Free chapter 路 Read without an account
CHAPTER NINE
by Ummubasheer 路 MAHAIFIYA TA
AHAIFIYA TA abar sona*馃挌
*MAHAIFIYA TA abar alfahari na*馃挏
*MAHAIFIYA TA abar k'auna ta*馃挋
*Wannan litafin sadaukarwa ce baki d'ayan shi ga duk wata MAHAIFIYA a duniya, wacce suka rasa ta Allah ya jikan ta da Rahma, Wanda suke tare da nasu Allah ya basu aron ta, Ameen*
*Ummu Love's you more*馃А
*Page 45~49*
*Idanun* su ne ya had'u dana juna lokaci d'aya, da sauri Najma ta sunkuyar da kanta k'asa, shi ko mamakin irin kyan da tayi yakeyi. Driver ne ya fara driving a hankali babu Wanda yayi magana har suka isa Wani had'aden guri, tunda inda motar yayi parking aka shimfid'a wani dogon carpet blue har zuwa inda za'a shiga k'ofar gurin, Wanda friends d'in shine suka had'a mai dinner d'in.
Sultan ne da Salma suka fito cikin wata mota, driver ne ya fito ya bud'e ma Saif, Sultan zuwa kusa dashi yayi "Dan Allah friend ka daure kayi abinda da nace ma please saboda mutane"
Tsaki Saif yaja ya bud'e side d'in Najma, fitowa tayi suka fara tafiya a Jere sunzo tsakiyar gurin kenan takalmin ta ya turgudaar da ita, da sauri ya rik'e hannun ta, lokaci d'aya suka ji wani irin Electric shock, kallon shi tayi da sauri sai dai ko kallon ta baiyi ba suka cigaba da tafiya zuwa cikin hall d'in, mutane sai d'aukar su pictures da video suke.
Suna shigowa mutanen gurin suka mik'e tare da fara clapping hands suna zama a high table, sannan mutanen suka zauna,
Sultan ne ya fito ya bada labarin Saif in briefly, sannan Yusra ma ta fito ta bada labarin Najma in briefly, nan akayi clapping hands, wani cake ne mai hawa shida white and blue, aka umarce amarya da ango su fito su yanka cake.
Rik'e hannun ta yayi suka isa gurin sai da ya yanka ya bata a baki sannan ita ma ta bashi, kowa kallon su yake cike da sha'awa saboda yanda sukeyi sai ku rantse massoyan juna ne.
Haka dai akayi dinner, ya k'ayatar sannan aka fito dan tafiya gida, sultan yaji dad'in yanda Saif ya nuna ma Mutane Najma zab'in shine.
Washegari akayi bud'an kai, sosai ya k'ayatar around 4:00pm y'an uwan Najma suka shirya tafiya, tana zaune kan Royal bed d'in ta anyi mata make up tana sanye da atamfa pink and light blue colour jewelry d'in ta na silver ne, kuka sosai take kamar ranta zai fita tana rik'e da hannun Yusra, ita kanta ma kuka take yau zata rabu da aminiyar ta ,yau ce rana ta farko da zasu rabu, rabuwa irin Wanda sai dai a ziyarci juna.
Wata cousin d'in Najma ce ke basu hak'uri suyi shiru.
"Aminiya Allah ya baku zaman lafiya"
"Kina nufin dagaske tafiya za kiyi ki bar ni, haba Aminiya"馃槶
"Dole zamu rabu, sai dai muyi hak'uri, but I promise zamu dinga waya"
Haka dai suna kuka suka rabu sauran y'an uwan ta suka tafi bayan sunyi mata nasiha, komawa tayi ta kwanta tana kuka, a haka dai y'an uwan Ummi ke zuwa suna mata sallama zasu tafi, har zuwa magriba, sannan tayi wanka ta d'aura alwala, cikin material d'inkin riga da skirt red colour ta saka, ko make up ba tayi, sai tayi Sallah har akayi sallah isha'i.
Around 9:00pm
Saif ne da Sultan cikin mota sun raka friends d'in su Hotel d'in da suka sauka dan sai washegari zasu bi flight, sauran abokanen dake kusa kuma sun koma.
"Bari inyi parking in sai maka kajin amarci" cewar Sultan
Banza yayi dashi har yaje ya siyo fresh milk da gasashiyar kaza,
"Friend yau za'a angwance, shikenan ka huta da ciwon Mara, ina ma nice yau aka kai min Salma ta"
Tsaki yaja ko kallon shi baiyi ba shi ko baiyi shiru ba sai tsokanar shi yake har suka isa gidan, Sai da suka shiga side d'in Ummi suka gaishe ta sannan Sultan ya mik'a musu wani ledar suka fita.
Ummi ko wani irin zafi take ji a ranta, ya zama dole tasan abinyi domin ita ta tsani Najma.
Bud'e k'ofar parlour'n sukayi tare da shigowa ko'ina yayi kyau,
"Friend shiga ka kira mun ita Mu gaisa zan wuce tunda na rako ka"
Tsaki yaja ya harare, ni nace ka rako nine ko ban San hanyar bane"
"Tunda wulak'anci za kayi min tunda kayi Aure bari in tafi"
Har waje ya raka shi sukayi musabaha har zai tada mota sai kuma yace"Dan Allah Soldier kabi yarinyar nan a hankali, kar kayi barna"
"Kai fa d'an iska ne"ya fad'a yana d'aure fuska
Dariya Sultan yayi ya tafi shi kuma ya koma ya kulle ko'ina, ya shiga bedroom d'in shi yayi wanka ya shirya cikin kayan barci sannan yaje k'ofar bedroom d'in ta yayi knocking.
