Free chapter · Read without an account
30
30
" Ina d'ana?
"Ina ka kaiman shi?
Tayi maganar tana shak'ar wuyan Ammar, murmushi yayi had'i da nuna mata bayanta yace " gashi nan a bayanki, sunanshi na kira, da sauri Nayan ya k'arasa inda Hajiya Tanya ke tsaye,
ya tallafeta yana fad'in " lafiya Mom?
Kwat ta had'iye yawo ba shiri tana bin Nayan da wani kallo na ashe zan k'ara ganinka, bayyiwa Ammar magana ba, ya wuce bedroom da ita,
Shakira da Zaman suka bi bayansu,
fridge Shakira ta nufa ta d'auko ruwan sanyi ta bawa Hajiya Tanya tasha tare da sauke ajiyar zuciya, sai da ta d'an nitsa ta dawo cikin hayyacinta kana tabisu da kallo d'aya bayan d'aya,
tace " tabbas akwai bak'in munafuki a cikin mu, akwai wanda yake cin dunduniyarmu, muna tare dashi kuma yana tare da Ammar,
akwai wanda yake d'ibar maganganun mu da duk wasu shirye-shiryen da muke yi yana fad'a mishi, cikin rashin fahimta Nashwan yace " kamar yaya ban fahimceki ba?
"Kamar yadda yake tsallake duk wata GADAR ZAREn da muka k'ulla mishi, Allan musuru ne dashi da zai san mun cire mishi birki?
"Koko d'an duba ne shi da zai san mun zuba mishi guba a abinci kuma yaci a gabanmu babu abinda ya same shi?
"Ta yaya akayi ya san yau zamuje kashe shi?
Kallan kallo suka fara yi a tsakaninsu kowanne yana zargin d'an uwanshi, cikin gamsuwa da maganganun Hajiya Tanya Nashwan yace " maganarki gaskiya ce,
akwai abin dubawa a cikinta, dan haka mu tsaya muyi tunani mu lura da takun kowa, a hasale Hajiya Tanya tace " bamu da lokacin da zamu tsaya lura da wani taku,
danni tuni na gano wanda yake yi mana zagon k'asa, gaba d'ayansu suka had'a baki wajen cewa " waye?
Kai tsaye Hajiya Tanya tace " Shakira kece wacce kikeyi mana zagon k'asa saboda tun farko kece kika k'i yarda da maganar kashe Ammar,
haka kece kika zuba mishi abinci ranar, sannan yau bayan an gama meeting kin fita kince kina zuwa zaki shiga toilet,
duk cikin mu babu wanda ya fita saike, cikin in ina da rawar baki Shakira tace " ni Hajiya?
" Ni zaki zarga da fad'awa Ammar k'ulle-k'ullenmu?
"In bake bace to uban waye?
"Nashwan...! cewar Zaman yana gyara tsayyuwarshi, gaba d'ayansu suka kalli Zaman kana suka mayar da kallansu ga Nashwan,
" me kake san kace?
Nashwan ya fad'a yana tsare Zaman da ido, shima ido ya kafe Nashwan d'in dashi yana fad'in " abinda kaji na fad'a, duk cikinmu babu wanda yake da kusancin da kake dashi da Ammar,
tare kuka taso, tare kukayi gaba d'aya rayuwarku dan haka cin amanarshi ba abu bane me sauk'i a gareka, kai zayyi wuya ma ka iya cin amanarshi,
a dururuce Nashwan yace " ban gane nafi kowa kusanci dashi ba, bayan ga matarshi a cikinmu?
"Kuma lokacin da akace za'a kashe shi banyi musu ba itace tayi musu, sannan ni nake sanar daku kokai akan dukiyar tayaya zaku zarge ni?
Numfashi Nayan ya furzar yana fad'in " to kodai CCTV Camera ya saka mana?
