Free chapter ยท Read without an account

17

by faridat mshelia ยท ๐Ÿง‘โ€๐Ÿฆฝ๐Ÿ˜ญSUN GUJE NI ๐Ÿ˜ญ๐Ÿง‘โ€๐Ÿฆฝ

๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿ˜ญSUN GUJE NI๐Ÿ˜ญ๐Ÿ‘จ๐Ÿปโ€๐Ÿฆฝ

(SANADIN CUTAR LAKKA)

IT BASED ON TRUE LIFE STORY.


LABARI DA RUBUTAWA:FARIDAT HUSAIN MSHELIA(UMMU-JIDDAH).





***




*Wannan Shafin na ki ne Maman Amatullahi (masoyiyar Muhammad ๐Ÿ˜€) alhairin Allah ya Kai Miki tare da ahalin ki*



SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI.


MAGANIN BIRI KAREN MAGUZAWA.



Ji ya yi tamkar Yana da k'arfin da zai shaketa ta mutu ko zai huta da bak'in cikin ta,Kalmar ta na karshe ji ya yi tamkar ta buga mi shi guduma,nan ya ji Wani hawayen bak'in ciki Yana zarya a kumatun shi Dan yanda ya kwallafa rai akan wannan cikin saboda ba ya tunanin zai k'ara Wani dogon zango a irin wahalar ciwon nan da ya ke ciki amman shine wannan mahaukaciyar za ta yi mi shi haka?,


Lallai Annabi ya yi gaskiya da ya umurce mu da zabar mace tagari,tabbas da Allah zai ara mi shi tsawon rai da ya zamto Mai yi ma al'ummar Annabi nasiha akan zabar mace tagari Dan tabbas ya ga illar rayuwa da jahilar mace irin Ra'isat,



muguwa azzaluma lallai Ra'isat ta cancanci dukkannin Wani Kalma daga gare shi saboda salwartan mi shi da gudan Jinin sa da ta yi,


Ganin yanda ta yi mi shi kerere Akai ya sa ya ce"yanzu cikin nawa ne a bola saboda ke azzaluma ce"



"kwarai kuwa kai a tunanin ka zan cigaba da dakon gudan Jinin ka alhalin kai da Yan'uwan ka ba so na ku ke yi ba?,


"yanzu lokaci ne na d'aukar fansa,lokaci ne na ramakon akan dukkannin ababen da ku ke aikatawa a gareni, ya ka ga wasanya fara Dadi ko?ta yi mi shi fari da Ido tana haske shi da Wani irin dariya na alamun nasara,



Ga ka a kwance shememe kamar gawan sababi ni da ka ke cema komai zero ban iya komai ba gashi Allah ya dawo da Kai mara koman ka ga makomar ka tun anan duniya kafin muje can.........



Wani irin ihu ya yi Wanda ya janyo hankalin ilahirin mutanen da ke kokarin shigowa wajen shi bayan sun idar da sallan,


Zagaye shi su ka yi a rude suna tambayar sa "lafiya meyasa me shi?"


Ra'isat kawai ya ke nunawa da hannun sa da ya ke daga shi da kyar ya gagara cewa uffan saboda yanda k'irjin shi ke dukan uku-uku,


"Me ki ka masa"cewar Nihal wacce ke shigowa cikin d'akin a rude,


"Me ki ka masa nace"ta furta hakan tana tunkarar ta tare da shakota saboda yanda hankalin ta ya ke a tashi,




"Bazaki yi magana ba sai na zamto silar shekawar ki barzahu ne"ta yi shiru tana muzurai saboda yanda ta mamaye ta tare da shaketa a jikin Bango da kyar ta samu ta ce"to me ki ka ji ya ce na yi ma sa da kike kokarin rabani da numfashi na?",


Aka yi kan su saboda yanda su ke kokarin kacame wa da kokawa Amman sai Yusuf ya katse su da cewa"ku fitar min da wannan shaidaniyar daga gidan nan,shin waye ma ya sa aka kawo ta bayan an San mara Imani ce ba ta da babban buri fa ce ta ga bayana?


