Free chapter · Read without an account
5️⃣
ABIN DA YA BAKA TSORO...🦋
(Arrow Of Destiny)
بسم الله الرحمن الرحيم
*EWF*
5️⃣
Duk kasuwar babu wanda baya jin yarinyar har cikin rashin, gashi Baaba Me kosai mace ce da take da tsafta shi yasa itama yarinyar kullum zaka ganta cikin tsafta, ko irin majina ko tasono babu ba zaka tab'a gani ba, sabida kulawar da take samu.
A bangaren Uwarta kuwa kawai sai dai godiyar Ubangiji, amma jikin ta kara tabarbarewa yake, domin ta kai sai an kwantar da ita an tayar da ita, haka ya kara tadda hankalin Malam dan haka ya shiga mata addu'a Rabe yana mata rubutu, sannan wani zuwan Alie ya suka kaita babban asibitin Niymia musamman bangaren ƙwaƙwalwa, inda ta kwashe wata bakwai ana bata kulawa. Ta warke amma ba zata iya baka labarin abinda ya faru da ita, ko ta tuna bayan ta. Asalima yanayin haukar yana tashi lokaci zuwa lokaci.
★
Bayan shekara bakwai.
Duk da bata cika shiga cikin yara yan uwanta ba, sai dai ta saba da mutanen kasuwa domin ya zama ko sallah ce kayan da take samu daga hannun su ya wuce tunanin mutane unguwar su, gashi ta sanadin karatun da ake a wurin Malam yasa Baban Alie ya gina babban islamiyya me azuzzuka, sai dai duk da wannan cigaban bai saka Meriama ta sake cikin Yara ba, domin tana shiga zasu fara kokarin koranta da tsangwamar ta.
Tunda Alie ya gama Jami'a, aiki yake na bank, a nan Niymia amma asabar da Lahadi, yana Birnin Bayero koyarwar Islamiyya. Idan yazo bai da wani lokacin yan gidan su. Kasancewar gidan yanzun babu Buhayyah sai yaran da Matar baban shi ta dauko daga Mali, Yan mata uku babban cikin su ta kai shekara goma sha bakwai, sunan ta Shukurah sai wacce take bin ta sunan ta Nadra, tana da shekara goma sha huɗu, sai karamar su me suna Widad ita ce zata kai sa'ar Meriama. Yaran Allah ya daura musu kishin Meriama musamman da suka ga Alie baya ta kansu, duk da kuwa suna da dangantaka me karfi, amma haka ya tattara su ya watsa a gefe, ya zuba hankalin shi da rayuwar shi akan Maram.
Yadda suka ji labarin a bakin yan unguwa musamman waɗanda basu shiga harkan Baaba me kosai, yasa dan gulma wata juma'a bayan sun dawo daga makarantar boko, dan makarantar su daya da ita Maram din shi Alie din yake biya. Dake an fara sauke ta a gidan su kafin a wuce da su, da sauri suka bi bayan ta har cikin gidan. Ta shiga da sallama.
"Mamma kina aiki ne?" Dake ta same ta tana wanke gero a bakin rijiya.
Dauke kai tayi tana aikin ta, idan da sabo ta saba da halin Mahaifiyar ta a duk lokacin da ciwon ta yake son motsawa toh baki daya sai ta daura mata tsana da kiyayya kamar me.
"Yar mahaukaciya ce dama ita ake cewa jikar Baaba me kosai" inji Nadra tana tab'a Shukurah.
A razane ta juya tana kallon su.
"Yar macikule mahaukaciya. Idan muka kara ganin ki a motar makarantar mu sai mun gayawa yan ajin ku" suka gaya mata haka cikin zarewar idanu. Gyada musu kai tayi domin tana da mugun tsoron fada bata son fada. Fita suka yi abin su ita kuma ta shige dakin su ta sauya kaya. Tana gyara hargitsattsen gashin kanta, Maman ta shigo dakin juyawa tayi ta kalle ta. Sannan ya fara kokarin hada gashin. A hankali taji hannun ta a kanta tana kame mata gashin. Bata ce mata kome ba dan dama ba magana suke ba,.ta daure mata gashin har da kitse mata jelar gashin.
Sannan ta wuce ta, ta zauna tana kallon yadda Meriama take tsaye.
Mika mata hannu tayi, da sauri ta isa jikinta. Ta kwanta a jikin ta tana shafa mata baya. Duk da bata gane kanta ainun amma tana gane idan Meriama din tana cikin damuwa, idan da ace Rabe ko Alie ko Baaba suna gida toh tasan ba zasu barta cikin kunci ba, haka yasa taji ba zata iya barin ta a damuwa ba, kuma yaran da ta gani dazun tabbas sun mata abu ne dan taga suna fita ta share hawayen da ya zubo mata.
