Free chapter · Read without an account

16.

by Nusaiba · SARAUTAH TAH CE

👑👑👑👑👑


*SARAUTA TAH CE*





*DATA...🗣️DATA...🗣️🗣️DATA...🗣️🗣️🗣️*



*INA MASU SON SIYEN DATA AKAN FARASHI ME SAUKI? YAU GA GARABASA TA SAMU💃🏻 DATA ME SAUKI AKAN FARASHI ME RAHUSA🥰👌🏻 NUCEEYLUV NA MUKU MARABA DA SIYEN IYA KUDIN KA IYA SHAGALIN KA🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️💃🏻*



*500MB - N200*

*1GB - N300*

*2GB - N600*

*3GB - N900*

*5GB - N1500*



*1 month validity*


Call👇🏻 or cht me private👇🏻👇🏻


***


*ANA TURO KUDI TANAN👇🏻*


Via....1445626295 Nusaiba Mustapha Access bank.


*BANA KARBAR KATI PLS👏🏻😁*



*KUNA TURO KUDI ZAKU JI ALERT DIN DATA INSHA ALLAH BABU BATA LKCI🙅🏻‍♀️ KO BANA ONLINE KU KIRA DIRECT A SAKO MAKU DATA😹👌🏻*





*Free page*




*Wattpad*

@nuceeyluv





By

Nuceeyluv😘




16....





Kafin ace bilqees tayi Wani yunkuri tuni yareema yaseer ya iso wajen idonsa a kanta, dagowa lauwali yyi d nufin yiwa bilqees mgn sai kuma yaga Wani mutum tsaye a kansu kikam ya harde hannayen sa Yana karewa bilqees kallo,


"kutm*r ub*n can kayyasa Wanne Dan tsinanniya ne Kai da zaka tsaya akan ma'aurata kana kare masu kallo saikace maye?"


Lauwali ya furta Hakan a zuciye Yana takowa gaban yareema yaseer da ko gizau beyi ba bare yasa ran dashi yake mgn.


Kirjin bilqees na bugawa da sauri2 tayi saurin Shan gaban yareema yaseer tana wara hannu jikinta na rawa Tace,


"Shine fa bakon."


Tayi Hakan da nufin dakatar dashi Dan taga alamar Kai masa Addar hannunsa zaiyi.


"Ba... me??"


"Bako."


Bilqees ta bashi Amsa d sauri tana girgiza Kai.


"Dur***n uw** billahillazi idan na yadda da tarayyar ku shege nake, Wannan gardin zan bari ya dinga rabar ki? Ke kinsan yadda nake d kishi kuwa? Al-kur'anin Allah saidai ya fice daga kauyen Nan yau, yanzu ma basai anjima ba Dan bazan juri ganin ku tare ba."


Bilqees zatayi mgn taji hannun yareema yaseer ya kamota ta Baya da nufin su tafi domin hayaniyar da lauwali keyi duk ta isheshi sannan tashi guda yaji zuciyar sa najin zafin mutumin tun bayan daya shanyo kwana zuwa layin su bilqees din ya gansu tare take yaji Wani mugun Abu ya soki zuciyar sa.


Juyowa tayi a firgice tana shirin kwacewa kafin lauwali ya farga da Hakan yareema yaseer yaki sakin hannun saima Janta daya fara yi akan su tafi.


Tsalle lauwali yyi ya dire a daidai saitin tsakiyar bilqees da yareema yaseer Yana huci bayan idonsa ya kyallo yadda yareema yaseer din ya rike mata hannu. Zaro takobin sa yyi yana zare ido yace,


"ko ka saki hannun matata ko billahillazi na shafce maka hannu."


Yatsina fuska yareema yaseer yyi beyi mgn ba ya dubi bilqees d idonta ya fara kawo ruwa tace,


"Dan Allah ka sakar min hannu Annur."


Dauke kansa yyi da sauri yanajin bazai iya sakin hannunta ya barta da Wannan mutumin da zuciyar sa taki aminta dashi tun farko ba.


