Free chapter · Read without an account

CHAPTER 1

by Amina Shuaibu Musah · BURIN DUNIYA

🌎🌎🌎🌎🌎

   🌎🌎🌎

      🌎

          *BURIN DUNIYA* 

         🌎🌎🌎🌎🌎

            🌎🌎🌎

               🌎 


      *STORY & WRITTEN* 

             *BY* 

         *MEENERH* 

    *(AUTAR PERFECT🧝🏻‍♀️)* 


*THE OWNER WRITER OF* 👇

*NAJMAH* 

*WASU KAWAYEN (Masifa* *ne)* 

*ALAKA (Paid book)* 

        *AND* 

            *NOW* 

      " *BURIN DUNIYA"* 


*PERFECT* *WRITERS* *ASSOCIATION* 🌞


(WE '''AREN'T PERFECT BUT, WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR''' ~'''READERS'''~ 💪)


***


       *P.W.A✍️* 


*DEDICATED TO MY* *BLOODY SISTERS NAH* 😘

*NAFISAT SHUAIBU* *MUSAH* 

*LAWIXA SHUAIBU* *MUSAH* 

*HAJARA SHUAIBU MUSAH* 

*AISHA SHUAIBU* *MUSAH* 

  *ALLAH YA* *BAR MU* *TARE* 🥰* 


*Alhamdulillah am back again💃with another hot one, so what are you* *still waiting for?? Oyaa Macoya's cm forward it's very interesting and meaningful👌nd* *u'll never regret wasting ur lokaci for reading,* *am always ready to entertain you!! But, only if you gv me a maximum* *cooperation....* 


  " *Ur sweets commenting motivated me to keep on typing".........* *One luv kawai💖✌️* 


   *'''WARNING❌❌

"NO PART''' '''OF THIS PUBLICATION* MAY BE REPRODUCED OR TRANSMITTED IN ANY FORM, OR BY ANY MEANS WITHOUT AUTHOR'S PERMISSION"🧏‍♀️


''' 


*ALLAH KAI NE MASANIN ABINDA KE CIKIN ZUKATAN BAYINKA.....* *MU KUMA MARUBUTA NE, YA ALLAH* *KA CIGABA DA TSARKAKE MANA ALƘALUMANMU* *DAGA NAJASAR RUBUTA ALFASHA, KA KUMA BAMU* *IKON ISAR DA SAƘON* *DAI_DAI* 👏 


" *Bismillahir rahmanirrahim* 


........1️⃣


"Sa'adatu Abdul_ƙadir Mai gishiri shine ainihin cikakken sunana, Ina da shekaru goma sha takwas (18) a Duniya, Mahaifina mazaunin garin Miga ne, da ke ƙaramar hukumar Miga da ke cikin Jihar Jigawa".


"Malam Abdul_ƙadir Mai gishiri shine cikakken sunan Mahaifina. Laƙaninshi (Mai gishiri) inda ya samo asaline daga sana'ar shi ta gishiri da yake siyarwa a Kasuwa, wanda kuma ya gadota ne a wajen Mahaifin shi Malam Sallau Mai gishiri, wanda tun kafin Mahaifinmu ya yi Aure yake bin Malam Sallau mai gishiri zuwa Kasuwa inda anan ne ya koyi sana'o'i daban_daban har Allah ya yassare mishi shima nashi nasibin ya kafu da kan shi ya kafa rumfar shi, inda ya ke siyar da abubuwa daban_daban na amfanin yau da kullum, shikenan km sunan shi ya yi ƙarfi sosai kusan kowa da yake hada_hada acikin Kasuwar yasan shi, sbd Allah ya mishi farin jini km Allah ya taimake shi ya fara sana'ar da hannun dama, daga ƙarshe har ya hana Mahaifin shi zuwa Kasuwa, domin a cewarshi hakan bai kamata ba tunda shima ya taso dole ya samu nashi ladan ko da kaɗan ne sbd haka ya huta a gida shima lokacin hutunshi ya yi". Toh kasan yanayi irin na tsufa da kyar dai aka samu Malam Sallau Mai gishiri ya hakura da zuwa Kasuwa ya zauna a gida, cikin taimakon Allah Mahaifina ya fara bunƙasa ta wuce kima kowanne nauyi na Gidansu yana kanshi, duk da cewar Malam Sallau bai gaza ba wajen yiwa kanshi komai da komai, saboda shima ba wai ya dogara bane da iyakacin kasuwar bane, a'a babban Malami ne sosai kawai dai shi irin mutanen nan ne da basa son zaman kashe wando.(Ba cima zaune bane).


