Free chapter 路 Read without an account

_*TWENTY SEVEN*_

by Sadiya Auwal 路 BAKAR AYAH

     ____****馃枻馃枻****_____     


  馃枻 *BA茦AR AYAH* 馃枻


     馃枻 _BOOK1_ 馃枻



Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA

[ _瞥ar mutan Jama'are_ ]





    *WATTPAD*

***


    *AREWABOOKS*

https://arewabooks.com/u/sadeesakhna


______________****_______________





Page 馃枻27馃枻





Bayan shekara biyu.............



Kyakykyawa kana farar budurwace sanye da riga da wando farare,tayi 蓷amara da wani jan 茩yalle a mulmulallen kunkuminta wanda yabaje yabada siffar mata masu cikakken diri,saidai daga ganin jikin kasan ana yawan motsashi,dan a tsikeyake tsama.

Juyi take tayi gaba tayi baya da sanda a hannunta,wanda take tafiyar dashi a iska cike da bajinta da kuma 茩warewa.

Tayi kaman sa'a guda tana yi,amma batada alamar dainawa ko nuna gajiyarwata.

Sai can kaman da da茩i茩a uku ta tsayah tana maida numfashi sama sama.

Duk da rigar wuyanta nada 蓷an sama,amma kasantuwar tsallan data sha nakusan awa guda,yasa wuyan rigatata yin kasa,da yanda mutum na iya kallon saman fararen albarkatun 茩irjinta.

Jan rigar tata tayi tagyara,har sannan bata daina fidda nimfashi ba sama sama.

Nufar wajenda ta ajiye kayanta tayi tareda 蓷aukar gorar ruwa takafa a bakinta.

Da yawa tasha ruwan kafin tasaki ajiyar zuciya nauyayya..

Shuru ta 蓷anyi ka蓷an jin wani motsi yana nufo inda take,idonta ta bu蓷e a wajen da kunnenta yajiyo mata motsin..

Kasantuwar girman tafara suma idanuwannata sun samu damar 茩ara yin dara dara farare tass,茩wayar idonta kuma yanzu tasake yin wani shu蓷i mai she茩i sosai,Motsi shu蓷in cikin idon yake yi,daga 茩arami yakoma babba daga babba yakoma 茩arami,sakamakon daidaita hasken ranar dayake haskawa zuwa cikinsa,wanda ganyen bishiya yake mata inuwa kuma yana karka蓷awa.

Dan shi kansa ganinta saidayi training sosai akai,yanda zata saita kallonta da rana da kuma dare.

Motsin datake jine yafara yawa kana kuma yana matsowa kusada ita..

Cikin zafin nama ta cafki kwari da bakarta tareda saita wajen da idonta ya tsaya akai.

Sauke kwari dabakar tayi tana kallon wani 蓷an matashin yaro dabazai wuce shekarunta ba wato sha biyar.

茒aga hannu yayi sama alamar yayi sarranda lokacin data nunashi da kwarinnata,sai kuma yayi murmushi tareda jingina a jikin bishiyar da take kusada shi.

"Waye kai?"

Bombee tafa蓷a cikin tsare fuska,alamar babu wasa a gameda tambayar datayi masa.

Takowa yafarayi a hankali har zuwa kusada itah,kana yasaka hannunsa yana shafa jikin kibau 蓷im dake kan kwarin.

Har zuwa lokacin murmushin dayake kan fuskarsa bai bace ba.

"Shin zaki ajiye kwarin idan nace ni aljani ne?"

"Bana san shashanci ka fa蓷amin kai waye,ko kuma duk abinda nayi maka karka ga laifina akai"

"Ba shanshanci bane nima tambaya nayi miki,amma karki 蓷au da zafi,sunana Aliyu,amma ana 茩irana da haidar,ina so muyi abota ne dake,shin zaki yarda dahakan"

Sake daure fuska Bombee tayi jin maganar wanda yakira da kansa haidar 蓷in ya bafa蓷a.

Harara ta gallamasa tareda sau茩e kwarinta tayi wajen da ta ajiye kayanta.

茒auka tayi ta sa茩ala a kafa蓷arta tareda yin hanyar inda zata fitar da ita daga cikin dajin.

Binta yake a baya yana magana,amma ko waiwayowa batayi ba ballanta na ta kulashi.

Hakanne yasa ya dakata da binta,tareda yin dariyar gefen baki,shareshin datayi karon farko na haduwar ta dashi sai yaji ya burgeshi.

Tun sati daya dayayi yana yimata la'be yana ganin mai takeyi dama yayi tunanin hakan daga gareta.

