Free chapter · Read without an account

10

by Hauwa A Usman · SAKI RESHE..

SAKI RESHE...!*_

*(CIGABAN GADAR ZARE)*


*HAUWA A USMAN*

_JIDDARH_


_Masu buk'atar cigaban littafin *SAKI RESHE...!* zasu biya 300 ta account number Hauwa Auwal Usman GT Bank 0153259310 idan aka turo kud'in sai ayi screenshot (shaidar biya alert sms) a turo ta WhatsApp number 07020489340, ko a turo katin waya na 300 ta WhatsApp number 07020489340 banda kira please WhatsApp chart kawai_


Free Page


1️⃣0️⃣


Turus sukayi gaba d'ayansu ganin abinda ke faruwa Umar ya kalli Usman, Aliyu ya kalli Abubakar kafin gaba d'ayansu suka mayar da kallansu ga Ya Mu'allim,

dake tsaye tamkar an dasashi mak'ogwaranshi ya bushe, yawun bakinshi ya d'auke, k'irjinshi ya shiga buga da tsananin k'arfi,

ido ya runtse da k'arfi yana karanta duk addu'ar data zo bakinshi, yau 'yarshi ta cikinshi tsaye a titin Allah rungume da wani k'ato,

jikinshi na kerrrrrma da tsuma ya dafe bango yace " Usman jeka taho da ita, yace Usman ne dan yasan duk cikinsu babu mai sanyin zuciyarshi,

jikin Aliyu na rawa yayi saurin cewa " bari naje Abba, ya fad'a yana nufarsu, Ya Mu'allim bazai iya dakatar da Aliyu ba saboda yadda yake jin jikinshi,

Aliyu bayyi wata-wata ba ya kifawa Zaman mari had'i da fisge Basmah daga jikinshi, yana fitar da iska me zafi daga bakinshi,

" ka rabu da k'anwarmu babu kai babu ita dan bazamu tab'a baka aurenta ba, guntun murmushi Zaman yayi kafin yace " kana wasa da wuta yaro,

amma nayi maka uzurin rashin sani ne yasaka yin haka, dan haka karka k'ara, 

sannan maganar k'anwarka kuma ita ya kamata ku fad'awa in zata iya rabuwa da ni danni baku da iko dani, babu kuma abinda zaku iya yi min,

itan ma da kuke da iko da ita ku fad'a mata ta rabo da dani idan kuna ganin zata ji, kun makara kunyi sake, dan haka kada ka k'ara cewa na rabu da k'anwarku, 

" d'an iska basik'i ba auren Basmah kake san yi ba lalata ta kake san yi, murmushi Zaman ya kuma yi a karo na biyu kafin yace,


" Na fad'a maka ka kadaina danganta ni da abinda bai shafeni ba kuma bani da alak'a dashi,

da Basmah kuke da iko ba Zaman ba itace 'yarku kuma k'anwarku dan haka ita zaku takura ku hanata kula ni, ita ya dace ku tsawatarwa ba ni ba,

kuma da kake cewa zan lalata ta, ni na shiga har gidan na fito da ita?


" Ko igiya na zarga mata na jawo ta dole?


"Kaga babu d'aya da kanta da k'afafuwanta ta fito, da kuka fito kuka ganta a jiki na kunga alamar na tilastata?


"Ko kunga muna kokawa tana tirjewa?


" Dan haka ka gyara bakinka, kuma aurenta nake san yi dan imba aurenta zanyi ba da tuni an wuce wajen danna samu dama a kanta yafi a irga, 

ka sani ma ko an d'an d'ana....! ya k'arasa maganar yana kashewa Aliyu ido, 

" duk da haka ba damuwa idan zaku bani aurenta zan aure ta ko yau ko yanzu anan take zaku aura min ita ina so, so ba lalata da iskanci ya kawo ni ba,

a zuciye Aliyu yayi kanshi yanajin tuk'uk'in bak'in ciki na tsark'e mishi k'irji, saurin shiga gaban Zaman Basmah tayi ta tare shi, tana kuka tace,

" ba laifinshi bane Yaya duk abinda zakuyi ni ya kamata kuyiwa bashi ba dan bashi da laifi,

ina sanshi Yaya, shi kad'ai nake so, wai meyasa kunk'i ku fahimce ni ne?


