Free chapter 路 Read without an account

_*EIGHTEEN*_

by Sadiya Auwal 路 BAKAR AYAH

                   ____****馃枻馃枻****_____     


  馃枻 *BA茦AR AYAH* 馃枻


     馃枻 _BOOK1_ 馃枻



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA

[ _瞥ar mutan Jama'are_ ]






    *WATTPAD*

***


    *AREWABOOKS*

https://arewabooks.com/u/sadeesakhna


______________****_______________







Page 馃枻18馃枻





Wulgawar Bombee innayi tagani tana cin abinci, yaukuma ta dawo da wuri.innayin tafa蓷a a ranta,kullum sai yamma li茩is take dawowa idan ta tafi makaranta,wani lokacinma sai dare yayi tukunna.Sau uku mlm Ahmadu yana kamata yana dukanta,amma ko kuka batayi,sannan kuma bata fa蓷i inda take zuwa ba,sannan kuma bata fasa kaiwa daren ba.

"Inna Daneji Addah Bombee tadawo tana 蓷akinmu"

"Yau蓷in kotaji magana babannku kai,amma a wanne yanayi tashigo"

"Uhm hannun duk jini har ya bata mata uniform 蓷in jikinta"

Innayi ta fa蓷a a hankali,cikin sigar gulma,saboda kar addar tata tajiyo ta,aikuwa Al茩alamin ya 茩arye,dan duk maganar da takeyi a kunnenta sarai.

"Jini kuma wanne iri,yauni kuwa mai zangani a duniyar nan,hadda jini"

"Ahh toh Bombee ai tazama abinda tazama sai du'a'i,ke kuma ban hanaki shiga harkarta ba ne,sai tazo tana dukanki koh"

Inna laari tafa蓷a tareda zabgawa innayi harara,yanzu kowa yasan inna laari haushin Bombee takeji,saboda a rana idan ta duka innayi yafi a 茩irga,wani lokacin ma wai dan kawai ta kalleta,a wajen kwanciya kuwa wajibine saita yi mata na bacci. In abun bai zo ba kuwa saitayi sati bata kulata ba.

Hanyar 蓷akinnsu Daneji ta nufah tareda tsayawa akan Bombee,wacce take zaune a tsakiyar gadon ta bawa 茩ofah baya.

Zaro ido Daneji tayi data kalli yatsun Bombee,dan dama su tazo gani domin da ta tabbatar da zancen innayi,aikuwa hakane farcenta za茩o za茩o duk jini a jikimsu tamkar faratun mayu,yaushe ta tara wannan faratun haka babu wanda yasani.

"Bombee menene haka a hannunki kaman jini,na wanene?"

"Jinin bello ne,yatareni zai 蓷au fansar abinda nayiwa 茩anwarsa,nikuma na yanka masa fuska da farcena"

"Yanzu dan yazo 蓷aukar fansa saiki yanka masa fuska,bazaki kawo 茩ara ba gida,kinkuwa san hukuncin hakan"

"Nasani kuma babu abinda ya isa yayi daga shi har iyayensa,idan aka sake nima zan sake,batun nakawo 茩ara kuma menene amfaninsa,shin tunda nake an taba ramamin idan wani ya zalunceni,saidai a bani ha茩uri zancen ya wuce,dan haka ni gaskiya bazan sake yarda da wanannan tsarin ba,dole na kawo nawa tsarin nima".

Dan takaici Daneji bata sake cewa komai ba,saima fita da tayi tabar 蓷akin,abin yafi 茩arfinta yanzu kam.

Fitowa tayi daga 蓷akin tana mi茩a tareda yin hamma,ruwa ta 蓷iba a bokiti tashiga ban蓷aki tayi wanka. Lokacin data fito innayi tashiryah cikin kayan islamiyyarsu da jakarta a hannu.