Ganin haka lauwali ya daga takobin sama zai Sara bilqees tasa Kara tana janye hannunta d karfi yareema yaseer yaki saki, dayan hannunsa yakai kan hannun lauwali d beyi tsammani ba yaji ya rike masa shi tamau. Bilqees d tayi kasa d kanta taji shiru Hakan yasa ta dago d kanta anan taga yadda lauwali ke kiciniya Yana son kwace Hannun sa me dauke da Adda daga yareema yaseer ya kasa.


Mmki ne ya isheta sai kawai ta zuba masu ido tana kallon ikon Allah. Har lkcn lauwali huci yake yana janye hannun Amma kamar Wanda aka daure Masa su da igiya Sam ya kasa cire hannun nasa daga rikon da yareema yaseer yyi Masa.


Tun Yana mmki kasa-kasa har Dan shakku ya fara kama shi Yana zare ido yace,


"Idan ba Aljani ne Kai ba shege nake, kur'ani rikon rauhanai kamin ka sakeni tun kafin nayi kuruwa yanzu dakarun Aljanu na su fito daga daji."


Zuba Masa ido yareema yaseer yyi yaga sai Wani huci yake kamar Wanda yyi dambe Hakan yasa ya sake hannun nasa Yana turar dashi can gefe hade d Jan tsaki. Taga-taga lauwali yyi kamar Zai fadi sai kuma yyi kokari ya cake yace,


"Idan na yadda da Wannan tsafin naka kace ba sunan uwata lawisa ba, na rantse da Allah saina Karya duk karfin tsafin da kke dashi ayau dinnan"


Lauwali ya furta Hakan yana juyawa da sauri zai tafi, sai kuma ya juyo yana kallon bilqees data bishi da kallo yace,


"ki gayawa tsohon ki jibi zanzo a daura Mana aure zanga Dan shegiyar dazai Hana..."


Yana Ida mgnr ya juya Yana ci gaba da tafiya batare daya sake waiwayowa ba.


Sauke ajiyar zuciya bilqees tayi tana dafe kirjin ta a lkcn yareema yaseer ya sakar mata hannun ya Kuma kafeta da ido. Saida ta nutsu kafin ta dago tana duban sa fuskar ta a daure tace,


"meyasa dazu Ina maka mgn kayi banza dani? Bakasan mutumin can yanada illah ba?"


Tabe baki yareema yaseer yyi yace,


"Illah? Kamar ya illah?"


Bilqees tace,


"Badan Allah ya tsare ba kana tsammanin zaka sha ne daga wajen sa? Yadda yyi niyyar sare maka hannu tsaf sai yyi Dan ba mutunci ne dashi ba, Dan haka Nan gaba idan ka ganshi ka kiyaye domin komai zai iya faruwa."


Gani tayi yyi murmushin gefen baki kafin ya hade rai Yana yatsina fuska yace,


"Zamu gani"


Bilqees tace,


"Ban fahimce ka ba me kke nufi?"


Yareema yaseer ya ware hannun sa yace,


"Nothing."


Bilqees zuba Masa ido batayi mgn ba sai taga yyi murmushi a hankali yace,


"Meya faru?"


Bilqees ta kawar da Kai a hankali tace,


"Dan Allah zaka koyamin karatu?"


Gwalo ido yareema yaseer yyi yace,


"karatu Kuma? As in how?"


Bilqees tace,


"harda Ingilishin ma."


Yareema yaseer yace,

"kamar ya? Bakiyi karatu bane?"


Bilqees ta girgiza Kai da sauri tace,


"Nayi primary shekara shida saidai dakyar nake iya rubuta Sunana bayan shi bana iya rubuta komai."


Da mmki ya rike haba shikuwa a nasa duniyar gani yake da karatun ma aka haife shi Dan haka yace,


"Toh ni d ban shekara shida Ina karatu ba taya zan Koya maki?"