"Meyasa idonku ya rufe akan k'iyayyar masoyin ahalinku, wanda yake son had'a jini daku?


"Dan Allah ku barni na aure shi dan girman Allah, wallahi ina sanshi, ta k'arasa maganar tana durk'ushewa had'i da fasa matsanancin kuka,

da ido Zaman yayiwa Aliyu alamar ka gani ko?


Aliyu ya d'aga hannu zai naushi Zaman ya jiyo muryar Ya Mu'allim a galabaice na cewa " karka tab'a shi Aliyu ya fimu gaskiya, hala baka ji abinda yace ba?


"Gaskiya ne shi ba d'anmu ko d'an uwanmu bane, haka bamu da wani iko akanshi, bamu da iko sashi komu hana shi, da Basmah muke da iko,

ita muke da ikon lankwasawa da tankwarawa, ka rabu dashi yaje ba laifinshi bane, kana gani da kanta da k'afafunta ta fito, bamu da hujjar da zamu k'alubalance shi,

yana kaiwa nan ya juya ya shige gida yana matsar hawaye, Umma na daga cikin get tana jin duk abinda ya faru ta bi bayan Ya Mu'allim da kallo cikin tausayi tana share hawaye,

ido Umar ya zuba mata na tsayin lokaci kafin yace " kin kyauta Basmah tunda abinda kika zab'awarka kanki kenan,

kuma kike ganin ya dace da rayuwarki ki saka mahaifanki zubar hawaye, ki saka su kuka saboda bak'in cikinki,

nasan kin san illar hakan basai na sanar dake ba, kin san sakamakon d'igon hawayen iyaye akan d'ansu, so basai na tunatar dake ba,

yana kaiwa nan ya shige gida, Aliyu da Abubakar suka rufa mishi baya, " Sister kina ganin kin kyauta?


"Kina ganin kinyi dai-dai kin sakawa Abba da Umma da alkhairi?


"Kina ganin wannan hanya me b'ullewa ce kika zab'arwa kanki ta saka iyayenki kuka akan d'a namiji da bashi da tabbas Basmah?


Sautin kukanta ta k'ara had'i da sunkuyar da kanta k'asa, " a gabanki ya tsaya yana fad'awa mahaifinki da Yayyanki bak'ar magana,

Basmah namijin daya tsaya k'erere agaban mahaifinki ba jin kunyar ya rungume ki batare da aure ba yana fad'ar cewa aka sani ma koya sanki a 'ya mace shine kika zab'arwa kanki abokin rayuwa?


"Shine kika zab'arwa 'ya'yanki uba?


Ganin maganganun Usman na neman yin tasiri a zuciyar Basmah yasa Zaman saurin zamewa k'asa had'i da fasa kuka yace,

" I'm sorry Brother nasan ban kyauta ba but.....! hannu Usman ya d'aga mishi had'i da cewa " ba da kai nake magana ba, hala ka manta abinda kace yanzu?


"So da 'yarmu kuma k'anwarmu nake magana dan haka ba ruwanka.


"Kayi hak'uri Yaya wall....! saurin kama hannun Basmah Usman yayi ya shige gida da ita, sosai hakan yayi masifar d'agawa Zaman hankali,

har bedroom d'inta Usman ya kaita ya zaunar da ita a bakin bed yace " ki tuna da alkhairan iyayenmu akanmu, na tabbatar sun sauke duk wani nauyinmu da Allah ya d'ora musu,

dan haka kema kiyi k'ok'arin sauke nasu nauyin dayake kanki, bai jira tayi magana ba ya fice,

ta yunk'ura zata mik'e taji vibrating wayarta kamar ta share shi amma sai zuciyarta ta kasa, jikinta a sanyaye tayi picking ta kara a kunnenta batare datace komai ba,

sautin kukan dayake yasa zuciyarta daskarewa ta shiga tsalle tamkar zata tsaga k'irjinta ta fito.


