Free chapter Β· Read without an account
Part6
A secret writer:ππππππ
WAYE
MAHAIFINA..?
ββββββ
~Written~
~By~
~A secret writer~
A new story by a new writer with a new style.
This is my first novel happy reading...!!!
π Ώ 6
Ranan suna anyi shagali sosai, yan'uwa da abokan arziki sun hallara a wannan biki kasancewar ba'ataba haihuwan tagwaye ba a familyn nasu.
Wasu kam ma sai a lokacin sukaga idon mama saboda lokacin bikin ba ayi wani taroba.
Wannan haihuwa da ummi tayi ya karamata so da kuma bakin jini a idon makiya irinsu umma da mama, saboda Dady ya kashe kudi sosai kamar akansu akafara haihuwa a gidan.
Yakumbo wato mahaifiyar alhaji bayan suna tace bazata koma ba sai jikokinta sunyi kwari, saboda haka sai da ta share wata biyar a gidan kafun ta koma kano.
Wannan abun ya konawa umma rai sosai.
Yanzu shekarun Ummi 4 da aure su hassan kuma sunada shekaru 3 a duniya.
Usman da kuma muktar sa'annin juna ne zan iya cewa kusan a tare aka haifesu Saboda a rana daya aka haifesu sai da dan awannin dake tsakaninsu.
Yanzun haka suna karatu a kasar Egypt dukansu course daya suke karantawa.
Habib kuwa wato kanin Dady yana hada deegree dinsa na biyu a dubai, shi ke turowa yayansa kaya daga can,kasancewar bussiness ya karanta.
Kuma har yanzu baiyyi aure ba.
Ahmad yana tare da shi a dubai shi kuma yana karanta building engineering.
Mustapha kuwa autan umma kenan shi kam a garin kano yake karatu dan yace ba zayyi nesa da gida ba.
Wannan abu da yayi ya bakantawa ummansa rai saboda ta sha fari yan cewa yayanta bazasuyi karatu a nigeria ba.
Shi kuma jin furucin mahaifiyarsa ne yasa yace bazashi ko inaba.
Ba yadda batayi ba kan ya amince yabar kasan amma yaki.
haka ta hakura tunda autan ta ne tanaji dashi.
Yanzun haka yana Part 4 a jami'ar Bayero dake kano.
Khadijah tana aure a abuja da yaranta guda uku.
Amina kuwa tana kaduna da yaranta uku itama.
Hauwa kuma a kano take tanada yara biyu
basma ma tayi aure tana zama a garin kano,kuma har yanzu bata haihu ba.
Ummul-khairi tana yawan zuwa jalingo hakan yasa suka saba da ismat sosai take son maganar ismat din.
Ismat,mimi,ummul-khairi da Afifa wannan shekaran suka zana waec nasu suna jiran result din su.
Wannan hutun a kano sukaje shiyasa gidan yayi shiru.
Mimi ma saboda za suyi musabaqane shiyasa batajeba.
Wannan shine takaitaccen tarihin Ummi.
Kubiyoni don jin ya labarin zata kasance.
CIGBAN LABARI
Sunyi musabaqa cikin nasara,Ismat ce tazo na daya,kuma itace aka zaba wanda zata wakilci garin taraba state a musabaqan da za'ayi na garuruwa baki daya a garin ABUJA.
Result nasu ya fito kuma Alhamdulillahi sun samu sun haye (siradin boko kenan) lol.
Daman kuma sun rubuta jamb.
Cikin lokaci kankani Dady yafara nema musu Admission a BUK harda Afifa batare da yafadawa kowa ba.
Ismat ta gama shirinta tsab saboda saura sati daya su wuce gurin musabaqar da za'ayi, kuma a wannan musabaqarne za azabi wacce zata wakilci nigeria a musabaqan da za'ayi na kasashen duniya a kasr saudi.
Yaune ranan tafiyarsu Ismat saboda gobe zasu fara musabaqan nasu.
Kuma daman ana son mutane uku suyi maka rakiya a cikin ya'uwanka, Sai kuma ma Malamin makarantarku guda daya.
Saboda haka ta tafi Cikin Rakiya Dady, Mimi, da kuma Afifa,saboda Ummi tace bazataba.
Tunda daga can zasu wuce kano.
Daga alkalaminβπ»βπ»βπ»
sabuwar marubuciya