Free chapter ยท Read without an account

CHAPTER TWO

by Ummubasheer ยท ZURI'A D'AYA


*Thanks for your love and support* ๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜






*Bayan* ankai amarya gidan ta ne mutane suka watse inda ya rage ita kad'ai a bedroom, da missalin k'arfe 9:00pm ne Nasir ya shigo gidan direct bedroom d'in Aisha ya nufa,tana ganin shi ta mik'e da sauri tana cewa"Ango kasha k'amshi"


Dariya yayi yace"Aisha ke ko kishi na ba Kya yi ne,har wani nasha k'amshi kike cewa"


Dariya ita ma tayi tace yazo suje ta kaishi d'akin amarya, sai da yayi wanka ya shirya suka nufa d'akin,


Zainab na kwance har ta fara gyangyad'i sai taji sallaman su, bayan sun shigo ne an gaisa yayi musu nasiha sannan Aisha ta bar bedroom d'in, Nan dai sukayi salla da K'yar Zainab taci Naman kajin Dan a tsorace take da shi duk da zuciyar ta na k'aunar shi,



Aisha ko ta kasa yin barci a wannan daren domin wani irin kishi takeji sosai sai zagaye bedroom d'in takeyi, ji take kamar taje ta shak'e wuyan Zainab tace ta fasa had'a plan d'in ta,Ni ko nace kin makara Dan aikin gama ya gama,tuni Nasir ya kusanci Zainab,



Washegari da safe


Aisha ta gama had'a breakfast,amma taji shiru basu sauko downstairs ba haushi duk ya ishe ta,wani irin kishi takeji,ganin su tayi cikin shiri sun sauko, sannan suka gaisa, Zainab ko kunyar had'a Ido takeyi da Aisha wani irin kunyar ta takeji, Nan sukayi breakfast, Nasir ya bar gidan su Kuma suka d'anyi hira,







A kwana a tashi ba wuya gashi yanzu har anyi wata biyu da auren NASIR da ZAINAB, Aisha kan nuna ma Zainab cewa ita ce matar gida, Dan haka za suyi ta soyyayar su ko a gaban ta ne, sai dai ta kawar da Kai amma tana Jin kishi,ba daman tayi wani abu yanzu Aisha za tace bata yarda ba Dan miji da gidan nata ne, sosai Zainab ke hak'uri da duk abin da suke mata, shi ko Nasir tausayin ta yake ji,Kuma yasan tana da hak'uri da biyyaya shiyasa yake tausaya Mata,




Cikin dare Zainab ta tashi da wani irin azababen ciwo, ga amai da take kwararawa kamar hanjin ta zai fito, duk ta galabai ta dayake kwanan Aisha ne,suna can tare, zuwa safiya duk ta wahala, dauriya kawai take yi, ranar ta fito parlour kenan taga Aisha na gyara ma Nasir necktie zai fita aiki, cikin sauri ta k'arasa tana gaishe shi gani tayi kawai ya fita ba tare da ya amsa mata ba, Aisha ce ta kalle ta ganin yanda lokaci d'aya ta canza Nan tace" Zainab meke damun ki ne?"


Cikin dane damuwar ta tace"ba komai Aunty Aisha me Kika gani?"


Tace"no kawai Naga you look somehow ne ko baki da lafiya ne please ki fad'a min?"


Girgiza kai kawai tayi tace"lafiya na k'alau"


Tace"ok amma in wani abu na damun ki let us know kinji"


Tace"okay"



Cikin kwana biyu ciwo takeyi sosai ga amai da take fama da shi ko abinci bata iya ci,tun Nasir bai lura ba har ya gane bata da lafiya idan ya tambaye ta sai tace malaria ce kawai, a haka har sukayi wata d'aya, a wannan lokacin ne Aisha ta lura tace ai Ina sai doctor ya duba ta, Nan ko Nasir ya kira doctor, yana zuwa ya duba ta yayi test d'in urine, Nan ya gano tana d'auke da ciki, mik'a ma Nasir hanu yayi yace"congratulations matar ka na d'auke da ciki"


Tunda ya zo duniya bai tab'a tsintar kanshi cikin farin ciki irin wannan ba sujudud shukur yayi ya gode ma Allah, Aisha ko rasss taji gaban ta ya fad'i,sai Kuma taji farin ciki Nan tayi ma Allah godiya domin ji takeyi kamar ita ce da cikin, Zainab ko wani irin dad'i da sanyi taji a ranta lokaci d'aya taji k'aunar abin da ke cikin ta, 