Tunda yake bai taba ha蓷uwa da macen data burgeshi kamarta,ta yarda da kanta,sanann kuma bata kunyar nuna jarumtarta,duk da kasancewarta kuwa 拼a mace.

"Zamu sake ha蓷uwa Bombee dole sai na miki abinda zaki kulani"

Daga haka ya juya yayi wata hanyar daban yana jijjiga kai.

Itama Bombee a nata bangaren mamakin yaron data hadu dashi take,shin anya kuwa mutum ne,bata taba ha蓷uwa da wanda yakalleta batareda tsoron halittarta ba sai yau,idan tacire goje wanda shi bata sakashi cikin jerin mutane.

In mutum ne mai yakeyi a cikin jeji.....kai itama ai mutumce kuma take zuwa jejin,mutum ne ma dam bataji wani yarr a jikinta ba,irin wanda take ji idan mai aljanu ko kuma wajen da aljanu suka wulga ba.

Yanda taga shigar kayansa da kuma yanayinta,su kansu basuyi mata kamada irin na mutanen yankin su ba.

"Haiiidarrr???,koma waye kai bai shafeni ba,inka shiga gona ta ba raga maka zanyi ba"

Tafa蓷a cikin 茩warin gwiwa(confidence).

Gidan inno ta nufah,saida taci abinci tayi sallahr azahar kafin ta nufi gidansu.

Ko salama batayiba ta shiga gidan,babu kowa a tsakar gidan,dan haka 蓷akinsu ta wuce kai tsaye.

Innayi ce a kwance kan gadonta ta tsuga mata sayi na baccin rana,dan dama ita tana fitsarin kwance.

Kallonta take tareda kama kunkumi tana kallon innayin,babu abinda yake tasomata a zuciya sai takaici.

Gashi dama babu wuyah sai ranta yabaci,ita kanta tana mamakin yanda koyaushe sanzawa take daga yanda take a baya.

Wani lokacin bata ganin laifin mutane idan suna aibatata,dan tasan tanayi musu abin muzgunawar ba bayanda zasuyi,saidia itama babu yanda zatayi,in anyi mata laifin daya bata ramaba ji take kaman zatayi hauka,muryar datake zugata a cikin kanta bazata taba barta tayi bacci cikin salama ba.

Dawo da tunanin ta tayi kan innayi wacce take jagab cikin fitsarin datayi mata kan gado.

"Yau zakici bantan innarki laari a gidannan innayi,dama ina taraki da gulamar dakikeyimin a cikin gari,shegiyar yarinya kai"

Takarisa magana tareda ficewa daga 蓷akin tana cijan baki.

Fitowar inna laari daga 蓷akinta taga wucewar Bombee cikin 蓷akinsu ta bulali a hannunta dogaye guda biyu tana yimusu tuka.

Zaro ido tayi dan tafi kowa sanin mai Bombee zatayi dasu.

"Keeee Bombee wazaki daka da wannan bulalin haka?"

"Ki zuba ido kiga wa zan daka dasu mana,miye kike wani gaggawa"

Ta 茩arisa maganar tana watsawa inna laarin harara.

Tana shigewa 蓷akin ta rufo 茩ofar kirif,ko minti biyu ba'ayiba 茩arar dukan bulala ya jiyarci kunnenta,da kuma kukan 拼ar tata wacce take har 茩asan ma茩oshinta.

"Wayyo ku ceceni zata kasheni wayyo,innata innata ki taimakeni innaaaa"

Ganin inna laari bazata jure ihun 拼ar tata ba yasa ta nufi 蓷akin Daneji wacce itama take bacci,ga kwanannnan laulayin ciki take mai wahala,har ya yi wata biyar amma wahalar sa ta茩i barinta ta huta.

"Daneji bakyajin Bombee ne zata kashe 拼ar uwarta a 蓷aki"

Zabura Daneji tayi ta tashi dakyar tareda nufar 蓷akin su Bombee,wacce bakajin komai sai 茩arar bulalin dakuma ihun innayi wanda yafara dushewa.

"Ke Bombee ki bu蓷e 蓷akinnan nagayamiki,wai meyake damunki nene kam a gidannan,anya kuwa kanki daya,ki bude dakinnan kafin raina ya baci inagaya miki"

Bu蓷e 茩ofar tayi tana huci kaman sunyi dambe da bijimi,kanta a 茩asa bata bari sun hada ido da Daneji ba,wacce in kallo yana huda mutum daya hudata a lokacin.

"Mai tayi miki kika mata wannan mummunan dukan?"