"Ke wato ina jinki kina gulamata 蓷azu koh,idan kin dawo daga makarantar ki wankemin kayana,idan basu fitaba kuwa........hmmmmm bazan 茩arisa ba"

"Bazata wanke ba idan ke kika haifamin ita,ko wankin kayanta banfara bata,amma ke kin fara bata naki dan mugunta"

"To karta wanke,wannan bai dameni ba,tunda na riga na fa蓷a mata shikenan"

Da sauri innayi tayi magana cikin muryar kuka kafim inna laari tasake cewa wani abun.

"Ahah inna zan wanke mata kayan idan nadawo daga islamiyya,na iya wanki fah"

Cikin takaici babu yadda zatayi ta jijjiga kai.

Riga da wando tasaka irinna pakistan,wanda mlm Ahmadu yasiyo musu a taraba dayaje kasuwanci,hula da saka kanta kawai,babu hijabi tayi hanyar waje.

"Ke ina zakije haka babu hijabi,dama ba islamiyyah zakije ba naga kinyi wanka"

Daneji ta fa蓷a,tun dazu sai yanzu tayi magana,dan tasan idan tayi ma aikin banza tayi,an doki kashi.

"Wancan Alwasun yace karna 茩arayin kusada makarantarsa satin daya wuce,nice dama nacigaba da zuwa,saboda akwai abinda nakesom 茩arisawa,yamzu kuwa na gama.

Yawo zanje kawai cikin jeji idan wani abune a aika innayi takirani,tasan inda nake.

A bakin 茩ofar gidan sukaci laro da gaji,aikuwa caraf tari茩e kunnen Bombee suka shigo gidan tare.

"Dan bantan ubanki mai kikayi wa bello a fuska,dan tsabar abinnaki yawuce gona da iyaka shine kika yimasa yanka da wu茩a a fuska ko,da nayi ha茩uri,amma yanzu kam bazaja sabu ba,kotu zan yi kararku a zo a daureki,abun ai yayi yawa shege da hauka,gaba蓷aya a kwanaki ka蓷an kin dasawa 拼a拼an anguwa tsagwaron tsoronki?"

Tunku蓷a Bombee tayi a 茩asa a gaban Daneji,har sannan bata bar masifa ba ita 茩arfinta.

Zagi takeyi da uwa ta uba,inda tashiga batanan take fitaba,bakinta har kumfah yakeyi dan masifah.

"Wallahi bazan yarda ba,ku jirayi sammaci a gobe,茩ara zan kai gobe,bama a cikin garinnan ba can Sardauna zan kaiku 茩ara kuma da ku蓷in tara mai yawa.

Har ina da wannan abun,yaro yana can fuska tayi sumtum idon wajen ko gani bayayi tashi,jiki ya dau zafin zazzabin wahala kamar motace ta bugeshi.

Kuma a goben saita fadawa Al茩ali mai tayi masa,daga nafara maganar 蓷aukar mataki jikinsa zai fara rawa,yarinya 茩arama tasakashi a cikin asirinta,dolen uwarki ma idan kikaji wahala zaki kunceshi da kanki"

A haka tagama fa蓷an ta son ranta tafita ta bar Daneji ta sharar 茩wallar ba茩inciki,hararar Bombee tayi wacce zaune a 茩asa idonta a soye kaman fa蓷an ba'a kanta akayi shiba.

茒akinta tashige tafara ribzar kuka kozata samu ta huce da suyar da zuciyarta take mata.

"Mtswww ji yanda ta batamin kaya kuma tasaka innata kuka,aradu zanyi maganinki ne,bar ganin ki tuleliya bai dameni ba"

A hankali tayi maganar tana tura baki,kafin tajuyah tabar gidan,ta nufi inda tayi niyyar zuwa tun farkon barinta gidan.


Sallama Daneji tayi a gidan gaji da sassafe washagari,dan dama sunyi magana da mlm Ahmadu da daddare akan zataje sasanto gaji kan abinda yafaru.

Wata 茩atuwar tukunyace akan murhu ann 蓷umame yara zasuci su tafi makaranta.

Ga gidannan duk tarkacen kayan wanke wanke.

