Free chapter · Read without an account
9
by Fadimafayau · Fajaruddeen
Da dabara irin tasu ta manya umman fajar ta gane Fa'iza bata da wani saurayi hasalima ta fiskanci yarinyar tafi maida hankalunta zuwa ga karatun ta hakan yasa yau ta kudiri niyar yima fajar maganar.
Zaune suke fajar nacin abinci yayim da ummansa ke ninke kaya yayi yayi ta bari ya kammala cin abincin ya ninke taƙi hira suke sosai irinta ɗa da uwa ummansa tace Deeni yadda ta kira sunan nasa yasa yasan abu mai mahimmanci take san su tattauna hakan yasa ya janye hannunsa daga kwanon abincin ya maida hankalinsa gabaki ɗaya ga umman tasa.
Na gaji da ce maka kafito da mata kana zuzzuƙewa hakan yasa na nemo maka da kaina yanzu bawai shawara nake baka ba inasan dole a ƴan tsukunnan kayi aure nida mahaifinka muna ɓuƙatar ganin jikokinmu indai baso kake kuma se mun mutu ba tukun kayi auren.
Sosa ƙeya yai kafin yace wallahi mami ba haka bane inaso in ƙarasa phd ɗina lokacin albashina yaƙaru yadda zan iya ɗawainiyar matar da ku naji aure dole kayi da yawa basa samun yadda kake samu sa'annan ɗawainiyar su tafi taka haka sukayi auren kaima haka zakayi arayuwa in kace se ka samu yadda kake so to kuwa abubuwa da dama zaka tsufa bakayi su ba komai daki daki ake binsa umarni nake baka ba shawara ba inma tsoron gurin zama kake ga ɗakimka nan dana mahaifin ka inma yai muku kaɗan se ku haɗa da ɗakin fatima inyaso ita se ta dawo nawa falon da kwana ku zauma kaida matar kafin Allah ya hore maka naka.
Anman umma....bata bari ya ƙarasa ba tace anman me kaga nasani yarinya ce baka samu ba ni nasamo maka yarinya mai hankali nida mahaifinka mun yaba da tarbiyyar ta gabansa ya yanke ya faɗi shikenan angama dashi yasan halin ummansa cikin ƴan ƙauyensu taje ta samo masa mata shida ko ƴar birnin ba kowacce yake ganin zai zaman aure da ita ba.
Kamar tasan me yake tunani tace faiza ɗalibar ka na zaɓar maka na yaba da hankalunta inasan kaje ku daidai ta a tsorace ya kalleta umma wace faizan kana da wata ɗaliba faiza da nasani ne anman umman yarinya ce fa yarimyar ni wallahi kallon ɗiya nake mata umma tasa salati faizan ce yarinya kaga katuwar budurwa kace kana mata kallon ɗiya tafa yi candy kai ina ka haifi kamarta.
Naji koma kallon me kake mata seka dena ka maidashi kallon mata kanaji na kaje ka sameta ku dedai ta na faɗa maka to umma yace ya ci gaba da cin abincinsa badan yana masa daɗi ba sai dan yasan in ya tashi yabarshi umma zata masa faɗa.
Yana gama ci ya shige ɗakinsa rai duk a tunkushe shi ta ina ma zai iya tunkarar faiza da sunan soyayya tabbas wannan umarnin na ummansa akwaishi da nauyi.
******************
Faruk ne tsaye ƙorar shagon da ke kallon mai awararsa kamar kullim yauma ɗim bata fito ba ya dubi mai shagom bayan ya amshi ledar da ya miƙo masa yace pls in tambayeka man inajinka inji mai shagon faruk ya nuno masa inda fatiha ke suya pls yarinyar can gurinfa address ɗinta nake nema mai kantin yai ɗan shiru kamin yace ehto gaskiya ban sani ba da yake ni ba ɗan unguwar bane anman ai tana fitowa da daddare ok inji faruk nagode yai gun motarsa da zummar zai dawo anjima ɗin.
*****************
Ita kuwa Fatiha gabaki ɗaya hankalinta yayi makaranta dan satinsu guda da komawa ta dawo ta tarar babansu yazo Allah ya temaketa bai ce daga ina take ba zatonsa taje gun suyarta ne sedai yau satinsa guda kenan yaƙi tafiya tasan karatu tuni yai nisa ga wayarta ta lalace balle taji ko ana karatum dan yanzu ta amshi numbobin wasu Yan ajinsu da suke ɗan gaisawa dan babu wanda zata ce tai sabo da shi ko ita.