Doctor ya tayasu da murna Dan yasan shekaru da dama suna neman haihuwa gashi yanzu Allah ya amsa addu'an su ya basu haihuwar, Nan yace suje hospital a k'ara duba ta da abin da ke cikin, ai Nan suka tafi, anyi mata bincike ba abin da ke damunta sai laulayi, anyi scanning cikin wata uku kenan, sunji dad'i sosai,




Tunda suka gano tana d'auke da ciki suka fara ririta ta tare da nuna Mata gata, duk abin da take son ci sai an nemo mata, ga abubuwan da ake siyo mata har da na banza, duk wani abin kwad'ayi sai Aisha ta kawo mata, Nasir ma Yana ji da ita haka zasu tasa ta agaba da ci wannan Sha wannan, abu kad'an sun tafi hospital, wani lokaci sai Aisha ta tasa ta agaba da tambayoyi ko akwai abin da ke damunta, shima haka zaiyi ta tambayar ta ko akwai abin da ke damunta, murmushi kawai takeyi tace ba komai,  



Zainab ko haka zata zauna wani lokacin tayi ta kuka dan tana son cikin ta gashi za'a raba ta da abin da zata haifa, sai taji wani irin bak'in ciki, a wannan lokacin ne suka je gidan su Hajja tana ji da ita wani irin kulawa na musaman take Mata, Baban tane yazo shida ALIYU yaron yayan shi, Nan suka gaisa dayake su kad'ai ne nan tayi musu bayanin duk abin da ke faruwa, har sakin da Nasir zaiyi Mata , ai ko baba yayi Mata fad'a yace meyasa zata yarda da irin wannan auren kenan sunyi amfani da ita ne, Wanda ko a musulunci bai dace ba, nasiha sosai yayi Mata sannan suka yi sallama yana cikin tausaya Mata, Aliyu ko cewa zai kira ta a waya akwai taimakon da zaiyi mata,






Cikin ta wata takwas kenan yayi girma sosai gashi yana samun kulawa, dan su Nasir su na nuna Mata gata, cikin dare ta tashi cikin matsanan damuwa ya zama dole ta bar gidan nan idan har ba so takeyi a raba ta da abin da zata haifa, dama ta yanke shawaran barin gidan ta tafi inda baza su ganta ba, dama sun shirya da Aliyu cewan zaizo su bar gidan, dama tana da wani kud'i Nan ta kwashe ta had'a kayan ta cikin akwati sai ta kira Aliyu cewan yazo da asuba su tafi, dan akwai wani k'auye da zasuje, d'aukan biro da wani papper tayi tayi rubutu tana kuka sannan ta ajiye, shafa cikin ta tayi cikin kuka tace"bazan Bari a raba ni da Kai ba zan tafi da kai in Raine ka da kaina in baka tarbiyya domin nice mahaifiyar ka bazan yarda a raba mu ba"ta fashe da kuka,


K'arfe 4:00am Aliyu ya kira ta cewan gashi nan a k'ofar gidan ta fito, kasancewar su Nasir sunyi barci yasa ta fito da k'yar komai tanayi a hankali har ta bud'e gidan ta fita, lokacin da taje wurin gate ta cire duk wani key da sak'ata dayake d'akin maigadi a gefe yake, gashi dama sarkin barci ne,duk baiji ba har ta fita daga gidan,



Aliyu ta gani yayi tashar mota Nan yasa akwatin ta a ciki, suka shiga Nan suka d'auki hanyar wani k'auye,




 Lokacin da Nasir yaje masalaci dama idan ya dawo Yana shiga gurin ta yaga ko tana lafiya, aiko shigan da zaiyi sai yaga bata nan har toilet ya duba bata nan hankalin shi ya tashi haka ya k'ara zagaye gidan amma bai gan ta ba da sauri ya samu Aisha a bedroom yana tambayar ta ko taga Zainab cikin rashin fahimta tace bata ganta ba aiko ya fad'a mata shima bai ganta ba, cikin rud'ewa suka cigaba da zagaye gidan amma Babu Zainab babu alaman ta ko da suka zo gate sai gani sukayi a bud'e da aka tambaya maigadi yace bai san lokacin da ta fita ba, Aisha tayi mai fad'a sosai tace ba amfanin gadin da yakeyi tunda har za'a fita gidan yace bai sani ba, cikin bedroom d'in Zainab suka shiga Nan suka ga alama babu wasu kayan ta Dan ta hargitsa Kaya, kan bed d'in suka ga wani paper Nasir ne ya d'auka ya fara karanta abin da yake a rubuce kamar haka,



