Free chapter 路 Read without an account

8.

by Nusaiba 路 SARAUTAH TAH CE

馃憫馃憫馃憫馃憫馃憫



*SARAUTA TAH CE*





*Free page*







*Wattpad*

@nuceeyluv






By

Nuceeyluv馃槝






8....






Saidai Sam bata nuna Hakan a fuska ba domin daure fuskar tayi sosai tana kawar da Kai batayi mgn ba,


"Baalkiii"


lauwali ya furta Hakan yana buga kujerar gabansa yace,


"dake nake fa Baalkiii"


rai bace tace,


"Dan Allah ka daina kirana haka Nan banaso."


Washe baki yyi yace,


"Wlh 'yar muryar Nan taki yaseen dadi ne da ita kan uba tamkar Ana busa sarewa"


Wani takaicin ne ya sake kamata batayi mgn ba tanajin Inama ta iya bude kofar kawai ta dira saidai babu dama sbd driver ya fara tafiya. Ita kuwa Shema'u tsoro ne fal ranta haka taki kallon side din da suke tana kallon window burinta su isa gida kawai ko ta samu salama.


Mutanen motar kuwa babu wanda ya iya tankawa lauwali Dan ba bakon wajen bane yyi kaurin Suna. Harara ta ballo Masa da manyan idanun ta masu haske tana Jan tsaki kasa2 lauwali yace,


"Irin Wannan farin nakeso ki dinga min idan munyi aure."


Ganin abin nasa bana karewa bane kawai ta juyar da fuska batare data Kara yin koda tari ba haka ya karaci surutun sa yyi shiru har suka isa kauyen na JIRAGO.




*MASARAUTAR MANARAS*


Kallon mgnin tayi tana sake kallon boka Markus, boka Markus yace,


"Lkci na kurewa ya kamata kisan dabarar da zakiyi a zuba Masa a abin cinsa ko shansa"


hankalin sa'adiyya ne ya tashi tana sake kallon mgnin dake cikin 'yar karamar kwalba kamar turare tace,


"taya ni zan iya zuba Wannan mgnin acikin abin sha ko cin yareema yaseer? Mutumin da tsabar Rashin yadda ko bayi masu hidamar sashen sa babu? dakyar fa ya yadda da dogaran kofar sa, Amma sauran hidima ta cikin dakinsa babu ko daya. Kanwar sa ce kadai kekai Masa abinci fah?"


Boka Markus yace,


"dukda haka ya kamata kisan abin yi domin matukar aka wuce daren gobe ba'a aiwatar da aikin ba komai zai iya faruwa"


Tashin hankali ne karara ya bayyana akan fuskarta ta mike da sauri tana gyara tsayuwar ta tace,


"ni kuwa da ace komai ya lalace gara duk yadda zanyi nayi domin na Tabbatar yareema yaseer yaci abinci da Wannan mgnin"


boka Markus yace,


"Wannan itace kadai mafitar ku da zaisa yyi bcci me nauyin da koda anzo daukar sa cikin dare bazai farka da wuri ba."


Cike da amincewa kwarkwara sa'adiyya tayi Masa sallama tana fitowa daga maboyar su. Wani Abu ne ya fado mata a rai take ta saki murmushin jin dadi tana dafe goshi Ashe akwai hanya mafi sauki ma da zata sadar da aikinta batare da sunsha wahala ba.


Can cikin dakinta ta shige tana latsa wayarta take ta kamo number sa tana karawa a kunne, daga dayan bangaren aka Amsa cike da girmamawa,


"ranki shi dade barka da Wannan lkci"


kwarkwara sa'adiyya tace,


"Inada Wani muhimmin aiki da zaka min"


"fada taki ce ni Kuma na cika domin a koda yaushe ke nake yiwa aiki."


Murmushi sa'adiyya tayi kafin ta sanar dashi bukatar ta na sawa yareema yaseer mgni a abinci, dafe kirji yyi a tsorace yana waige2 yace,


"Allah yaja kwana ranki shi dade bana tunanin abinnan zaizo da sauki"


"Me kkeso kace? Meye amfanin ka a Wannan matsayin?"


Sa'adiyya ta furta Hakan cike da tsawa. Hakuri ya Bata tace,


"zan Aiko Dan Sako ya baka ka aiwatar da Abinda na saka banason shirme."


An gama ranki shi dade, ya furta Hakan yana kashe wayar sa.