Bata da ikon fitowa koda tsakar gidane yanzu zai hauta da faɗa bare kuma tace zata makaranta indai ba suyar awara ba shima inbe ganta da kayan ba bata isa ta fita ba.
Addu'ar ta kullin Allah yasa ya tafi ko ta samu taje makaranta dan tasan intai kuskuren tafiya yana nan yasamu labari tas zai koreta daga gidan dan yai rantsuwa kan cewar in ya sake ganin taje makaranta seta bar gidan ta rasa me yasa dan dai tasan bawai dan baya san boko bane tunda yayyenta da ƙannenta suna zuwa be hana ba inma dan ita mace ce ai shi yakai asiya da kansa tama kuɗi yake kuma biya mata komi.
Kiran dataji ya kwala mata yasata saurin goge hawayen fuskarta tai saurin ficewa gami da isa gunsa ta durƙusa tana faɗin gani Baba dan tsabar iskanci kina jina inata kiranki kikai banza wato ga ɗan iska ko mahaukaci na ihuu.
Dan Allah Baba kayi haƙuri tsaki yaja jibeta kamar wata ta kwarai hannu ya miƙa mata ta kalleshi alamar me kije duk kuɗin sana'ar nan taki ki kawom zatai magana ya daka mata tsawa jiranki nake ina sauri tai saurin miƙewa ta kawo masa bai ko irga ba ya tusa a aljihu yaja mashin ɗinsa ba tare da ko yima umman su fatihan sallama ya kaɗa kansa yai waje.
Fatiha ta share hawayenta duda ƙasan ranta na mata ɗaci sedai farin cikin tafiyarsa yafi yawa.
Ummanta ke bata haƙuri ta share hawayenta karki damu umma ni wallahi ko kaɗan banji haushin kwacen kuɗi da baba yai ba inda ina da wanda yafi haka duk zan iya bashi ba tare da damuwa ba sabida mahaifina ne yamin gata ya haifoni ta hanya me kyau wasu sunanan suna so ace suma sunada uba koda kuwa kullin komai suka samo se ya amshe ni abu guda ke damuna yake kuma sani takaici shine tsanar da baba yake nunamin.
Hawayen da ya tawo mata umma tasa hannu ta goge karki damu ki cigaba da haƙuri da yimasa addu'a Allah ya ganar dashi insha Allahu zai dena yanzuma ya fahinci abubuwa bai baine
💞 Don't forget to vote, comment and follow 💞
Umma yau bazani gurin awara ba inji fatiha Ibrahim yace to inji umma da ban markaɗo ba ai gabaki ɗayama yau an haƙura a'a gwanda dai yaje ɗin ko kya samu kuɗin zuwa makaranta goben kedai ki kintsa sosai tunda kince karatum safe gareku to umma ta shige ɗaki.
Kayan da zata sa ta ɗebo dan wankewa dan tun da babansu yazo bata samu tai wanki ba dan yanzu yace ta jiƙa gida ya hauta da faɗa.
Washe gari tsaf ta shirya sai makaranta koda suka fito daga morning lecture gurin zaman ta ta nufa wani ta hanga zaune agurin ta baya ta biyo hakan yasa bata gane ko waye ba kamar ta koma tadai ƙarasa yayanta fajar ta gani nanta taɗaɗa murmushinta ta ƙarasa.
Sallamar ta ce ta dawo dashi daga tunanin da ya tafi shima murmusawa yai suka gaisa yaɗan gyara ta zauna.
Kinsan harnai fishi taɗan waro dara daran idanunta masu ƙara mata kyau tana faɗin towa Allah dai yasa badani akai fishin ba yaɗan haɗe rai to dawa ye kuwa inba dake ba ta kuma waro ido ni kuma me nayi ace adawo hutu sati biyu ki ƙi zuwa tace lah wallahi nazo satin farko to anji satin da ya wuce me yasa bakizo ba tai shiru dan bata da amsar bashi ya kuma cewa kuma kika kashe waya.
