💠💠💠💠💠
©®2020.
*♡MAKTOUB¸.•💥*
((Dᴱƈᴱᴘᵀɪᵛᴱ Lᴼᵛᴱ))
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
*Wattpad link:* ***
*For u habibtiiys ♥ My REAL HAFSY & MAMAH ZEE 😍,kuji dad'in ku ahabbakum-thiir²..*
🆓 Pᴀɢᴇ..
🅿»6⃣
#Rᴇᴍᴀʀᴋ
"Innalillahi! Ya Allah! Ya rabbi! Ya salaam!" Was the first words da suka zo bakinta a mugun tsorace ta fara k'ok'arin gangarawa gefe kamar yadda motar data daka yayi,Badriyah dake gefenta ta zaro ido ganin Ismat kamar za tayi kuka a rikice tace "Sweetheart mene haka kika yi?" D'auke kai Ismat tayi hurriedly ta zare belt tana k'ok'arin fita daga motar,da sauri itama Badriyah ta bud'e side d'inta ta fita da niyyar suje tare su bama mai motar hak'uri kamar yadda Ismat take niyya,suna gama fitowa Ismat bata yarda ta kalli Badriyah ba suka fara tafiya,shi kam mai motar ma yana gama fahimtar abunda suke niyyar yi bai jira sun k'araso ba ya tada motarsa ya barsu nan tsaye,da mamaki ko fitowa ya duba b'arnar da suka masa bai yi ba yayi tafiyarsa,Badriyah dama tana ganin haka ta tab'e baki tace "ka kyauta ma kanka" sai ta juya ta rik'e hannun Ismat tace "let's go" a hankali Ismat ta juya suka fara tafiya hankalinta duk ya tashi ganin ta yi masa b'arna bai tsaya ko hak'uri ta bashi ba ya tafi,a sanyaye ta dunga bin Badriyah,suna zuwa Badriyah ta shigar da ita mota,then tayi changing nata ita ta koma driver seat,tana tada motar kuwa tace "dawa Allah ya had'a ni ba da titi ba" nan ta fara sharara gudu,ba'a yi taking long ba suka k'araso get d'in new side,lokacin da suka shigo arean faculty d'insu bayan Badriyah ta yi parking suna fitowa za su wuce,Ismat ta d'aga kai za tayi magana idanunta suka sauka kan motar da suka bugawa babu jimawa,ta kalla tana ware idanu da sauri tace "habibtiiy look here!" Badriyah tana d'aukar handbag d'inta a back seat tace "what?" Ismat tace "motar da muka buga yanzun a hanya" da sauri Badriyah ta juya tana kallon inda take nuna mata,a hankali kuma ta d'auke kai tace "Ohh! I see" Ismat ta marairaice tace "kou muje yanzun mu basa hakur'in?" Zaro ido Badriyah tayi tana kad'a kai tace "ni kinga babu inda zanje,thought munyi niyyar ba shi hakur'in tun farkon da muka yi masa laifin,tunda ya nuna bai buk'ata why yanzun za muje? Kawai ki wuce mu tafi idan ba so kike muyi missing test ba" rau² idanun Ismat tayi tace "please habibtiiy" bata k'arasa ba Badriyah ta fizgi hannunta tace "Allah babu inda za mu,ki wuce kawai muje" babu yadda ta iya da halin Badriyah haka dole ta wuce tana binta sai waigen motar take yi har suka shige cikin faculty d'in. 7:00am Ya gama shirin fita cikin k'ananun outfit,black trouser with white slong sleeve sai suspenders (Garter belt) da ya kawo bak'i ya saka a saman shoulders d'insa ya ratso da shi ya mak'ale down to the front of his trouser,a hankali ya dunga kallon kansa ta cikin magnifying mirror da yake tsaye gabansa,kusan mintuna biyu ya d'auka a haka duk ji yake ba ya son zuwa but ya zaiyi tunda Daddy yayi maganar kuma itama Mami ta sa baki,dole haka zai yi hak'uri yaje tunda FADL d'in ma ba ya k'asar duka,and da ya dawo kuma shirye²n bikinsa ake magana dan yanzun abunda ya rage kai kayan lefe ne kad'ai,sannan kuma ya ji Daddy yana batun Fadl d'inma da matarsa