  *Assalamu Alaikum*

*Ku yafemin domin gaskiya bazan iya yarda in haihu in bar muku abin da na haifa ba Ina son baby na bazan iya rabuwa da shi ba, Aunty Aisha ki gafarce ni domin bazan iya baki abin da na haifa ba, Nasir Ina son kasan da cewar Ina k'aunar ka soyyayar da nake maka ne yasa na tafi da gudan jinin ka, Ina rok'on gafarar ka, kada kuyi wahalan nema na domin nasan lokacin da kuke karanta wannan letter nawa na Jima da yin nesa da ku, nayi nisan da baza ku gani ba*,


 *Matar ka Zainab*




Zama yayi kan bed yana fad'in sunayen Allah hannun shi ya rik'e kanshi da shi yana girgizawa, ganin hakan da Aisha tayi sai ta d'auki letter ta karanta, tana gama karantawa ta fad'i k'asa sumamiya, cikin tashin hankali ya d'ebo ruwa ya yayafa mata, d'ago ta yayi yana fad'in ta tashi kar ita ma ta tafi ta barshi,


Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta rushe da kuka, Nasir ma dauriya kawai yakeyi Nan ya fara bata hak'uri, cikin kuka tace" wallahi Zainab bazan tab'a yafe Miki ba, kin cuce mu"ta fashe da kuka,


Cikin lalashi da k'arfin hali yace" kukan nan bashi ne mafita ba yanzu ki tashi muje gidan dan su Hajja su san abin da ke faruwa"


Gidansu suka nufa inda Nasir ya fad'a musu abin da ke faruwa, Aisha ko kuka kawai takeyi, Hajja ko bata yarda hakan Zainab ta gudu ba sai dai ko sunyi mata wani abu, Nasir bai b'oye mata komai ba tun daga abin da Aisha ta had'a har zuwa yanzu, sai dai yayi ta bada hak'uri Kuma yayi nadama da yace zai saki Zainab, gashi ta tafi ta barshi, habawa ran Hajja ya b'aci sosai tayi musu fad'a Kuma tace Aisha ta cutar da yar'uwan ta gashi yanzu Hajja Bata san inda zata nema Zainab ba dan bata san inda mahaifin Zainab d'in yake ba ko dan halin Rayuwa tsabar bak'in kishin Abba ya Hana ta sanin komai dan gane da baban Zainab, dan lokacin da akayi auren k'anwar ta Amina cikin birni suka zauna, bata san k'auyen da yake ba,



Sun d'auki sati biyu suna neman Zainab amma Babu labarin ta abin duniya ya dame su, Nasir na ganin cewa yayi ganganci gashi har ya rasa matar shi da abin da zata haifa wanda yake bala'in son cikin gashi yanzu babu su, ita kuma Aisha tana ganin cewan Zainab ta cuce su ta gudu da ciki bayan tun samun cikin Nasir yace ya bata abin da za'a haifa, gashi tana k'aunar cikin ji takeyi kamar ita ke da cikin, ga son yara da yake damunta,



Anyi kwanaki da barin Zainab gidan inda Aisha ke cikin matsananciyar damuwa dan bata hak'ura ba so takeyi ta ganta da baby, bale idan ta kalla d'akin wasan yara da bedroom d'in su sai tayi ta kuka, ana cikin haka ne kwatsam sai gashi tazo gidan da yarinya, 


Nasir ya dawo aiki sai da ya huta take fad'a mai cewa ta samu yarinya, tana cikin driving sai taga anyi accident ko da ta fito mota sai taga wata mata ce aka buge ga tsohon ciki, shine aka sa ta cikin motan sukaje hospital, bayan sunje aka shiga da ita theater room inda aka ciro yarinyan mahaifiyar Kuma ta rasu, to ganin babu Yan'uwan matar ne Babu Wanda yasan ta ga alamun matar kamar mahaukaciya shine tace ma doctor d'in zata rik'e yarinyan insun yarda, Kuma sun amince Dan har police sunzo Kuma sun yarda, Nan ta nuna ma Nasir takardun sa hannu na amincewa, ya Kuma gamsu da maganar ta Nan ta d'auko Mai baby'n ya rik'e, lokaci d'aya yaji wani irin k'aunar yarinyan tare da son ta, gata Kuma kyakyawa, Aisha tace yasa mata suna aiko Nan yayi mata hud'uba yasa mata suna *NUWAIRA* ,