Kallon tausayi tayi Masa, wai be taba shiga aji ba toh saidai batasan matakin karatun nasa ba dai, bilqees tace,


"A cikin naka tunanin zaka fara koyar Dani, kamar dai sunayen mutane, dabbobi,da abubuwa marasa motsi."


Shiru yareema yaseer yyi yana tunani can ya yatsina fuska yace,


"ban gane ba."


Bilqees tace,


"kaga yanzu Ana kirana da bilqees ko?"


Ya gyada Kai, tace,


"Toh sai kayi amfani da kalmomin da kke ganin ya dace a cikin tunaninka ka rubuta Sunana."


Yareema yaseer ya danyi shiru kadan Yana maimaita sunan bilqees saiya fahimci harafin da zaiyi amfani dasu a hada sunan a hankali yace,


"B..."


Bilqees ta gyada Kai da sauri tana murmushi


"I..L..Q..E..E..S. BILQEES."


Yareema yaseer ya furta Hakan yana murmushi. Bilqees ta washe baki sosai tace,


"haka yake Wlh. Dama iya Sunana na iya rubutawa yanzu saika koyamin sauran kaji? Zan dinga fadan Abu Kai Kuma saika fadamin yadda yake kaji?"


Zuba mata ido yyi bilqees ta girgiza shi tace,


"kanaji na kuwa?"


Yareema yaseer yace,


"Amma meyasa kikeson karatu haka?"


Bilqees ta danyi shiru yanayin ta na canjawa tace,


"Wannan shine buri Mafi girma Dana taso dashi tun Ina 'yar karama ta, tun muna zuwa primary nake kaunar karatu.


Dukda dai ba Wani karatu ake sosai ba sai muyi wata kafin Azo a koyar damu dake malamin kwaya dayane aka turo daga birni shima daya ga wahalar zuwan yyi nisa da Inda yake ya yage.


A haka zamu je makaranta babu malami mu karaci zaman mu, wasu na dinkin hula wasu na Saida kayan kwalama a haka har lkcn tashi yyi mu koma gida ba inifan, ba sandal, ba komai dai a haka har muka shekara shida aka yayemu ko nace muka yaye kanmu domin aji daya ne dal.


Yaro idan ya shiga bazai bar ajin ba saiya shekara shida a ciki sai a fita na baya wato kananne mu Suma suka fara zuwa mu Kuma mukaci gaba da sana'ar mu a dandali,


Naso ace inada wata hanya da zanje birni da kuwa nayi karatu domin shine burina."


Kallonta yake tun dazu Yana sauraron ta harta gama ya sauke ajiyar zuciya kafin yace,


"Alright zanyi iyakar bakin kokari na naga kinyi karatun akan Abinda na sani."


Murmushi bilqees tayi tace,


"Da ka gama min komai a rayuwa kenan, Wlh shine kadai Abinda nakeso a duniyar Nan, domin ko aure baya cikin lissafin rayuwata, bana son aure, na tsani Aure Amma da alama sai anyimin dolen d bana so..."


Ta Ida mgnr bakinta na rawa yareema yaseer ya rikota zai rungume ta kwace d sauri tana waige2 tace,


"A kofar gidanmu muke fa? A kowanne lkci Wani Yana iya ganin mu Dan Allah ka daina."


"Sorry."


Ya furta a hankali Yana matsawa can gefe yana zama akan dakalin kofar gidan nasu.



Wata mata dake bayan su ta rike haba tana afkawa cikin gidan nasu bilqees batare da sun lura da tsayuwar ta a bayansu tun farko ba.


"Yaya Zabba..yaya Zabba."


Haka ta dinga kwarara Kira tun daga kofar gida. Zabba'u da komawar ta daki kenan ta leko d sauri tana kallon me kiran nata ba kowa bace face Saude kanwar ta 'yar autar su wacce batayi aure ba har yanzu kusan shekara ta 20.


Gwalo ido inna Zabba tayi tace,


"Auta yau kece a gidan namu."