Tana bak'in ciki da lafiya ta sannan Banda makiyiyar da ya wuce wannan azzalumar matan, ku fitar min da ita daga gidan nan na tsane ta na tsani ganin ko Mai irin sunan ta Dan ta zalunce ni ta cutar da rayuwata"ya fashe da Wani irin kuka tamkar zai shide saboda bak'in ciki,


Ganin yanda k'irjin shi ke ciccira tsabar bak'in ciki ya sa hankalin ilahirin yan'uwan na shi su ka yo kan shi suna babba shi hakuri tare da kwantar ma sa da hankali,gumi sosai ya ke tsiyayo wa daga jikin shi dan haka su ka fara shashshafa mi shi ruwa a jiki ana fiffita shi,ruwa su ka ba shi ya sha saboda harzukan da ya yi bakin shi har Wani kumfa kumfa ya ke yi saboda fushi,


Umman shi ce(k'anwar innar shi)ta kalle shi ta yi gyaran murya sannan ta ce"to yi maza-maxa ka ba ta damar salwantar mana da rayuwan ka a banza da wofi,ita d'in banza me wannan mahaukaciyar za ta fad'a Maka a yanzu Wanda ba ta fade shi a baya ba har shine ka ke Wani ciccira bayan ita d'in Bata da banbanci da tunkiya,ka fitar da lamarin yarinyar nan a ran ka tun kafin Raina ya Baci"shiru kawai ya yi Yana sauraron ta sai girgiza kai ya ke yi alamun Umman shi ba za ta Gane Wani irin cuta ne ballagazar nan ta yi mi shi fa?


Asarar rai a cikin wannan yanayin da ya ke ciki may be rabon shi kenan fa a duniya ba zai k'ara samun Wani ba,Jin yanda cece-kuce ya yi yawa kowa na ta ba sa baki da hakuri ya sa ya ji zuciyar sa ta fara sanyi,


Nihal ce kadai ta fahimci yanayin da ya ke ciki dan haka a hankali ta dinga rada mi shi Kalmar"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,Allahumma ajirni fi musiba ti wa ahlifni Khairan min ha"bin bakin ta ya ke yi Yana furta shi har ya ji Wani irin nutsuwa ya fara sakko mi shi a hankali har Wani lafiyayyen bacci ya yi awon gaba da ita su ka fice tare da barin masu jinyar na sa.


Kai tsaye d'akin da ake saukar Baki su ka isa inda su ka tadda Ra'isat ta na hada kayanta bak'in ciki tamkar ya kashe ta ganin yanda Nihal ke shafa ma Yusuf ruwa a jiki tare da furta mi shi addu'a ita da ta ke nesa da su sai ta ga tamkar rada ta ke mi shi a dalilin kalmomin ta ma su Dadi har Wani bacci ya yi,


Tukuki ta ke ji Dan matuk'ar ta cigaba da zama a gidan nan tabbas bak'in cikin su zai kashe ta Kuma yanda ta lura anan Sam ba za su dauki salon iskancin ta ba duka za su yi ma ta tamkar sun samu jaka(ni kuwa na ce to menene maraban ki jakan tunda ba ki da hankali ai maraban mutum da Dabba kenan),


Cikin Shan mur Umman Nihal ta ce"uban wa ya kawo ki garin Kano?",


Kan ta a sunkuye ta ce"Ummata"


"Garin ya ya Hakan ya kasance,ku ka shigo tare da Yan'uwan sa",


"A tasha mu ka hadu saboda yan'uwan Yusuf sun ce ba za su kawo ni ba ni ni Kuma inason zuwa gurin mijina",


Murmushin takaici Umman ta yi Jin yanayin maganan da ta mata ba alkunya bakomai, a zuciyar ta ta ce lallai wannan yarinyar ba k'aramar mara kunya ba ce,


"Dole yan'uwan mijin ki su ki kawo ki saboda ba ki da hali Sam,a yanda na lura da ke tarbiyya ta mi ki karancin Dan haka umurni zan baki ki tattara ya na ki ya na ki yanzu aje a saki a mota ki koma gida, alhamdulillah Daman yau Salisu(d'an'uwan Yusuf ta bangaren uba)zai koma kin ga sai ku tafi tare"


A razane Ra'isat ta d'ago Kai"Ni ba in da zani wallahi....."


