Free chapter · Read without an account
18
_*SAKI RESHE...!*_
*(CIGABAN GADAR ZARE)*
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
1️⃣8️⃣
Baibi ta kanta ba ya ciro wuk'ar daga cikin me gidan ya k'ara luma mishi, salati yayi da k'arfi kafin ya sulale k'asa rai yayi halinshi,
" kai ka bada babbar gudummuwa wajen taimakawa Basmah ta gano waye ni, dan da baka azalzaleta ba dabata fita nema na ba,
saida ya tabbatar ya mutu yana yabar inda yake ya isa gaban Basmah ya kifa mata mari da iya k'arfinshi, zafin marin ne yasa Basmah farfad'owa daga suman da tayi a razane,
karaf idonta ya sauka akan Zaman dake durk'ushe gabanta rik'e da gabgegiyar wuk'a jikinta duk jini, a tsawace yace " zaki mik'e ko saina caka miki wuk'ar kema?
Tsoro ne yasa Basmah kuma komawa suman ta sulale daga zaunen, tsoki yaja had'i da mik'ewa ya shiga bathroom ya watsa ruwa,
a gaggauce ya shirya dan yau suna da casu a Karma Club da *SHAKIRA..! DADIRONSHI* bai b'ata lokaci ba ya fita ya barta anan inda take sumen,
Zaman bai dawo gidan ba sai washe gari da safe ya shigo parlour'n bakinshi d'auke da fito, rigarshi na sak'ale a kafad'arshi,
yayi as down, kallo d'aya zakayi mishi kasan a buge yage tatul da giya, jin yayi karo da abu yasa shi cewa " kai wanne shegen ne ya aje abu a hanya?
Yayi maganar yana kallan abinda ya buga, ko kad'an bai girgiza ba balle yayi mamakin ganin Basmah kwance a sumen kamar yadda ya barta,
tana nan yadda ya barta a kwance bata ko motsi, durk'usawa yayi a gabanta had'i da busa mata hayak'in wiwin bakinshi yana fad'in " ke dan kan ubanki baki motsa ba har yanzu?
"Ko ni kike jira na tashi ki?
Yayi maganar cikin maye yana nuna kanshi, dariya ya sanya irin ta 'yan maye yana tangad'i yace " au Allah da gaske bazaki tashe ba sai na tashe ki?
Ganin bata motsa ba yasa shi kifa mata mari yana fad'in " ke tashi dan uwarki, *SHAKIRA...* bazaki tashi ba?
"Bari ki gani tunda abun naki shak'iyanci ne ya fad'a yana dube-duben abun duka, dariya ya kuma sakawa yana cewa " shegiya ashe kema kina san a daketan,
ya fad'a yana nuna 'yar yawo, yana fad'uwa yana tashi ya isa wajen da 'yar yawon take ya d'auka ya nannad'a ya zubawa Basmah dake kwance bata motsi,
ganin bata motsa ba yasashi d'aga kanshi sama yana fad'in kodai da gaske bata da lafiyan?
"Bari muga, ya fad'a yana sungumar Basmah yayi waje daga shi sai gajeren wondo jikinshi babu riga,
yana tafe yana tangad'i yana surfawa duk wanda ya gifta ashar while yana zuk'ar wiwinshi har ya isa abisiti, duk inda ya nufa a asibitin hanya yake bashi,
dan sun san ba arziki a tattare dashi, cikin office d'in likita ya yakaita ya kwantar da ita a saman tebur d'in dake gaban likitan yana fad'in " matata ce bata da lafiya ka dubata,
bai jira abinda likitan zaice ba yayi waje, likitan yabi bayanshi da kallo yana sauke ajiyar zuciya kana ya kira nurses aka duba Basma,
har aka dubata bata farfad'o ba dan haka aka bata gado, had'i dayi mata allurai da jona mata k'arin ruwa, Zaman kam yana fita daga asibitin gida ya koma yayi kwanciyarshi,
bai dawo asibitin ba sai Magriba, bayan yayi wanka tsaf kamar ba shine d'azu yake tijara ba, tare da likita suka shiga d'akin da aka kwantar da ita,
tana kwance har lokacin bata farfad'o ba, likitan ya soma k'ok'arin cire mata k'arin ruwa yana fad'in " meya tsoratata haka?
Maimakon Zaman ya bashi amsa sai ya mayar mishi da tambaya akan tambaya " meke damunta?