Saude ta jefar da ledar buhun data kullo kayanta a ciki tana zubewa akan ledar buhun data ga an shimfida tace,


"sammako nayi na taho a kafa."


Dafe kirji inna Zabba tayi, tace,


"Lpy dai ko?"


Fuska a hade Saude tace,


"Inafa lpy? Ai babu lpy Sam Wlh."


Gwalo ido inna Zabba tayi tana kamo hannunta tace,


"ke tashi mu shiga daki zancen bana tsakar gida bane"


mikewa Saude tayi tana tafa hannu tace,


"Na rantse da Allah idan na yarda shegiya uwata ta haife ni."


Inna Zabba ta fisgota d sauri tana tura keyarta cikin daki itama tabi bayanta tace,


"ke saude wanne irin shashancin banza kike fadi ne yanzu? Sai mgn kike na kasa gane Inda kika dosa gashi bakin ki yaki shiru kalan kishiyata taji suyi Mana dariya sakarya."


Tura baki Saude tayi tana gyara Dan kwalin ta tace,


"Toh duk ba a gidan Nan aka batamin ran ba."


Da mmki inna Zabba tace,


"A gidan Nan Kuma? Toh wanne Dan iskan ne ya taba ki ban sani ba?"


"Wa ancan mayun Mana kishiyarki da 'yarta."


Kan inna Zabba ya daure tace,


"Meya hadaku?"


Saude taja majina ta hadiye kafin tace,


"Haka kurum Dan azabar maita su Rasa zuciyar Wanda zasu lashe saita lauwali? Sbd sunga yyi suna akaf kauye da kewaye? Toh Wlh bazata sabu ba."


Inna Zabba tace,


"Toh ke Ina ruwanki da kasancewar su da lauwali? Me Kuma za'ayi da lauwali Allah na tuba."


Gwalo ido Saude tayi kafin tace,


"lallema yaya Toh Wlh idan baki sani bama ki sani akan soyayyar lauwali yasa naki aure tun wuri dama can ba iska bace Ina sane."


Zaro ido inna Zabba tayi tana tafa hannu hade d tuno yadda Saude tayi tsalle ta dire tace bazatayi aure ba wai sarkin Aljanu ya aureta Ashe Duk Karya ne.


"Saude...?"


Inna Zabba ta furta d mmki, Saude ta juya keya tana girgiza a hankali tace,


"Tunda naji lbrin cewar Bilqees yakeso na kasa bcci jiya lbrn ya riskeni shiyasa ko bccin kirki banyi ba asubar fari na fito ayita ta kare Dan Wlh bazan bari bilqees ta kwace min lauwali da nake matukar so ba."


"Shikenan zauna"


Inna Zabba ta furta mata Hakan Suna zama akan dandalin kasan dakin kafin tace,


"kin Tabbata akan lauwali kikayo Wannan sammakon?"


Saude tace,


"Haba yaya zan maki Karya ne? Akansa na baro kauyen mu na taho Nan."


Shiru inna Zabba tayi tace,


"Toh amma gani nayi me zakiyi da lauwali? Wanda be aje ba bare ya dauka?"


Gwalo ido Saude tayi tace,


"Ashe kenan karamin sani kuka yiwa lauwali Toh ai kauyen su d namu ba nisa, wa billahillazi babu Wanda ya kaishi kudi akaf fadin kauyen su."


"Ke dgske??"


Inna Zabba ta furta Hakan tana zaro ido d sauri. Saude tace,


"kwarai ma kuwa."


Rike haba inna Zabba tayi baki na rawa Tace,


"Ashe da tuni na dade da tafka babban kuskure da nake goyon bayan aura Masa bilqees Ashe ban sani ba gidan hutu zan kaita."


"Atoh, kema Kya fada, Dan haka nazo ayi ta kare Dan bazan zuba ido wata yarinya can bilqees tayi min tsakiyar da ba ruwa ba."


