Free chapter · Read without an account

13

by Fadimafayau · Fajaruddeen

Ta Ɓangaren Farida kuwa tun randa malam Fajar ya faɗa mata game da auransa Farin ciki ya barta sai dai sosai take basar da muradin zuciyarta take walwala dan ko Ma'u bataga wani sauyi na cewar tana cikin damuwa ba.


  Duk wani abu da zai ɗebe mata kewa shi take yi sai dai fa da ta zauna ita ɗaya tuni ɓacin rai ke rufeta duda Farida ta rage damuwa sai dai kullun damuwar mahaifinta cikin ƙaruwa take duda yanzu yaɗan samu kwanciyar hankali na ganin tana walwala.


 Ya rasa meke damunta duk binciken da zaiyi yai ya tambaye ta sedai ta buba ba komai hakan ke ƙara tsoratashi yake kuma zargin kansa na zaton abinda yaike ya shafi ɗiyar tasa har take fama da ƙuncin zuciya na haka kawai.


  ********


Ita kuwa Fatiha ganin kwana uku da bikin Malam bai zo makaranta ba duk sai tausayin kanta ya cika ta na amincewa da zata jirashi na yadda cewar yana santa kwata kwata ko sati baiba da aure har ya mance da ita in har da gaske yake yana santa koda baizo makaranta ba ai ko kiranta ne awaya in ma tsoron matarsa take ai yana fita salla da sai ya kirata yaji ya take.


  Hawaye ne ya wanke mata fuska tai saurin goge su gami da kallon wayarta ji take kamar ta kirashi sedai bata da tabbas ko baya gida karta kira ta haɗashi da matar sa duda tanajin koda tasan baya gida bazata iya tsaga ballenta ba har ta kirashi.


*******


Umman Fa'iza ce tafe zuwa wani shago data hanga nesa dasu dan siyo musu abinda zasuci dan mahaifin Fa'izar yace basai an faɗawa kowa abinda Faizar taiba hakan yasa da isha'i yace Bashir ya tafi gida kar suji shiru sannan ya gargaɗeshi da kar ya faɗa ma koda ummansa ne dan bayasan in Faizan ta tashi surutun tai yinƙuren kashe kanta ya dameta har ya kuma ƙara mata wata damuwar.


 Wajen tara mamin su Fa'izan tace da mahaifinsu Fa'iza ɗin Alhaji ko zata tafi gida tunda jikin nata da sauƙi mun bar yara a gida ga dare banajinma gidan a buɗe yake nasan bazai wuce su shiga maƙota ba hankalinsu bazai kwanta ba.


  Sai alokacin ya tuna da yaran shima hankalinsa ya tashi gasu duk mata biyu ne kawai maza suma ƙanana anman mai zai hana ni in zauna ke ki tafi kodan kiyo mana karin safe ya buƙata a'a Alhaji kai kaje ɗin sabida kasan zata iya farkawa inta ganka hankalinta zai tashi dan zatai tunanin ko zata mata wani abu sabida zuciyar tata duda likitan yace temporary ne.


  Yai shiru kafin yace haka ne bari inje ɗin yawwa inyaso sai zainab ta girka abincin nasan ma yanzu indai gidan a buɗe yake ta musu girkin dare ya shafa kan Fa'izar da take kwance bisa gadon masu jinya kafin ya wuce gida.


*********

  Deeni umma ta kira fajar da take gyarawa mahaifinsa kwanciya yace na'am umma daman game da aikin ka ne tumda yaji sauƙi ya kamata ka koma kasan da Allah muka dogara sa'annan da albashinka karkayi lefi na rashin zuwa ka samu matsala in yaso sai Adamu ko ummaru su dunga zama lokacin aikin kai ka dinga zuwa da daddare daman da yau nai niyar zuwa in bada bayani a'a kayi yadda nace ɗin to umma insha Allahu.