a satin da aka gama biki za su bar Nigeria,har ya kammala shirin fuskarsa babu wani isashen walwala,yana gamawa ya juya yana gyara wuyan rigarsa da ya bar button d'aya bai rufe ba,ya d'auki sauran kayansa da ya bari ya fice ransa duk babu dad'i dan yadda ya tsani koyarwa shi a rayuwarsa sam bai ga dalilin ma da Daddy zaice sai shi ne zai je ya taking abunda Fadl d'in yake yi ba,kai tsaye apartment d'in iyayensan ya nufa bayan fitowarsa,yadda iska yake kad'a kyakykyawan gashin kansa abun gwanin burgewa,da yake fitowarsa kenan bai saka glasses ba sai yayi wani masifaffen kyau,he look so charming and breathe taken,yana tafiya hannunsa d'aya rataye da jakar laptop d'insa d'ayan kuma zube cikin pocket na jean d'insa,yana shigowa apartment d'in bai wani dad'e sosai ba ya yiwa Mami sallama,kyakykyawar matar da idan ba wanda ya sani ba bazai tab'a cewa ita ta haife shi ba saboda kyaun jiki da Allah yayi mata tayi masa addu'o'in fatan alkhairi,har ya juya zai fita Mami tace "but kayi breakfast za ka fita?" A hankali yana ci gaba da tafiya yace "No! Zan ci idan na fito daga class" tace "alright! Allah tsare min kai baby,kada ka manta ka ci abinci kana fitowa kada yunwa ya makamin kai" d'an murmushin gefe ya saki wanda ya k'arawa fuskarsa matuk'ar kyau,dimple d'insa dake side ya lotsa,a hankali cikin husky voice yace "sai na dawo Mami na" tace "Allah tsare hanya" yace "Ameen" then ya fita da sauri saboda ganin lokaci ya fara tafiya,yana fitowa wajen motar da yasa a fito masa da shi ya nufa wani sabon Mercedes benz C300 bak'i da bai tab'a hawa ba sai shek'in sabunta yake yi,kafin ya k'araso Bala dake aikin rage flowers ya ajiye scissors ya nufosa da sauri yana fad'in "Barka da fitowa Yallab'ai" Aadil ya kalleshi kad'an da gray eyes d'insa wanda hasken farar rigarsa ya mayar da su wasu iri sai suka sake yin haske da kyau,ya amsa yana kallon wristwatch d'insa,Bala ya mik'a hannu yace "Kawo a kai maka" kai ya d'an girgiza yace "No! Thanks,je kayi aikinka" Bala yayi murmushi yace "Allah ya tsare hanya" Aadil ya d'anyi taking step forward slowly ya zaro hannu daga pocket yace "Take" quickly Bala ya k'araso ya karb'i kud'in da Aadil yake mik'o masa,ya fara jero masa godiya da addu'o'i,ya wuce ya barshi nan tsaye,yana tafiya Bala ya duba k'udi yaga 5k yayi murmushi yana godiya ga Allah dama ba shi da k'udi tashinsa da safen,ga matsalar rashin lafiyar mahaifiyarsa,ciwon k'afa yasa daren ranar ma da kyar tayi bacci sai da aka rok'o aboniki a mak'ota aka shafa mata sannan suka d'an samu sauk'i,ai kuwa ya tura kud'insa a aljihu da sauri ya d'auki scissors ya ci gaba da aikinsa cikin walwala da jin dad'i,yana aiki yana sake jerowa Aadil d'in addu'o'in fatan alkhairi,saboda Aadil ya kasance wani irin mutum mai yawan alkhairi,lokuta da yawa idan zai yi kyauta baka sanin zai baka sai dai kawai kaji yace "Karb'i",sannan yana da saurin fahimtar damuwar mutane,ko yaya yaga fuskar wani cikin hadiman gidansu ya sauya duk da ba shi da yawan magana,sannan baya damuwa yasan matsalar dake damunka matukar ba kai ka fad'a masa ba but yana k'ok'ari yaga ya sanya murmushi akan fuskarka,wannan d'abi'ar tasa tun yarinta a haka ya taso,and halayyar Proff Junayd