Free chapter · Read without an account
03
🦽👨🏻😭SUN GUJE NI😭👨🏻🦽
(SANADIN CUTAR LAKKA).
IT BASED ON TRUE LIFE STORY.
LABARI DA RUBUTAWA:FARIDAT HUSAIN MSHELIA(UMMU-JIDDAH).
SHAFI NA UKU.
DAMO SARKIN HAƘURI.
Jin Yusuf bai ce ma ta komai ba ya sa ta juya tana ƴan waƙe-waƙen ta duk da ya na matuƙar buƙatar taimakon ta a lokacin na ruwa amman haka ya bar ta ta wuce dan jikin sa ya yi sanyi kun san amai da kashe jiki.
"Wannan mutum ce ko dabba?ya tambayi kan sa,
Mutum ce wacce ba ta san ya kamata ba sam ganin tunanin ma wani ƙara chaza ma sa kai zai yi ya sa ya miƙe da bokiti ya ɗebo ruwa a randa ya tsafta ce jikin sa da gurin ya bi gefe-gefe ba tare da ya bari ya taka kayan da ta watso ba ya shige cikin ɗakin har a lokacin in ya tuna abin da ta watso mi shi sai ya ji zuciyar sa na tashi,nan ma ɗakin a birkice ya taras da shi tamkar wanda a ka yi yakin basasa acikin shi duk ta yamutsa komai na ɗakin,duk yanda ya so kwanciya ya gagaran masa dole ya lallaɓo ya dawo falo ya kwanta a kan doguwar kujera na zaman mutum 3,
Jin sa ya yi luntsum acikin ruwa bai san sanda wani irin hawaye na tausayin kan sa ya zubo masa ba ya rasa mai ma zai yi ya kuma rasa wani irin mataki ya kamata ya ɗauka akan wannan matar ta sa ganin ko ƙarfin magana ba shi da shi ya sa ya mirgono ƙasa ya kwanta akan saman ledar da ke malale a tsakar ɗakin,
da ƙyar ya cire kayan da ke jikin sa tare da yin jifa da shi wai ko zai huce haushi da ya ke ji sai a sannan sahoramar ta shigo falon ba ko sallama ɗauke da wani ƙaramar tukunya wanda ya yi baƙiƙƙirin alamun ya jima bai haɗu da soson waya ba,
Ƙoƙarin ajiyewa ta ke yi a kusa da shi ya yi saurin dakatar da ita ya ce"ki ɓace ma ganina tun kafin in yi ƙasa-ƙasa da ke anan gurin mai suffar mahaukata",
Sum-sum ta shige cikin uwar ɗakan tana gunaguni ba ta musa masa ba ne ba saboda yanda ta ga ya yi maganan cikin tsare gida,taɓe baki ta yi cikin rashin damuwa ta ce"kan ka ake ji wai maƙocin mai akuya ya sayi kura"dire tukunyar ta ta yi a ƙasa ta fara sharɓar taliya ƴar murjin da ta dafa rabi taliya rabi ruwa haka taliyar ba kayan miya ma acikin ta,cin abincin ta ta ke babu abinda ya sha mata kai sai ci ta ke tana lashe hannu saboda yanda ta iya zuba kafi zabuwa abincin na ta na zaƙi sosai dan ita sam ba ta damu da magi dunkule ba saboda tsabar gida dan ci,
wata ƙatuwar gyasa ta yi bayan ta cinye abincin ko hannu ba ta wanke ba ta goge shi ajikin zanin ta ta miƙe a wajen ba tare da ta kawar da tukunyar ba da kofin ruwan wani nannauyan bacci ya yi awon gaba da ita miyan bacci na ta kwarara abin ba kyan gani(Goodnight shugabar ƙazamai lolz).