Shiru sukayi dukkaninsu kamar masu jiran k'et su arta ana kare, suna bin dak'in da kallo cike da tsoro, shan yaji Hajiya Tanya tayi tana dafe da kanta tace " kuje zan san abinyi,
babu wanda yayi magana suka fice, Shakira daba cikekkiyar lafiya ce ta isheta ba ta zube saman gado tana mayar da numfashi,
zumbur ta mik'e tayi bathroom da gudu ta durk'ushe ta shiga kwarara amai, ta dad'e tana kakarin amai sannan ta mik'e jiki a sanyaye,
tunanunnika kala-kala ta shiga yi, tunda take bariki bata tab'a samun ko targad'a ba bane tayi ciki, da sai tace ciki ne da ita, juyawa tayi tana daga kwancin data tuna lokocin ganin period d'inta ya wuce tuni,
dan a k'alla ta k'ara kwanaki goma kenan akai, tana jin wayarta nata faman rori amma ta motsawa balle ta d'auka, yadda taga rana haka taga dare bata tuntse ba,
sai azababban ciwo dake cinta kamar zata mutu, daga dare zuwa safiya tayi amai yafi a irga, jikinta ba kwari ta mik'e ta shiga bathroom ta watsa ruwa,
simple doguwar riga ta zura ta fice ta nufi asibiti, kwatin farko aka tabbatar mata tana da shigar ciki na wata d'aya,
ta tabbatarwa kanta bana Ammar bane dako hannunta bai tab'a rik'ewa ba, haka ba cikin Zaman bane, dan baya kusantarta ta gaba saita baya,
hakan yasa ta tsaida tunaninta akan cikin Nayan ne, jikinta ba kwari ta mik'e ta fice daga asibitin, tana isa gida part d'in Nayan ta nufa,
ta iske shi ya fito daga wanka, da sauri ya nufeta ya had'e tazarar dake tsakaninsu, ya rungumeta ta baya yana fad'in " lafiyarki kuwa?
"Naga kin rame sosai hope ba abinda ke damar min ke?
Zame jikinta tayi daga mashi ta juya ta fuskance shi ido cikin ido batare datayi magana ba ta mik'e mishi sakamakon gwajin da akayi mata, " meye?
Yace yana bin takadar da kallo batare daya amsa ba, " ka karb'a ka duba, zaka ga komeye a ciki, bayyi magana ba ya amsa murmushi yayi yana barin inda take yace " shege Ammar yana cewa bayaso-bayaso shine harda ciki?
" Na tayaki murna, idonta kanshi tace " kamar yaya fa?
"Ban gane abinda kake nufi ba?
"Ban gane baki gane ba?
"Ina tunanin maganata bata da wahalar da zaki kasa ganeta, sai da ta gyara tsayuwarta kana tace " wannan ba cikin Ammar bane cikinka Nayan,
" what?
"Me?
"Ciki na fa kika ce?
"A idan uba ya zama ciki na?
"A gidan uban da kake zuwa ka kwanta dani kayi releasing a ciki yasa cikin ka ne, fashewa yayi da dariya sosai harda buga k'afa, yace " ki newa cikinki uba tun dare yayi maki,
dan ko giya nake sha bazan karb'i cikin karuwa ba, wanda ke kanki idan za'a tsareki da bingida bazaki iya fiddo uban da yayi miki ciki ba,
amma tsabar renin hankali da renin wayo ki kalli idona kice ninayi miki ciki duk tarin kwaratanki da manemanki, keda har dadiro kike dashi,
kina rawa a club tsakiyar 'yan giya duk cikinsu babu wanda yayi miki ciki sai ni saboda nine marenin yawonki ko?
