Free chapter 路 Read without an account

CHAPTER FOURTEEN

by Ummubasheer 路 KE HASKE CE

Alhamdulillah* mutane sai zuwa suke tunda aka sallama su LAILAH a hospital. MAHEER bakin shi har kunne dan farin ciki. Mommy ta iso sai ji take da LAILAH ta zame mata tamkar uwa. A haka maijego da baby'n suka cigaba da Samun kulawa har ranar suna.




Yaro yaci sunan Mahaifin MAHEER ana kiran shi da Junior tubarkallah yaron yayi goshi dan sosai LAILAH ta samu kaya da kud'i gaskiya.



Y'an group d'in ke Haske Ce suma ba'a barsu a baya ba dan sunzo sunji shinkafa rengem sun deb'o rawar shoki馃拑馃拑 abin dai ba'a magana dan ni kaina banyi tunanin zasuje ba nasha sai matar SAMEER ta haihu sai gasu Luxurious biyu sukayi suka zo ma LAILAH suna ai ko sunyi K'okari da zasu tafi LAILAH ta kawo surveynious sunji dad'in yanda ta karama su.


Taro yayi taro an watse taro sai dai muce Allah ya raya Junior. Amin




Sunyi jegon su lafiya cikin kulawar Hajaju kullum yana gurin ta sai Idan yayi kuka Hajaju ke kawo mata shi ta bashi abincin shi. MAHEER na son junior dan yakan yi rainon shi Idan yana gida. Soyaya tsakanin MAHEER da LAILAH kam ba'a cewa komai dan MAHEER ya kosa tayi arba'in ko yaushe Idan yaga LAILAH in ba Hajaju sai ya makalkale mata.



A haka har sukayi arba'in ai ranar ba'a cewa komai dan MAHEER kusan zaucewa yayi. Ba karamin gyara Mommy da Hajaju sukayi mata ba.


Da asubah sai sa mata albarka yake. Ai ko sai ga sabuwar mota dal tukuici. LAILAH fa sai Zuba mai addu'a take tana bashi kiss dan motar tayi mata.




A wannan lokacin AISHA ta haihu y'a mace mai kama da ita AYAAN sai rawar kai yake duk ya rude saboda murna Mommy tace sai dai ya kai mata ita tayi wanka a gidan ta. Da k'yar ya amince suka tafi ranar suna su LAILAH suka je har da MEENAL wacce ita ma cikin nata ya fara tsufa.



Baby taci sunan LAILAH kowa yayi mamakin hakan sai dai AISHA ce ta matsa asa sunan sunji dad'in hakan ko LAILAH har da kuka baran ma da ta tuna lokacin da AYAAN ya fad'a mata yana son ta har da kuka. MAHEER ma yaji dad'in sunan.



Satin su LAILAH d'aya a gurin Mommy dan ma MAHEER ya takura sai sun dawo ne.




Bayan dawowan su da sati d'aya suka je k'auye. Kawu sai sa musu albarka yake MAHEER yaga yana cikin halin buk'atar taimako nan ya taimaka mishi da bashi riba domin fara Sana'a sosai kawu yaji dad'i ya dinga sa mai albarka. Har gidan kawu aka rushe Akayi ginin zamani mai kyau kaka taji dad'i sai godiya take ma MAHEER.






Bayan wani d'an lokaci matar SAMEER ta haihu ta Haifa D'a namiji mai kama da Baban shi. SAMEER ranar farin ciki ba'a magana nan ya dinga waya ya sanarwa. Y'an uwan MEENAL sun zo Maman ta ne ta zauna da ita. Matan yayyen ta duk sun zo ranar suna yaron yaci sunan Baban SAMEER suna kiran shi da Khaleel. Taro fa yayi albarka mutane da dama sunzo ciki harda fans d'in SAMEER. Sai dai muce Allah ya raya.







LAILAH ta koma makarantar ta na nursing. Hajaju na kular mata da Junior. MAHEER da LAILAH zaman lafiya mai cike da soyaya shine sukeyi. 

















*Bayan Shekaru Hud'u*





Lokaci na tafiya da rana ya fito nan da nan sai ya fad'a lokaci na gudu kamar kiftawar ido. Gashi yanzu an kwashe shekaru hud'u. Zaman lafiya ne mai cike da tarin soyaya akeyi a families guda uku Wato iyalan SAMEER. MAHEER da AYAAN.




SAMEER da MEENAL yanzu yaran su biyu maza Khaleel shekarar shi hud'u sai kanin shi mai shekaru uku Habibullah. Yanzu MEENAL tana d'auke da tsohon ciki. Zaman lafiya suke tare da kaunar juna. K'anwar SAMEER ma tayi aure ta Haifa baby girl taci sunan maman su.