Ganin banzan kallon da Umman ta bi ta da shi ya sa ta hadiye sauran maganan da ta yi niyyar furzar wa,


 Umma kuwa kokarin dannar zuciyar ta kawai ta ke yi saboda matsayin suruka Ra'isat ta ke a gurin ta Kuma Sam ba zai Yu ta biye ma haukar ta ba Dan haka ta ce"ni ba'a min musu dan haka ki hanzarta tun kafin in saba mi ki"ta fice ta ba ta guri,


Zaman dirshan ta yi a wajen tana Jin tamkar ta tsala ihu Dan bak'in ciki wannan shi ake kira a Dake ka a Hana ka kuka,tunanin yanda ta zo garin Kano ta fad'a yanda har abokan shi tayi-tayi da su Amman sun ki kawo ta Dan haka ta gudu zuwa gida gurin maman ta da kud'in da ke hannun ta su ka zo garin Kano da ya ke mahaifiyar ta na da cikakken address da bayani akan yanda yan'uwan Yusuf za su zo a ranar shiyasa ma su ka shigo tare Amman ace yanzu za'a komar da ita wallahi da sake Dan haka har lokacin tafiyan ya yi Bata kintsan ba Umma da ta shigo ta ganta a zaune yanda ta bar ta ba ta ce mata uffan ba sai dai d'aukar jakar ta da ta yi ta hahhada ma ta sauran kayayyakin da taki hadawa,Nihal ce ta fatattake ta Dan dole ta yi gaba, haka ta wuce ba tare da sun bari ta k'ara ganin Yusuf baA sauka rababa Shugabar mahaukata.


****** ***** ******* *****

Ko da Yusuf ya farka Sam Bai nemi sanin yanda aka yi da Ra'isat ba shi dai bai gan ta ba har gari ya waye su ka yini Bai ji motsin ta ba,ta bangaren sa ma bai tambaya ba saboda yanda ya ji ya tsane ta dan haka ya shafe babin ta a rayuwar shi,dan ya lura da idan ya ce zai Sanya damuwar ta a ran shi tabbas za ta kashe shi tun lokacin sa Bai yi ba.


Haka rayuwar ya cigaba da tafiya Yusuf Yana ta k'ara samun sauk'i Dan har likita ya ba su izinin a fara koya ma sa zama,


A ranar da aka dagashi ji ya yi tamkar wuyar shi zai bar gangan jikin sa dan tsabar azaba sa da Wani irin ciwo da wuyar ya ke masa,nan aka tattalabe shi da filulluka tamkar jaririn da aka fara koya ma sa zama,


Ko minti kadan ba ya yi sai ya ji ya gaji haka za'a k'ara kwantar da shi,tun ana irin haka har ya dawo Yana iyayin awa d'aya a zaune har ya zamto zai iya wuni kwanciyar ta sa sai jefi-jefi,


Ganin yanda ake samun sauk'i ya sa iyayen shi aro juriya aka cigaba da jinyar sa tare da siya ma sa magunguna masu Dan Karen tsada sai dai abin ka ga masu karamin k'arfi su ka fara gazawa,


Shawarar da Yusuf ya kawo na k'anin shi ya Saida Vesfar shi a kawo kud'in domin acigaba da yi masa magani shine ya k'ara ta da kura domin Ra'isat ta yi tsalle ta dire akan ba'a isa a Saida kayan Yusuf ba.




*Littafin nan ba kirkirarren labari ba ne ga masu korafi, tun a farko nafada mu ku labarin nan ya faru da gaske so bani da ikon canza abinda ya faru domin faranta ma ku Readers,in Kun ga xaku cigaba da bibiya fine in Kuma Bai yi muku ba kuna iya bari*




*Ummu-jiddah.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.