Ƙiran sallan farko a kunnen Yusuf dan haka a wahalce ya lallaɓa ya tashi zaune yanajin ko'ina na jikin sa na masa ciwo saboda kwanciyar ƙasan da ya yi abin ka da ba sa ban ba,
miƙewa ya yi a hankali ya nufi banɗaki dan har yanzu jikin sa ba ba ƙarfi saboda aman da ya kwarara jiya,wanka ya fara yi kafin ya ɗauro alwalla ya fara raka'atanul fajri,Alƙur'ani ya janyo ya fara karatun sa cikin sanyayyar murya har aka fara ƙiran sallan asuba ,tashi ya yi ya tafi kai tsaye zuwa ɗakin amarsu ,nan ya ci karo da ita a yashe a ƙasa sai minshari ta ke miyan bacci duk ya bushe a bakin ta da kumatun ta,duƙawa ya yi a natse yana ƙiran sunan ta ya ke cikin taushin murya ta buɗe ido haɗe da hangame zungureren bakin ta ta yi hamma kafi tace"To sarkin sallah ka zo kenan,to na ji a sauka raɓaɓa",
Miƙewa ya yi tsam ya fice zuwa masallaci dan sam bai da lokacin yin musayar yawu da ita amman abin mamaki ko da ya dawo nan ya same ta a inda ya barta tana baccin asara cike da ɓacin rai ya fara tashin ta sannan ya ce"Amman ke kam kin yi asara wallahi,ta kowani fanni kin zama sifili ke ba tsafta ba,ba iya kula da miji ba,ba iya magana ba,ba iya kwalliya ba da tattali,ba iya girki ba sannan bangaren addinin ma kina baya,wace iri ce ke wai,Sallar kan shi yanzu ba za ki tashi ki yi ba anya kina neman gamawa da lafiya kuwa?,
Miƙewa ta yi a fusace ta ce"daɗin abin dai kai ba Ubana ba ne mahaifi balle in ce in ka yi min baki zai kamani sannan sallar da ka ke magana a kan sa na ga ba kai na ke yiwa ba kaina na ke ma to na ka a wanne da har ka ke niyyar aibata ni kaci min mutinci asubar fari?,
"Na ga kabari na daban na ka daban dan haka ba zan yi sallar ba sai in ga abin da zaka yi,ta ƙarashe maganan cikin tsiwa tana hararar sa,
"Ba zan yi komai ba hakki ne dai na sauke na tabbatar Allah ba zai tambaye ni akan sa ba"ya na faɗin haka ya fice ya bar ma ta ɗakin kan kujera mai zaman mutum biyu ya koma ya miƙe amman haka ta hana shi bacci a cewar ta "ai ita ma tana cikin baccin ta mai daɗi ya hana ta so sai ya tashi su ci uwar da za su ci",
Ganin da gasken ta ke yi ya sa ya miƙe ya fara da gyaran uwarɗakan na su inda ya canza zanin gado sabo wanda shi kaɗai ya rage musu sauran duk sun yi datti,
tattaro sauran kayan wankin da su ke zube a ƙasa ya yi ya fiddo su tsakar gidan da ta bar shi da kaya tamkar tsakar gidan mahaukata,
komawa ya yi ciki ya sharo ɗakin da tsintsiyar tsaye ya gyara falon shima tare da wanke banɗakin ganin har a lokacin ba ta ɗau matakin gyara tsakar gidan ba ya sa ya koma ciki ya ɗakko belt ya fito haɗe da ƙwala mata kira,
Ra'eesat wacce ke rashe a kicin tana sarrafa abin karin ta na dankalin turawa za ta soya shi da ƙwai ta yi mishi banza,
Amman jiyo shi yana dunfaro madafar ya sa ta amsa a daƙile tare da kashe rishon dan har ta tsoma dankalin cikin kwai bayan ba ta dafa ba jin yanda ya yi saƙe-saƙe alamun bai nuna ba ya sa ta kashe rishon,
"Fito"ya umurce ta,
"maza-maza ki tattara komatsan ki guri guda",
ɓata fuska ta yi amman ganin yanda ya ɓata fuska ya sa ta fita ta fara tattaro gefe ɗaya,
Umurtan ta ya yi da ta je ta ɗakko sabulu da omo ta fito nan ma ta shige tana harare-harare ko da ta kawon jefa su kan kayan wankin ta yi za ta shige madafa,
ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar yi mata alamu da hannu akan wanki za ta yi,kuka ta fashe da shi cikin kururuwa ta ce"Kashe ni kawai ka huta Yusuf,asubar fari ka tada ni wai in yi sallah ka yanke min bacci dan tsabar shiga haƙƙi,yanzu kuma ko karin kumallo ban yi ba ka haɗa uban wanki wai in yi to wallahi ban iya ba dan ni a gidan mu ummana ke min",
"za ki koya kuwa daga yau dan nan ba gidan Umman ta ki ba ne da ta gagara ba ki tarbiyya wai ke ga auta,nan gidan ki ne in da za ki rayu tsawon rayuwar ki,ki hayayya fa kin ga ke ma uwa ce watarana, shin in ba ki iya ba ta ya ya suma za ki koyar da su?",
"oho ma ka ni kawai ka bani hanya in yi wucewa ta yunwa na ke ji",
Harara ya dalla ma ta cike da ƙosawa da lamarin ta ya ce"a hakan za ki ci abincin bayan alhalin ko wanke fuska ba ki yi ba ba,kin ko yi sallah ma?",
Surutai za ta fata yi mi shi ya ɗaga bulalar............
UMMU-JIDDAH.