Free chapter · Read without an account

Kashi Na uku 3

by Shuraihu Usman · Budurwar Sirri

BUDURWAN SIRRI

Gajeran labari

Marubuci Shuraih Usman

@hausaebooks.cf

@shuraih 99%

Page 3

.

Gargadi:- wannan littafi mallakar shafin hausaebooks ne don Allah kada wani ko wata ya juya wani bangare ko barin littafin nan batare da iznin wannan shafi ba karkashin jagorancin Shuraih Usman

.


na daure na mike tsaye na tunkari wannan kofa, ina isa bakin kofar na sanya hannu na bude , ko musu kofar baiyiba yabata wata kara "kikkir kikkirrrrrr" alamar ana bude kofar, kofa kofar ta gama wangamewa ta budu nan take nai arba da abun da ya tashi tayar mani da hankali ainun,kwakkwalwata ta kusan daina aiki,idanuwa na sukafara lumshewa a hankali tamkar me gyangyadi,gaba dayan lakar jikina ya mutu,!!!

.

Ba komai nai arba da shi ba face wata tsaleliyar kyakkyawar budurwa wacce saboda tsananin kyawunta ne nama kasa sarrafa kaina,

.

TABA RAKALLAHU AHSANUL KHALIQEEN, lallai Allah yayi halitta , ita dai wannan kyakkyawar mace wacce ta kasance bantaba ganin ta ba sai ayau, shekarunta ba za su wuce goma sha tara ba, tsananin tsabar kyawunta nema yasa har wasu dausayin fararen haskene ke bibiye da ita,

.

Na tabbata ko da cikin duhu ne mai tsanani wannan budurwa ta miko hannunta toh take duhun zai bace haske ya maye gurbinsa,

"Shuraih! "

Zazzakar muryarta wadda tafi na komai dadi aduniya ta katse mani tunanina , a irin salon yadda take kiran suna na, ji nake babu wanda ya iya kiran suna na face ita, koda wannan zazzakar muryar tata kawai mutum zai saurara toh da sai ya gwammaci ya saurara fiye da abashi kyautar makudan dukiya

.

Firgigit na dawo cikin hayyacina tamkar wanda ya farka daga barci na dubeta baki na sai kakkarwa yake amma na kasa fadan komai dakyar da sidin goshi na iya fadin "nnnna - m"

.

Murmushi tayi wanda ya kusa zautar dani don kuwa alokacin da gefen kuncinta suka lotse sai naga tama fi kyawu bisa kan da,

.

Koda taga halinda na shiga adalilin wannan murmushinn da tayi sai ta kyalkyale da dariya, ai saboda dadin sautin wannan dariya nata ban san lokacin dana sulale a kasa sumamme ba,

Iya abin da masarrafin kwalkwata ya iya dauka shine daukewar dariyar wannan budurwa daga nan kuma ban sake sanin meke faruwa ba

***

.

A hankali nafara bude idanuwana, mutane ne nafara ganinsu dishi dishi akaina, na mike na zauna sai a sannan ne kwalkwalwata ta dawo aiki hankalina ya dawo jikina

.

Na dubi mutanen da suke gefena suna yimini sannu, sai naga ashe ma yan mata ne kyawawa, sanye da fararen dogayen kaya, sai a sannan na lura da dakin danake ciki

.

Karamin dakine an kawata shi da kayan ado na mutanen da, zaune nake a kan wani luntsumemen katifa, wadda yake bisa wani katakon gado, na budi baki na ce wa yan matannan "su waye ku, a ina nake sannan waya kauni nan?"

Wata daga cikinsu tace ainan kana gaban birnin sin ne cikin garin LAJUJ

.

"Ina ne kuma garin lajuj, na tambayesu" na tambayesu cikin mamaki

Wacce ta bani amsa da farko ta sake cewa "ai garin lajuj garine na Aljanu don kowa daka gani anan garin aljanine, mutum dayace kawai ba aljana ba, amma itama ba mutum ba ce, kuma itace ta kawoka wannan birni namu, "

.

Cikin rudewa na mike a firgice ina neman hanyar gudu don kuwa na riga dana gama firgita da maganarsu,

Na nufi kofar fita daga dakin cikin gudu na kama mabudin kofan na murda take kofan ya bude

.

Ban jira komai ba na nausa a guje, wata doguwar hanya na gani ta mike santa wannan hanyar na zura a guje, ko waigowa baya bana yi,

ban dade da fara bin hanyarba sai na hangi wata kofa karshen hanyar, wannan kofa abude take,

.

Turus naja na tsaya a yayin dana shige cikin wannnan daki da yake da wannan kofa,

.

Zaune take akan wata luntsumemiyar kujera haryanzu wannan murmushin nata yana nan a fuskarta,

Ta dubeni tai mani nuni da wani kujera tace na zauna

.

Babu musu naje na zauna akan wannan luntsumemen kujera wanda saboda tsabar laushinsa sai danayi tsammanin ko bulalliyar kujerace,

.

Zamana keda wuya sai na cigaba da kallon kyakkyawar fuskarta wadda banki nayi shekaru talatin ina zaune ina kallo ba, karar budewan kofar dakin shine yaja hankalina inda na maida dubana ga wajen

.

Daya daga cikin matannan ne ta shigo tana dauke da wani faranti a hannunta mai dauke da akushi sai wani tambulan na zinare, tazo ta ajjiye a gabana

.

Tana ajjiyewa tayi ficewarta kyakkyawar budurwan ta dubeni tace "ga abunci nan kaci in kama sai muyi magana, "

Ba musu na bude akushin wanda yake rufe sai nayi arba da dafaffiyar kaza, sai a sannan ne ma cikina ya fara kuka na tuna cewa wunin ranar ban ci komai ba , kuma banji yunwa ba sai yanzu

.

Toh dama ina cikin wannan hali ina zanji yunwa, cikin kankanin lokaci na gama da wannan kaza banbar komai a cikin akushin ba sai kasusuwa, nan na kora wani lemu mai tsananin zakin gaske sannan nayi hamdala ga Allah

.

Koda ta fahimci na iddar da abuncin sai ta fara magana da daddadan sautin muryanta wanda kan iya zauta mutum, "shuraih ka sani cewa ni sunana haseena tun ranar dana fara ganinka shekaru biyar baya naji zuciyata ta kamu da tsananin sonka, naji babu wanda nake so aduniya sama da kai,

Tun a wancan lokacin na so na sanar dakai irin zunzurutun son dana ke maka Amma naji tsoron Abu daya, Wato naji tsoron SALMAN"

Haseena tayi shiru ga barin magana llokacin data sadda kanta kasa,

.

Na tsinci kaina acikin wani irin Ni'ima wanda tunda nazo wannan duniya ban taba tsintar kaina a ciki ba, wai ni take so tabbas abun da Al'ajabi

Cikin dakewa irin ta maza na dubeta bakina sai rawa takeyi nace HAS-sss Ena ta dago da kanta ta dubeni fuskarta na murmushi a gareni in ka ganta tamkar wata ran daren goma sha biyu

.

Nan da nan naji na samu kaina ina mai cemata "lallai babu mutumin da zaiyi arba dake baiji cewa yana sonki ba, tun dana fara ganinki nima zuciyata take bugawa ban taba gani ko jin labarin wata mai kyau irin nakinnan ba,, I na sssoosssonki Haseena"

.

Tayi murmushi sa'annan ta kama hannuna ta mike tsaye tace zo muje na gabatar dakai a wajen mahaifana, naji abun banbarakwai amma na dake nace mata masoyiya kafin muje mai yasa ba za kidan bani labarin wannan birni naku ba mai matukan ban Al'ajabi

.

Haseena ta dubeni da wani kayataccen kallo sa'annan Tace "habibina mai zai hana"

Muka koma muka zauna akan luntsuma luntsuman kujerun dake makare a cikin dakin

.

Haseena ta dubeni tace "shuraih sunan wannan birni namu LAJUJ kuma wannan birni bayana kan Duniyarku bace ta mutane

Wannan birni na Lajuj birnin Aljanu ne amma mun kasance musulmai kamar kai, mahaifina sunansa Nasaruddin kuma shine sarkin wannan gari namu.....

..Rayuwa haka take wakana yau lafiya gobe akasinta, dazu-dazu lafiya yanzu-yanzu rashinta

Allah ka baiwa dukkan musulmi marasa lafiya masu lafiya kuwa Allah ka kara masu ,,,,

Its 99% awakening from three 3 days sickness

Yo sai mun Hadu MAKO mai zuwa

Daga - ***

.

Marubuci:- Shuraih Usman

Typing:- Shuraih 99%

Hakkin mallaka (m) hausaebooks page


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.