" I'm sorry nasan ban kyauta ba, banyi dai-dai ba dana tsaya gabansu Abba ina fad'ar maganganu haka ba, but nayi hakan ne dan nema mana mafita,

na fad'i abinda na fad'a ne dan sama mana mafita nayi tunanin idan na fad'i hakan zayyi tasiri a zuciyar Abba ya bani aurenki,

ban san kuskure nayi ba, ban san abinda yake dai-dai da wanda ba dai-dai ba, a gidan marayu nayi rayuwa,

acan na taso na tsinci kai na babu mai sani ko me hana ni, bani da wanda zai nuna min dai da wanda ba dai ba, ban san asalina ba Basmah, 

ban san waye ni ba, ban sani ba ko hakan yana da alak'a da rashin bani aurenki, ya k'arasa maganar cikin matsanancin kuka mai cin rai,

take taji zuciyarta tayi sanyi ta nemi laifinshi da take gani ta rasa, taga abinda yayi dai-dai ne bayyi laifin komai ba, cikin ranta tace " me yayi?


"Wanne laifi ya aikata dan yana nemar mana hanyar cikin burinmu?


A zahiri kuma tace " ka daina fad'ar haka dan Allah, kaima mutum ne kamar kowa, babu wanda ya fika har awajen Allah sai wanda ya fika tsoranshi.


"Dole na fad'i haka Basmah kowa baya so na, zamani ne na daga k'auri sai gwiwa kowa daga shi sai nashi, shiyasa babu wanda ya damu da marayu irin mu,

babu wanda ya damu da matsalar wani balle a taimake shi, " kayi hak'uri in sha Allah da sannu zamu cika burin mu,

" to! kije ki kwanta, ya fad'a yana sauke ajiyar zuciya had'i da kashe wayar, washe gari Safiyyah ta zo ganin kwana biyu bata ga aminiyarta ta ba,

a tsakar gida ta iske Umma tana aiki, Safiyyah ta d'anyi mamaki dan a iya saninta Basmah ke yin komai a gidan,

cikin ladabi Safiyyah ta karb'i aikin da Umman keyi ta k'arasa, kana ta shiga ciki wajen Basmah, 

kwance ta iske ta saman bed rigingine tana waya da Zaman, jin an shigo yasa Basmah yin firgigit a d'an tsorace dan tayi zaton wani ne ya shigo cikin 'yan gidansu,

siririn tsoki taja cikin ranta tana komawa kwanciyar tace,


" Kin bani tsoro na zata wani ne ya shigo, ta fad'a cikin rashin kulawa dan haushin kowa Basmah ke ji, Safiyyah bata kula da yadda Basmah tayi mata magana ba tace " Basmah kina nan kwance Umma na can na aiki?


"Yaushe kika canja haka Basmah?


" Canjawa wacce iri?


Basmah ta fad'a idonta kan Safiyyah, murmushi Safiyyah tayi tana kallan Basman tace " sosai kin canja Basmah, idan ma baki sani ki sani,

" wani abu kika gani ko kika ji?


Basmah tayi magana tana mik'ewa zaune, "a'a banji komai ba, sai dai na gani da ido, " ina zuwa Dear!, Basmah ta fad'a zata kashe wayar Zaman yayi saurin cewa,

" please kada ki d'auki zugar Safiyyah wata k'ila turo ta akayi ta hure miki kunne ki rabu dani, please don't let anyone to separate us please,

ya fad'a cikin wani irin yanayi dake nuni da kuka ya kusa kufce mishi, " ka ganka ko?