kenan,kusan komai na daga kyawawan halayensa da rashin son magana duk gadon su yayi a gurin mahaifin nasa. Ko a get ma da zai fita bayan Malam Jibrilla ya bud'e masa get,kafin ya bar gidan sai da yayi masa alkhairi then yaja motarsa ya bar gidan,tafiyar mintuna kad'an yayi bai wani jima da fitowa daga cikin unguwar rijiyar zaki ba yana tafiya kan titi wani mota ya daki nasa,a hankali ya gangara gefen titi da niyyar ya duba matsalar da aka samu,sai yaga motar ta biyo bayansa,tunda ya tsaya da yake nasa glasses d'in masu duhu ne yayi zamansa yak'i fitowa,almost 5 minutes ya d'auka zaune yana kallon motar da ya parker nesa da shi kad'an,ai kuwa yana ganin y'an matan biyu suna fitowa hankalin wacce ke driven d'in a d'an tashe,da ya nutsu yaga duk ma yara ne and kamar akwai inda suke niyyar zuwa suna sauri kawai sai bai tsaya ba ya ja motarsa yayi gaba,yana kallon yadda fuskarta tayi alamun bata ji dad'i ba ya tab'e baki ya taka motarsa da mugun gudu ya barsu tsaye a wajen. Har ya shiga New side abunda ya faru bai wani dameshi ba dan shi bai ma fito ba bare yaga mene ne matsalar da aka samu? A gaban faculty of science ya parker motarsa daga gefe,haka kawai bayan tsayawarsa a gurin yaji bari ya d'an zauna kad'an ya b'ata wasu mintuna though yana matuk'ar mutunta lokaci a rayuwarsa but ya san idan ya shiga lecture yanzun wasu a cikin d'alibai ko hanyar tahowa makarantar ma basu kama ba,yana nan a zaune cikin mota,motar su Ismat yazo wajen ya tsaya,shi duk bai ma kula da zuwansu ba,har suka gama rigimar su ita da Badriyah akan zuwa su bashi hak'uri Badriyah ta janyeta suka wuce,suna barin wajen ko minti guda ba'a k'ara ba ya ajiye iPad d'in hannunsa da yake clicking,a hankali ya juya ya d'auki glasses d'insa mai duhu ya saka then ya fito ya rufe motar,cikin wani irin takun nutsuwa yake tafiya hannunsa rik'e car key d'insa,ya wuce zuwa theatre da yaga nan ne venue a jikin timetable da Daddy ya bashi,tunda ya fito yana tafiya duk inda ya bi kallonsa ake ba mata kad'ai ba hatta samari masu ji da gayu da aji binsa suke da kallo suna yaba tsarin halitta da kyaun wannan halittar ta Ubangiji,yana shiga theatre muryarsa a low tone yayi sallama,wad'anda suka fahimci abunda yayi suka amsa,direct ya wuce saman deck ya tsaya yana kallon students d'insa da suka bishi da wani kallon mamaki,abun haushi yana tsaye wajen wasu har lek'owa suke su sake ganinsa,ni dai nace (an fad'i ba nauyi,mutane dai suna fama da rashin class,kawai suyi ta jawowa ana zaginmu ana cewa y'an ghetto area ne,al'halin su kansu masu kud'in idan sunga abun kallo kalla suke,ko da kuwa talaka ne yazo wucewa sai kaga sun bisa da kallon k'asan ido na munafirci duk dan ace wai basu kalla ba,nan kuwa sun gama kallewa ma tuni..Lol) Since ya tsaya gurin duka theatre ya d'auki wani irin shiru na musamman kowa jira yake yaji me zai ce,ai kuwa ya sake gyara tsayuwarsa for the second time ganin anyi tsit shi kad'ai ake saurare aji daga bakinsa,yayi gesturing face yana tura hannunsa d'aya cikin pocket da wannan husky voice d'insa ya fara gabatar da kansa cikin tsadadden pure turancinsa kamar baturen k'asar amuruka,as he introduced his name *AADIL JUNAYD MUTALLAB* gaban Ismat yayi wani