Tunda ya fara magana ta tsareshi da ido harya dire, " ba abin mamaki bane dan mashayi d'an iska kuma fasik'i yayi haka,
musamman idan akayi duba da halin wacce tayi goho da tsugunnan haihuwa, za'a san duk abinda kayi ba'a k'asa ka d'auka ba,
a nono kasha, ka bud'e kunnuwanka kaji ni dakyau cikin jiki na bana kowa bane face kai, dan haka ka shirya d'aukar d'an gaba da fatiha,
ka shirya karb'ar ribar bariki, da ladan iskanci, dama kyan iskanci kayi guzuri,
a hasale yayo kanta kamar zai tsigeta yana fad'in " ni zaki nunawa halinku na karuwai 'yan bariki?
"Wallahi idan baki janye alak'anta ni da cikin nan ba saina ga bayanki....! cikin masifa tace " wallahi nima idan baka karb'i cikin nan ba saina kwantar dakai,
banza hoholaho hotiho solob'iyo asararrare wanda yake tsoron ribar bariki, inda nasan kai k'aramin d'an iska ne, k'aramin mara kunya me zai za nayi harka dakai,
wanda yake gudun abun fad'a, wallahi ka bani kunya Nayan, dana san kana da sauran guntuwar kunya da ban soma fara nema dakai ba, zanyi magana suka jiyo tafa hannu daga bakin k'ofa,
da sauri suka juya suka kalli k'ofar tsoro k'arara ya bayyana asaman fuskarsu, kai Hajiya Tanya ta girgiza kana ta talk zuwa tsakiyar d'akin tana fad'in " meye na damuwa dan kun samu k'aruwa ta arziki?
" Kun samu riba biyu...! d'a zaizo gidan ubanshi, kallanta suke cike da neman k'arin bayani, murmushi tayi tace " yaro dai yaro ne, ku zo muje na baku shawara,
bayan sun zauna Hajiya Tanya ta tsara musu yadda zasuyi ta d'ora da cewa " kunga kun samu babbar kadara ko?
Cikin farin ciki da zumud'i Shakira tace " wow...! Hajiya kanki na ja wallahi, kina bala'in kawo wuta, baki tab'a yin abinda yayi min dad'i ba kamar wannan,
dan banyi wannan tunanin ba, danayi dako shi Nayan d'in bai sani, Hajiya ta mik'e tana cewa " ato sai kiyi k'ok'arin aiwatar da komai yau,
dan ayi abun akan lokaci, idan kun rufawa kanku asiri kunci arziki to idan kuma halin barikin ya motsa kunyi tawatsimar nasi a bayyanar juma'a ku kuka sani,
jikin Shakira na rawa tace " hakan ma bazata faru ba, in sha Allah.
A ranar da daddare naga Shakira tana zuba wani abu cikin abincin Ammar, duk ilahirin jikinta na rawa saboda tsoro,
jin taku yasata saurin barin wajen ta koma corridor inda Nayan, Zaman da Hajiya Tanya ke lab'e suna lek'enshi akan idonta ya cinye abincin tasss kana ya mik'e ya koma saman sofa ya kishingid'a yana kallan labarai,
bai dad'e ba maganin ya fara aiki, Ammar ya soma jin wani irin yanayinshi na canjawa, a hankali ya zube nannauyan bacci yayi awon gaba dashi,
suna ganin haka suka fito daga inda suke lab'e Nayan da Zaman suka ciccib'eshi suka kaishi bedroom d'inta Shakira suka kwantar saman bed,
har sun kai bakin k'ofa zasu fita Hajiya Tanya ta juyo ta kalli Shakira tace " karki manta da tsarin fa, kaita d'aga mata tana me tabbatar mata da komai zai tafi normal yadda suka tsara,
Ammar be farka ba sai k'arfe 10:30 na safe, kanshi ya dafe yana salati,
a hankali ya mik'e zaune yana bin d'akin da kallo, ganinshi a d'akin Shakira ba k'aramin bashi mamaki yayi ba, musamman daya ganshi zindir ba kaya, jikinshi ya shiga kallo while yana bin d'akin da kallo kukan Shakira daya jiyo ne yasashi saurin kallan inda yajiyo kukan,
itama tsirara ba kaya a jikinta sai bedsheet dataja ta rufe jikinta ta had'a kai da gwiwa tana faman kuka, cike da mamaki yace " lafiyarki?