Fa蓷a gaji take rabawa tsakanin Zulaiha da yayarta akan kunun wai,fa'izah ta蓷au Zulaiha bayan itace na ashirin ta siyo bana talatin ba.

Sallama Daneji ta cigaba ta kwararawa amma har yanzu gaji bata jitaba,saida wani yaro yakirata tukunna kafin tajuyo takalli danejin.

茒an alamar tsorone akan fuskarta amma tayi saurin kawar dashi tareda 茩a茩alo murmushin dole.

"Ahhh Daneji kece sannu daxuwa,ga kujera zoki zauna a zubo miki 蓷umame"

"Ahh nagode ma,an tashi lafiyah ya gidan"

"Gida kalau,lafiya naganki da sassafe haka,hala dai mutane gidan kalau"

Abinne yabawa Daneji mamaki har takasa boye mamakin nata akan fuskarta.

"Uhm gaji nace ba,akan zancen kaiwa kararnan nazo,dan Allah a 茩ara ha茩uri,a sansanta cikin rufin asiri,kaiwa kotun bashida da蓷i.

Mlmn ne ya turoni nasake baku ha茩uri,sannan za'a biya ku蓷in maganin inyaso".

"Laah karki damu bakomai fah,fa蓷an yarane dabaka iyarmusu,babu komai yawuce bazai sake faruwaba,ki fa蓷awa mlm Ahmadu bakomai ya wuce baza'a sake ba"

Kasa jure tantamarta tayi,hakan yasa ta tambayi gaji mai yafaru.

"Amma gaji dan Allah mai ya faru naga kin sanja daga iya jiya,ina fatan dai hakan bayada nasaba da Bombee koh"

"Uhm Daneji kibar zancennan dai kawai,amma tunda kin matsa sa茩o daya nakeso ki kaimata,dan Allah ya kice mata 拼a拼ana bazasu sake shiga harkarta ba,itama ta taimaka tafita daga rayuwar mu,kowa hadu da daidan sa a yanzu"

Baki sake cikeda mamaki Daneji ta baro gidan gaji,a hanya babu sakar jakin da batayiba akan shin mai Bombee tayiwa gaji da 拼a拼an ta kuwa,kodai zancen mutane dagaskene kai,kai anya kuwa,in akwai wanda yasanta to bayana ne ai,kuma a sanina da ita bata tsafi bare nace shi tayi musu,to mai yake faruwa?

Tana cikin hakanne ta isa gida,zuwa lokacin rana ta fito yara sunata tafiyah makaranta,suma su Bombee sun shirya zasu tafi makaranta.

Daneji bata 'baata lokaci ba takama hijabin Bombee tareda janta cikin 蓷aki.

"Maza maza ina jinki yimin bayani mai kikayiwa gaji naga ta sanja a dare guda?"

茒an murmushin dama nasan haka zata faru tayi,kafin ta jijjiga kai.

"Ni babu abinda nayi musu mai zanyi musu"

"Bombee ki fa蓷amin gaskiya mai kikayiwa gaji take haka,tabbas akwai wani abu,kuma kece kikayi ba kowa ba"

"Inna baki yarda dani ba ne?"

"A da kenan,amma vanda yanzu dakika sauya daga yanda kike"

"Eh to ba wani abu bane babba,kawai dai na 蓷an le茩a gidansu ne da daddare nayi musu gagar蓷i"

"Gargadin me,ke 茩arama dake zaki iya bawa wannan 茩atuwar matar garga蓷i,ai koni ban isa yimata kashedi ballantana ke,ki fa蓷amin mai kikayi musu Bombee,ni yanzu kin fara bani tsoro da halayyarki"




............Daren jiya..........


Karfa labari ya gundureku kunga an tsaya a waje guda 蓷aya,komai da sannu ake warwareshi.

Dafatan zakuyimin hakuri dai....馃槒馃槉馃槉馃槉.





馃枻 Sadi-Sakhna ce馃枻

拼ar mutan jama'are

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.