Sai asannan tace wallahi wayar ce ta samu matsala ban samu nakai ta gyara ba shike nan anmiki uzuri anman karki kuma fashi tace insha Allahu ya miƙe bari ni in wuce yabar gurin.
Azahiri yazo gurin ne dan su tattauna abinda ke damunsa ko zata bashi shawara dan ya rasa ta yadda waishi zai iya zuwa gurin faiza bema san me zaice yajeyi ba saidai yadda yaga fatihan duk ta rame murmushin ma da take ya kasa ɓoye damuwar da take ciki yasa shi basarwa dan yana ganin indai mace yarimya Kamar fatiha zata iya ɓoye damuwarta har tayi dariya ina gashi namiji.
*****************
Faruk bai samu ya koma unguwar su fatiha ba sai yau sabida ayyuka da suka sha masa kai duda kuwa hankalinsa kaff yana kanta saidai yau ɗin ma baiyi sa'ar samunta ba saidai ya samu Ibrahim yana ƙoƙarin kunna wuta da alamu yanzu ya fito suka gaisa faruk ya zauna gefen bencin dake gun za'a iya cewa karo na farko kenan da faruk ya taɓa zama a irin wannan gurin.
Adabarance yake jan Ibrahim da hira duda ya kula yaron miskili ne bai cika san magana ba sai da yaga ɗan saki jiki dashi yake ce masa kwana biyu bakwa fitowa da rana? Ibrahim yace eh ai kasam ankoma makaranta bamu da lokaci ayya har yayar taka eh shiyasa yauma na fito dan ta gaji da ta dawo Allah sarki kace makarantar tasu da nisa?.
Eh ai kasan Buk new site ai da nisa sosai makam akwai nisa anan area din take karatun eh a buk ɗin take cike da mamaki faruk yace buk Ibrahim yace eh kafin faruk ya kuma magana Ibrahim yace ta nawa zan zuba maka ta ɗari uku ok yace ya zuba ya miƙa masa faruk ya amsa yabar gurin ba tare da ya tambayi abinda ya kawoshi ba wato address ɗin su ba dan ya kula yaron ya ƙosa ya tafi.
Koda ya koma gida mamaki yai tayi yadda yasan ɗaliban jami'a da ɗan bamzan girman kai musanman hausa fulani bai taɓa zaton za'a samu bahaushiya yar jami'a na talla ba yasan dai sauran yare akwai sosai anman dai hausa sai yakejin da wuyar samu tuni yarinyar ta kuma birgeshi ashe shiyasa idanunsa suke mata kallon ƙima ashe shi yasa yake ganinta a nutse ashe shi yasa yake ganin bata masa kama da ƴan talla ba ashe da illiminta tabbas me illimi a ko ina daban yake.
Shiko fajar tin randa sukai maganar faiza da ummansa ya dena zama hira agidan kai zaman gidanma sai ya dena shi duk dan kar ta taso da batun.
Yau ya samu ummansa tana lazimi sosai yaji daɗi dan yasan bata magama se ta kammala yace da Fatima tace mata ya fita har yakai zaure fatima ta fito da sauri tana faɗin yah kazo inji umma saida gabansa ya faɗi ya daure ya shiga ɗakin.
Saida ta idar da addu'ar sannan ta dubeshi ka kuwa je gurin yarinyar nam in kaje ya kukai yadda yake wani sun sunkwi da kai yana shafa sumar sa yasa ta gane be jeba kaje ne ta kuma tambaya dan tabbatar wa cikin rawar murya yake faɗin daman bari nai.....bata bari ya ƙarasa ba tace shikenan Deeni tunda ban isa da kai ba ban isa insa kayi ko karka yiba.
Shikenan karkaje kayi yadda kake so tai ficewarta yai saurin binta a baya yana bata haƙuri tai masa banza dan Allah umma kiyi haƙuri zanje karma kaje wallahi zanje yau inna dawo daga aiki shikenan tunda kace zaka na haƙura anman wallahi nasamu labarin bakaje ba karka nefi afuwata.
Murmushin dole yai zani ma shike nan jeka Allah yai albarka yace amin ya miƙe yabar gidan ta bishi da addu'a can ƙasan ranta batasan takura masa saidai ta fahinci inba haka taiba bazaiyi aure ba bata san ya rasa faiza dan tanaji ajikinta yarinyar zata zame masa alkairi.
💞Don't forget to vote, comment and follow 💞