 **********

Umman Fa'iza ce zaune gefen gadon da Faizar ke kwance hankalinta duk atashe haka ma bashir dan tun safe yazo duda likita ya tabbatar musu da komai lafiya bacci kawai take saidai su hankalinsu yaƙi kwanciya ganin har azahar bata farka ba ido kawai suka zuba mata dan ko abinci duk sun kasa ci.


 Da kuka ta farka tahau ƙoƙarin cire ƙarin ruwan dake hannunta tana kuka ummanta da Bashir sukai gunta tana ganin mamin ta kuma fashewa da kuka mami dan Allah karkuce min ban mutu ba dan Allah suka hau rarrashinta baki mutu ba Fa'iza .


  Rushewa da kuka ta kuma yi tana faɗin me yasa kuka hanani mutuwa me yasa kuka ceci raina bacin kun rabani da mesona sudai sukaita rarrashinta dagyar suka samu tai shiru.


  Yinin ranar yinsa Fa'iza tai tana kuka inda basa gajiya wajen rarrashinta ciki kuwa harda Abbanta dan yagane faɗansa ɓata komai yake.


  Ganin taƙi cin komai ne ummanta ta fito dan siyo mata maltina da madara ko zasu samu ta sha.


  A gefen shagon ta tsinkayi muryar matashiyar budurwa na faɗin lah mami ina wuni kamar tasan muryar ta juya Fatima ƙanwar Fajar tagani suka gaisa Fati me kike anan wallahi Abbanmu aka kwantar tun randa abin ya faru ya faɗi ayya a ina ne Fatima ta nuno mata da hannu au bama nisa muje in duba shi.


  Abakin ƙorar ɗakin suka tadda ummansu Fatiman a zaune kan tabarma tana lazimi ba yabo ba fallasa suka gaisa da umman faizan nan ta mata ya me jiki ta ce da sauƙi inda shiru ya ratsa kamin mamin tace bari in shiga in dubashi sai in wuce.


  A'a inji umman Fajar basai kin shiga ba ganinki zai iya tada masa da ciwon munsamu yaji sauƙi hakanma ya isa Allah ya bada lada.


Murmushi mamin Fa'izan tai kamin tace haka ne daman Fa'iza ce baji daɗi ba Ayya Allah bata lafiya umman Fajar ta faɗa da alamun ƙosawa ba tare da ta tambayi me ya samu Fa'izan ba guba tasha mamin ta faɗa ba tare da damuwa da ƙosawar umman Fajar ɗinba.


Innalillahi wa'inna ilahi raji'un umman fajar ta faɗa hankali tashe nazone dam Allah in roƙi alfarma Fajar yazo yama yarimyar nan nasiha sabida tanajin zancensa gashi kuma Deenin baya nan Fatima bita kiga ɗakin in yazo seki rakashi.


  Sun miƙe zasu tafi Fajar ya ƙaraso gun Fatima tace lah umma ga yayan nan ba haka taso ba ko kaɗan bataso yaje ba sai dai ba yadda ta iya tace yawwa Deeni kaje wai Fa'iza ce tasha guba innalillahi wa'inna ilahi raji'un ya faɗa kamin yace Allah ya bata lafiya anman ai ina ganin basai naje ba.


Mami tai sauri cewa a'a dan Allah kazo muje ɗin ceton rai zakai zai magana ummansa tace kuje ɗin karku zauna rai ɓace yabi bayan mamin Fa'izan da ƙanwarsa da sukai gaba.


Thank you for reading 😍


Kai tsaye Inda aka kwantar da Fa'izan sukai ransa duk a ɓace dan gaskiya yadda ya tsara babu ganin Fa'izan a yan kwanakin nan sedai ya zaiyi umarnin ummansa ne dole yaje.


