Free chapter 路 Read without an account

PAGE 6

by Gimbiya Ayshu 路 馃尲馃尲馃尲 ZUBAR HAWAYE NA馃尲馃尲馃尲

馃帯馃帯ZUBAR HAWAYE NA馃帯馃帯


STORY AND WRITTEN BY 


AISHA MA'ARUF (GIMBIYA AYSHU) 


ELEGANT ONLINE WRITERS 馃摎


      WHATPAD NAME

      *AISHAMAARUF*


    馃摎馃摎PAID BOOK馃摎馃摎

   


         *FREE PAGE*


PAGE 6


___________________________Fita yayi daga office din dad ya nufi na shi, baifi minti 5 ba ya dawo hannun shi rike da jakan laptop si key din motan shi a dayan hannun. Dad muje yana daukan jakan laptop na dad suka fita a office din, parking space suka nufa, bodyguard na ganin dad suka taso da tsauri, duk gaishe su sukayi da girmamawa, "ina bodyguards dinka suke" hannu yasa yana tsosa keyen shi yana kallon kasa. Dad na ganin haka yayi gaba kawai, bayan motan duk suka shiga, guards biyu a gaba, daya na tuki daya kuma ya zauna a wuin mai zaman banza, sai kuma wani mota a bayan su. Baifi minti 11 ba suka isa direct hall din da za'a gudanar da meeting din suka nufa, suka shiga da sallama suna shiga duk mutanen dake zaune duk tashi suna mai sannu da zuwa hadi da gaisuwa. Amsa dad yayi while Arif ya gaishe su dan duk sun girme shi abokan harkallan dad ne. Kujera suka nufa suka zauna aka fara meeting. Bayan Awa biyu suka fito, ana raha da dariya kowa ya shiga motan shi, duk suka bar wurin. Company suka dawo, a hanyyan su ta dawowa yaga wannan yarinyar a dai-dai inda yasaba ganin ta, kallon ta yake duk hankalin shirt da komi yana tare da ita harda yai ta mishi magana amman shiru. "Kallon inda Arif ya kura na if ido dad yayi, daya Kali wurin sai ya kale shi, abun ko ya bashi mamaki, toh! mai yake kallo anan? , Ko dai yanayin rayuwan su yake kallon? Haka dai yayi ta tsake tsake ba mai bashi amsa, tabo shirt dad yayi, iko firgigit yadawo" kallon dad kawai yake yace "lfy ka kuwa son mai kake kallo a chan" babu komi dad, kawai dai yanayin rayuwan su nake kallo, "dad na jin haka sai duk tanbayoyin dake zuciyar shi ta wanke" Arif najin dad bai ce komi ba sai ya juya ya cigaba da kallon wurin, amman dam bai ganta ba, Ina taje? " juyowa dad yayi with much surprise yace Ina itawa? "Arif najin abinda dad yace sai da cikin shi yabada wani Kara kulllllllllllllllll!............, kallon shi dad yake da kyau yace wace yarinyar ce wannan? Kallon dad yayi da dan jarumta yace dad wata karamar yarinya nagani tana tallah shine yanzu na juya bangan ta ba shi yasa nace haka, ya karasa yana tsosa keya kanshi a kasa. Girgiza kai dad yayi dai-dai nan motan su ya fara tafiya. Baifi minti 10 ba suka isa company. Suna fita a mota direct liftan da zai sada su da office din dad suka hau"liftan da babu mai hawan shi sai dad ko Arif"bayan minti 5 suka kai office dinshi dake hawa na 7( last floor), Arif ne ya bude kofan yaba dad hanyya ya shiga ciki sannan yabi bayan shi, yana shiga ya ijiye ma dad jakan shi ya zauna, suka dan tattauna akan meeting din da sukayi, bayan sun gama ya nufi office din shi. 


A bangare Nasreen ko karfe 4:30 ta tashi, da Addu'a a bakin ta, fitowa tayi a dakin ta day buta, wani dan roba da take cikawa da ruwa ta nufa ta dibi ruwa ta shige bayi da Addu'a a bakin ta, bayan ta fito ta yi alwala ta nufi daki, kayan jikin ta ta chanja zuwa wanda zata iya yin sallah da shi, ta sa hijab sannan ta shinfida darduma tayi raka'a tanul fijir, bayan ta idar ta dauko Al-Qur'anin ta wanda yana daya daga cikin kayan Ammin ta, rera karatun Qur'ani tafara cikin zazzakan muryanta, in kana waje kaji yanda take karatu zaka zata yar shekara 18-19 ne, amman batafi 13 ba. Sai da tayi minti 30 tana karatu kafin a ka tayar da sallah a masallaci, tana daki taji fitowan baba daga daki, sai ta tuna jiya bata cika roban shi ba, ta cika amman mama ta juye tayi anfani da shi,tuna hakan yasa ta fita da tsauri, tana zuwa gaban baban shi ta gaishe shi amman bai amsa ba, yai kaman baisan da tsayuwan mutun ba. Butan hannun ta ta mika mai jikin ta a tsanyyaye, amsa kawai yayi ya nufi hanyyan bayi, binshi da Ido Nasreen tayi har ya shige bayi, yana shiga ta juya ta nufi dakin ta idon ta na taruwa da hawaye, wani irin zafi zuciyar ta ke mata, tanada uba amman kaman bata dashi, baya shiga tsapgarta, baya amsa gaisuwan ta, ko kallon arziki bai hadasu, daya mata kallo daya zai dauke kan shi, kuka ne ya kwace mata, yin shi take kaman ranta zai fita, baba dake waje yaji tsautin kukan ta daga jai kawai yayi yakalli kofan dakin, wani irin abu yakeji a zuciyar shi amman yakasa tantancewa, tsungunawa yayi yai alwala sannan ya fita daga gidan. 