"Ka fiya saurin kuka kamar ba namiji ba, gaka a ido kamar jarumi amma abu kad'an sai kuka,

" dole nayi kuka dan ina ganin samu da rashi ne, kuma ma a irin san da nake yi miki dan nayi kuka ba komai bane dan zan iya bada rayuwata akanki,

" naji ni dai karkayi kuka, ka jira ni na gama magana da wannan kaji sweetheart, ido Safiyyah ta kafe Basmah dashi jin sunan data kira ta,

" wannan! ta maimaita a k'asan ranta, " lalle Basmah ta canja Zaman ya gama hure mata kunne sai dai addu'a kawai, 

abinda ya k'ara d'aurewa Safiyyah kai shine yadda Basmah ke zuba soyayya a gabanta babu ko kunyarta,

" ni dai please karki bari ta shiga tsakaninmu please, ya fad'a a shagwab'e,

kwaikwayon muryarshi tayi tana dariya tace " to naji!, yana dariya yace " harda tsokana ko?


" Bye i love you, sai munyi magana letter, zayyi magana ta kashe wayar tana dariya, ta mayar da kallanta ga Safiyyah tana cewa " ops! sorry fa, ina magana da sweetie na ne.


Safiyyah da mamakin canjawar Basmah ya gama kashe ta a zaune ta sauke ajiyar zuciya " hmm gaskiyar masu magana da kance namiji yafi bak'in kumurci dafi,

dan dafin maciji yana da magani amma dafin namiji bashi da magani, haka ne da ake cewa " saika shekara 20 kana yiwa 'yarka tarbiyya cikin seconds 20 namiji ya ruguje maka ginanniyar tarbiyyarka,

ya lalata abinda kayi shekaru kana ginawa, ganin Safiyyah ta kafeta da ido batare datace komai ba,

yasa Basmah tab'ata tace " ke wai lafiyarki irin wannan kallo haka kamar baki sanni ba?


"Mamakinki nake yi Basmah.


" Ke! Kin dame ni da mamaki, mamaki, mamakina na me?


"Meyasa kika bar Umma tana aikin gida ita kad'ai bayan da ke keyi?


D'an tsuke fuska Basma tayi kafin tace " da kika shigo bakiga abinda nake yi ba?


"Eh! na gani kina waya da wani k'ato kin bar mahaifiyarki na aiki, k'ara murtuke fuska Basmah tayi batare data ce komai ba,

Safiyyah ta cigaba da cewa " har yafi mahaifiyarki da bazaki iya fad'a mishi zakiyi aikin gida ba Basmah?


"Bana jin dad'i ne, Basmah ta fad'a tana kwanciya, " yaushe kika zama haka Basmah?


"Basmahn dana sani me kunya da bin iyaye ce, me hak'uri, kara da kawaici, ban san ki da rashin kunya ba, ban sanki da taurin kai ba,

Basmah karki biyewa namiji yakaiki ya baro ki, kada ki bashi damar rabaki da iyayenki, kada ki bari ya shiga tsakaninki da kowa naki,

ni wallahi kwata-kwata hankali na bai kwanta da Zaman ba, na kasa yarda dashi ,

yayi kama da mayaudaran maza masu hurewa 'ya'yan mutane kunne, nasha ji ana cewa duk namijin daya fiya yiwa mace kuka munafuki ne,

kuma kinga Zaman........! a hasale Basmah ta daka mata tsawa,

" dakata...! dakata....! Safiyyah dama abinda ya kawo ki kenan?


" Kin zo ne ki ciwa masoyi na fuska a gabana?


" Ina ruwa na idan hankalinki bai kwanta dashi ba, ko dan hankalinki bai kwanta dashi ba shikenan sai nak'i aurenshi dan kina k'anwar uwata?


"To bari kiji ko Umma ce bayyiwa ba saina aure shi balle ke karan kad'a miya, idan turoki akayi ki koma ki fad'awa wad'anda suka turoki hak'onsu bai cimma ruwa ba,

ki sanar dasu zugarki bata shiga kunne na ba, dan haka idan abinda ya kawo ki kenan fice min a d'aki tun kafin a jimu dake,

ta k'arasa maganar tana nunawa Safiyyah k'ofar fita, data gama tsinkewa da al'amarin Basmah tace,

" ko d'aya babu wanda ya turo ni na zuga ki, tsakaninmu dake nake ganin kamar ya kamata idan kina yin abunda ba dai-dai ba na fad'a miki,

ke kanki kin san abinda kike yi ba dai-dai bane, bai kamata ba, dan wallahi Zaman munafuki ne mayaudari ne, ba sanki yake ba,

dan inda yana sanki da bai hore miki kunne haka ba, bazai zama sanadiyyar sab'awa iyayenki ba, ai Basmah ji tayi tamkar Safiyyah ta watsa mata wuta, bakinta yana kumfa tace.