Janye jikin Meriama tayi ta fito ta nufi dakin Malam, da sallama yana zaune yana addu'oi.
"Malam ina Baaba da kawu Rabi'u suka tafi?"
"Sun tafi duba jikin Matar Ghali ce da ta haihu kuma bata da lafiya "
"Toh Allah ya dawo da su lafiya " ta fada tana me nufar kitchen, ta dibi abin ta fito ta samu Mamanta tana zaune, ajiye abincin tayi ta nufi ɗaki ta dauko taburma ta shimfida musu, ta zauna ta fara kokarin ci kenan su Widad suka shigo da gudu, tare da jifar su da duwatsu, a razane ta kare kanta. Kafin ta yi tunanin haka Maman ta, ta dauke ta sun shige daki. Jifa sosai suke a gidan ran malam ya B'aci ya daka musu tsawa.
Fita suka yi suna fadin mahaukaciya yar macikule, kuka kawai Meriama take, hango Baaba da Rabe yasa suka gudu. Lokacin da suka shiga cikin gidan, sun sami malam yana ta fada, nan yake gaya musu abin ya faru. Basu wani dauki abin da muhimmanci ba, dan haka suka watsar da maganar a wurin.
Washi gari suka tafi Islamiyya, dake tun juma'a ya dace Alie yazo bai zo ba, haka yasa bata damu sosai ba, da wuri ta shirya. Ta fito tsakar gida ta ce.
"Malam na tafi, Mamma bata da lafiya naga tana ta barci zan dawo anjima"
"Allah ya dawo dake lafiya, ya bada abin da aka fita nima"
"Amin Malam" ta fada yarinya ce qarama amma tana da fahimta sosai kodan Allah yasa tana cikin mutanen kirki ne.
Tana fitowa ta hadu da su Widad gaban ta ne ya fadi, kanta a sunkuye ta wuce su. Tana tafiya burinta shine ta nisance su. Har sun kusan isa islamiyyan, suka tsare ta a hanyar da wata yarinya me suna Jalilah itama suka hadu suna dukan ta.
"Kusan Umma na ta gaya min wai shegiya ce bata da Uba! A kasuwa aka samu cikin ta." Ita dai bata ce musu cikan ku ba, har suka gama maketa sannan ta shige abin ta, bayan an tashi musu break ta nufi gida ta duba jikin Mamanta suka taro yara suka biyo ta, suka ta jifarta har cikin gidan. Lokacin Maman ta, ta fito tana shara. Ganin yadda suka koro mata Y'a bata san lokacin da ta dauki ita ce ta bisu da gudu ba, ta fita waje har zaninta yana kuncewa, tuburan yara suka saka Yarinye take hauka.
Ranar Meriama tayi kuka tayi danasanin dawowar ta, Allah da ikon shi ashe Alie yana gida, kuma aka rasa wanda zai kori Yaran, sai da yaji hayaniya yana harabar gidan su. Ya fito, kusan yaran islamiyyan baki daya suka zo wannan tijaran. Daukar zanin ta yayi ya daura mata idanun shi Jajjur yana hango Shukurah da Nadrah suna dariya, ya riko hannun Yarinye ya kaita har cikin gidan. Anan ya same Meriama ta hada kai da gwiwa tana jin kirjinta yana zafi da suya.
Saka Yarinye yayi a daki sannan ya fito, ya jima akan ta domin yadda ya tsaya a gaban ta hasken ranar da yake kanta ya kare da bayan shi bai saka ta d'ago kai ba, ya jima a haka amma bata d'ago ba.
"Meriama yaran gidan Alhaji Hamza ne ko?" Bata d'ago kai ba ta ce.
"A'a Malam basu bane" tana fadar haka ta mike ko inda yake bata kalla ba, dan haushin kowa take ji. Riko hannunta yayi yana faɗin.
"Malam sune karya ta maka" juyawa tayi tana tura baki.
"Malam Alie kai ma kaga abinda suke mata ko? Wannan abin da suke zai kuma tunzura laluranta don Allah a dakatar da haka"
"Insha Allah Malam"
Sannan ya sake hannun ta ya juya zai fita.
"Toh meye nawa da kike fushi da ni?"
Shigewa daki bata kula shi ba, ai duk laifin yan gidan su ne, dan haka ba zata kula shi ba,.tayi shigewarta dakin tana tura baki.