Bata kula shi ba taci gaba da kukanta, " baki da lafiya ne Hurayya?
Still banza tayi dashi, sai da ya k'ara tambayarta a karo na uku kana ta d'ago kanta idonta yayi jajir, fuskarta a cab'e da hawaye da majina,
" dole mana ka tambaye ni lafiyata bayan abinda kayi min, babu tausayi balle tausayawa baka kula da cewar ni budurwa bace ka haik'e min ta k'arfi ka biya buk'atar,
shine bayan ka gama biyan buk'atarka zaka tambaye ni lafiyata, ina zanga lafiya bayan ka fatattakani, " what?
"Me!?
"Ni nayi miki me...?
"Ke kina hauka ne?
Yayi maganar a lokaci d'aya yana mik'ewa, kuka ta k'ara fashewa dashi tana fad'in " dole kace haka Ammar tunda buk'atarka ta biya,
kanshi ya dafe yana had'i da k'ura mata ido yana san tuna abinda ya faru amma ya kasa, kanshi ya kawar gefe yana k'ok'ari shiga bathroom idonshi ya sauka akan jikin dake saman bed,
da wanda ke tsakiyar d'akin ido ya zaro a tsorace yana sake bin jinin da kallo, shatin k'afar Shakira ne daga kan gado zuwa inda take zaune,
jinin ya zuba sosai, jikinshi ya kalla yaga jinin har kan joy stick d'inshi, kanshi ya talle da hannu d'aya, d'aya hannun ya rik'e k'ugunshi had'i da fad'in " oh! God.... nisawa yayi ya kalleta yaga yadda take kuka bilhakk'i da gaskiya,
idonshi ya runtse had'i da cewa " Ya Salaam.... me nayi?
"Mena aikata haka....?
"Me yazo kaina yau nayi wannan d'anyan aikin?
A hankali ta dafa wardrobe a dudduk'e zata mik'e tsaye tana raba k'afa kamar 'yar kaciya, ido ta runtse had'i da cije lips da k'arfi tace " washhhhhh!,
ganin bashi da niyyar taimaka mata yasata yin bayi kamar zata fad'i yayi saurin tareta yana fad'in " kiyi hankali,
rungumeshi tayi had'i da fashewa da kuka tare da cewa " jiki na ciwo yake min, k'afafuwa na rawa suke, k'asana zafi kamar zan mutu, yadda tayi maganar yasa tausayinta kamashi,
bayyi magana ba ya nufi bathroom yana d'auke da ita, da kanshi yayi mata wanka bayan ya gasheta da ruwan zafi, tana ta shagwab'a tana ciccije lips da runtse ido,
d'aki ya mayar da ita ya taimaka mata ta shirya, kana ya goge inda jinin ya b'ata ya canja zanin gado, ya fita ya had'o mata kakkauran tea ya bata tasha,
ya bata magani yace " kiyi bacci , bai jira abinda zatace ba ya fice, yana fita ta dire bisa k'afuwanta ta buga tsalle had'i da ficewa, tayi part d'in Hajiya Tanya,
ta fad'a musu yadda sukayi, tafawa Hajiya Tanya da Shakira sukayi, suna dariya.
Basmah ta kitchen tana dafa indomie taji motsi a bayanta batayi zaton komai ba dan haka bata juya ba, jin an rik'e mata k'ugu yasata yin dariya tana fad'in " matsoraci yau an samu gwarin gwiw......!
sark'e mata maganar tayi sakamakon arba da tayi da Zaman, cikin tashin hankali da matsanancin tsoro ta soma kiciniyar kwace kanta,
murmushi yayi had'i da kashe mata yace " haba Basmah... baki missing d'ina bane?
"Idan bakiyi missing d'ina ba ninayi naki shiyasa nazo mu gaisa, baki kyauta min ba da kika karya dukkan alk'awarin da kika d'aukar min, na bazaki tab'a rabuwa dani ba,
a kowanne irin hali zaki kasance dani da bin umarni na ko kin manta....?
Ya fad'a yana k'ara shigewa jikita, tattaro gaba d'aya k'arfinta tayi ta ta hankad'e shi, kafin ya mik'e tayi waje da gudu har tana tuntub'e, ta shige bedroom ta rufe,
dariya me kamar da murmushi yayi yana shafa kanshi, kana yabar wajen, ta kasa zaune ko tsaye a d'akin ta had'a gumi sharkaf,
tana cikin wannan hali taji an murd'a handle d'in k'ofar baya ta soma cike da tsoro tana girgiza kanta had'i da zubawa k'ofar ido kamar mutuwarta ce zata b'ullo ta jiki,
d'an bubbuga k'ofar Ammar yayi yana kiran sunanta " Basmah.... ko bacci kike yi?
Jin muryar Ammar yasata saurin isa ga k'ofar ta bud'e ta fad'a jikinshi tana fashewa da kuka, saman gado ya zaune while tana rungume dashi,
ya shiga shafa bayanta saida ta tsagaita da kuka ya soma k'ok'arin zame jikinshi daga nata,
k'ara shigewa jikinshi tayi tana fad'in " karki tafi ka barni please tsoro nake ji, muryarshi k'asa yace " ruwa zan d'auko miki a fridge,
tana rik'e dashi gama suka d'auko ruwan ya bata tasha, babu irin tambayar da beyi mata ba tace bakomai kanta ke ciwo, yaso fita amma fafur tak'i sakinshi daya mik'e take mik'awa,
ranar ko bathroom tare suke shiga, a saman jikinshi ta kwana tana ta zabura cikin bacci.
A gurguje bayan wata d'aya da kwana d'akin Shakira da Ammar yayi ta soma laulayin cikin k'arya, kwana biyu bata da lafiya yana bata kulawa sosai, dan kusan shike jinyarta,
Hajiya Tanya na zaune gefen Shakira fuskarta cike da jimami tace " Hurayya kodai ciki ne dake?
Da sauri Ammar ya kalli Shakira itama ta kalleshi, Hajiya Tanya ta d'ora da cewa " ciwonki yayi kama da laulayin ciki gaskiya, ya kamata aje asibiti aji,
kan Ammar k'asa yace " dama yanzu nake san na kaita a dubata, Hajiya Tanya tayi murmushi tana cewa " haba Ammar gani a gida saika kai matarka asibiti da kanka?
"Ai ni ya kamata nakaita, ka bari zan kaita anjima, bai kuma yin magana ba, da daddare bayan Ammar ya dawo Hajiya Tanya ta tare da murna, tace " albishirinka?
Cikin rashin fahimta yace " me?
Bakinta a washe tace " Hurayya nada ciki na wata d'aya ta fad'a tana mik'a mishi takardar sakamakon gwajin, hannunshi na rawa ya amsa ya shiga dubawa,
yaga kwankin cikin sanyi dai-dai da ranar daya kwana d'akin Shakira, kasa danne murna da farin cikinshi yayi, bakinshi yak'i rufuwa,
" Alhamdulillah Alhamdulillah ala kulli halin, Allah na gode maka a bisa ni'imominka, Ammar ya fad'a yana kallan Hajiya Tanya,
da sauri ya mik'e yace " ina zuwa, bai jira jin abinda zatace ba ya fice, tabi bayanshi da gwalo had'i da dak'uwa, Shakira da Nayan suka fito daga inda suke lab'e,
" banzaye da kun tsaya kuna shiriritar banza, ba gashi an lik'a mishi ya amshe yana murna ba, Shakira da Nayan suka saka dariya.
Basmah na kwance a d'aki Zaman ya shigo dan yaga shigar Ammar BQ wajensu Madu zai sanar dasu maganar cikin Shakira,
dan haka ya samu damata, tana kwance taji an kwanta ta bayanta idanuwa ta lumshe had'i dayin murmushi dan a zatonta Ammar ne,
mararshi ya shiga gogawa a saman mazaunanta yana jin shauk'in da baya jinshi ga sauran mata, ya rasa dalilin dayasa Basmah kad'ai yake sha'awar kasancewa da ita,
ita kad'ai yake kishi ba a duk lokacin dayaganta da Ammar ji yake kamar ya mutu, in banda Hajiya Tanya na tausarshi da tuni me afkuwa ta afku,
idanuwanshi lumshi ya kwantar da kanshi saman kanta yana jin nishad'in da bai san daga inda yake zuwar mishi ba, numfashi ta shak'a da k'arfi ta bud'e baki zatayi magana,
kwakwalwarta ta tantance mata k'anshinshi idanuwanta waje kamar wacce akayiwa turaren barkono ta yunk'ura ta mik'e tana fad'in " Allahumma Ajirni Fi Musibati......,
katseta yayi ta hanyar cewa " ni ne masifar?
" Idan da abinda yafi masifa to kaine ga rayuwata, ta fad'a tana neman hanyar fita, tsare k'ofar yayi ya wani babbake yadda bazata iya fita,
idonshi kanta yana sakar mata shu'umin murmushi yace " bakiga komai ba Basmah, sai ranar da kika ga gawar Ammar kwance a gabanki,
ai dama na fad'a miki ni dake *MUTU KA RABA....* (MY NEW NOVEL) mutuwa ce kad'ai zata iya shiga tsakanina dake, bayan mutuwa babu wanda ya isa ya koda gifta ne ta tsakaninmu,
jiiinta na b'ari tace " baka da ikon aiwatar da komai akan kowanne bawan Allah face abinda Ubangiji ya zartar akanshi,
kai baka isa ka kashe ko ka raya ba, dan rai da rayuwa da mutuwa ba'a hannunka suke ba, kai ma a yanzu idan Allah yaso sai fad'i kayi mushe a d'auki gawar banza me bak'ar fuska ta mushiriki, basik'i d'an wuta, ajefar,
ko a ba karnuka su cinye, ta k'arasa maganar cikin k'arfin hali, step ya d'auka biyu zuwa yana nufarta while idonshi kanta yana murmushi, ganin yana nufota ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba,
tsoro da kid'ima suka shigeta k'afuwanta suka soma ruwa saboda firgici, barin jikin k'ofar da yayi ya nufota yasa ranta ya bata ta samu damar ficewa,
da gudu tayi k'ofa zata fice yayi wuff ya rik'e ta yana tuntsurewa da dariya, tsoro ne ya sanya fitsari kwace mata, ta saki k'ara da k'arfi batare data sani ba, saurin sanya hannunshi d'aya yayi ya rufe mata baki had'i da cewa "shhhhhhhh,
yana zare mata ido, cikin k'ank'anin lokaci ta had'a uban gumi sharkaf, tayi buzu-buzu da ita, kallo d'aya zakayi mata kasan tsoro na gaf da tsayar da numfashi da bugawar zuciyarta,
" matuk'ar kina san rayuwar masoyinki, matuk'ar kina san ki ceci rayuwar Ammar ki cigaba da ganinshi a doran k'asa to ki bani had'in kai, ta hanyar mallaka min kanki,
ya fad'a yana lashe hawayenta dake gangarowa, ido ta runtse da k'arfi jikinta na b'ari ta tattaro d'an sauran gwarin gwiwar daya rage mata ta sanyawa kanta,
zuciyarta na bugawa ta hankad'e shi had'i da tufa mishi yawu a fuska, ido Zaman ya runtse da k'arfi gami da kawar da kanshi,
ya d'auki second biyu zuwa uku kafin ya bud'e idonshi da suka koma asalin jajaye, lokaci d'aya ya koma mata Zaman d'in data sani, idonshi kanta yana kallan kwayar idonta ya sanya hannu ya lakuto yawun data tofa mishi a fuska,
duk ta tsorata da yadda ya koma cikin d'an lokaci kad'an hakan bai hanata jefa idonta cikin nashi tana kallan eyeball to eyeball ba,
ta nunashi da yatsa cikin dakewar zuciya tace " banza fajiri bak'in kare, wulak'antacce wanda bai yake tafiya da ka bada k'afafuwa ba, wanda bai inda inda yake masa ciwo ba, wanda bashi da tabbacin gobenshi,
jaki dabba mahaukaci tsinannan Allah, wanda ina da tabbacin da mala'iku na gajiya da la'antar wani aban k'asa da sun kaji da la'antarka.......!