MAHEER da LAILAH sun zama hanta da jini domin tsananin soyaya da kulawa da juna tare da mutunta juna. LAILAH ta gama nursing school d'in ta har ta fara aiki a wani hospital shekarar Junior uku ta Haifa baby girl wacce taci sunan Mahaifiyar LAILAH Rukkaya suna kiran ta da Little yarinyar na kama da LAILAH sosai. MAHEER na matukar son little da ji da ita yana nuna mata gata ita da Junior. Hajaju na tare dasu tana kuma jin dad'in zama dasu. Rayuwa Mai dad'i sukeyi. MAHEER na k'ara Samun bud'i. Suna yawan kai ma Mommy ziyara junior ma yana zuwa Hutu. Mommy na matukar son LAILAH yanzu kamar y'ar ta.



AYAAN da AISHA suna zaman lafiya da soyaya ta Haifa baby boy ita ma sunan shi Muhseen shekarar shi biyu yayin da little LAILAH keda 4yrs. AYAAN na son AISHA saboda biyayyar ta.




Tsakanin LAILAH. MEENAL da AISHA sun had'e kan su zumunci sukeyi sosai dan kusan duk weekends akan taru a gida d'aya tare da yaran su duka. Yaran ma sun shak'u da juna. Gashi school d'in su d'aya. Rayuwar farin ciki ne ke gudana a tsakanin su sometimes dukan su da yaran su sukan kai ma Granny ziyara. Tana jin dad'in hakan sosai.






MEENAL ta haihu ta Haifa baby girl wacce taci sunan Maman ta. Gaba dayan su sun had'u a gidan da yaran su.



Suna d'aki sai jin kukan little sukayi da sauri suka fito dan jin fad'a.



Junior ne da Khaleel ke dambe yayin da LAILAH karama Wato y'ar AISHA take ihu tana cewa"Junior na k'ara mai kar ka raga mishi"



AISHA ce ta raba su tana tambayar meke faruwa.


Cikin huci Junior yace"Allah Mami (da haka suke kiran ta)Yaron nan ya raina ni dukan little nayi ta cije Laila ta shine na duke ta sai ya dake ni. Ki fad'a mai ni ba sa'an shi bane"


Dukan su mamaki ne ya kama su dan tun ba yau ba suka lura akwai shak'uwa a tsakanin Junior da Laila.

Khaleel ma a fusace yace"Idan ka sake dukan little sai naji ma ciwo"


MEENAL ce ta buge bakin shi"kar ka sake cewa zaka ji ma d'an uwan ka ciwo bad manners ne wannan"


LAILAH tace"to shine sai kin bugan min suruki na. Kaji zo muje rabu dasu ai little taka ce"


Laila ko dariya takeyi AISHA tace"ke Wato kece mai had'a su ko zo nan kiji babu kyau had'a fad'a"


 "Bazan sake ba Mami sorry"


Ta rik'e hannun Habibullah sukayi waje shi yaron ba ruwan shi shiru shiru ne. 



Little kuka tasa tana kiran Daddy'n ta. AISHA ta d'auke ta suka Shiga d'aki.



Da daddare mazajen su suka zo daukar su. 



Anyi taron suna an watse. Sosai LAILAH da AISHA sukayi mata abin alkhairi.










Kwance suke kan ta na kan kirjin shi idanun ta a lumshe.


Yayin da MAHEER ke kallon sama shafa kan ta yayi yace"Baby kin tuna wani abu?"


Dago kai tayi"mene kenan My luv?"


 "Ranar da kika fara zuwa gidan mu aiki, ko Kinsan tun lokacin sai in dinga jin wani abu akan ki sai nayi tunanin ko tsana ce Ashe asalin soyaya ce"


Murmushi tayi"Amma ka kasa gane hakan sai daga baya. Kuma shine kazo min da Soyayyar nuna isa da tak'ama ko" ta fad'a tana dariya.



Dariyar shima yayi"Allah baby baza ki gane bane. Wallahi ina mutuwar kaunar ki ta dalilin ki fa nayi accident na kusa mutuwa"


 "Wayyo My luv wallahi da bazan tab'a yafe ma kaina ba. Amma gashi yanzu muna tare a matsayin ma'aurata kuma da yaran mu. Mijina yanzu kai ne abin Alfahari na. Zuciya ta kai kad'ai take kauna da muradin kasancewa da kai har abada. I love you so much" ta kare da bashi hot kiss.


K'ara kissing nata yayi"I love you too my Wife. LAILAH kin zamo tauraruwar da take haskaka min zuciya. LAILAH *KE HASKE CE kuma KE ALKHAIRI CE* domin kin taimake ni a rayuwa banyi tunanin zanyi Rayuwar farin ciki ba sai gashi ina farin cikin da banyi tunani ba har abada bazan barki ba. *KE HASKE CE*"



Rungume ta yayi ya fara kissing ko'ina na jikin ta tana dariya yayin da yake maimaita Kalmar *KE HASKE CE, KE HASKE CE, KE HASKE CE*馃挕







Ni Ummu Basheer tare da massoya na muke cewa *LAILAH KE HASKE CE*馃挕






 *ALHAMDULILLAH*



Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.