" Dalla malama rufewa mutane baki, banza munafuka annamimiya 'yar bak'in ciki, nasan babu abinda ke damunki sai bak'in ciki,

kuma wallahi sai dai bak'in cikinki ya kashe ki, ba tun yau na lura da irin kallon da kikewa Zaman ba, dan kinga bai sanki shine kike san ki raba mu,

to kul d'inki Zaman haramiyarki ne, kona mutu babu abinda zayyi dake, a hankali Safiyyah ta goge siraran hawayen da suka zubo mata tace " baki da abinda zanyi miki bak'in ciki Basmah,

wallahi ko gaba d'aya duniya da abinda ke cikinta kika mallaka baki isa nayi miki bak'in ciki ba, kuma gaskiya ce bazan fasa fad'a miki ba.


" Fita!, Basmah ta fad'a cikin tsawa tana nuna mata k'ofar fita, batare da tayi magana ba ta fice tana share hawaye,

duk abinda ke faruwa tsakaninsu Ya Mu'allim da Umma naji, ganinsu a parlour yasa Safiyyah b'uye fuskarta, ta durk'usa tace,


" Na tafi Umma!, sai da Umma ta fitar da numfashi kafin tace " kiyi hak'uri kinji Safiyyah, Basmah ta canja fiye da yadda kike tunani, " bakomai Umma, bayan fitar Safiyyah Umar ya kalli Ya Mu'allim daya kasa magana yace,


" Abba ni fa ina ganin akwai waya a hannun Basmah, saurin kallanshi Ya Mu'allim yayi batare daya ce komai ba, da alama k'arin bayani yake nema daga wajen Umar d'in,

ya cigaba da cewa " idan ba waya a hannunta ya akayi tasan yazo ta fita ta same shi?


Abubakar yace " nayi tunanin haka nima, dan nasha fitowa zan shiga toilet cikin dare najiyo ana magana k'asa-k'asa daga d'akinta,

" idan ko har haka ne yaron nan yayi min illa, amma bakomai, yau kada wanda yayi bacci zamu kamata idan da wayar a hannunta, Ya Mu'allim ya fad'a yana danne abinda ke taso mishi,

kamar yadda suka tsara hakance ta kasance, babu wanda yayi bacci a cikinsu, tana kwance saman bed ta saka wayar a handfree suna waya Zaman yace.


" Dear na samo mana sabuwar shawara fa, cikin zumud'i tace " wacce iri?


Sai da ya karya muryarshi kafin yace " ina tsoron kada ki kasa fahimta ta, fargaba ta kada kiyi man raguwar fahimta, kiyi min mummunan zato,

kada yardar da kikayi min ta ragu, bana san zargi ya shiga tsakanimu amma ina ganin wannan ce kad'ai mafita, 

a hankali Ya Mu'allim ya gyara tsaiwarshi zuciyarshi na bugawa da tsanani, yayinda gwiwowinshi suka shiga rawa, dan yasan k'arshen maganar,

a sanyaye Basmah tace " ka fad'a bakomai in sha Allah zan fahimce ka,

" kin tabbata zaki fahimci maganata?


Kai ta d'aga mishi kamar yana ganinta, cikin salonshi najan hankali yace " me zai hana ki bani kanki na kwanta dake, ina ganin idan mukayi sex dole Ya Mu'allim ya amincewa aurenmu,

a firgice Basmah ta mik'e zambur tana fad'ar " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, kasan me kake cewa kuwa Zaman?