Ya fad'a idonshi kanta, " ba wani babban abu bane firgici ne sai kuma *CIKIN DAKE JIKINTA NA WATA UKU* dummmm! Zaman yayi, yana jin shuuuuuu cikin kunnenshi,
yana jin wani abu dabe san komeye ba yana tsarga mishi tun daga tafin k'afarshi har tsakiyar kanshi, wani irin yanayi yana shiga cikin jikinshi,
tsikar jikinshi ta mik'e, kwakwalwarshi ta shiga juya kalaman Doctor na k'arshe, cikin ranshi yace " ciki?
"Impossible! wanne irin ciki kuma?
Bai san maganarshi ta fito fili ba sai da yaji likitan ya amsa mishi da " ciki dai wanda ka sani na haihuwa, ko baka san tana da shigar ciki na watanni uku ba?
Ihuuuu Basmah ta kurma tana fad'in " wayyyo Allah na shiga uku, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma Ajirni fi musibati wa'aklifni khairan minha,
Astagfirullah Astagfirullah Allah na tuba Allah ka yafe min, Ya Ubangiji kada ka d'ora min abinda bazan iya d'auka ba,
Allah ka sani bazan iya haihuwa na had'a jini da fasik'i mazinaci d'an giya ba, wanda bai d'auki manya-manyan laifuka abakin komai ba,
wanda ya d'auki zunubi abin more rayuwa, ya mayar da shaid'an abokin mu'amularshi, a gabana akan ido ya kash.......!,
marin daya d'auketa dashi ne ya tilasta mata yin shiru, ta dafe kuncinta da duka hannayenta tana mayar da nufashin wahala,
" shiga hankalinki ki tattaro duka nutsuwarki ki sakawa kanki dan ina san ciki na, ina san abinda ke cikinki, wallahi tallahi ban tab'a jin abinda naji yanzu a iya tsayin rayuwata ba,
zatayi magana ya k'ara d'auketa da mari yana k'ok'arin rufeta da duka likita ya janye shi yana fad'in " baka da hankali ne?
"Idan wani abu ya same ta fa?
Yana huci yace " ta mutu ma mana uban wa keda asara?
Ganin yana neman kwacewa daga hannun likitan yasa Basmah yin suman k'arya ta sulale saman gadon kamar ta suma,
sosai hankalin likita ya tashi ya tura Zaman waje ya dawo yana duba Basmah, idonta biyu har likita ya gama abinda yake ya fita,
tana ganin ya fita ta tashi zaune had'i da dafe kanta da duka hannayenta ta fashe da kukan bak'in ciki da takaicin rayuwarta,
sai da tayi me isarta sannan tayi shiru ta shiga tunanin mafita, ta dad'e tana tunani kafin ta yanke shawarar ta *GUDU*,
babu kokwanton komai ta amincewa zuciyarta da shawarar data bata, bata b'ata lokaci ba ta mik'e da sauri jikinta na kerrrma ta fice,
get ta nufa babu ko takalmi bare d'an kwalli tana waige-waige kallo d'aya zakayi mata kasan bata cikin hayyacinta, a masifar tsorace take,
tana fita ta tsaida me adai-daita sahu tana cikin yi mishi bayani ta hango Zaman ya nufo ta fuskarshi kwata-kwata babu annuri, " ina zaki?
Ya tambayeta idonshi kanta, bakinta na rawa a duburburce tana kame-kame tace " am....am da..ma, lafiyayyun marika ya d'auketa dasu, cikin tsawa yace " nace ina zaki?
Zafin marin ne ya rud'ata tayi sub'ul da baka " guduwa zanyi, ta fad'a ba tare data sani ba tana dafe da kuncinta, what! guduwa zakiyi Basmah?
"Kina tunanin yadda kika gujewa iyayenki cikin sauk'i haka nima zaki guje min?
"Ko kina tunanin yarda kika bar iyayenki, danginki, ahalinki da 'yan uwa lami lafiya haka nima zaki iya bari na?
" Har kina tunanin da cikina da gudan jinina a jikinki zaki gudu?
Fashewa yayi da dariya harda buga k'afa yace " kinyi wauta yarinya da kika bari k'aramar mahaukaciyar kwakwalwarki ta kissima miki haka,
kinyi ganganci Basmah, kinyi ganganci, babban gangancin da kikayi shine na sani na a rayuwarki, guduwa da kike tunanin yi daga gare ni kuskure ne babba Basmah,
dan dai-dai yake da mutuwarki da kawo k'arshen numfashinki, matuk'ar kina raye ina raye a duniya kina taka doran k'asar nan da muke tawa baki isa ki guje min ba,
wallahi wallahi tallahi matuk'ar kika guje min saina k'arar da ahalinki, na kashe zuri'arku kaf, saina yiwa wancan tsohon banzan me gemun d'an taure, d'an iska me kama da d'an akuya yankan rago,
kinga yadda na kashe me gidanmu a gabanki akan idonki ko?