Najma ko duk taji lokacin shigowar su, hijab tasa, sai gashi ya shigo ko kallon ta baiyi ba yace" akwai abinci a dining kije kici" yana fad'a ya fita.
Tsaki taja lalai wannan d'an rainin sense ne ai ko zata koya mai hankali.
Straight office d'in shi dake cikin wani corridor ya shiga yana wani aiki tare da shan coffee, Sai around 11:30 pm ya fito, ya wuce dining yanda ya ajiye komai haka ya gani, D'aga kafad'a yayi he doesn't care ita ta sani, ya koma d'akin shi sai barci.
Najma ko bata bi takan abincin ba tasha kukan rabuwa da mamin ta da y'an uwan ta tare da Aminiyar ta can sai gaban ta ya fad'i lokacin da ta tuno da Muhseen d'in ta, kuka tayi sosai sannan tayi alwala tayi sallah tana rok'on Allah yasa hakan shine mafi alkhari a gare ta.
The following Day
Knocking ne ya tashe ta barcin da ta koma, hijab tasa taje ta bud'e k'ofar, Salma ce rik'e da kwando na abinci, murmushi tayi, ta shiga ciki.
"Aunty na barka da Safiya brak fast na kawo muku"
Murmushi tayi tana shirin karb'a tace ta barshi ta kai kan dining, ita da kanta ta shirya musu break fast har Ummi na fad'a wai dan mai yasa za tayi, ita ko Salma tana son Najma ne.
Sai da tayi wanka ta shirya cikin riga da wrapper zani d'inkin yayi mata kyau light make up tayi sannan tayi break fast, ta gyara ko'ina a gidan sannan ta kuna karatun Qur'ani.
Cikin barci ya dinga jin sautin karatun Qur'ani tashi yayi ya shirya ya fito parlour'n yayi break fast lokacin ita kuma ta fito kitchen, ko kallon shi ba tayi ba, yaji dad'in wannan qira'ar Qur'ani da tasa, yana gama breakfast yazo zai wuce ta gaban ta da gangar ya taka mata k'afa y'ar k'ara ta saki cikin jin zafi.
Ba tare da ya kalle taba yace"haka aka koya miki a gidan ku kar ki dinga gaishe da mutum koh"
Murgud'a baki tayi"Allah ya isa na, ka taka min k'afa ba ko sannu"
K'ara taka k'afar yayi ta saki ihu, toshe kunnen shi yayi da hannu"Will you shut up marar kunya kawai" ya fita saboda ihun da take, koda ta kalla k'afar ta sai taga yayi jaa, tsaki tayi-tayi.
Yana fita side d'in Ummi ya nufa ya gaishe ta.
Salma ce ta zo ta raka ta gurin Ummi ta gaishe ta sai dai bata ji dad'in yanda Ummin ta amsa mata gaisuwa ba.
Bayan sati d'aya
Najma tun ranar da Saif ya taka mata k'afa basu sake had'uwa ba, kullum tana gyara gidan ta yayi k'amshi, tana zuwa gaishe da Ummi tayi girki takai ma mata, sai dai hakan bai sa ummi tayi tunanin fara son taba, Salma kullum sai tazo suyi ta hira tana debe mata kewa,gani take kamar Yusra ce, tana yawan tuno da Mamin ta har tayi ta kuka, gashi an sace mata wayar ta, Saif koh Washegarin ranar ya koma aikin shi a cewar shi hutun mai zai d'auka, koma fa an bashi hutun one week, da wuri yake tafiya lokacin Najma na barci ya dawo around 9:00pm shima tana barci cause tana barci da wuri. Sannan ya rasa mai yasa yake jin wani feelings akan ta.
Yau ya kasance weekend ne, kamar yanda ta saba ta gyara ko'ina sannan tayi wanka ta shirya cikin Wasu English wear na riga da wando sun matse ta wando black ne sai rigar na ciki white saman shi boy friend jacket ne black, tayi doghonut da gashin ta tasa hair band, wet lips da eyeliner kawai sai powder ta shafa.
Tana kitchen tana had'a Coconuts juice, Saif ne ya shigo domin yana San shan coffee, yana sanye cikin blue d'in riga da blue jeans .
Hard'e hannuwan shi yayi yana kallon every movement nata, ba k'aramin kyau tayi mai ba, yana jin wani feelings da bai tab'a ji ba, ita ko Najma aikin ta kawai take, can sai jin tayi an rungume ta tabaya da sauri ta waiga tare da sakin ihu, ganin d'an cute lips d'in ta bai San lokacin da yakai nashi kan nata ba, wani irin tsotson lips d'in ta yake, Najma sai kok'arin ture shi take ta kasa, phone d'in shine ya fara ringing Wanda sai a lokacin ya dawo hayyacin shi, da sauri ya fita yana answer phone d'in shi.
Rik'e sink tayi tana kuka, amma Allah ya isa, naso ace first kiss na da Hubby nane sai gashi abanza wannan yazo yana wani kissing na, ta fad'a a ranta, share hawaye tayi tana cewa"MAHAIFIYA TA nake ma Biyayya" ta cigaba da aikin ta tana jin tsanar Saif....
Last free page