Jiri ne ya d'ebi Ya Mu'allim yayi baya zai fad'i, cikin zafin nama Usman ya tare shi yana kiran " Abba....! Abba....!, a tsorace Basmah ta saki wayar hannunta,

dan bata san sun shigo ba sai jin kiran sunan Abba da Usman keyi tayi, a tare sukayi kan Ya Mu'allim, suka d'auke shi, suna shirin fita dashi ya bud'e baki dakyar yace.


"Ku kaini d'aki na ba sai kun kaini asibiti ba, ba musu suka shigar dashi d'aki, sai da yasha fama dasu kafin suka tafi d'akinsu,

washe gari, wajen k'arfe sha biyu na rana Ya Mu'allim yana zaune a parlour Umma, Umar, Usman, Aliyu da Abubakar na zaune a gefe,

jiki ba kwari ya kalli Usman yace " kira min ita, bai jima da tashi ba suka dawo tare, tana b'uya a bayan Usman,

ido ya zuba mata na tsayin lokacin kafin cikin sark'ewar murya Ya Mu'allim ya kira sunanta.


"Basira...!, kanta a k'asa ta amsa da " na'am, " na isa dake?


Da k'arfi zuciyarta tayi muguwar bugawa, bakinta na rawa tace " eh! Abba.


"To! matuk'ar na isa dake, kuma nine mahaifinki na rabaki da wannan yaron, na kuma saka ranar aurenki nan da kwana goma ke da Ammar,

a kid'ime ta mik'e tana girgiza kanta tamkar zararriya, zuciyarta da k'irjinta sukayi muguwar bugawa a tare, taji tamkar ranar mutuwarta aka sanar mata,

jikinta ya shiga mazari yana tsuma kanta ya shiga juyawa tana ganin kowa bibbiyu.


"A'a Abba dan Allah karkayi min haka wallahi Zaman nake so, danshi zuciyata ke bugawa, idan ka raba mu ina iya mutuwa dan Allah kada ka raba mu,

" Basira nayi bincike akan yaron nan babu wanda yasan asalinshi, da sauri tace " Abba bashi da iyaye a gidan marayu aka reneshi, " ya kike abu kamar marar hankali kowacce batada ilimi ke yanzu kin yarda da labarin k'anzon kuragen daya fad'a miki?


A rud'e tace " wallahi Abba ba k'arya yake ba, " kiyi hak'uri na gama yanke hukunci, a makauce tace " hukuncinka be yanku ba Abba tunda ba hukuncin Allah bane,

ba kuma rubutaccen al'amari bane, kamar yadda kayi alk'awari haka nima nayi mishi, kuma duk alk'awari sunanshi alk'awari.


"Na shiga uku ni Saratu yaushe kika zama fitsararriya Basmah?


Umma ta fad'i tana fashewa da kuka, " wai meyasa kun fiya san kanku ne?


"Meyasa babu wanda ya kula dani da zuciyata da halin da zan shiga idan aka raba ni da wanda nake so?


"Ko sau d'aya babu wanda ya kula dani, babu wanda ya tab'a fahimtata balle kuyi min uzuri, babu wanda ya tambaye ni ina san wanda za'a aura min ko bana sanshi,

zan kasance cikin farin ciki dashi ko zan kasance cikin bak'i ciki idan aka aura min shi, wacce irin rayuwa zanyi da mijin da bana so,

wanda ban tab'a so ba, asalima ban tab'a saninshi ko ganinshi ba, san kanku ya rufe muku ido zakuyi man auren dole bayan kun san ina da ZAB'I NA,

ko sau d'aya kun tab'a tambayata ina sanshi?


"Ko sau d'aya kun tab'a tunanin rayuwar k'uncin da zanyi?


"Abba bana san Ammar zab'inka, Zaman zab'i na shi nake so, bak'in cike ne ya sanya Umma kifawa Basmah marika, tana fad'ar " na shiga uku, me nake shirin gani yau?


Sautin kukanta ta k'ara tana cewa " koza'a kashe ni bazan auri wanda bana so ba..... kafin ta k'arasa Umar, Aliyu da Abubakar sun rufe ta da duka,

duk da dukan da ake yi mata baisa bakinta ya mutu ba.