  Da mahaifinta suka fara cin karo ran Fajar ya kuma ɓaci ya haɗe rai ji yake kamar yaje ya rufe shi da duka sabida duk sabida shine mahsifinsa ya faɗi ganin Fatima na gaidashi yasashi daurewa shima yace Barka da yanma ya me jiki shima mahaifin Fa'iza ɗin rai ɓace ya amsa.


  Umman Fa'iza ce tace da Bashir ya shigar da su ɗakin ita kuma tai gun mijin nata dan fahintar dashi me yakawo Fajar ɗin.


  Suna shiga ɗakin Fa'iza tai zunbur ta miƙe tana kuka yai saurin ƙarasawa inda take yana faɗi yi zamanki ai zan ƙaraso yah dan Allah ka faɗan zuwa kai kace baka saken ba dan Allah kace mun mafarki nake.


 Ya girgiza kai Fa'iza ba mafarki gaskene anɗaura mana aure sedai baida tsawon rai bawai hakan dan lefin ki bane sedan haka ƙaddarar mu take ta kuma fashewa da kuka.


  Ya kamo hannunta kiyi haƙuri Fa'iza nasani ke mutunce me tunani gami da illimi hasalima hakan yasa naji kin dace da zamowa matata Fa'iza ki daure karki ban kunya dan Allah karki sa inyi zaton tarbiyya da illimin da na baku ya tafi a kawai nasan kina cikin ɗalibaina da suka fi kowa sanin wanda ya kashe kansa ɗan wuta ne ko ta gyaɗa kai.


  Ya kuma cewa to me yasa zakisha guba tai shiru haba Fa'iza ina illimin naki haba Faiza ko so kike inyi zaton baki yadda da ƙaddara ba tai saurin girgiza kai to me yasa zaki sha guba kan wani can da in anje lahira bazai iya miki komi ba tai saurin kallonsa eh kinsan dai ni a cikin duniya ma ba kowan kowa bane bare alahira me yasa zakisha guba sabida ni ko an faɗa miki ni kaɗai ne namiji ta girgiza kai alamar a'a.


  Kamin tace bakai kaɗai bane namiji saidai ni kai kaɗai zuciya ta takeso yai murmushin takaici kamin yace se kuma aka ce miki bazata kuma san wani ba meye anfanin shekara goma sha da kikai kina zuwa islamiyya inhar baza ki ɗauki ƙaddara ba ki kuma dage da anfani da illimin naki wajen neman sauƙi ta hanyar yawaita salloli da karanta alƙur'ani da zikiri ki kaiwa Allah kukanki ki roƙeshi ya baki mafiyi na duniya da lahira.


  Ita rayuwa Fa'iza bata taɓa zuwa yadda muka tsara ta saidai zamu iya yin farin cikin ciki ayadda tazo mana indai muka zamto masu tawakkali asannu ma se muga ashema yadda tazo manan tafi yadda muka tsara daɗi indai muna addu'a da haƙuri.


  Kinsan wani ta girgiza kai yace babu ta yadda daman zai zama farim ciki kawai ke cikin rayuwar mu dole akwai matsaltsalu da duhuwa lokaci lokaci sedai in aka daure komai lokaci ne sannu komai zai wuce musanman inmuka saka aranmu ita rayuwa gabakin ɗayanta ta kunshi sabon shafi kinga kenan da ka shiga wani sabon shafin shafin baya fa ya zama tarihi ko da antuna baƙin cikin bazai zama kamar lokacin da kake tsaliyar shafin ba inma kaima shafin nisa sedai ka dinga tuna lokacin baya ashe kuskure nai da na damu kan wancan abin.


  Nasiha sosai ya mata seda ya fuskanci zuciyar tai sanyi sannan ya mata faɗan karta kuma ƙoƙarin kashe kanta dik runtsi taji daɗi kamin ya miƙe ni zan wuce ki daure ki dinga cin abinci badan ranki yanaso ba sedan jikin ma za'a tambayeki yadda kika tafi dashi ran gobe ki kuma dinga Addu'a Allah ya yafe miki ya kuma baki miji na gari nima ki dimgamin Allah yaban mata ta gari kinji karki cireni matsayina na malaminku sedai ki mance cewar mun taɓa soyayya ta masa godiya ranta ya mata daɗi yanzu dan tanajin aranta kamar zata iya rayuwa yanzu.