****

Suhaima na hanyar ta na zuwa kaiwa yareema abinci suka hadu da Musa ya matso wajenta da sauri cike da sakin fuska yace,


"Gimbiya kawo na taimaka maki"


girgiza Kai suhaima tayi tace,


"No basai kayi Hakan ba"


"Haba Mana Nima wajen shi zanje kawo na Karasa miki dashi"


Suhaima ta kalli agogon hannun ta dama sauri take ummi ta Bata umarnin a kaiwa yareema yaseer abinci Dan haka tace,


"toh Dan Allah ka kula iya fruit ma kawai yake bukata yau"


murmushi bafaden Musa yyi yace,


"Insha ALLAH zan kiyaye Allah ya huta gajiya"


tana mika Masa basket din ta juya daga wajen. Shima nufar sashen yareema yaseer yyi a nutse Harya kai ga zuwa parlon nasa,


lkcn yareema yaseer na cikin dakinsa be fito ba, Hakan yasa Musa ya koma gefe yana jiran fitowar tasa tunda dama ya kirashi ne suka hadu da suhaima a hanya.


Ba'a dau lkci sosai ba yareema yaseer ya fito cikin shiga ta kananun kaya yyi wanka sosai Yana zuba kamshi tamkar zaije Zance, cike da girmamawa Musa yace,


"Barka da fitowa yallabai."


Be kalleshi ba bare yasa ran Amsa Masa direct ya wuce kan kujera ya zauna Yana canja channel kafin ya dauko wayarsa dake ringing Yana Amsa Kira. Bayan ya gama Amsa kiran ne ya gyara zamansa sosai yana kallon wasan kwallon da ake bugawa na Barcelona da Real Madrid Musa ya matso cike da girmamawa yace,


"yallabai a kawo maka fruit din naka ne Nan?"


Banza yyi dashi har saida Musa ya sake fadin,


"yallabai..."


hannu ya daga Masa alamar ya dame shi sannan yace,


"Get out"


ya furta Hakan hankalin sa na kan wasan har yanzu be dago ya kalleshi ba, kamar Zai fita sai kuma ya dawo. da mmki yareema ya kalleshi yanzu fuskar sa a hade, Musa ya zube a kasa yana Kara dukar da kansa yace,


"Allah ya baka yawan rai ban shigo da kayan Nan ba saida Gimbiya tayi Mani umarnin lalle a baka Kaci Kuma Hakan na nufin Sako ne daga wajen Gimbiya Falmata, Dan Allah kada nayi lefi a duba bukata ta."


Tsaki yareema yaseer yyi yana dauke kansa fuskar sa na sake hadewa a lkcn daya ga cewar anci team din da yake kallo, har lkcn musa be motsa ba Yana Nan zaune, ba'a jima ba kuwa sai gashi team din da yake bi sunci nasu kwallo murmushi yyi yana tuna last zuwan da yyi lkcn Yana cikin mutanen da ake kallo Banda yanzu daya dawo Nigeria badan maimartaba da ummin su ba da babu Abinda zai hanashi tafiya tun jiya Amma besan meyasa suka rikeshi ba Sam gsky yyi missing 'yan matan da yake hutawa dasu ya kagara ya koma domin ko a matan ma yafi ganewa da matan na can kasashen ketare sbd gani yake sunfi iya harka sosai....


"Kawo min"


ya furta a hankali har yanzu be juyo ba, badan ace bafaden Musa ya tattara hankalin sa a kansa bane da bazaiji me yace ba bare yyi tunanin dashi yake.


Mikewa yyi da sauri yana nufar Inda ya aje basket din ya dauko Masa gabansa ya aje akan center table Yana risinawa yace,


"gashi nan yallabai."


Girgiza Kai prince yyi beyi mgn ba Hakan yasa Musa ya juya Dan barin parlon.


"Wait..."


Yaji yareema ya furta Hakan da nufin dakatar dashi, juyowa Musa yyi yareema yaseer ya dago kansa yana masa alamar yazo, dawowa baya yyi yareema yaseer ya nuna Masa waje yace,


"zauna."


Zama Musa yyi yana mmkin me Kuma zaiyi? Kamar daga sama yaji yace,


"cinye."


Gwalo ido bafaden Musa yyi a kidime Yana rarraba idanu yace,


"wa..wat... what????"


Juyowa yareema yaseer yyi yana kallon sa, sai kuma bafaden Musa ya washe baki yace,


"dama nace ni Kuma? Haba ai ban isa ba wlh, Wannan ba hurumi na bane yallabai."


Dauke kansa yareema yyi yana sake gyara zaman sa beyi mgn ba, Musa ya Rasa abinda zaiyi sai zare ido yake, yareema yaseer yace,


"Tashi ka fita."


Wata kyakkyawan ajiyar zuciya Musa ya saki Hakan yasa yareema yaseer ya juyo yana kallon sa. Mikewa yyi da sauri yana kawar da Kai kawai ya fice daga wajen gaba1.