Inna Zabba tace,


"Ai ni zuwanki yamin dadi Auta kan bala'i ai fasawar auren bilqees da Lauwali kamar anyi an gama ne yaseen."


Sai yanzu Saude ta washe hakora Yana dariya tace,


"haka nakeso naji daga gareki Al-kur'an."


Inna Zabba tace,


"Sha kurumin ki bari naje ayiwa tufkar hanci tun wuri."


Dakatar da ita Saude tayi d sauri tace,


"Wancan mutumin Dana ganshi da bilqees a kofar gida waye shi?"


Dawowa inna Zabba tayi ta zauna tace,


"Ba tare da lauwali kika gansu ba?"


Girgiza Kai Saude tayi d sauri tace,


"A'a Wannan fa Wani ne daban kamar ma b Dan Nan garin bane ko shine bakon da akace tazo dashi gari?"


Inna Zabba taja tsaki tana gyada Kai tace,


"Tabbas shine Dan me nacin tsiya koda yake itama yadda kasan kaska haka take."


Saude ta rike haba tana ci gaba da fadin,


"Harfa rungume ta fa naga yyi, billahillazi tantiririn Dan iska ne."


Gwalo ido inna Zabba tayi tana tafa hannu tace,


"Tabbas ruwa baya tsami banza duk yadda akayi akwai wata a kasa irin yadda suka nacewa junan Nan nasu dole akwai alamar tmby."


Saude tace,


"Ba shakka yaya ya kamata mu Samo mafita d wuri nidai lauwali ya rabu da waccar shegiyar."


Mikewa inna Zabba tayi tace,


"Bari na duba idan mlm be fita ba sai naji Inda zancen auren ya kwana."


Da haka tabar Saude da tafa hannu tana rantse-rantse tace,


"kur'ani na fiku iskanci duk Wanda zaisha min gaba saiya gwammace kida da karatu."


***

Dan kallon sa tayi sai taga ya rike goshin sa a hankali Yana cije lips, bilqees tace,


"Baka da lpy ne?"


"My head."


Yareema yaseer ya furta Hakan yana yatsina fuska sbd yadda yaji kansa na sarawa lkci guda. Matsawa tayi kusa dashi tace,


"Tashi mu koma can gidan a baka mgni kasha."


Ta fadi Hakan tana kallon d alama kansa yake nufi tunda shi yake rikewa. Beyi mata musu ba domin ji yyi kan nasa na Kara tsanani sai daurewa yake.


A kofar gida suka tarar da kawu Isa zai tafi Gona d sakin fuska ya karbe su yace,


"Ba yadda banyi ya zauna ba Wlh yace shidai bilqees tun asuba fa? Dakyar ma ya bari gari ya waye."


Ya furta Hakan lkcn da suka karaso. Bilqees tayi murmushi tace,


"Ina kwana kawu."


Amsawa yyi da murmushi yace,


"ki duba dakin nasa an aje Masa Karin kumallo."


Kallon gefen yareema yaseer tayi sai taga ya saka hannun sa a saitin kansa fuskar sa a yatsine tace,


"kan ne?"


Kawu isa yace,


"ciwon Kai yake?"


Bilqees ta girgiza kai tana fadin,


"dazu ya fara jin ciwon Toh Amma ban sani ba ko d ciwon kan ya kwana."


"Ikon Allah, ciwo farat daya haka? Toh Allah ya sauwake ki nuna Masa abincin yaci bari na kawo garin mgni ki jika Masa."


Bilqees tace,


"Toh."


Mgn tayi Masa suka shiga dakin daya kwana jiya, kayan Karin kumallo na jere a gefe Koko ne da 'yar tsala wacce taji yajin kuli sai kamshi take aka aje Masa a wajen. Zama sukayi bilqees ta tsiyaya Masa kokon a cup tana miko Masa gabansa tace,


"kasha Wannan bari na karbo mgnin"


Ta juya da sauri ganin sai cije lips yake alamar kan ya fara Masa tsanani. A hanya suka hadu da kawu Isa ya jiko magnin a kwarya yace,


"gashi ki bashi yasha."