Yana fita makarantar ya nufa, tun a hanya ya karyi Bulala sannan ya nufi cikin makarantar. Ya saka aka buga kararrawan komawa aji. Ya nufi ajin su Shukurah ya ce.
"Fito"
"Sayyid kayi hakuri don Allah"
"Fito nace" ya daka mata tsawa,
Ta fito sannan ya juya yana kallon fuskar yaran ajin.
"Kema fito Kema fito" ya ciro waɗanda idanun shi ya gani, sannan ya ce musu.
"Ku fitar min da yan iskan da suka raka ku"
Dan mugun ta wasu basu tafi ba amma haka Jalilah ta fitar da kusan rabin ajin, wasu daga cikin mazan ajin suka ce mishi.
"Malam wallahi Basmah da Khameela da Nana basu fita ba, muna tare dasu muna muraja'a"
"Koma ku zauna, su kuma mu tafi"
Haka ya tafi ajin su Nadrah, nan ya kwashi yaran da ya gani sannan suka nufi ajin su Widad. Sukan baki daya ajin ya fitar da su waje. Yasa suka durkusa sannan ya shiga dukar yaran aka gayyata ya kuma kore su a makarantar.
Sannan ya dawo kan Shukurah da Nadrah da Widad, hannu bibbiyu yake zane su, wani irin mahaukacin duka yayi musu dan Widad sai da ta suma, Ita kan Shukurah tsabar duka fitsari tayi a jikin ta. Nadrah kan taurin kai da zuciya yasa ko kuka bata yi ba.
"Gobe idan kuka ga Meriama kar ku fasa nima ba zan fasa ba! Jahilai kawai" duk da yana ganin haka zai sama mata nutsuwa a'a sai ya kuma jefa tsanarta a zuciyar su, sauran yaran kuwa tsoro yasa baki daya suka yi alkawarin ba zasu kuma shiga harkanta ba.
Anan ya bar su ya dawo gida, sai da yayi wanka da ruwan zafi, domin bai saba ba, bai ma tab'a dukar wani ba.
Koda su Baaba suka dawo suka ji labarin abinda ya faru, ranta ya ɓaci dan haka ta ce.
"Baki sake zuwa makarantar."
"Akan me? Yanzu ta fara zuwa duk wanda yaga ba zai iya ba ya bar makarantar" ya fada yana shigowa cikin gidan.
"A'a Aliyu ba zaka gane ba, babu wanda ya tab'a cin zarafin Yarinye irin yau dan haka ta zauna ai tana karatu a wurin Malam"
Dakyar Baaba ta yarda, lokacin da su Widad suka dawo gida, suka fadawa Matar baban shi, a madadin tabi bayan su ai kuwa ta ce su tattara su koma Mali ba zasu ja mata magana da yan unguwa da mutanen arziki ba. Bayan sallah isha ta shiga cikin gidan Baaba ta basu hakuri sannan ta ja meriama tayi ta rarrashinta.
Bayan fitar ta ne Iyayen yaran suka bawa Malam hakuri da suka zo karatun dare, yayi maganar da ta shiga cikin zuciyar su ta zauna.
"Babu wanda yafi karfin ƙaddara sannan babu wanda ya isa yace Allah ba zai jarabce shi ba, daga Meriama har mahaifiyar ta, basu ki farin ciki da kyakyawar makoma ba, amma qaddara ta musu karan tsaye, kowani mutum akwai yadda Allah ya ke jarabtar shi, dan haka ku gayawa Matan ku da Yaran ku, babu wanda yafi karfin ƙaddara..."
Hakuri dai suka bashi da rokon ya saka baki Malam Alie ya mai da yara makaranta, murmushi yayi sannan ya ce musu.
"Insha Allah zasu koma"
Bayan an tashi yana shiga cikin gidan, yana jin Rabe yana mata kari, tana biyawa murmushi yayi a yan shekarun ta, tayi nisa a cikin Alqur'ani. Baya ga sauran littatafan da take zuwa daukar karatu wurin shi. Ya yarda mutane masu baiwa suna daga cikin wadanda Allah yake jarabtar su, Meriama baiwar Allah.
Yana shiga dakin shi Alie yana shigowa.
"Baaba a bani tuwo don Allah ba zan iya cin shinkafa da Hajiya ta girka ba"
"Ai kuwa tuwo ya kare sai hakuri" inji Rabe.
"Ai kai Rabe nasan ki gidan ka naje sai nayi da gaske zaka bani ruwa"
"Eh mana"
"Meriama dauko mishi abincin shi" tashi tayi tana bata rai, tana dauko abincin ta dangwara mishi zata wuce.
"Ke meye haka?" Rabe ya daka mata tsawa,
"Kayi hakuri " ta fada Muryan ta yana rawa.