fad'uwar da ta rasa dalili,gaba d'aya ma ita ko ido ta kasa d'agawa ta kalli direction d'insa but kunnuwanta duka suna gurin tana saurarensa tsab,while a gefe d'aya kuma since ya fara magana Badriyah ta d'ago itama sau d'aya ta kalleshi ta tab'e baki bata yarda ta sake kallonsa ba ta ci gaba da clicking wayarta,even though a sahun gaba suke zaune but hakan bai wani dameta ba,Ismat dai ta yi k'ok'ari ta mayar da hankalinta tana sauraren duk abunda yake fad'a,yana gama introducing kansa ya juya kad'an rik'e da marker then ya fara musu tambayoyi game da abunda suka yi a baya kafin tafiyar *Dr FADL JUNAYD MUTALLAB* his elder brother kenan,ya samu dai an bashi amsar tambayoyinsa sosai,hakan da suka yi kuma sai ya k'ara masa k'warin guiwa,cikin abunda bai wuce mintuna da zuwansa ba after sun gama tattauna abunda ya gabata yace "Topic d'inmu na yau za muyi sa ne akan rainon ciki da irin matakan da suka dace mahaifiya ta kula da su saboda muhimmancinsu a fagen kare lafiyar jiki da ruhin yaron da zata haifa" kowa ya nutsu yana saurarensa banda Badriyah da ta mayar da hankali kan phone kad'an² take d'aga kai ta saurara,a nutse ya furta "Idan baku manta ba a lectures d'inku da ya gabata,though ba ni nayi muku ba,na san Dr yayi bayani kan batun rainon ciki ne da matakan da suka dace mahaifiya ta kula da su saboda muhimmancinsu a fagen kare lafiyar jiki da na ruhin yaron da zata haifa gami da gargad'i kan nisantar munanan dabi'u ciki har da nisantar cin abincin haram,hak'ik'a addinin Musulunci ya jaddada muhimmancin lura tare da tantance tsakanin abincin halal da na haram domin tasirin kowanne daga cikinsu a fagen tarbiyyar mutum. Ya zo cikin tarihi cewa:Imam Husaini (R.A) yana fayyace dalilin k'iyayya da gabar mak'iyansa a kan iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka da cewa:"Su cikin cikinsu ne da haramun don haka (haram) ya lullub'e musu zuk'ata,sakamakon haka ba zasu karb'i gaskiya ko saurararta ba." Abincin haram yana da mummunan tasiri a kan tsatson mutum,daga cikin fitattun malaman tarbiyya da kyawawan dabi'u wani malami yayi bayani kan tasirin abinci da cewa:"Hak'ik'a abincin halal da ke taimakawa wajen samar da maniyyi yana gagarumin tasiri na ban mamaki a kan kyakykyawar tarbiyyan yaron da za a haifa da wannan maniyyi. Kamar yadda abincin haram yake da mummunan tasiri wajen gurb'ata tarbiyyan yaron da za a haifa da wannan maniyyi,yana mai fayyace cewa:"Abincin haram da dukiyar haram sun fi muni a kan duk wata gobara,kuma matuk'ar maniyyin yaro ya samo asali ne daga abincin haram,to lallai shiriyarsa lamari ne mai cike da tarin matsala." Wasu suke cewa:An ce wa wani mutum bawan Allah mai daraja cewa:"Lallai d'anka ba ya da tarbiyya! Sai ya ce:"mene ne ya aikata?" Sai aka ce masa:"mai dakon ruwa yana d'auke da jakar fata da ake d'ibar ruwa ciki a kan kafad'arsa,yana cikin tafiya sai d'anka ya soka allura a jakar fatar,lamarin da yayi sanadiyyar hujewar fatar tare da zubar ruwan da ke ciki." Sai wannan mutum mai daraja ya yi tsananin fushi kuma ya d'auki matakin titsiye matarsa,sai matar ta shiga cikin damuwa,tace "lallai babu mamaki." Cikin mamaki wannan mutum ke cewa:"Don mene ne babu mamaki? Sai matar ke cewa:"A lokacin da nake d'auke da cikinsa na zauna a k'ark'ashin wata bishiyar ruman mallakin wasu mutane,bayan da sha'awar ruman d'in ta kama ni,sai na d'auki matakin huda ruman guda da allura inda na sha ruwan ta wannan kafar da na huda." Sakamakon laifin huda ruman d'in mutane tare da shan ruwanta ba da izini ba,shi ne tasirin wannan laifi ya wurga d'ana cikin wannan mummunar dabi'a ta huda jakar ruwan mutane." 