Washegari da safe


Suka zagaya dangi da iyyaye suka gabatar da NUWAIRA Kuma an taya su murna inda akayi jimamin b'acewar Zainab, sunci gaba da kula da NUWAIRA cikin so da k'auna kamar su suka haife ta, lokacin da NUWAIRA ta cika shekaru goma da haihuwa akayi mata birthday dan ana nuna Mata gata, a ranar birthday d'in ne wata ta gaya ma NUWAIRA cewar ai su Aisha ba iyyayen ta bane, ai ko tayi ta kuka sosai inda Aisha tayi fad'a da matar, Nasir da Aisha duk sunyi mata bayanin komai suka lalashe ta ita ma ta cigaba da d'aukan su a matsayin iyyayen ta Dan tana k'aunar su,




 *Mene ne labarin Zainab bayan ta bar gida?*




 K'arfe 2:00pm suka isa wani k'auye dama Aliyu akwai mahaifiyar Maman shi a k'auyen, gidan ta suka nufa da yake tasan da zuwan su Nan ta karb'e su cikin mutunci, bayan Zainab ta huta taci abinci ta fara tunanin gida da halin da Nasir zai shiga, 


Cikin Zainab ya Kai wata tara inda ta haifa kyakyawar y'ar ta mace Mai Kama da mahaifin ta, Zainab ta sa Mata sunan mahaifiyar ta wato *AMINA* za'a dinga Kiran ta da *MEENAL* ,haka Zainab ta cigaba da kula da *MEENAL* har tayi shekara d'aya sannan suka koma k'auyen da mahaifin ta yake, 


Lokacin da Malam Zakariyya yaga y'ar shi yayi farin ciki Dan ciwo ne ya kwantar da shi dalilin da yasa bai je cikin Abuja ba kenan bare yasan abin da ke faruwa, Nan ta fad'a Mai komai dama tak'i zuwa Nan ne Dan kar mahaifin ta ya matsa Mata sai ta koma gidan Nasir, Nan Malam Zakariyya yayi Mata fad'a yace bai dace tayi haka ba, Nan tace ita bazata Koma ba, Nan ya k'yale ta Dole wataran ta koma da kanta Dan shi Yana fama da ciwo,






*********** ***************





 *AFTER EIGHTEEN YEAR'S*



 *BAYAN SHEKARU GOMA SHA TAKWAS*




 Cikin tafiyar k'asaita take saukowa daga upstairs kamar ba zata take k'asa ba, kyakyawar budurwa ce chocolate colour ce tana sanye da armless d'in riga da three-quarter ko d'ankwali babu a kanta, *NUWAIRA* kenan,


Zuwa tayi ta zauna kusa da Hajiya AISHA, cikin shagwab'a ta kwantar da kanta a cinyar ta, cikin murmushi Aisha ta shafa gashin kanta tace" Daughter na an kawo kayan da Zaki sa na Graduation d'in ki, sai ki duba idan yayi Miki" ta mik'a mata wasu gown masu shegen kyau colours daban-daban, 


Karb'an kayan tayi ta ya mutsa fuskar kamar za tayi kuka tace"mom I don't like this design gaskiya a canza wani duk basuyi kyau ba" 


Da sauri tace"okay sorry daughter yanzu zan sa ayi miki irin Wanda kike so kinji don't worry" Nan ta d'auki waya ta kira ma'aikatan company d'in ta nayin Kaya ta fara musu fad'a cewan wanna kayan baiyi ba su shirya wani,


Nuwaira kwantar da kanta tayi a kafad'ar mom(Aisha),




********** *********



Wata kyakyawar budurwa ce tana sanye cikin uniform cikin natsuwa ta shigo cikin wani gidan k'asa, cikin zazak'ar muryan ta tayi sallama ta shiga tare da cewa"Ummie na dawo"


Zainab ce ta fito daga d'aki da sauri budurwan Nan ta rungume ta tana cewa"miss you Ummie na"


Janta tayi tace" wai *MEENAL* so kike ki k'arya Ni ko?"