"Fitsari tayimin akan gado,bayan tasan na hanata hawa min gado"

"Yanxu dan kawai rayi miki wannan lafin shine kika yi mata duka haka,"

"Fa蓷amata dai,anyi mata aure ta kasheshi da ba茩in halinta,ta dawo gida ita ba auruwa zatayi ba tana musgunawa 拼an gidan.akan fitsari shine zakiyimata wannan dukan dan ba茩in hali,nasan ma ba iya akan fitsari bane akwai wani mugun nufinki dai daban"

"Ehh akwai mungun nufin,tunda take zuwa tana munafurcina ko kuma takemin raini kin taba hanata ne,shine danna 蓷au mataki za'a ga laifina,in kinji haushi ki rama mata mana,kiga in ban kasheta a gidannan ba muss har lahira kum.........."

Fasss bata gama kaiwa ayah a maganar tata ba taji Daneji ta wanketa da wani zazzafan mari a kumatunta,kafin ta juyo tasake da蓷a mata a 蓷ayah kuncin.

Idonta har kan茩ancewa yakeyi jikinta yana rawa saboda bacin rai,nuna Bombee tayi da yatsa tareda cewa.

"Bombee........yanzu har kinyi girman da a gidannan zaki bu蓷i baki ki fa蓷awa addah laari haka,ehh lallai yau na tabbatar da baka haihuwar 蓷a kuma ka haifi halinsa,kin nuna min iyakata tabbas,kuma naji da蓷i da nunamin wanann halin da kikayi kinji"

Kecewa da kuka inna laari tayi jin abinda Bombee tafa蓷a mata akan idonta,wanda suna cikin hakanne mlm Ahmadu shima ya shigo gidan.

Tambayar mai yake faruwa yayi,amma babu wanda ya tanka masa,ita Daneji tana faman yiwa Bombee fa蓷a,yayinda ita kuma inna laari take aikin share hawayen idonta da gefen zaninta,itakuwa wacce tafi dakuwa kukanta yafi na kowa yawa a gidan.

Larai kuma taga kan katanga tana sallallamin jin abinda Bombee tayi 蓷in,dan tun ihun innayi na biyu take kan katangar.

Shi mlm Ahmadu dayake ta faman tambayar mai yake faruwa,bai samu sanin hakan ba daga wajen su,sai a wajen inna larai wacce take kan katanga tana kwararo masa bayani kaman recorder.

Tun kafin tagama fa蓷amasa mai yake faruwa ya zari igiyar awakai dake gefensa ya hau Bombee da duka,wacce take tsaye 茩inkam yana dukannta.

Tun yana dukannata da igiyar har saida ta yayyage ta baje a hannunsa,amma Bombee tana tsaye ta rufe idonta,sai ya zabga mata bulalar ta蓷an runtse ido ka蓷an.

Shatu ce itama dake kan katangar tasamu damar fa蓷in

"Yanzu Bombee bazaki gudu ba irin wannan duka da ake miki"

Bayan ita babu wanda yayi magana,kowa baki ya bu蓷e yana kallon Bombee,yayinda shikuma mlm Ahmadu duk bayan duka 蓷ayah sai zuciyarsa ta 茩ara tafasa.

Jefar da igiyar yayi yasake tsinkar tashanyar su ya cigaba da dukan Bombee da ita.

Wanda ita kuma a nata bangaren ba dukanne yake wahalar da ita ba,illah 茩o茩arin datake wajen cin galaba akan muryar datake yimata amo a cikin kanta.

Ba abinda take umartarta dashi illah tarama dukan da mahaifinta yake yi mata a lokacin,wanda har abada bata fatan taga hannuwanta sun aikata hakan.

Salatin dataji su inna laari sunayine yasakata bu蓷e idanuwanta da sauri,ba komai ta hanga ba sai mahaifinta kwance a 茩asa yana dafe da zuciyarsa,wanda tasan ko tantama bazatayi ba ta sanadiyyartane hakan ta faru.

Abin haushin kuma duk yadda taso 茩wakwalwarta tasaka zuciyarta jin haushinta abin ya faskara,saima haushin mahaifinnata daya turnu茩eta.

Tsugunnawa tayi a hankali zatakai hannunta kansa,caraff taji an rike mata hannu.

"Karki kuskura ki taba shi,wlh bakida wannan damar,ki bacemin daga gani yanzunnan"

Daneji ce tayi maganar wacce idonta yayi jajur ta tsanar halin Bombeen.


Ohhhh nagaji......i hope dai yana sugar littafin koh????




_*Sadi-sakhna ce*_


Share

Comment

Like

Follow

Fisabilillah 馃檹馃徏


Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol