Free chapter · Read without an account
4
by Khadeeja Candy · CIWON SO
ABIEY POV.
“Aliyu, hakuri ake yi da rayuwa, dan adam kullum rayuwarsa a cikin wahala take ko da kuwa wasu na maka kallon kana jindadi ne, shi musulmi baya zama babu jarabawa, Allah babu ruwansa da kyauka muninka asalinka kyau ko muni, kana cikin wata jarabawar zai iya karo maka wata, sai dai shi musulmi an sanshi da hakuri da yardar da kaddara”
A wannan gabar ne ya daga kai ya kalli Momy dake magana.
“Momy idan ban yi hakuri ba hauka zan yi? Na yarda jarabawa ce shiyasa na tashi babu soyayyar mahaifi, bayan kuma na samu Zahra mun shaku da juna, ita ma kaddara ta hana ni aurenta, Momy kin sani ina da iko ina da karfi ina da kudin da zan yi amfani da su na kashe auren Zahra ko na rabata da mijinta na aureta amman ban yi ba, as long as zata zauna cikin farinciki tare da wannan azzalumin sheidane abun farinciki ne ni a gurina, ina son farinciki Zahra ko da ni zan cutu, Momy ina son Zahra ina sonta sosai Momy Allah ma ya sani”
A sirrance Momy ta sauke ajiyar zuciya tana tausayin dan Kishiyarta.
“Allah ya sasssauta maka Abiey Allah ya baka wanda ta fi Zahra”
“Babu wata mace da zan gani ta burge ni kamar yadda Zahra ta burge ni, dan haka a gurina babu wata mace da ta fi Zahra, komai na Zahra dabam yake Momy she's social, unique... Everything about her is beautiful...”
Ya furta yana murmushi zuciyarsa na masa wani irin zafi, kami ya daga ido ya kalli Yasmin da ke kokarin mika masa ruwa.
“Thank You”
Ya furta sannan ya bita da kallo har ta shige dakinsu, after like 20min ta fito sanye da uniform din makaranta.
“Momy zan tafi islamiya”
Ya mike tsaye.
“Lemme drop you”
Momy ma ta mike tsaye suka jera ita da shi suka nufi kofar fita falon Yasmin na bayansu.
“Ka yi ta addu'a Allah ya yaye maka abun da kake ji a zuciyarka akan, kuma kar ka yarda son Zahra ya hada ka da mahaifiyarka da yan'uwanka, ita tana can tana yi aure tana rayuwarta cikin farinciki kai kana nan kana fama da Ciwon So, kar kuma son ya hana ka son wata mace ka rika tausayawa kanka, a musulunci ma ba a yardar mutum ya cutar da kansa da kansa ba, hakan da zaka yi shi zai kara tabbatar da cewar ka yardar da kaddara...”
Haka Momy ta yi ta masa kalama na kwantar da hankali da lurarwa har suka isa gurin motar.
“Na gode”
Shi ne abun da ya fada sannan ya bude motar ya shiga driver side ya zauna, Yasmin kuma ta zagaya ta bude front seat ta zauna, sai da yayi reverse sannan aka bude masa gate din gidan ya fice, yana hawan titin unguwar ya mika hannunsa ya riko hannun Yasmin sai ta kallrshitda sauri gabanta na faduwa, domin be saba yi mata haka ba.
“Abiey ba kyau fa...”
Ta fada da kamar tsoro sai yayi murmushi ya janye hannunsa.
“Haka Zahra take min idan na rika ta, sai ta ce wai kai miyasa kake son taba ni kamar dan'iska”
Ya karasa yana busar da iskar bakinsa, Yasmin dai ban da kallonsa babu abun da take tausayinsa ya cika mata zuciya. Adaidai gate din makarantar ya faka sai ta bude mota ta fita ta rufe masa, kallonta ya tsaya har sai da shiga ciki sannan ya yi reversed ya hau titi, be yi minti uku da hawan titi ba kiran Dr ya shigo wayarsa, hannunsa ya saka aljihu ya ciro wayar ganin yayarsa ce ya saka ya aje motar a muhalin da aka tanadar mata a cikin tsadaddiyar motar, haka kiran ya shigo har ya tsinke wani ya sake shigowa ya ki ya daga. Kiran Dr Zainab na yankewa na Ammy ya shigo, sai a nan ya mika hannu ya dauka ya saka speaker.
“Aliyu, baka ga kiran Zainab ba?”
“Na gani Ammy”
“Haba Autana ka dawo gida yanzu ina son magana da kai”
“Dr tana nan?”