'Daya daga cikin muhimman al'amuran da suke kara gadarwa jariri kwanciyar hankali da nutsuwa a cikin mahaifiyarsa shi ne:Mace mai d'auke da juna biyu ta kasance a cikin kwanciyar hankali da nutsuwar ruhi,hak'ik'a matuk'ar mace mai juna biyu tana cikin damuwa da tashin hankali musamman na ruhi,hakan yana yin mummunan tasiri a kan jaririn da ke cikinta musamman a rayuwarsa bayan zuwansa duniya. Wannan fad'akarwa tana da tushe a shari'ar musulunci,kamar yadda bincike na ilimin zamani ya tabbatar da hakan. A b'angare guda kuma gwargwadon irin matakin da mace mai juna biyu ta d'auka na nisantar ayyukan laifi da munanan dabi'u,kwatankwacin irin kwanciyar hankali da nutsuwa gami da tsarkin rayuwa da jaririnta da ke cikinta zai samu a rayuwarsa ta nan gaba a bayan haihuwarsa kenan. Har ila yau d'aya daga cikin al'amura masu tasiri a fagen gadar da kwanciyar hankali da nutsuwa ga jariri a cikin mahaifiyarsa shi ne:Irin mutanen da mace mai ciki take rayuwa tare da su a k'ark'ashin inuwa guda,gwargwadon irin matakin da mutanen da suke rayuwa da mace mai ciki suka faranta mata rai a irin hirarrakin da suke gudanarwa da ita,kwatankwacin irin kyakykyawar tasirin da hakan zai yi a kan jaririn da ke cikinta,kamar haka ne idan mace mai d'auke da juna biyu tana zama da mutanen banza masu furta munanan maganganu ko take halartar wuraren batsa da alfasha,hakan zai iya yin mummunar tasiri a kan jaririn da ke cikinta a bayan zuwansa duniya. An ruwaito hadisi daga Annabi (S.A.W) yana bayyana cewa:"Maganganun abokin zama na gari,kamar misalin mai sayar da turare ne,idan har bai yayyafa maka turaren ba,to duk da haka zaka amfana daga k'amshin turaren,haka nan maganganun abokin zama mutumin banza,kamar mak'eri ne,idan har tartsatsin wutar k'irarsa bai k'ona ka ba,to mummunan warin wutar k'irar zai yi tasiri a kanka." Sakamakon haka dole ne a kan mace mai juna biyu ta d'auki matakin kiyaye hukunce²n shari'a ta hanyar nisantar ayyukan laifi da suke haramun gwargwadon iyawarta ciki har da furta munanan maganganu da suke matsayin alfasha tare da nisantar da kanta daga majalisin gulmace² da yi da mutane. Hak'ik'a matakin gudanar da addu'o'i da zikirin Allah suna da gagarumin tasiri a kan cikan lafiya da amincin jaririn da mace mai juna biyu ke d'auke da shi. Tabbas mace mai juna biyu kamar mai jihadi ne a tafarkin Allah da addu'arta ke saurin karb'uwa a wajen Allah mad'aukaki,hak'ik'a gudanar da addu'ah da neman buk'atu a wajen Allah suna daga cikin mad'aukakin matsayi da ke fayyace kasantuwar mutum a matsayin hak'ik'anin bawa ga Allah,kamar yadda ya zo cikin Suratul-Furk'an a aya ta 77 cewa:"Kace Ubangijina ba zai kula da kuba,ba domin addu'arku ba." Sakamakon haka ya zama dole a kan mahaifiya matuk'ar tana buk'atar zuri'ah ta gari da y'ay'a masu kyawawan