Karba bilqees tayi ta koma dakin a lkcn Harya kwanta jikinsa na rawar sanyi a tsorace ta dafa shi sai taji jikin da zafi kadan a hankali tace,


"Annur..Annur..Ann..."


Bata Ida na ukun ba ya Amsa dakyar Yana bude ido a hankali. Sauke ajiyar zuciya tayi kafin tace,


"Dan Allah ka mike ga mgnin Amma ka danci Wani Abun kaji?"


Yatsina fuska yyi alamar bayaso Yana kokarin juya Baya bilqees ta kyabe fuska kamar zatayi kuka Tace,


"Dan Allah Kaci."


Jin yadda muryarta ta fara rawa yasa shi mikewa d sauri cikin dauriya ya miko mata hannu alamar ta bashi, miko Masa cup din kokon tayi yasha dakyar Yana matse baki a haka Harya Dan sha kadan 'yar tsalar kuwa cewa yyi bazaici ba bilqees tace,


"Toh karbi mgnin kasha"


karba yyi ya zubawa ruwan mgnin ido kamar bazai sha ba Amma yadda bilqees ta kanainaye Masa yasa dole ya kurba dakyar Yana yamutse fuska bauri duk ya dame shi.


Sakin ajiyar zuciya tayi ganin yasha din tace,


"ka kwanta ka huta kada ka taho zan dawo na sameka kaji?"


Gyada mata Kai yyi domin a yanzu ji yake kamar Yana dauke da kayuwa goma sbd nauyi a hankali ya sulale ya fadi Yana numfashi dakyar.


Zuba Masa ido tayi na 'yan dakiku tana mmkin Wannan ciwon kan na lkci guda? Koda yake Ikon Allah yafi gaban Nan.


Haka ta mike jiki ba kwari ta jawo Masa kofar ta fito lkcn kawu Isa ya tafi ta shiga cikin gidan suka gaisa da larai matarsa sannan ta Bata guntun abincin nasa daya rage larai mace me kirki tace,


"zauna ki cinye bilqees da alama kema baki Karya ba."


Girgiza Kai tayi da sauri tace,


"Nagode."


Larai tace,


"dadina dake akwai bakunta Wlh ayita miki tayin Abu kiki ci."


Murmushi bilqees tayi larai tace,


"zan fadawa kawun naki idan ya dawo nace kince...."


"Da Sauri bilqees ta jawo kwanon tana tare ta da fadin,


"shikenan zanci"


Saidai ta koshi kafin tabar gidan gaba1 bayan tayi mata sallama.


****

"Mlm ya mgnr auren lauwali da bilqees ne?"


Inna Zabba ta furtawa Mlm Musa Hakan lkcn da yake saka hula zai fice. Tsaki yaja Yana Bata rai yace,


"Ohon masu dai wai sai Nan da wata daya nifa wlh na gaji kur'ani zan iya bada ita sadaka a yanzu ma idan yanaso"


IInna Zabba tace,


"Haba ba'ayi haka ba, Toh Amma kace Masa yyi bincike akan bilqees din kuwa?"


Juyowa Mlm Musa yyi da sauri yace,


"Wanne bincike?"


Inna Zabba tace,


"Ah.. Ina nufin yadda akeyi a aure Mana ya kamata a binciki yarinyar Bata 'yan biye...biye ko?"


Tayi mgnr a rarrabe, gwalo ido Mlm Musa yyi yana gyara tsayuwar sa yace,


"Ke zabba'u kiji tsoron ALLAH bilqees din ce take biye2? akace maki bansan da kanta taki kula kowaba bawai Dan ta Rasa masoya ko bakin Jini ba?"


Kirjin inna Zabba ne ya buga d karfi tana jimamin da alama kafin da tayiwa Mlm Musa ya fara rawa tunda harya fara kare bilqees a gabanta Wanda ya kasance shine karo na farko a rayuwar su tun bayan data shigo gidan.