Dr Zainab da idanuwanta suka gama kumbura saboda kuka ta girgiza ma Ammy kai alamar tace aa.
“Aa bata nan”
“You won't lie to me Ammy”
“Tana nan and she want to talk to you, akwai abun da zamu fada maka, dan Allah ka zo”
“Gani nan zuwa”
Ya fada sannan ya katse kiran, ya juya motarsa ya dauki hanyar da zata sadashi da gidansu. Bayan Ammy ta sauke wayar Dr Zainab ta share hawayenta ta ce
“Da can idan kika bata masa rai ko Mai Martaba, gurin na take zuwa, ko gurin Sauban a lokacin da ya hadu da Zahra kuma gurinta yake zuwa, yanzu kuma ya bata da ni, Zahra kuma bata nan, Sauban kuma yana ta hidima Abiey abun tausayi ne Ammy”
“Na sani, amman idan muka ce zamu biye shi to zai bata ransa ne kuma ya bata damu, duk abun da ya faru kaddara ce, rashin sonsa da mahaifinsa yake yi wannan daga Allah tun da ban masa komai ba, shi ma kuma ba masa laifin komai ba, rasa Zahra kuma kaddara ce tun dukanmu muna son yarinyar muna kaunarta to me zai saka ba zai yi hakuri ba, sai riga dorawa wasu laifi”
Ammy na rufe baki kiran Momy ya shigo wayarta, sai ta dan tabe baki ta yi murmushi sannan ta daga.
“Ina fatar karata aka kawo miki”
“Be kawo min kararki ba, amman dai ya zo min abun tausayi, Ammy danki yana cikin tsananin damuwa, yana bukatar taimako na addu'a da kuma kalamai masu kwantar da hankali, kar halin da yake ciki ya jefashi cikin wata rayuwa wanda mu da ke duka mu kasa cetonsa, ki dage da addu'a ki yi duk abun da zaki yi na ganin mahaifinsa ya shirya da shi, sannan ki natsu ki samo masa wata yarinya wanda hankalinsa zai kwanta da ita su yi rayuwar aure ko da ba zai so ta kamar Zahra ba”
“Addu'a ina kan yi kullum Hajiya Uwani, babu dare da bana kaiwa Allah kuka akan dana, amman Inshallah zan kara dagewa zan yi duk abun da ya kamata na gode sosai”
“Allah ya taimaka, mu ma zamu kara yi Inshallah Allah ya yaye masa danuwarsa”
“Amin Hajiya uwani”
Wannan karon da damuwa Ammy ta sauke wayar sai ta kurawa hoton Abiey dake gaban wayarta ido.
“Allah sarki Autana”
Motsin takowa upstairs suka ji, daga ita har Dr Zainab kofar shigowa bedroom din suka kalla, sai ya turo kofar dakin ya shigo tare da kamshinsa, ko kadan be kalli inda Dr take zaune ba, sai mahaifiyarsa yake kallo har ya karasa cikin dakin ya zauna kusa da ita.
“Abiey...”
Dr Zainab ta kira sunansa da muryar kuka hawaye na sauko mata, bnza ya mata kamar baya cikin dakin.
“Me zan maka na gyara kuskuren da na yi?”
Sai a lokacin ya kalli gefenta.
“Babu kin riga kin bata komai, kin gama komai kin yi kuskuren da ba zai taba gyaruwa ba, na rasa Zahra to me zaki yi yanzu? Kin riga kin shafa min bakin fenti da ba zai taba goguwa ba, Zahra ta auri mutum da br dace da zama mijinta ba, ni kuma tana min kallon wanda ya kasa taimakon ya kasa yi mata rumfa ya zame mata inuwa a lokacin da take cikin rana, ta auri wacan banzan mashayin tana kallonsa a matsayin mai gaskiya, duk abun da abun da ya faru ke kika ja Dr”
Ya karasa yana kallon fuskarta, ko kadan baya jin tausayin hawayen da take zubarwa.
“Zainab ta aikata abun da ya dace ta aikata a lokacin, amman so ya rufe maka ido taya kake ganin zata bada rayuwar mijinta saboda Zahra? Ka auna kanka a matsayin yadda kake son Zahra da kuma yadda ita ma take son mijinta, miyasa baka dora abun a mizani na hankali da yardar da kaddara ba? Ta ya kake iya gusar da farincikin wani saboda ka samu farincikinka Aliyu?”
Ya kalli Ammy.
“Ta yadda Deen ya gusar da farinciki saboda ya samu nasa farincikin, ta yadda Dr ta gusar da farinciki saboda ta samu nata farincikin”
Dr Zainab ta sauko daga saman kujera da take zaune ta zauna kasa kamar mai neman gafara.