"To haka zan kashe iyayenki da yayyanki kaf, dan haka ki daina tunanin guje min, ki daina bari zuciyarki tana ainaki miki zaki iya b'ace min dan naga alama baki san waye Zaman ba,
na lura baki san waye Michael ba har yanzu, na lura kamar wad'anda suka baki labari na basu gaya miki komai akaina ba,
basu gaya miki waye ni ba, idan kuma taurin kanki ne ke neman jawo miki wahala keda ahalinki to, ya k'arashe maganar yana cije lips,
" Basmah ni bala'i ne, ni masifa ne, sani na ba alkhairi bane, ina san cikin jikinki Basmah, dan tab'a neman mace ta gabanta ba balle tayi ciki,
akanki na fara sanin mace ta gabanta, akanki na fara sha'awar mace idan baki manta ba ai na tab'a fad'a miki ranar dana d'auke ki na kaiki restaurant,
akan hanyar dawowa da jikina ya tab'a naki na fad'a miki ban tab'a jin abinda naji akan mace ba sai akanki,
akan cikin jikinki zan iyayin komai, zan iya zama hitila na biyu na yak'i duniya, kamar yadda kikaji nace komai ina nufin komai dan ko k'ark'ashin k'asa kika shiga saina biki akan cikin jikinki,
kalamanshi ba k'aramin b'ata mata rai sukayi ba, take taji ta nemi duk wani tsoranshi da take ji ta rasa, zuciyarta ta k'ek'ashe,
ta kalle shi ido cikin ido, ta cikin kwayar idonta ya hango tafasar da zuciyarta keyi, " wallahi Allah ni kuma kozan mutu bazan tab'a had'a jini dakai ba,
dana had'a jini dakai na gwammaci mutuwa sau dubu Mugu, kana kafiri, gafalalle, shak'iya zan had'a jini dakai?
"Na cewa abinda zan haifa me?
"Me zan cewa mahalicci na?
"Na auri tab'abb'e na haihu dashi kome?
"Ka sawa ranka koda zan rasa raina saina zubar sa cikin na......! bai bari ta k'arasa ba ya d'auke ta da gigitaccen mari wanda yasata hantsawa,
ta fad'i bakinta ya fashe, jinin dake zuba daga bakinta tasa hannu ta gogo ta kalla tayi murmushi tana fad'in " ko zaka kashe ni bazan haihuwa dakai ba,
macuci azzulumi, ka ha'ince ni, ka yaudare ni, ka raba ni da iyaye na da farin ciki na,
kasa na bijirewa iyaye na, Allah ya isa tsakani na dakai, ina fatan Ubangiji yayi maka abinda kayi min, na tsaneka! na tseneka..... zafin kalaman da take fad'a mishi ne sanya tsumin mayenshi ya motsa,
idonshi ya rufe ya zage iya k'arfinshi ya rufeta da duka, hannu da k'afa ya sanya yana dukan Basmah a titin Allah yana fad'in
" A gidan ubanki na rabaki da iyayenki?
"Ni nace ki zab'e kibar iyayanki?
"Ko ranar da mahaifinki ya kafa miki sharad'in kinji na saka muku baki, kinji nayi magana?
"Ko tari banyi ba, amma saboda harri shine zaki ce na raba ki da iyayenki, tunda nake dake na tab'a cewa ki rabu da ahalinki akaina?
"Ko dole nayi miki na saka igiya najawoki?
"Naga da k'afarki kika biyo ni, asalima har zab'i iyayanki suka baki, amma dayake keba 'yar halak bace kika zab'e ni, shegiya 'yar mage,
yana fad'a yana nad'a mata na jaki a titin Allah, kanta babu d'an kwalli bare takalmi, kafin kace me mutane sun taru sun cika wajen mak'il,
anyi dandazo an zagaye su, bai daina dukanta ba saida yaga bata motsi ya fasa mata kai, bakinta sai zubar jini yake, ko hannunta bata iya d'agawa babu abinda ke motsi a jikinta sai kwayar idonta,
ganin mutane sun zagayesu yasa Zaman rik'e k'afarta d'aya ya soma janta a k'asa kamar dabba, d'uwawunta da bayanta na gurjewa, d'ago idon dazatayi idonta ya sauka akan Ya Mu'allim, Abubakar da Usman dake rik'e hannunsu Aliyu da Umar..............!