Shagwab'e fuska tayi ta k'ara langwab'ewa a jikin ta, Aliyu ne ya shigo Yana cewa" ai Ni bansan ranar da Meenal zata girma ba, sai shagwab'a"


Turo Baki gaba Meenal tayi tace" Kawu Aliyu Ni ban girma ba a gurin Ummie na"


Ummie (Zainab) tace" Ni d'aga Ni kije ki cire uniform, kin tsaya surutu"


Mik'ewa tayi ta shiga wani d'aki,





*TAKU CE UMMU BASHEER*โœ๐Ÿป

[07/01 5:21 pm] Sis Ummu Bashir: ๐ŸŒน *ZURI'A D'AYA*๐ŸŒน


         ๐ŸŒน


   { *A story about Relationship, love and Friendship*}



 

  *NA*

*UMMU BASHEER*



ยฎ *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

  (We don'nt only entertain and educate,but we touch the heart โคof reader's๐Ÿ“š)_



#***

*#IG PML WRITERS*

#***

#***





 *WARNING*


*Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad'akarwa da nishad'antarwa , duk wace ta canza min zan d'auki mataki dan haka akiyaye*



*PAGE* *5*~*6*



*Dedicated to Badiyerh (beauty queen) & Maimounath o.g*



 *Ina son ku irin totally d'in nan buri na mu zama ZURI'A D'AYA, domin ku d'in na daban ce Allah ya k'ara had'a kanku ya Kare ku daga sharin makiyya da mahassada Ameen*


 *Kawaliya kawar Arzik'i Ina yinki sosai Allah ya kaimu biki mu kwashi shoki*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


*Sis Ina gaban ki kina baya na bazan barki ki wuce niba, muje k'asar waje mu kaiki amarya, Allah ya Kare min ke I love you wujiga wujiga*๐Ÿ˜


 *Hussaini 80k ban manta da alkhairin ka gare Ni ba Allah yasa ka gama exams lafiya Allah ya bada nasara*โœ๐Ÿป

 








An had'a ma Nuwaira party na Kamala secondary School da tayi, naira yayi kuka anyi b'arin kud'i sosai an raba abubuwa iri-iri, Nuwaira sai farin ciki takeyi ta gama school, Daddy (Nasir) ya sama mata gurbin karatu a Open University of Abuja inda zata karanci business,


Wani mota ne guda biyu suka yi parking cikin wani gida mai shegen kyau, driver ne ya fito da sauri ya bud'e mata k'ofa, Nuwaira kenan tana sanye cikin Riga pink da wando black Wanda ya kama jikin ta, gashin Nan an zubo shi gyale ya rufe rabi, sauran gashin na waje tasha make up, rik'e take da waya, har ta isa cikin parlour'n gidan, 


K'arasawa tayi inda mom take tayi Mata kiss a goshi tare da cewa"hey Mom I'm back"


Cike da kulawa tace"welcome back sweet daughter, kunyi waya da Daddy'n ki kuwa?"


Cikin shagwab'a tace"yeah he said he's not coming back this week, and bana son fara zuwa University baya nan"


Tace"don't worry daughter ai Ina tare da ke ok"


D'aga Kai tayi tace" I'm hungry now" ta turo baki,


Da sauri mom ta k'wala ma Mai aiki Kira,sai gata da sauri ta iso, Nan ta shirya ma Nuwaira abinci da sauri Dan yanzu sai ta hau ta da massifa,




 *********************



Yau ranar farin ciki ne a gare ta domin taci jarabawar ta na fita secondary School, gashi ta samu schooler ship an d'auki nauyin karatun su ita da wasu guda biyu a makarantar su, Nan ta fad'a ma Ummie sai dai sam Ummie tak'i yarda dan a Abuja ne, ita ko bata son duk wani abu da zai kaisu Abuja bare kuma Meenal, dan tunda Meenal tayi wayau ta fad'a Mata cewa mahaifin ta ya rasu tun kafin a haife ta,



Zama tayi a tsakar gida tayi shiru tana tunanin wani hanya zata bi dan Ummie'n ta ta amince ta tafi karatu a University na Abuja, can dabara ya fad'o Mata Nan ta shiga wani d'aki inda Malam Zakariyya yake zaune,