Da sauri tace,


"Allah ya baka hakuri ba haka nake nufi ba Wlh. Da akace ayi bincike a aure shine fa nayi tunatarwa bawai da nufin komai ba."


Tsaki Mlm Musa yaja kawai ya zari buhun ledar gabansa yyi gaba yyinda inna Zabba tayi sororo a tsaye a wajen dauke da mugun mmki.


Har Saida yabar gidan kafin ta koma daki hankalin ta a tashe Saude ta mike tana kallon yadda take safa da Marwa tace,


"Lpy dai yaya?"


Inna Zabba tace,


"Akwai matsala Saude ya kamata muyi Wani Abun."


Saude tace,


"Ban gane ba?"


Zarar gyalenta inna Zabba tayi tana fadin,


"Biyoni."


Ba shiri Saude ta zaro nata mayafin suka fito waje a tsakar gida suka tarar inna habi na shara suka banko mata harara ita kuwa ta girgiza kai tana fadin,


"Allah ya shiryeku."


~~~~

Direct gidan Alaramma Idi bilqees ta wuce sbd karbar mgnin Karya sihirin da yace zai Bata yau, tayi sa'a Yana gida suka gaisa a mutunce. Alaramma Idi yace,


"Ya kwanan bakom namu? L"


Bilqees tace,


"lpy."


Alaramma Idi yace,


"Toh Madallah karbi wannan jarkar"


karba tayi kafin yace,


"Addu'o'i ne na Karya sihiri da akayi da ganyen magarya ki bashi yasha sannan yyi wanka dashi ko kuma a samu tsumma mekyau ya goge jikinsa dashi Insha ALLAH matukar Asiri ne silar mancewar tunanin sa zai karye."


Da murna bilqees ta karba tana godiya tace,


"Allah ya saka da Alkhairi."


"Ameen Yah hayyu yaa qayyum"


Alaramma Idi ya Amsa d Hakan. Bilqees tayi Masa sallama ta tafi.


Inna habi kadai ta samu a gidan ba kowa duk sun fice, Hakan yasa suka samu sakewar yin mgn bilqees na nuna mata jarkar mgnin hade dayi mata bayanin Abinda Alaramma Idi yace.


Cikin gamsuwa inna ta gyada Kai tace,


"Allah ya fishshemu Alkhairi."


"Ameen Yah hayyu yaa qayyum."


Bilqees ta Amsa da hakan tana mikewa tace,


"Ya kamata na Kai masa yanzu domin na barshi bayajin dadi."


"SUBHANALLAH me Kuma ya samesa?"


Bilqees tace,


"ciwon Kai yakeyi daga Baya Kuma saiya fara rawar sanyi."


Cike da tausayawa inna habi tace,


"jeki Kai masa Wannan din da sauri Nima anjima zanzo na duba sa saiki koma wajen larai ki zauna yadda Zaki dinga duba shi lkci bayan lkci."


Bilqees tace,


"shikenan bari na kwaso sauran kayan itatuwan Nan kamar yafi sonsu."


Inna habi tace,


"toh ki Kai masa sai yaci."


Sallama tayi mata tabar gidan tana sauri ta samu taje wajen yarima yaseer da hankalin ta yake kansa tun dazu.


°°°°°° "Bir..bir..bokoto...tooto..tair..tsir...."


Lauwali ya furta wa'annan kalaman idonsa a rufe tsaye yake gaban wata katuwar kuka me kogina bakwai a jikinta Yana karanto Wannan Abubuwan wata farar wuta na tashi daga kowacce kofa tana nufar cikin gari...


Bude ido yyi tarr idon ya kada yyi jawur cike da fushi yace,


"Saidai uwarka ta haifi Wani yaseen"


Yana Ida mgnr ya juya Baya Yana nufowa cikin garin.



••••••

Gidan shugaban 'yan borin garin suka nufa inna Zabba da Saude Nan suka tarar baya Nan Dan haka suka dawo gida gwiwa a sake.