  Ada Bashir yanajin haushin Malamin su Fa'iza dan tun tana yarinya in yazo yakan kaita makarantar ko kaɗan jininsa bai haɗu da malamin ba yadda yake masa kallo shine mutun ne me ji dakai har mamaki yake yadda lokacin Fa'izan na ƙarama magana kaɗan ai malam Deeni yayi abu kaza yace kaza se yau ya fahinci me yasa yaran kesan malamin nasu wato shi zuciyar sa me kyau ce sosai yaji daɗin nasihar da yama Fa'izan musanman da ya dawo daga rakasu yaga tana cin abinci wato taji nasihar malamin nata.


  Kwanan Fa'iza huɗu a asibiti aka sallameta duk ta saki ranta duda har lokacin zuciyarta bats mata daɗi sedai ta yadda da cewar malam inta basar lokaci ne zata nemi damuwa ta rasa.


  Kullin Bashir yana gidansu duk wani abu da zai rage mata damuwa shi yake mata mahaifinta ma yaji daɗin sauyawar datai yakuma ji daɗin bayanin da bashir ya masa na Nasihar da fajar ɗin ya mata tabbas shi kam dabadan rashin asali ba babu abinda zai hanashi bawa Deeni ɗiyar tasa.


********** 


Tsaf Fajarudden ya kintsa dan yau lecture ɗin safe yake da ita bakuma yasan ya makara hakan yasa bakwai ma yabar gida dan yana da nisa da new campus.


  Yana fitowa wajen goma ya duba time table ɗin su Fatiha dan yana da ita tun randa aka dawo ya karbo dan yasan lokacin da bata da aji ilai kuwa bata da aji hakan yasa ko office baije ba yai gun motarsa nan yajata sai agric.


  Ta baya ya shiga sedai bai hangeta ba hakan yasa ya ƙarasa gurin mamaki sosai yai na rashin ganinta zama yai gami da ciro wayarsa yahau kiranta seda ya kirata sau uku kamin ana huɗun ta ɗaga.


  Murya adaƙile tai masa sallama kamin ya amsa yace kina inane nazo gurin mu bakyanan ta turo baki kamar yana gurin naje wani guri ne ok kimaza kizo pls ina jiranki zamuyi magana tana da mahimmanci bai jira amsarta ba ya kashe wayar ranta ya kuma ɓaci mutumin nanfa ya rainan hankali yayi aurensa ya mance dani sannan yanzu koma yaji ina inane sedai kawai yaban umarni wai in wani zo.....


  Nasa dariya nace taɓ Fatiha kina da aiki wato kishi ke damunki kan mutumin da koma soyayya baku fara ba.


Farida ce zaune riƙe da hannun mahaifinta tana faɗin pls Dad kabarni inje ya ɗan kalleta haba Jariri na kin mance kuna da makaranta ne ki bari Semester tazo tsakiya se kije a break ɗin da kuke tafi pls Dad I really want to go nayi missing ɗin makurɗi dasu Hajiya pls.


  Naga kun kusa tafiya pls Dad kwana uku kawai kaga bama lectures ran friday da asabar ran alhamis kuma malami ɗaya ne kawai damu shi kuma yayi aure yana hutu seda gabanta ya faɗi lokacin da ta anbaci yayi aure ganin yadda fuskarta ta sauya ta shiga damuwa lokaci guda yasa Dad ɗin nata saurin cewa shikenan Jaririn Dady ki shirya se wani cikin yayyenki ya kaiki ta faɗa jikinsa tana murna Dad's my Dad I love u yai murmushi love u more suka sa dariya baki daɗi ya kamashi ganin yadda take annashuwa yaji inama ace ta dawwama ahaka.


Ran laraba tana dawowa ta shirya tsaf yayyanta suka kai mata kayan da zatai tsaraba zuwa mota kasantuwar duk suna da abinyi yasa Dady yace Driver ya kaita ita da Faruk haushi duk ya cika ta dan baida aiki sai tsokanarta ko kaɗan basa shiri tana ɗaga musu hannu suna ɗaga mata driver yaja mota sai makurɗi.


  Suna isa ko isasshen parking driver baiba ta fito tai ciki da gudu Hajiya babba na zaune Habiba na mata tausa ta faɗa kanta tana murna Hajiya ta tureta keni bansan sakarci karki karyani ta turo baki kai Hajiya Alhaji ya fito daga ɗaki yana faɗin zonan yar leleta kyaleta in bata sanki ni ina sanki ta miƙe tai gunsa tana faɗin ai nima na fi sanka yasa dariya nima nasani.


  Faruk ne ya shigo yana masifa kan shi ba bawan ta bane take ta ɗebo kayanta kuma driver bazai kawo mata ba tasa kuka tana faɗin Alhajina ka ganshi ko kyaleshi ni muje in ɗauko miki mantawa yai kina da bawan ki na daban tasa murna suka fice Faruk yabita da harara.


  Seda suka shigo da kayan sannan suka gaisa sosai kakan nin nata se nan nan suke dasu musanman ma ita daɗi duk ya cika ta.


  Fatahu najin labarin Farida na Makurɗi ya shirya shima sai makurɗi yadda kowa ke nan nan da ita inka ɗauke faruk da yake gwaleta shima cikin salon tsokana yasa ta mance da wani malam bare takaicin aurensa ji take kamar ma karta dawo garin kano tai zamanta makurɗin.


*********


Ta ɓangaren Fa'iza kuwa ta warware ta koma rayuwar ta baya farin ciki take sosai duda wani zubin takan tuna da malam ranta kan mata ɗaci sedai in ta kuna da nasihoyinsa sai taji sanyi.


 Abu guda yafi damunta ayanzu shine in ta fito farfajiyar su taga kayan gadon da aka siya na aurenta wanda gidansu fajar suka dawo dashi duk se hankalinta ya tashi hakan yasa koma zaure batasan zuwa bare farfajiyar gidan.


  Fahintar hakan yasa maminta sanar da mahaifinsu aikam ba shiri yasa aka kwashe kayan sosai hakan yamata daɗi ta kuma murmurewa.


  Dakansa mahaifinsu Fa'izan ya samo me aiki ya kuma fashewa Fa'izan bayan gidan inda yake da siminta ya siyo mata irin shukoki kalala harda ja mata fanfo bayan gidan dasu mesa na ban ruwa yayi hakan dan yasan arayuwar Fa'iza ba abinda ke ɗebe mata kewa sama da ta zauna taita shuke shuke.


  Hakan kuwa da yayi yai mata daɗi dan kusan koyaushe kazo gidan tana bayan gida tana faman shuka da kula da ƙananun shukokinta Bashir ma kusan lokacin sa kaf ya kwashe ya maidashi na Fa'iza da shukokinta dan da wuya kazo gidan bazaka tadda shi tare da ita suka kula da shukokinba hakan ya ƙara kusanta shaƙuwarsu duda daman can Fa'iza bata da wanda ta saba sama dashi shine yayanta aminta kuma abokinta.


  Yadda yake kula da Fa'izan yama ummanta daɗi duda can ƙasan ranta batasan shaƙuwar dake tsakaninsu sedai ayanzu farin ciki da kwanciyar ɗiyar tata shi yafi komai ko sa samu ta dawo hankalinta sosai ta dena tunanin mutuwa.


  ********


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.