"Kyale ta yarinta ke damun ta "
"Yarinta ko rashin kunya? Shi sa'anki ne?"
"Kawu kayi hakuri" ta fada tana kuka.
"Haka don Allah kyale ta mana "
"Allah Alie bana son reni."
"Laifi aka mata fa " inji Alie ya fada.
"Idan an mata laifi sai ta kare akan ka, kai sa'anta ne? Me yasa bata tare su ba, na kara ganin kin yiwa Babban rashin kunya zai na zane ki idanun ta kamar na tsaka "
Da sauri ta shige dakinsu tana kuka.
"Kayi hakuri don Allah wallahi yarinta ke damun ta"
"Malam ka daina haka zata rena ka, sannan ta rena ni nima "
Mai_Dambu
*TOP-NOTCH WRITERS*
*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*
_Kasancewar bikin kanwata ake ta biyar me suna Zahrah sai kaiwa da komawa nake Hankalina yana kan Babbar kawata Farisah tsaki nayi na wuce can na kuma dawowa na zuba mata ido cikin takaici mahaukaciya ta zare_
_Malama kin zo biki ne ko kin zo karanta chat kin yi shiru kin b'ata shiru_
_Wani banzan dariya ta saka min tana d'age min gira_
_Hmmm Bestie wai ke ko irin karance-karancen social media baki yi irin su Wattpad,Okada, Arewabooks baki yi?_
_Sake baki nayi ina kallon ta. When rabona da Hausa Novel Allah na tuba tun Iyatuh Abba tana karanta a gidan Radion B.R.C tabe baki nayi na ce mata_
_Ke rabani da kayan wahala rabona da Hausa novel tun zamanin Iyatuh Abba_
_Innalillahi!, Tace tana kallona kafin ta ce. Jasmin yanzun don Allah duk cigaban da aka samu baki san da shi ba? Lallai kin wuce yadda nake tunani kin gani wuri na karanta book din da nake fama da shi_
_Cikin mamaki na wuce na dawo na zauna kusa da ita nace mata don Allah daura ni a hanya ina ganin kowa na karance-karancen amma ban dani_
_hmmm lallai zata fashe... Toh saurara da kyau nan da kike gani na karanta books nake na marubuta daban daban amma idan ana dara ana fidda uwa... Kin ga last na ga The Governor's Wife, one to three, after ma gama na karanta Zaytoonah.... Abun dad'i sai na cikaro da Affiyah da Unaisah_
_Allah Aunty Rukayyah kina karanta online hausa novel ne? Lallai toh ai yanzu ina karanta Zayn Malik Jiya na gama karanta Zanen ƙaddarata,_
_Kanwata Amaryan da muke bikin ta ta saka mana baki a she ba banza yarinyar nan ta nace daga gama sakandare tace a direta gidan miji_
_Amarya Zahra toh kuwa nima Zayn Malik nake karantawa musamman rigimar Hajiya da Uncle Bashir, da Zayn da Abul amma kin san zata fashe on October?_
_Don Allah fa_
_Hmmmm gamayyar marubutan nan sun hade wuri guda za ta fashe sun fitar da sunan Team din su_
_Aunty Don Allah ya sunan Team din?_
_TOP-NOTCH.... Za ta fashe a books uku Sahla A Paris, Bani Da Laifi Abin da Ya baka Tsoro_
_Wow da gaske?_
_Zan Miki karya ne?_
_Ina da number Mai_Dambu bari na duba nasan zata daura a status...._
_juyawa tayi ta kalle ni ina bin su sa kallo ke kuma ko garzaya Wattpad ko duba Ribar Uwa, Mutum Mugu, Wadata, Uwargidan Bahaushe, Bororoji,Kallabi does story sun tab'a ni_
_Kut nace sannan na cigaba da cewa don Allah ga Iphone dina daura Wattpad ke kome ma daura min nima ta fashe dani_
_Tabbas za ta fashe amma fashewar alkhairi....._
_Books din da zasu zo kamar haka_
1- Sahla A Paris
2-Bani Da Laifi
3-Abin Da Ya baka tsoro.
Dukkan su Uku 1k
_Guda daya_ 350
_Guda Biyu_700
_Guda Uku_ 1k
_Zaku iya payment ta to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria_
_and send evidence to does number_
*****
Or
**** or ****
_Dukka zaku iya tura shaidar biya_
_Ga masu turo katin MTN zasu iya turawa Zahrahn Addah Ramlat da kuma Yan Nijar zasu turawa Nana A'ishah_
**** a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
*+22784506476*
_Welcome ta Top-notch Team_