Free chapter · Read without an account

Tsokaci

by Sadiya Auwal · BAKAR AYAH

Asslam makaranta barkanku da warhaka,ya bayan haɗuwa.

Na ɗan ɗebi hutu bayan gama littafin MABARACIYAH gashi to mundawo za'a cigaba da aiki.

Tsarin littafin BAƘAR AYAH shine,zamu fara da Littafi na ɗaya,wanda shi kyautane babu ko sisi,sai na biyu wanda zansa kuɗi kaɗan,saboda kowa yasan tsarin littafina. bana saka kuɗi dayawa.

Idan mungama littafin na farko zan tsayah da typing a ko ina,sai iyah AREWABOOK da kuma Paid Group na whatasapp.

Dan haka wanda bayason bata lokaci toya bimu ta arewa book yafi sauƙi.

Zantabo abubuwa da dama a cikin littafin,kama daga Barikin sojoji,abinda yashafi fashi a cikin jeji da kuma bangaren kasuwanci,musamman ma na company.

Dan haka wanda yaga kuskure a cikin yayi min uzuri kana ya gafarceniceni,banyi niyyar yin hakan da wata manufaba.


Masu bukatar karantawa a wattapad da arewa book sai su saka a reading list,sannan dan Allah ayimin follow ɗina,wanda suke a sauran media kuma suyi min magana domin shiga Groups ɗina.

Nagode sosai,ina fatan za'a nishaɗantu kuma a amfana da abinda na rubuta....,.........

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.