Fuskar tausayi tayi tace"Kaka dan Allah kayi ma Ummie na magana ta amince in tafi karatu please"


Gyara zama yayi yace" AMINA me sunan manya yanzu ke sai kin tafi karatu, kiyi hak'uri kawai kiyi auren ki, in Kuma kin tsufa a gida ayi auren da ni" ya k'are da dariya,


Kamar zatayi kuka tace" Allah ka cire maganar wasa wallahi Ina son yin karatu a Rayuwa ta Kuma an d'auki d'auyin karatu na yanzu ne nake da dama, kaga yanzu bamu da halin da za'a samar min wani karatun, please kayi mata ko zata yarda"


Ya tausaya Mata sosai ganin yarinya da gatan ta amma ji yanda rayuwar ta ya koma yace" karki damu me sunan manya, zanyi mata magana inshallah"


Murmushin farin ciki tayi tare da yin mai godiya, nan ta fito waje, Ummie ta gani tana dakan gero da yake tana d'an yin sana'a ana kawo mata dakan su gero da yaji,sai a biya ta,


Cikin tausayin Ummie'n nata take ta karb'a tana cewa" Ummie na ki zauna ki huta ni zanyi"


Ummie tace" Allah yayi miki albarka"


Ameen tace sannan ta cigaba da daka, bayan ta gama ne sai ga Aliyu ya shigo, da sauri ta same shi cikin murya k'asa-k'asa tace"Kawu please ku tayani rok'on Ummie na ta barni inje University'n Abuja please kaji Kawu"


Sai da yayi dariya yace"Abu Mai sauk'i, Ni kaina Ina son ganin kinyi karatu,dan haka ni zan shawo kanta ta amince idan Kuma bata amince ba zan shirya Miki komai ki tafi daga baya Dole ta hak'ura"


Cikin murna tace" Kawu gaskiya ka kawo shawara Mai kyau, kace infara shiri"


Dariya yayi yace"to sarkin sauri ai saiki bari kiji ya zamuyi"


Tace" toh Kawu na"



A haka kuwa akayi sun same ta sunyi mata magana tace ita Sam bata yarda ba ai su sunsan meyasa bata son Meenal taje can garin, sunyi-sunyi ta fahimce su tak'i,ganin idan suka bi ta nata Meenal baza ta samu karatu ba kawai sai suka yanke shawaran shirya ma Meenal Komai da student zata b'ukata har suka gama komai, amma Ummie bata san komai ba,


A ranar da zata tafi Kaka(Malam Zakariyya)yace da Ummie ta bar Meenal ta ziyarci wata k'awar ta da take can wani k'auye dayake suna shiri tace ai ba damuwa taje, aiko Aliyu ne zai Rakata, haka suka samu mota a Tasha sai garin Abuja,inda Aliyu ya kaita har makarantar, Nan aka nuna Mata hostel d'in da zata zauna, inda ta rabu da Aliyu cikin kewa, bayan ya bata waya Dan su dinga Jin ta, Nan ta shirya kayanta dayake har da kayan abinci duk su Kawu sun siyan mata,




 

*K'auye*


Lokacin da Aliyu ya koma gida ya fad'a ma Kaka cewan ya Kai Meenal lafiya, sai ya kira Ummie suka fad'a Mata gaskiya,habawa hankalin ta ya tashi ji takeyi kamar an raba ta da y'ar ta ne,ko kad'an bata so hakan ba, sai dai da Kaka ya fad'a Mata babban dalilin da yasa gara Meenal tayi karatu sai ta hak'ura tunda ba yanda zatayi,




 

*OPEN UNIVERSITY ABUJA*



 Sauri-sauri ta shirya cikin Riga da skirt na atamfa lemon green da d'igon light blue, wani k'aramin hijab ta d'auko light blue tasa sannan ta saka flat shoe Wanda shi kad'ai take da shi Kuma ya kusa tsinkewa,haka Nan tayi managing tasa, wayan ta ta d'auka tare da Kiran Ummie'n ta,


Tana Jin ta d'auka tace" Ummie na ki gafarce ni domin ban kyauta Miki ba,Dan Allah Ummie na kiyi hak'uri Sam bana son b'acin ran ki"