“Wallahi ban san son da kake yi ma Zahra ya kai haka ba Abiey, da na san da cewa bayan ka rasa Zahra zaka shiga wani hali, da babu abun da zai hana na salwantar da rayuwar mijina na baka farinciki, ana canja miji Abiey amman ba a canja dan'uwa, wata kila yadda abun nan ya dame ni kai kanka be dame ka haka ba, kawai bana fada ne saboda ko na fada ba zaka yarda da ni ba, I'm so sorry Abiey”
Ta karasa tana fashewa da kuka, lumshe ido yayi ya hade yawu.
“Duk wata yar'uwa da zata so ka a duniyar nan Aliyu tana bayan Zainab ne, haka duk wata uwa da zata so ka bata kai uwar da ta dauki cikinka ta yi nakudarka ta haife ka ba, kai ne dana na hudu, amman yadda nake nuna maka kauna da kulawa bana nunawa saurana, ka samu gata da soyayyah ta ko'ina sai dan ka rasa Zahra zaka kasa hakuri, Yanzu da ace ni Allah ya dauke ya bar maka Zahra fa? Yarinyar da ta hadu da kana kana sa hakora talatin da biyu? Haba Aliyu kana ganin dadi muke ji a halin da kake ciki? A maimakon ka kwantar da hankali muma mu samu natsuwa sai nemi daga mana hankali ka bata mana rai? Ni fa mahaifiyarka ce, wannan kuma yar'uwarka ce”
Ya sauke ajiyar zuciya da karfi ya sauke kansa kasa, gaba daya jikinsa yayi sanyi da kalaman da Ammy ta yi masa, ta wani bangaren tana da gaskiya sai dai wani lokacin son Zahra kan rufe masa ido ya kasa ganin komai...
ZAHRA POV.
A tare muka ci naman da ya siyo mana, sannan muka sha ice cream kana muka tashi muka gabatar da Allah isha'i a tare. Bayan mun gama ya dauko min kayan bachina na saka shi ma ya saka fajamas dinsa sannan ya fita ta rufe mana gida, dawo muka haye gado muka kwanta sai ya kunna wayarsa ya shiga YouTube ya kunna mana wani american film mai kyau, Tun muna kallon tare har bachi ya fara daukata, gyara min kwanciyata yayi a jikinsa sannan ya tofe ni da addu'o'i. Daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba sai safe.
Bayan mun gama sallah asuba ya na dauko alkur'ane na saka a gabana ina karantawa, sai ya kwanta kusa da ni yana lazimi.
“Ina kwana”
Na fada bayan na gama karantun na mana addu'a, sai da ya sumbanci goshina sannan ya amsa min fuskarsa da murmushi kamar kullum.
“Good Morning My Love kin tashi lafiya ya baby na”
Ya shafa cikina, sai na kwanto jikinsa cikin shagwaba.
“Baby kan yau gurin Hajiya take son zuwa”
“Aa ayi hakuri sai wani lokacin”
Na kara bata fuska.
“Ka san fa mun dade ba mu tafi ba, ina dai ina marmarin Hajiya gaskiya”
“Shikenan, zamu je anjima”
Na fara masa kukan shagwaba, saboda na san idan muka je tare ba dade zamu yi ba.
“Aa gaskiya ni kadai zan tafi idan dare yayi sai kaje ka dauko ni”
Ya fada kafadunsa.
“Duk yadda kike so Babyna”
Na yi murmushi, sannan ya dauke kur'anen ya aje ya rika ni na tashi zauna zuwa bakin gado, da taimakonsa na hau saman gadon na kwanta ya lullube ni ban farka ba sai 9:14am ko da na bude ido ya gama gada mana abun da zamu karya kuma ya share ko'ina na gidan ya wanke kayan da muka bata jiya ya goge dakin da falo komai sam kamar mace, dakina sai kamshin turaren wuta yake na burna da ya kunna.
“Deen”
Na kira sunansa, sai ya aje wayar da yake game da ita ya shigo dakin.
“Yeeeee Babe ta farka”
Na yi dariya.
“Sannu da aiki Allah ya maka albarka”
Yayi murmushi ya saka kansa tsakanin kirjina yana wasa da su.
“Good morning mine...”
Na yi dariya mai sauti na kai hannu na shafa kansa sai ya dago ya kalleni.