Tsaki yareema yaja kawai ya dauke kai Yana ci gaba da kallon sa. A haka yakai hannu zai dauki Apple din wayarsa tayi ringing. Sam, shine Abinda ke yawo akan screen din. Share kiran yyi yana daukar Apple din kiran ya sake shigowa Dan tsaki yaja ta cika damu, tun bayan daya bar America matan ke yawan damun sa da Kira, yatsina fuska yyi ya dauki wayar yana karawa a kunne.


"Prince I missed you, pls when will you come back?"


Beyi mgn ba kawai dai yakai Apple din bakin sa ne Yana gatsawa a hankali,


"Ina matukar kewar ka prince I missed everything about you, your lips.. neck... everything."


Lumshe ido yareema yaseer yyi,


"pls say something prince I want to hear your voice."


Wani Abu ne ya tsirga Masa yanajin bukatar macen yanzu kusa dashi gsky ba karamin missing yyi ba, anan kam bayajin zai samu madadi irinsu Samantha turawan dake bude komai ayi harka batare da jin kunya ko makamancin Hakan ba.


"Let's do s*** vid."


Ya furta Hakan yana mike kafarsa akan kujera. Dadi ne ya kama Samantha tace,


"Alright."


Nan suka koma vid call anan Samantha ta tube gaba daya kayanta tana fada masa dirty talks da Abubuwan da ta sake hautsina shi, take suka koma yin abinsu tamkar a Fili har Saida suka gamsu a Hakan koda yake yareema ne ya fara yin laushi da alama bcci ya fara kwasar sa wanda yasa dole suka hakura haka Nan, take yyi mata transfer na kudinta tana murna suka rabu lkcn Harya fara ganin double.


Mikewa yyi dakyar ya wuce can cikin dakinsa Yana dafe cikinsa a haka ya fada toilet yana watsa ruwa, shima dai da kyar ya fito yana mmkin yadda bccin yake kwasar sa tamkar Wanda yashawu, wayarsa ya duba be gani ba lkcn daya gama saka kayan bcci Dan haka ya fito parlo Yana hada hanya ya hango ta can kan center table, mika hannu yyi zai dauka yaji ya tafi gaba1 dakyar ya dafe kujerar gabansa kawai saiya dawo kanta gaba1 ya mike a kanta yana layi a haka wani irin nannauyan bcci yyi awon gaba dashi.





*KAUYEN JIRAGO*



Tunda suka sauka yake binta tamkar bindi bilqees ta Rasa abinda zata ce Masa Dan haushi, kicibis sukayi da mlm Musa daya fito daga gida, mlm Musa na ganin shi ya tare kofar gidan Yana zare ido yace,


"kai..Kai dakata uban waye Kai da kke kokarin sanyo min kanka a gida?"


Lauwali yaja Baya Yana harde kafafu irin na mafarauta yace,


"kaine baban Baalkiii?"


Bilqees data rakube a gefe mlm Musa ya kalla Yana hura hanci ya dauke kai yace,


"meyene kke tmby?"


Lauwali yace,


"madallah da alama dai zuwan nawa yyi daidai tohdai da farko Sunana lauwali Wanda akafi sani da lawi uban dawa"


sauke hannun sa mlm Musa yyi a tsorace yace,


"ban gane ba bawan Allah kace lawi uban dawa? Wanda dai mukejin lbri?"


Lauwali yace,


"kwarai kuwa nine Nan yau a kofar gidan ka"


Cikin mlm Musa ne ya kada sbd kowa dai yasan lawi Dan haka yace,


"Toh lawi Rashin kunya yarinyar Nan tayi maka yanzu nasa ayi mgninta?"


Lauwali yace,


"inaaa baba ai Wannan abin Alkhairi tayi"


washe baki mlm Musa yyi yace,


"toh...Toh.. bari a kawo taburma da alama zancen sai an zauna."


Lauwali yace,


"Hakan ma ya isa ai, domin akan hanya nake yau so nake na harbo Zaki ko damisa a dawa."


Mlm Musa yace,


"haka abin yake ai munajin lbrn jarumtar ka lawi."


Lauwali yace,


"madallah, Toh dai Abinda nake tafe dashi shine nidai na gani inaso, ma'ana dai Ina son 'yarka Baalkiii domin yarinyar Nan tamin kyau tamkar Aljana haka take da kyau, Kasan mu a dawa ba irin Aljanun da bama gani."