Ummie tace"Sam banji dad'in hakan ba sai dai ya zanyi bayan kun taru a kaina har da min dubara, yanzu ai shikenan, Allah ya sa ki fara karatu cikin nasara,Kuma zanja kunnen ki akan kici gaba da tsoron Allah, banda samari da k'awayen banza dan yanzu Babu na gari,kinji ko"


Tace"eh Ummie na inshallah zan kiyaye baza ki same Ni mai karya nasihar ki ba"


Nan tayi ta mata nasiha sosai tasa mata albarka sannan suka yi sallama, 




Meenal ce sai sauri takeyi wannan shine first time da zata fara shiga lecture bata son yin late, sauri kawai take Dan ta isa,



Kyakkyawan saurayi ne na k'arshe Yana sanye da Riga black Mai kwalliyan Stones da wando white irin na Indian Nan, waya ne a kunnen shi yana magana sai sauri yakeyi, dai-dai ya taho bai lura ba ita ma ta taho kawai sai sukayi karo yayin da suka fad'i k'asa, wayan shi ya fad'i ya k'asa ita Kuma litafan ta suka zube,


Mik'ewa tsaye yayi cikin b'acin rai ya kalle ta, yayin da ita ma ta mik'e tsaye, cikin b'acin rai yace"are you blind ko sama Zaki hau ne da baki kallon hanya"


Takalmin ta ta kalla ganin ya tsinke ga litafan ta sun zube ga Kuma maganar da yake gaya Mata, cikin haushi tace" Kai hankalin ka na Ina ne da baka kallon hanyar,Kuma bazan yarda ba sai ka biya ni takalmi na ehe"ta murgud'a baki,


Tsaki yaja tare da d'aukan wayan shi yace" idiot kawai baki da manners" ya fara tafiya,


Binshi ta fara yi tana cewa sai ya biya ta takalmin ta amma ko kula ta baiyi ba ga mutane sai kallon su sukeyi, ganin bai kula ta ba Kuma ga litafan ta a k'asa ga time d'in shiga lecture zai wuce kawai sai ta hak'ura ta dawo ta kwashe su, ta tafi tana tunanin irin abin da zatayi mai in sun sake had'uwa Dan babu abin da ta tsana irin aci mutuncin ta ko na wani,




After two days


Wata shegiyar mota ce mai kyawun gaske yayi parking cikin makarantar Open University, tsayawa nayi Inga ko su wane a cikin motar, hmm Reader's ko kunsan suwaye ne? Wani kyakyawan saurayi ne ya fito ta k'ofar zaman driver da alama shi ke driving d'in, wani saurayi ne shima d'in kyakyawan ne ya fito daga seat d'in baya sannan yayi nuni da hannu irin na ciki ta fito kamar yanda turawa keyi,


Nuwaira ce na gani ta fito tana sanye cikin Riga da skirt na English wear tasa takalmi hill, tayi rolling d'in gyale a kanta fuskar Nan tasha make up ga wani sunglasses da tasa, cikin k'asaita ta fito, Wanda yayi mata alaman ta fito da hannu ya kalle ta yace" my queen sai yaushe kenan?"


Cire sunglass d'in tayi tace"My prince charming you know bana jure zaman class I think Nan da two hours ka dawo ka d'auke ni mu tafi"


Murmushi yayi yace" duk yanda Kika ce haka za'ayi"


Tace"okay bye"


Shima ya d'aga mata hannu alamar bye, kallon na kusa da shi tayi Wanda tunda suka fito motar baice komai ba tace mai"Bye *FAWAS* "


Wanda aka kira da FAWAS d'aga Kai kawai yayi, na kusa da shi d'in ne ya buga bayan shi cikin Wasa yace" Kai banza ne wallahi kana ji my queen na maka sallama kak'i magana"



Cizan lips d'in shi yayi na k'asa irin wai shi yaji zafin nan yace" banson haka fa *KAMAL* sai bayan kun gama soyyayar ku ne zaku tuna da ni ba"


Wanda aka kira KAMAL yace" you know something idan Ina tare da queen d'ina mantawa nake da kowa"ya k'are da dariyan mugunta Dan yasan aminin nashi ya shak'a baya son maganar soyyaya dan yace soyyaya is just a wasting of time,


Tsaki FAWAS yayi ya shiga kusa da seat d'in driver yayin da KAMAL ya shiga gurin driver yayi driving suka bar school d'in,






*Shin su wane ne FAWAS da KAMAL?*


*Ku biyo ni domin Jin Asalin su*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.