  Mahaifina bai barin nashi Mahaifin ya yi komai, shine cefane, kula da harkokin yau da kullum da km biyan kudin Makaranta na 'Kannen shi, kasancewar shine babba Yana da 'kanne guda biyu Lawal da Salaha.


" Ganin irin ribar da yake samu sai Mahaifiyarshi ta buƙaci da ya yi Aure kasancewar shi bai yi karatun zamani mai zurfi ba, daga ƙaramar Sakandire bai cgb ba, amma ya yi mugun nisa ta bangaren Addini sosai da sosai dadin daɗawa Mahaifinshi shine Limamin Masallacin Juma'ar garin a wannan lokacin, sannan yana da Islamiyyah wacce yake koyar da bayin Allah. A tarihi Gidanmu Gidan Malamai ne sosai ga shi kuma babban gida sai dai kowa da nashi bangaren kowa dai yasan yanayi da km tsarinshi yake sai dai ya danganta da irin Dattijan da suke mulke da Gidan, toh yanzu km zumunci ya yi ƙaranci tun da manyan Gidan suka ƙare shikenan kowa ya kama gabanshi, sai dai ba wai abin ya yi tsamari sosai ba, sai dai akan ɗauki lokaci mai tsawo ba'a gana da wasu daga ciki ba, hasalima yanzu su Kawu Sule da Kawu Bello suke zaune acikin ainihin Gidan".


Duk da dai garin bai da wani girma na wani ku zo mugani, ba dai za'a ce karami bane amma dai ba wani tangameme bane sosai.

  Amma dai babu laifi masha Allah akwai ƴan boko da km ƴan siyasa masu kishin garin sosai.


  Toh dai wannan daliline ya sanya Mahaifina ya samu wannan laƙanin suna, wanda inkiyar Mahaifinshi kenan tun wancan lokacin.


Ba tare da ɓata lokaci ba, Innah (Mahaifiyar Babana) ta tisa Mahaifina a gaba lallai sai ya yi Aure, kuma ita akwai wacce take so ya Aura don dole ba da son ran Mahaifina ba aka ɗaura mishi Aure da Hadiza wacce take Mahaifiyarta da Innah Uwa ɗaya suke Ubane kawai kowa da nashi. Ba wai Yana sonta bane, a'a kawai ya yi mata biyayya ne a matsayin shi na Mai ilimi sanñan km da irin tausar da Mahaifin shi ya yi mishi a lokacin akan cewa ya bi umarnin Mahaifiyar shi, inyaso ko zuwa daga baya ne idan ya ga wacce ta kwanta mishi a rai, sai ya Aureta.


  Haka dai Mahaifina da Mahaifiyata suka yi Aure wanda na haɗin zumunta ne, ba wai na soyayya ba. 


 A kwana a tashi babu wuya a wajen Ubangiji, bayan shekaru kusan uku Allah ya azurta su da ɗiya Mace wacce aka sanya mata suna "Sa'adatu" wacce takwara ce ga Kakar Mahaifina, daga lokacin ne km zaman nasu ya fara samun tangarɗa wanda daman duk dai zaman hakuri Mahaifina ya ke yi da Mahaifiyata, a hakan dai a daddafe har aka haifi Fauziyya wanda kafin a zubar da wankanta Mahaifina ya kara Aure lokacin km Mahaifiyata ta birkicewa Mahaifina harda yajinta kasancewar kuma tana da magoya baya (Innah da Goggo Habiba) don su duk abinda ta ke yi, ba su gani koma dai menene ala tilass!! Itan ce da gaskiya. Haka za su tasa Mahaifina a gaba su yi mishi tatasss!! Su mishi wankin babban bargo. Hakan dai zai yi hakuri kasancewar shi Allah ya ɗiga mishi ruwan hakuri mai yawan gaske, wanda Ni dai tunda na ke a rayuwata ban taɓa ganin mai hakuri kmr shi ba, ba kuma wai na so kaina ba ne, ko km don yana matsayin Uba a gareni, a'a ita gaskiya kawai ko da yaushe sunanta gaskiya.