Mlm Musa yace,


"kwarai kuwa ni na shaida Hakan, domin alkcn yarintata Ina Mai Tabbatar maka da cewar harda Aljanu masu kofato da masu Kaho da bindi duk muna gani"


dariya sosai lauwali ya saka yace,


"Kai Ashe baba da kaima Dan iska ne."


Baki mlm Musa ya washe yace,


"Dan iskan gaske ma kuwa, ai nake fada maka yanzu ne girma yazo Amma da ai munyi yawon daji Dan samari."


Hawayen bakin ciki ne ya zubowa bilqees tana ganin yadda babanta ke zubarda kimarsa da mutuncin sa a idon lauwali tamkar wasu sa'anni kawai ta sulale daidai zata fada gidan ta jiyo mlm Musa na fadin,


"ai kasha kurimin ka indai yarinyar Nan ce bilqees na baka ita halak malak ko gobe za'a iya daura maku aure da ita...."


Karasa fashewa tayi da kuka me cin rai tana afkawa cikin gidan.


"Chau...Chau..."


ya furta Hakan yana hade hannaye irin gaisuwar mafarauta yaci gaba da fadin,


"Godiya nake Baba dole ranar biki ayi hawan zakuna da Kaina zan kawo Zaki kahau bayan sa Baba."


Mlm Musa na washe baki yace,


"kwarai kuwa harda giwa ka kawo domin tsumina na shekara da shekaru ne Zai tashi a ranar."


A haka dai sukaci gaba da mgnr su har lauwali yyi masa sallama ya tafi.



Jiki na rawa mlm Musa ya fada gidan Yana zabgawa bilqees da inna habi da tasa a gaba tun dazu tana mata mgn tayi shiru Kira.


Mikewa tayi a firgice sukayo waje dukkansu harda inna Zabba data fito bayi yanzu, Bakinsa har Kumfa yake sbd masifa yace,


"kekam ban Kara Tabbatar wa da cewar jaraba bace haihuwar ki sai yau"


dafe kirji inna habi tayi tana salati yace,


"ke ja can bakar munafuka duk bake kika jawo min Wannan bala'in ba? Yanzu gashi nan ace duk mazajen kauyikan Nan karankacakaf a Rasa Wanda zaice yanason bilqees sai wancan uban dawan lauwali???"


"Lauwali...???"


Inna habi da Zabba suka furta hakan a tare Suna dafe kirji, mlm Musa yace,


"kwarai Wanda dai kukejin lbri tare dashi suka taho tsabar nunawa duniya ta samu tantirin Dan iska..."


Inna Zabba tace,


"Yi kasa da muryar ka mlm inace shine yake Sara da suka?"


Kirjin mlm Musa ne ya buga tsoro na Kara shigar shi ya waiwaya a tsorace kamar ace ga lauwali Nan sai kuma ya juyo yana fadin,


"kunga irin masifar koh? Ni Wlh habiba kin cuceni, Ina zamana lpy kin haifo min jaraba shiyasa tun a lkcn nace na bada ita Dan banason fitina"


Dafe kirji inna habi tayi Tace,


"mlm Musa kace ka bayar da ita?"


Mlm Musa yace,


"kwarai kuwa akwai Wanda ya isa ya Hana Hakan ne?"


Kasa mgn inna habi tayi ta kamo hannun bilqees suka juya dakinsu hankalin ta a tashe.




*DAREN ASHIRIN DA BAKWAI*


mutane ne kusan biyar sukayi shiga irin ta badda kama sak tamkar bayin dake zirga-zirga a sashen yareema yaseer waiwaye suke Suna nufar parlon sa kaida ganinsu kasan cewar ba gsky a tattare da lamarin su, tacan baya suka lallbo ta wata siririyar hanya wacce ba kowa ya San da ita ba suka bi da alama masu kula da wajen aka saye Hakan ya basu damar shigewa parlon yareema yaseer Kai tsaye daya daga cikinsu hannun sa dauke da fruit masu yawa exactly irin Wanda aka kaiwa yareema yaseer Suna karasawa wajen suka canja frut din wancan aka kwashe.


Cikin mgn ta kurame Dan basason yin koda tari bare a samu matsala me Jan Ragamar tafiyar yyi masu alamar nuni da yareema yaseer dake kwance akan doguwar kujera yana bcci, hannun yareema yaseer suka taba a hankali sai sukaji ya sake tamkar Wani gawa.


Hakan ya basu kwarin gwiwar nufar wajen sa gaba1 Suna shirin zura shi a Wani katon buhu da suke tafe dashi.







*Zaki iya biyan kudin ki yanzu a saki a paid group*



It's 300 via... Access bank 1445626295


Nusaiba Mustapha


Then show your evidence ta Wannan number馃憞馃徎



***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.