" Wallahi ko zaku kashe ni ko zaku bani rayuwata a hannuna bazan rabu da Zaman ba, shi nake so kuma shi zan aura, 

Usman yaso ya daure yadda ake dukan Basmah dan har cikin ranshi yake jin kukanta, amma ya kasa,

jikinshi na rawa ya mik'e ya shiga ture Umar da Abubakar da Aliyu dake dukanta, yana cewa.


"Baku da hankali ne idan kuka illata ta fa?


Cigaba da dukanta sukayi batare da sun kula da maganar Usman ba, a zuciye ya hankad'e Umar da Abubakar, suka fad'i k'asa,

a tare suka taso da niyyar kwace Basmah daga hannunshi , bayyi wata-wata ba ya zubawa Aliyu mari had'i da nunasu da yatsa yace " wallahi babu wanda zai k'ara dukanta, 

cak suka tsaya tare da zubawa Usman ido, dan yaune karo na farko tunda aka haifesu da sab'ani ya tab'a shiga tsakaninsu, Abubakar yace.


"Baka ji abinda take fad'awa iyayenmu ba?


"Ina ruwanku?


"Yadda suke iyayanku haka suke iyayenta, yadda suka haife ku haka suka haife ta, dan haka kubar Abba ya yanke hukunci da kanshi,

a k'ufule Umar ya janye Abubakar dake gaban Usman ya tsaya a gaban Usman d'in yana cewa " kai ka isa ka fad'a man abinda ya dace nayi?


"Ko kai ina gaba dakai ba ita ba, " ni dai na fad'a muku babu wanda ya isa ya sake tab'a ta wallahi, Usman ya fad'a yana mayar da Basmah bayanshi, hankad'ashi Umar ya soma yi yana cewa " idan an tab'a tan me zakayi?


Nannad'e hannun riga Usman ya soma yana cewa " Bismillah ka tab'a ta sai kaga abinda zai biyo baya,

Umar ya d'aga hannu zai cafko Basmah Ya Mu'allim yace " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan min ha,

Umma kam kuka ta fashe dashi tana cewa " tur da wannan bak'ar rana, ranar da zanga ahalina suna fad'a, a gabanmu akan idonmu, tun muna raye kuka soma haka ina kuma da bama raye?


"Kada ku bari wani ya lalata muku zumunci da tunaninku dan girman Allah, sosai jikinsu yayi sanyi ganin yadda Umma ke kuka,

" burin Zaman ya cika ya tarwatsa min gida, ya raba min kan 'ya'ya, ya lalata abinda nayi shekaru ina ginawa, Basmah burinki ya cika, tunda na haifi 'ya'yana ban tab'a ganin ko musu sunyi ba, ko fad'a irin na k'uruciya basu tab'a yi ba sai yau a dalilinki,

amma yanzu yanzu zanyi maganin abun, ya mayar da kallanshi ga Aliyu da Abubakar yace " ku bawa Usman hak'uri, ba musu suka bashi hak'uri, 

" kaima Usman bawa Umar dasu Aliyu hak'uri, jiki a sanyaye ya basu hak'uri, " daga yau idan kuka k'ara fad'a ko musayar yawo ban yafe muku ba,

kansu a k'asa suka durk'usa k'asa suka bawa iyayen nasu hak'uri.


A hankali ya Mu'allim ya dafa kujera ya mik'e yana bin bango zai shiga bedroom d'inshi, yakai k'ofa yaji muryar Basmah na fad'ar maganar da ko'a mafarki bai zaci d'a zai iya fad'awa iyayenshi ba, 

maganar data gigiza duk mahaluk'in dayake wajen, maganar data tarwatsa kwakwalwar Ya Mu'allim, maganar data zama sanadiyyar faruwar komai,

maganar data tsayawa Ya Mu'allim akai da zuciyarshi, maganar data tarwatsa farin cikin gidan da zukatansu...........!


*KADA DAI A MANTA NA KUD'I NE, IYA KUD'INKU IYA SHAGALINKU.......*


MOMYN ZARAH. 'YAR BAIWA


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.