Free chapter 路 Read without an account
_*SEVENTEEN*_
by Sadiya Auwal 路 BAKAR AYAH
____****馃枻馃枻****_____
馃枻 *BA茦AR AYAH* 馃枻
馃枻 _BOOK1_ 馃枻
Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
[ _瞥ar mutan Jama'are_ ]
*WATTPAD*
***
*AREWABOOKS*
https://arewabooks.com/u/sadeesakhna
______________****_______________
Page 馃枻17馃枻
Jikinta sanyi kalau tashiga cikin 蓷akin su Bombee,domin batasan mai zata ganewa idonta ba,saidai duk da hakan tana fatan Allah yasa karta ga abinda zuciyarta take raya mata.
Labulen 蓷akin ta 蓷auke ta rataye ,hasken rana yashiga 蓷akin,domin yabawa 蓷akin ishashshen hasken dazata ganta dakyau.
A kwance take ta rufe idonta kaman mai bacci,saidai kana gani kasan ba baccin take ba.
"Bombee"
"Na'am ta amsa a dake"
Shuru Daneji tayi kaman mai nazari kafin ta zauna a kusada ita.
"Shin menene ya farune kika sanja a lokaci guda,duk abinda akayi miki nasha fa蓷amiki kiyi ha茩uri,karki bari bacin rai ya sanja miki rayuwa,abinda kikayi kimsaka mu damuwa gaba蓷aya,so kike kijawo mana magana.
Yanzu inaso ki fa蓷amin mai kikayiwa Zulaiha danaji innayi tayi maganar?"
"Karya mata hannu nayi,sannan kuma nayi mata duka kaman yanda itama tayimin,sannan bandamu ba tacemin mayyah,amma ke tacewa mayyah,sannan tace inna isa nanuna ina son kaina,shiyasa na nunmata ina son kaina 蓷in"
"Me Bombee karya mata hannu kikayi,wai nasan gaji bazatayi shuru wannan zancen ya tafiba saita 蓷au mataki"
"Tsawon lokaci ai nima Zulaiha tana dukana baki taba cewa komai ba,shine ita danna rama saita 蓷au mataki,to ta 蓷au matakin mana"
"Kee Bombee yaushe kika fara yin maganar manya da wannan rashin ladabin haka,karki dauki wannan halin ki saka ranki,hakan babu kyau musamman ga mace"
Cikin halin damuwa Daneji tafara yiwa Bombee nasiha dajan hankali. Tun bayan kwana uku dama ta kulada yanda Bombee tafara sauyawa,koyaushe tana cikin fushi,abu ka蓷an idan akayi mata saita 蓷aukeshi da zafi,sannan idan abun mugunta yafaru tafi kowa dariyar mugunta.
Jiya da ragon mlm Ahmadu ya sunkuci inna laari a kunkumi,data fara dariyah har fa蓷uwa saida tayi,sabanin da da idan hakan yafaru saidai tayiwa mutum sannu.
Tun a lokacin Daneji tafara kula dacewar ba lafiya ba,kwana tayi tana sallah da daddare,tareda kaiwa kukanta ga Allah,akan Allah ya kare mata rayuwar 拼ar tata.
Muryar Bombee ce tadawo da ita cikin tunanin data tafi,wanda hakan yasa tayi zumbur ta kalli Bombee,wacce take kallonta da mamakin wane tunani take haka.
"Inna nasan kina iya 茩o茩arin ki wajen nuna min rayuwa,sannan kuma keda baba ku ka蓷ai kuke nunamin so kaman yanda iyaye kewa 蓷ansu,nasan kuma kin kulada canzawa ta a yanzu wanda nima naji,saidai babu yadda zanyi inaga yanxu ne yanda nake,ba yanda kuke son na zama ba dafarko.
Bazan boyemiki ba,amma daga yanxu kaff garinnan samun zaman lafiyar yaro shine kar yashiga harkata,bazan iya yimiki al茩awarin zan 茩yaleshi ba"
Tun kafin Daneji tabawa Bombee amsa taji sallamar gaji a cikin gidan,wacce tajita dumm a 茩irjinta kaman ganga.
Har ta fita tadawo wajen Bombee tareda yimata garga蓷in akan karta kuskura tafito komai taji.
"Salamu alaikum ina mutanen gidanne ina ta raraka sallama,ehh zakuyi shuru mana sabo dodanniyar 拼ar ku taje zata kashemun yarinya a banza. To bilahillazi bazan yarda ba,ko ni ko ku ne a cikin garinnan,mlm Ahmadu yazo yanzunnan yabani ku蓷in 蓷ori da kuma nasiyan magani"
Tana cikin zazzaga masifarne Daneji tafito daga 蓷akin su Bombee tana kallonta.
Tsayawa tayi bata ce uffanba har saida gaji takai ayah a kan masifarta tukunna.
"Naji duk abinda kikace gaji,ha茩ika yarinya bata kyauta ba,amma inshaaallah za'a ja mata kunne,dan Allah ayi hakuri a sasanta a hankali"
"Sasanto? Ke kika sanshi nibansanshi ba,yanzu haka ma nasaka mlm idi ya nufi gidan mai anguwa yafa蓷amasa,dan baza tabs yarda ba,wannan abu ke keganinsa 茩aramar magana,amma a wajena tafi dutsen dala"
"Haba gaji,menene na kaiwa 茩ara kuma,abunnan fah yara ne suka aikata ba masu hankali ba,kuma inshaaallah zan ja mata kunne bazata sake shiga harkar 拼ar ki ba daga yau"
"Hmmm ke kuma tashafa,nidai sai an biya ku蓷i a radu,kuma wlh zata fito waje ai saina saka an babballamin ita,gayyar tsiyah kawai"
Tana gama fa蓷in hakan taja tsuka tareda yin hanyar zaure,zaninta a hannun sai kuncewa yake tana gyarawa.
Kafafun nan furuuru,kana ganinta kasan daga gaban murhu ta taso.
Sai wajen goshin la'asar kafin mlm Ahmdu ya shigo gidan,suna can wajen mai gari kan case 蓷in karayar da Bombee tayiwa Zulaiha.
"Sannu mlm ka dawo?"
"Eh sai yanxu muka samu 茩urar ta lafah"
"To Allah ya kiyaye ta gaba,ka basu ku蓷in gyaran ina?"
"Ban basu ba,cewa nayi bazan bada ba ai tsautsayine,sannan kaff anguwar nan babu wanda bai san irin izayar da 拼ayan mlm idi ke ganwa Bombee ba tun tana 茩arama,haka mukayi shuru muka kauda idanuwan mu,sai yanzu kuma dan tayiwa 拼ar su ace nabada ku蓷i,suma suje suyi jinyarta suji idan da da蓷i"
"Amma mlm bakace haka ba,kafi kowa sanin irin hatsarin dake tattareda yarinyar nan idan zata dunga 蓷aukar hukunci,bai kamata muyi shuru bamuyiwa tufkar hanci ba,saboda da alama tafara warewa daga yanda muka tukata"
"Zancenki ha茩茩une,amma to yakike ganin zamuyi,mlm Alwasu yariga ya fa蓷amana akan kar mu kuskura mu koma gareshi,amma zan le茩a ta wajensa nayi masa bayani,wata茩ila bazai rasa wani abu dazayyi mana ba"
Shuru sukayi jugum kowa yana sa茩a abu daban a ransa.
Saida aka 蓷auki kwana uku ana case 蓷in Zulaiha da Bombee kafim abin ya lafah,itadai an barta da ciwon hannu,babu damar zuwa makaranta.
Yanzu Bombee ta 蓷an samu lafiya a wajen yan ajinsu. Tunda ga wannan lokacin Bombee ta daina kula kowa,koyaushe harkar gabanta take,makaranta ma ba hanya 蓷aya suke bi da innayi ba,da alama inna laari ta garga蓷eta akan karta dunga shiga harkarta.
Saida akayi darasi 蓷aya aka sakeyi kafin Bombee tashigo ajin,da alama wani wajen tabi ,dan tunda wuri innayi tashigo makarantar.
Batayiwa kowa magana ba ta nufi wajen zamanta,ha蓷a ido sukayi da Zulaiha wacce har yanzu hannunta yana sa茩ale da wuyanta.
Wani mungun murmushi Bombee tayiwa Zulaiha,mai 蓷auke da gagar蓷i a tareda.
Aikuwa da alama sa茩on ta dake son isarwa ya isa inda takeso,don lokaci guda jikinta yafara rawa,tayi saurin sunkuyar da idonta.
Bombee tana zama taji muryar malaminnasu yana magana.
"Ke Bombee tashi ki fita daga ajinnan,dan iskanci sai yanzu kike zuwa makaranta"
"Kayi ha茩uri mlm,innata ce ta aikeni,kuma anyimin horon makara a waje"
"Babu ruwana da wannan horon,ki fitamin a aji yanzu nan,dama ana fa蓷an ke hatsabibiya ce ashe dagaskene,dolema ki bar makarantar nan"
Kallon mlmin Bombee take,tareda yin tunani a ranta. Kenan shima dama baya 茩aunarta kaman sauran mutane,saboda tanada ilimi shiyasa yake kulata ashe,duk wannan tsawon lokacin kallon hatsabibiyah yakeyi mata.
"Shikenan mlm zan fita,amma kaman yanda na aikatawa Zulaiha yauma zanyiwa Abdul 蓷an nursery 3 a hanyar tafiyah,inya tambayeni menene dalili saina ce jawo maka akayi.
Yanzu hakama idan na fita 茩iransa zanyi muyi wasa a can gefe"
Zaro ido malamin yayi jin Bombee ta ambaci sunan 蓷an sa dayake ji dashi,yaushe yarinyar nan tazama haka?
Ya fa蓷a a ransa,zaman sa lafiya ya rabu da ita,idan takaryawa abdul 蓷insa hannu yau ya zaiji.
"Ahah babu komai koma kiyi zamanki ma,basai kin fita ba"
Jijjiga kai tayi tareda fa蓷a蓷a murmushinta kana ta zauna.
Kamo hanyar gida tayi ita ka蓷ai,bata da abokiya ko kuma aboki,iya 茩anwarta ce,itama kuma anrabasu tun ranar da abinnan yafaru,bazata iya cigaba dajanta jikinta ba,bayan tasan basonta take ba.
Maganar bello taji a bayanta,wanda hakan yabata mamaki,musamman da taji da ita yake,rabonta dashi tun sanda yayi mata duka wancan watan.
"Ke ki tsaya a inda kike,hhhhh bantaba zaton yanda kike har zaki iya karya wani ma,waninma 茩anwata,ke wacece face dodanniya abar kawarwa. Bakiyi mamaki ba daban tareki ba kaman ko yaushe a hanyar gidanku,gaji ce ta hanani sumar dake tun wancan lokaci,saboda abinda kikayi yana sabo,amma yanzu zanga wazai 茩waceki a wajena,mutuwa ma zaitayi shakkar 茩watarki yau a wajena,saina saitamiki notin dayake son kuncewa a cikin kanki.
Duk maganar dayakeyi Bombee batace masa uffanba,sai binsa kawai take da idonta a duk lokacin dayaje ya zagayota.
Abinda bai kuladashi ba shine,yanzu idonta a tsaye yake babu alamar tsoro ko firgici sa'banin da,da yanzu ta tsugunna tana bashi ha茩uri.
"Ohh ashe naga da alama har 拼ar jarumta kika samo koh?"
Toshe hancinta tayi da hannunta tareda cewa.
"Banta'ba kulaba sai yau,ashe kai mungun 茩azami ne,bnada 蓷oyi babu abinda kakeyi,ga baki a dafe kana yaro 茩arami ka fara shaye shaye,shayeshayen ma na 茩ananan 蓷an iska,banza shashasha."
Daga bellon har su sule shuru sukayi suna kallon Bombee,wacce ta kafe bello da ido tana zubamasa magana babu alamar tsoro.
Hannu ya 蓷aga ya zanga mari mari a fuska.
Haka tayi 茩i茩im bata matsa daga inda take tsayeba,tofar da yawun dayake bakinta tayi mai ha蓷e da jini.
"Waifah irin wannan marin kakemin da sainaji tsoronka koh,ashe ma bakada 茩arfi,duk yunwa da sigari ta cinyeka,amma bari kaji nawa yayake?
Tun kafin yagama haddace mai tace a 茩wa茩walwarsa yaji wani mari a kuncinsa,ba iya marin ba harda wani zafi daya jiyarceshi a wajen.
Tangal tangal yayi kafin yasamu ya cake,hannunsa yasaka a wajen tareda zaro ido lokacin dayayi arba a hannunsa,jinine jajur a hannunsa.
Hannayenta biyu ta saka a wuyansa,ta nutsa faratanta a wajen.
Ihu yasaka iya 茩arfinsa saboda ciwon daya ziyarceshi.
"Banfara 蓷aukar mataki ba saida nashiryah,ko babban mutum idan yanason cin galaba a kaina bazai iya ba ballanta ku 茩ananan 茩wari,kusaka a ranku bazaku iyah cin galaba a kaina ba ko ka蓷an,mai son gwadawa kuma ga wajenan,mai tsoro ka fasa"
Sakin wuyannasa tayi,ta barshi a tsugunne yana tarin wahala,kan kaceme jini ya wanke gefen rigarsa inda ta karzamasa zanen faratunta.
"Ana zugaka shugaban yara,nibanga sarauta anan ba,dan haka na karbi sarautar daga yau,ko kanaso ko baka so ka bani matsayinka,Sannan babban jan kunne kar kowa yasake 蓷agamin yatsa cikinku,idan kunji kun tsira"
Tana maganar tana fita cikin murya kaman ba tata ba,sannan kuma tanayi tana wata irin dariyah kaman shai蓷aniya.
Kallon sule tayi wanda tun 蓷azu ya jefar da bulalar take hannunsa ta dukan Bombee 蓷in.
"Ka tahomin da jakata gida,sannan duk wanda yakeda niyyar 蓷aukar mataki akaina shima kada ya fasa"
Daga haka ta bar lungun ta nufi gidansu.
馃枻 Sadi-Sakhna ce馃枻
拼ar mutan jama'are