“Zahra wai wane bokan kika bawa sunana ne? Kullum safiya ta Allah sai na ji kaunarki ta yau ta fi ta jiya miyen sirrin fada min nima na mallakeki na huta”
Dayan hannuna na kai ya kama lips dinsa na ja har sai da yayi kara.
“Sirrin yana cikin nan”
Yayi murmushi mai sauti, ya hau saman gadon ya rumgume ni. Ko da sha daya ta yi har na shirya abun ka da mai neman kuka hausawa suka ce an fada masa mutuwa, daman can ni yawo a jinina yake tun kamin na yi aure da zarar safiya ta waye na bar gidan kenan sai kuma dare, babu irin dukan sa ba amin da horo amman bana dainawa akan yawo, har suka gaji suka saka min ido.
Kayan makeup ya dauko ya shafa min hoda yayi min simple makeup da dan man lefe, I'm professional makeup artist kayan yasa bana rasa kayan kwaliya a gida duk da kasancewar ya hana ni yin sana'ar yanzu, amman shi ma ta masa amfanin domin gashi ya koya har yana min.
“Kin yi kyau, amman kin san nikab zaki saka ko? Idan kin je gidan Mama sai ki cire”
“Ba gidan Mama zanje ba fa, gurin Hajiya”
Na fada da sauri domin ko kadan bana son tafiya gurin mahaifiyara saboda ba na jituwa da ita, abu ne mai wahala na zauna a gidan na awa daya bata min fada ba, amman uwar mijina ko hararata ba zata bari ayi ba, idan ta gan ni kamar ta hade ni.
“Na sani, amman dole ai zaki fara zuwa gidan Mama ki gaishe ta tukuna ki wuce gidan Hajiya bayan magariba zan zo na dauke ki”
“Aa da isha'i dai”
Na fada ina kanne kafada daya.
“Na ji, amman yanzu tare zamu je na sauke ki gurin Mama, i just want you make sure babu abun da ya same ki”
“Na yarda”
Hijab ya dauko ya saka min ya daura min nikab, sannan shi ma ya cire tawul din jikinsa ya saka shadda. A tare muka fito cikin gidan yana rike da hannuna, har muka isa babban titin da zamu samu abun hawa, soyayyar mu akun kwatancen kuma abun burgewa domin mijina baya jin kunyar nunawa duniya cewar yana kaunata, kamar yadda ni ma bana shayin nunawa duniya komai akan mijina. Napep din farko da muka tara akwai mace daya ciki kuma da alama budurwa domin yanayinta da shigarta ya nuna haka gashi sai kallon mijina take.
“Ni dai ba zan shiga wannan ba, yarinya sai kallonka take kamar mayya”
Daga mai napep din har yarinyar kallona suka yi, Deen ya kalleta ya kalleni ya kalli mai napep
“Malam dan Allah yi hakuri ka wuce”
Uffan mai napep din be ce bayan dariya da yayi yarinyar kuma sai hararata take kamar ta ga kishiyar uwarta.
“Ta kalleni ta ga me? Yadda ta ga na rike hannunki ai ta san ni mijin tace ne”
“Ta ga kyau mana, ga ka fari ga kyau ga iya wanka”
Yayi murmushi.
“Ya kamata na sama rigar da aka rubuta mijin Zahra ita kadai na saka na rika yawo da ita a gari, so that duk macen da ta gan ni ta san ni mijinki ne zata kauce”
“Zan siya maka ma”
Na fada ina dariya. Haka dai muka yi ta hira, sannan muka samu napep ta daukemu mu kadai zuwa jan bulo. Bayan ya sallami mai napep din ya fara shiga cikin gidan na bishi a baya, daman dan gida ne kusan ma sai na ce ya fi ni gata a gidan. Mama na ganinsa ta aika aka siyo masa lemun kwalba da ruwan sanyi nima sai na ci albarkacinsa aka ba ni, ba mu yi awa daya da zama ba ya ce zai tashi sai Mama ta kalleni.
“Tashi ki bi mijinki, ba za ki zauna kina saka min kabli da ba'adi na abun da zan yi da wanda ba zan yi ba a gida”
“Haba Mama sai ki yi da takura mata shiyasa bata son zuwa gidan nan, ace mutum da gidansu amman ba shi da ikon sakewa”
Deen ya fada yana kallon yadda na bata rai.
“Aa nan ai gidana ne, gidancan na can gurinka ba yadda zata hanani shakatawa”
“Ni daman ba nan gidan zan zo ba, kuskure aka samu”
Na fada ina turo baki, sai jin na yi ta buge min bakin.