A kofar gida suka hadu d bilqees tana gyara mayafin da zata kaiwa yareema yaseer ya rufa sukayi kicibis. Dubansu tayi sai kuma ta kauda Kai kawai tayi tafiyar ta. Inna Zabba tace,


"Kur'ani wajen Dan iskan zata tafi"


Saude tace,


"kwarton ta dai."


Gwalo ido inna Zabba tayi tace,


"da kamshin gsky fa a mgnr ki"


Saude tace,


"oho dai nidai naga d idona Yana kokarin kamota, ita kuma saita juya tana waige2 kome tace Masa? Oho naga ya kyaleta, kinga kuwa akwai alamar Rashin gsky a tattare dasu."


Inna Zabba ta kama haba tana jinjina mgnr tace,


"ke taso muje mu ganewa idon mu, idan bamu Samu mgnin d zamu rabasu da lauwali ba ai munyi masu kazafin da zai wargaje Tsakanin su."


Da murnar ta Saude ta juya suka fara bin bayan bilqees din da Bata San sun buyota ba lkcn har tayi nisa ma ta shige gidan larai.


Kusan a tare inna Zabba da Lauwali suka yiwa kofar gidan tsinke, a tare suka ja Baya kowa na karewa Dan uwansa kallo sannan kowa da nufin Abinda yazo a zuciyar sa.


*******

Bilqees kuwa Gidan larai ta shiga sai taga kofar ta a rufe tadan zaga makota Hakan yasa ta dawo kofar gidan Inda yareema Yaseer ke kwance ta bude kofar a hankali hade da sallama.


Can ta hango shi jikin bango ya matse sai rawar sanyi yake yana karkarwa. Bilqees ta Karasa da sauri tana ware mayafin data zo dashi ta lulluba Masa a jikinsa take yareema yaseer ya bude ido lkcn idonsa Harya kada yyi jajur alamar Yana Shan wuya sosai,


Hankali a mugun tashe bilqees tace,


"Ciwon ne harya Kai haka?"


Ta Ida mgnr tana dafa fuskar sa sai taji fuskar tamkar garwashin wuta, da sauri ta zare hannun tana janyo jarkar data zo da ita na mgni tana tsiyaya a Wani wajen tasa kyalle mekyau ta dangwalo ruwan tana gogawa a bisa fuskar tasa sai taga ya lumshe ido jikinsa na Kara tsananta rawa.


Bilqees ta fara rudewa Hakan yasa ta balle rigar jikinsa tana Kara Dora kyallen dake d ruwa a tsakiyar kirjinsa ta manne Masa, dayan hannun ta dauke da kokon data zuba ruwan zata Kara dangwala tajiyo shi yana furta


"Ahhhhhh....!


Yareema yaseer ya saki Wani marayan Kara sbd tsananin sanyin da yaji, hade d fisgo bilqees din a birkice take ruwan kokon ya kware Masa gaba1 akan sumar kansa a gigice ya manneta da kirjinsa yana matseta sosai gaba1 jikinsa na girgiza sai kace Wanda aka jona da socket sai Kara matseta yake yana numfarfashi.


Bilqees tayi kokarin kwace kanta ta kasa domin ba karamin riko yyi mata ba hatta bugun zuciyar sa tana iya juyowa yadda take bugawa da sauri fat...fat...fat....


"Qalu innalillahi wa'inna ilaihin raji'un."


Bilqees tajiyo muryoyi daban-daban an saki salati an dire Ana tafa hannu.......




*Wasshh Nayi typing na jiya, yau, gobe Idan Allah ya kaimu.👌🏻😹*




*Zaki iya biyan kudin ki yanzu a saki a paid group*



It's 300 via... Access bank 1445626295


Nusaiba Mustapha


Then show your evidence ta Wannan number👇🏻



***.



*Zaki iya turo da katin 300 MTN ta Wannan number ****

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.