 Da irin wannan abubuwan har Mahaifiyata ta dawo maimakon a zauna lafiya, amma inaa!!!! Sai ma wani bankin rashin zaman lafiya da aka bude a Gidan, duk da Matar da Mahaifina ya Auro bata da kau_kau, sai dai Mahaifiyata ta yi ta tsurkularta da masifa kala_kala ita kuma ko kallon inda take ba ta yi, hakan kuma sai ya ke ƙara hasalata, shi kuma Mahaifina ba zai ce komai ba, saboda dama ko magana bata haɗasu tun bayan dawowarta, saboda a cewarshi shi babu ruwanshi da ita tunda ba ta jin magana.


  


  Bayan wasu shekaru kamar uku, Allah ya sake azurta Mahaifina inda aka sake haifar Mace mai suna Sadiya, wacce ta ke ƙanwa a wajena, wanda itama kafin a haifeta an kayi ruwa rana. Sai itama Abokiyar zaman Mahaifiyata wacce itama lokacin da nake da watanni goma sha ɗaya a Duniya, ta haifi Namiji (Isma'il), daga shi km har yanzu Allah bai nufeta da samun wani cikin ba. 


(Wato dai a takaice Ni ce babba: Sa'adatu, Fauziya, sai Isma'il da km Sadiya).


Zaman su yaso karewa sai dai Allah ya rigada ya gama tsara komai. Bayan kmr kimanin shekara guda, Allah ya yiwa Matar Babana rasuwa a sanadiyyar haihuwa wacce daga ita har abinda yake cikin nata duk babu. Sosai rasuwar tasu ta girgiza kowa musamman Mahaifiyata wacce wannan girgizar bai sanya Mahaifiyata yin sanyi ba, balle ta yi nadama akan abubuwan da ta aikata a gareta, da abinda ta bari, wanda ta manta cewa Maraya ba abin wulaƙantawa bane, saboda ba'a san ta inda rana za ta faɗi ba.


Da ace ta yiwa kanta karatun ta nutsu, toh da ba'a kawo wannan lokacin da zata ciji yatsan ba..............


Matar Babana ita ce Mace ta farko da ya fara so a rayuwarshi. Idan ba kaddara babu wanda zai so ace ya rabu da Masoyin da ya fara haduwa. Tabbas rabuwar akwai ciwo......  

  Wannan dalilin, shiyasa ta kasa goguwa a zuciyarshi, wanda har yau nakan gano abubuwa masu tarin yawa a tsakanin Babana da Isma'il.


Babu yanda ya iya haka ya ɗauki dangana ya sanya a ranshi, ga shi dama gwanin hakuri...shikenan ya zama "Damo"..... Da wannnan damar Mahaifiyata ta yi amfani wajen cigaba da cusguna mishi, Shi kuma ya gama sanyayewa sai ya sakar mata ragamar take abinda ta ga dama, shi dai ko kanzill!!! Ba zai ce da ita ba, kawai ya zuba mata na mujiyane gashi an rigada an sangartata babu mai mata tsawa amma fa tana shakkar shi, kawai ya rabu da itane tayi abinda take so, tunda yanzu wacce zata ke kwantar mishi da hankalin bata Duniyah. Idan kuma ya tsaya biyeta toh ranshi ne zai ke ɓaci a banza da wofi, ga faɗan Innah na gaira babu dalili, itama sai da Mijinta ya taka mata burki, sannnan ta dena.


Da haka ya sallamata ya fawwalawa mai dukka komai, sannan ya tattara hankalinshi wajen Ɗalibanshi...................



*SOMIN TAƁINE* 😍🤌


*NEXT CHAPTER ZAMU SHIGA CIKIN LABARIN* *GADAN_GADAN.......YANAYIN COMMENTS ƊIN KU SHINE ZAI* *NUNA CEWAR KUN YI NA'AM DA BOOK* *ƊIN* 🤌



*MEENERH CE* ✍️


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.