“Ba zaki daina wannan ture turen bakin ba? Tun kina gidan nan na hanaki wannan abun wato ba zaki daina ba ko Zahra”
Kuka ne kawai Deen be yi ba, kana kallon fuskarsa kasan be jidadi ba.
“Mama zamu tafi”
“Da dai yafi da wannan abun haushi ba dan cikin nan ba sai na sa yayanta ya zaneta yau Wallahi”
Shi ya riga fada ni na riga mikewa tsaye daman nikab kawai na cire a take na daura abuna na nufi kofa, shi kuma ya saka hannu aljihu ya ciro kudi ya aje mata.
“Allah ya maka albarka ke kuma Allah ya shiryarki ya sa ki yi hankali ki gane kin girma, har yanzu tana nan da rashin iya girkin ko?”
“Aa da zamu fito ma ita ta girka”
Yana rufe baki na yi karaf na ce.
“Wallahi Mama ban iya ba, kullum shi yake yi, ai dai gidan mijina ne ba nan ba balle ki ce zaki doke ni da girmana”
Wannan karon dariya ta yi ta girgiza kai, Deen ma murmushi yake sai da muka fito sannan ya rika hannuna muka kama hanyar titi. Muna shiga napep bata sauke mu ko'ina ba sai rijiyar zaki gidan surukaina. Da gudu na fada cikin gidan ina jin kamar an biya min makka ita ma ta fito da sauri ta rumgume ni.
“Oyoyo 'yata”
Bahijja ce ta firo tana hararata.
“Ai fa yau mun shiga uku, tun da ta zo ba zan sake sakewa ba a gidan nan”
Na mata gwalo, tabbas idan na zo gidan bata da hutu komai nake so ita Hajiya take sakawa ta yi min abinci ma sai wanda nake so ake girkawa. Bayan mun shiga daki ya shigo ya gaisa da mahaifiyarsa a lokacin ba hijab ba har riga na cire na ja zanen na zuwa saman kirjina na haye gadon Hajiya ya kwanta, be wuce minti talatin ba yayi mana sallama ya fita da niyar anjima zai dawo ya dauke ni. A gidan na wuni, da rana Hajiya ta min kwadon kanzo da zogale na ci, da yamma ta siyo min cornflakes na sha da dare kuma ta yi min tuwon shimkafa da miyar ganye na ci iya cina har sai da na rasa gurin numfashi. Ina gama sallah isha'i na shirya na fito waje kasancewar an dauke nepa, kuma ba gidan masu abun duniya ba ne balle a kunna min engine, na zauna kan tabarmar da Hajiya take zaune na dora kaina a cinyarta.
“Hajiya solar ku ta lalace?”
“Eh Wallahi aikin Bahijja ne, kin san komai ita nata sai ta yi shi da hauka”
Dariya na yi Bahijja ma dariya ta yi.
“Hajiya dan kin ga Zahra kike min wulakanci?”
“To ga yata me zan yi da ke?”
“Uhmmm Hajiya fada mata dai...”
Na fada ina hamma. Shiru shiru har goma na dare Deen be zo ba, hakan yasa na kira shi a karamar wayata, be daga ba.
“Be daga kiran ba”
Na fada ina Kallon Hajiya, sai ta dan kalleni ta dauki wayarta ta kira shi ga mamaki na sai na ji tana magana da shi duk da kasancewar ba zan iya jin muryarsa ba, bayan ta sauke wayar ta kalleni.
“Yace wai ki kwana nan, dare yayi sosai kuma anyi fada a unguwarku wai police suna kame ba zai iya fitowa ba”
Gabana ya fadi, domin a iya sanina Deen baya yarda na kwana a wani guri ba kusa da shi ba.
“Amman miyasa be daga kirana ba?”
“Wai yaje ya daga sai wayar ta tsinke, zai kira kuma sai na kirashi”
Ban sake cewa komai ba, sai dai ina ta kallon wayata ina jiran kiransa ya shigo min domin mun saba idan har na kwana ba gida ba kamar idan tafiya ta kama zuwa wani gari to zai kira ni a waya mu yi hira, amman shiru be kira ni ba, yanayin Hajiya da Bahijja sai ya canja, sai dai ban ce musu komai ba suma kuma basu nuna min wata wani abu ba, sai dai ni na karanci damuwar dake fuskarsu wanda suke kokarin boyewa.
Washe gari bayan Hajiya ta yi min tea kuma ta dumamamin tuwon jiya, ga koko da kosai da ta saka aka siyo min duk ni kadai, amman na kasa cin ko daya saboda ban ji muryar mijina ba, na kai hannu na dauki wayata na kira shi sai ga kiransa ya shigo.