Bayan tagama cin kukan ta na kusan minti 10 ta tashi ta nufi waje, buta ta dauka ta wanke fuskan ta da yai ja dan kuka, idan ta ko yai dan ha da kumburi kadan alaman tayi kuka, "abunka da farin mutun nan da nan yake ja"daki ta shiga ta tada sallah dan lokaci yayi, a cikin sallah ta sujjadan karshe take rokon Allah ya kawo mata dauki, ya kawo mata ranan da zata ga karshen wannan rayuwan datake ciki, ya bata ikon cinye kaddaran ta, ya bata miji na gari da en uwan miji na gari, ya bata juriya da hakuri, ya kare ta a duk inda yake, "Ameeen", bayan ta idar ta danyi wasu Addu'an data sani, bayan ta kammala ta cire hijabin jikin ta ta fita waje dan fara aikin ta na kullun daya zame mata farillah,wuta ta fara hadawa ta daura ruwan abinci,sannan ta kwaso wanke-wanke ta farayi, bayan ta ta gama ta dibo wake ta gyra ta wanke sannan ta juye shi cikin ruwan dake kan murhu, sannan ta koma ta debo shinkafa mudu daya da gongoni hudu ta zuba a tire ta fito da shi tsakar gida, zama tayi akan kujeran nan na sugunno ta fara gyra shinkafan, tana cikin gyrawa taji an bude kofan mama, daga kai tayi dan taga wanda zai fito, Sa'ade tagani da daurin kirji tana mika da hamma, ko rufe bakin batayi ba, "buta ta dauka ta shige bayi", girgiza kai kawai Nasreen tayi dan ta saba ganin haka, basu tashi sallah sai 7,wani lokaci ko sai 8,tabe baki kawai Nasreen tayi tace Allah ya shirya "Ameen ". Tana gama gyran shinkafan ta dauka ta kai kitchen ta ajiye, tsintsiya ta dauko ta ta share tsakar gidan ta kwashe dattin da parker, ta kai Bola, bayan ta ajiye tsintsyan da parker ta dauriye hannun ta. Wurin murhu ta nufah dan ta duba yan abun da tasa a wuta, chokali ta dauka ta duba waken taga ya nuna, kullewa tayi ta wuce kitchen,daukan tiren tayi ta juye shinkafan a wani roba mai fadi, wankewa tayi sossai sannan ta zuba a cikin tukunyya tasa gishiri sannan ta motsa.daukan roban tayi ta nufi kitchen, kayan miya ta debo mai dan yawa ta fito waje sannan ta koma ta dauko turmi da tabarya, gyra kayan miyan tayi ta daka su tass!, bayan ta gama ta zuba a tukunyya ta kulle da marfin shi, ta ijiye shi a kusa da murhu, daukan tsinsiya tayi ta nufi dakin baba ta share shi tass! Ta kakkabe duk wani kuran dake dakin ta tsauya zanin gado, tunawa tayi tanada tulare Wuta a daki, fita tayi ta nufi dakin ta, zanin gadon ta dauka tasa hannu ta kwaso kwalaben dake karkashi, daukan daya tayi da kaskon wuta ta fita a dakin, wurin murhu ta nufa ta dau chokali ta dibi wutan dai-dai Wanda take bukata, daukan kaskon da gwalban turaren tayi ta nufi dakin baba, aje kaskon tayi ta bude turaren wutan ta dan Diba ta zuba a cikin wutan, daukan tsinsiyan da parker tayi ta miyar harda kwalban turaren, bayan ta ijiye shi ta nufi wurin murhu, chokali ta daukan ta duba shinkafan taga ya nuna, tsaukarwa tayi ta daura tumatir, dakin baba ta koma ta dauke kaskon dan tularen ya kare, kofan taja ta kulle. 


Bayan ta gama girkin ta zuba shinkafan a kwano yanda mama k mata daukan ragowan shinkafan da miya tayi zuwa kitchen,tana fitowa taga mama a tsakar gida, "ikon Allah sai yanzu, yau an makara sossai"ina kwana mama"wani irin Dan iskan kallo mama ta aiko mata da shi tace da ban kwana ba zaki ganni, maza je ki gyra min daki kafin ki wuce tallah" da toh! Nasreen ta amsa ta nufi inda ake ajiye tsintsiya, dakin mama ta wuce ta share shi ta gyra ko ina kafin ta fito, tsaye taga mama a kofan dakin baba ta zuba ma kofan dakin ta ido, hannun ta daya na bango daya na rike da kwankwason ta sai wani jijjiga jiki take tana hura hanci, tana ganin fitowan Nasreen tace k dan ubanki waya baki daman shiga dakin nan, "jikin tane ya fara rawa dan yanayin da taga mama ya matukar bata tsoro, ummmm...... Babu kowa gyrawa kawai nayi" wani irin zabura mama tayi ta chakumo Nasreen, akwai dan tazara a tsakanin su amman kaman kiftawan ido har takai gaban Nasreen, ba abin da jikin Nasreen yake banda rawa,tuni hawaye ya fara an baliya a fuskan ta....................... 



NO COMMENT NO POST 


BY GIMBIYA AYSHU 馃摑馃摑馃摑馃挒馃挒馃挒. 


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.