dabi'u ta kasance ta zage dantse tare da dawwama a kan addu'ah da neman kusanci a wajen Allah. D'aya daga cikin irin wad'annan addu'o'i shi ne kamar yadda ya zo cikin alk'ur'ani mai girma Suratu-aali imraan aya ta 38 cewa:"Ya Ubangiji ka azurta ni daga gare ka zuriya tsarkakakkiya,hak'ik'a kai mai karb'ar addu'ah ne." Har ila yau a cikin Suratul-Furqan aya ta 74 Allah yana cewa:"Kuma wad'anda suke cewa "Ya Ubangijinmu! Ka ba mu sanyin idanu daga matanmu da zuri'ar mu,kuma ka sanya mu abun koyi ga masu tsoronka." Hakika mahaifa miji da mata za su iya kiyaye irin wad'annan addu'o'i da suka zo cikin alqur'ani wajen rok'on Allah kan ya azurta su da yara nagari masu k'oshin lafiya da cikar halitta.." Wani irin tafi gaba d'aya theater ya d'auka saboda yadda bayanin da yayi ya masifar shiga zuk'atan students d'insa,but duk da hakan abun duk bai wani ba shi mamaki ba,haka yayi ta fayyace musu bayanai tare da ayoyi da hadisai cike da k'warewa,gogewa tare da amfani da d'umbin iliminsa,da yake course d'in 3 credit ne duka har lokacinsa yayi babu wanda ya farga,after ya tabbatar babu mai sauran tambaya ya kwashe belongings d'insa ya fice cikin takun isa. K'atuwar ajiyar zuciya Ismat tayi tana d'ago idanunta ta sauke kan Badriyah dake chat abunta hankali kwance,ta jinjina kai a hankali tace "habibtiiy lets go please ina son shan ruwa" amsawa Badriyah tayi a nutse ta mayar da wayar jaka ta mik'e tace "let's go" tashi Ismat tayi suka fito a hankali suna tafiya,wunin ranar duka a skul suka yi shi sai 4pm sannan suka dawo gida a mugun gajiye,Mom kam ita bata dawo daga aiki ba time d'in,haka suka wuce kowa tana fad'in wash,wanka suka fara yi da yake Ismat dama suna shigowa ita ta fara,lokacin tana fitowa ta wuce wajen phone d'inta dake ajiye saman bedside,daga ita sai towel dake d'aure jikinta,his length duka bai wuce cinya ba,ta zauna bakin bed ta kunna network then ta ajiye wayar ta mik'e,gaban mirror ta wuce ta fara murzawa jikinta lotion,ta yi applying chapstick ma lips d'inta,as she finished ta wuce closet d'insu,wani fitinannen crazy jean ta d'auka blue daga cinyarta duk a bud'e kamar an sa abu an yayyankasa,fresh skin na thighs d'inta da yake fara sol a bayyane kana kallo kamar ka tab'a jini ya fito,tasa y'ar k'aramar sleeveless pink da ta kama jikinta mai adon blue d'in flowers ta gaban,gashin kanta kam bata tsaya b'ata lokaci a kansa ba,tana gama gyarawa tasa clips ta matse shi,ta fesa turarukanta masu sanyin dad'i,a hankali ta fara takowa wajen data ajiye phone d'inta,tana d'auka ta wuce a nutse tace "habibtiiy ki same ni parlor please" tana fad'a ta wuce ta fita tana mak'ala earpiece a kunnenta...
#The book *MAKTOUB* isn't for free... It's ₦300,VIPs ₦500.
*HOW TO SUBSCRIBE+PAYMENT DETAILS..*
*1-ACCOUNT DETAILS.*
Acct name-Hauwa Muhammad Usman
Acct number-0060746882
Bank name-Access bank.
*Sai a tura screen shot na shedan biya zuwa ****
*2.MTN RECHARGE CARD/VTU TRANSFER.*
***
*A tura screen shot na shedan biya zuwa ***.*
*3- OTHER WORLD REMITS*
Acct name:Hauwa Muhammad Usman
Acct number:0060746882
Bank name:Access Bank
Phone number:***
City:Kano city.
For any other problem/complain/enquiry chat via ***.
#Share pls.
#Asli Smasher.