a k'ufule Zaman ya damk'i gashin kan Basmah ya gwara kanta da bango ihuuuu ta saki da k'ara saboda azaba tana tallafe da hannunshi daya rik'e kanta dashi,
ihuuun da Basmah ta sanya Ammar ya jiyo yana k'ok'arin shiga mota tsayawa yayi kasak'e kamar me nazarin wani abu, part d'in nashi ya kallo a karo na biyu, kome ya tuna iho ya zaro ido had'i da bud'e, cikin tashin hankali yayi baya da gudu,
da k'arfi ya banko k'ofar parlour ya shigo, Hajiya Tanya dake lab'e ta window tana kallan Ammar ta gane abinda ya faru, ta juya tana kallan Shakira tace " ina wannan d'an tauren?
"Wa?
Cewar Shakira idonta kan window tana lek'a harabar gidan, ganin Ammar yayi part d'inshi da gudu yasa Shakira kallan Hajiya Tanya a d'an tsorace itama ita take kallo,
a tare suka had'a baki wajen cewa " Zaman....!, batare da sun kuma yin magana ba suka mik'e a tare da gudu, jikin Hajiya Tanya na rawa gudun tonuwar asiri ta kashe mitar wutar lantarkin gidan,
dai-dai lokacin da Ammar ya shiga parlour'n wutar Nepa ta d'auke, Zaman da yayi kasak'e yana sauraran wanda zai shigo ganin an d'auke wuta yasa yayi saurin sakin Basmah ya fice,
a hankali ta durk'ushe had'i da sakin kuka mai cin rai, daga jin kukan daga zuciyarta yake fitowa ba daga bakinta,
da lalube Ammar ya k'arasa shiga bedroom d'in Basmah, " Basmah...! ya kira sunanta cikin kasalalliyar murya da kukanta ya haifar mishi, kasa amsawa saboda kukan dayaci k'arfinta,
sautin kukanta dayake ji yabi ya isa gareta, yana kai hannu zai tab'ata ta fad'a jikinshi ta k'ank'ame shi gam tana k'ara sautin kukanta,
kanta ya shiga had'i da bubbuga bayanta ya kasa furta komai, cikin kuka tace " ka d'auke ni daga please, muryarshi a raunane da kamar zai fashe da kukan shima yace " kiyi hak'uri komai yana da lokaci, ki nutsu ki fad'a min abinda ya faru,
tana girgiza kanta while tana rik'e da shi gam tace " ni dai ka d'auke mu tafi, bana san zama anan, bana zama da mutanen nan dan Allah,
" kiyi hak'uri Basmah in sha Allahu wata rana sai labari, yayi maganar cikin raunin da kukanta ya haifar mishi, jin kukanta yake har k'asan zuciyarshi,
itake kukan amma shike jin zafi da rad'ad'in rasa abinda zayyi yasashi lalabubar bakinta ya had'e da nashi, ya soma tsotsar lips d'inta da harshenta.
Kai Hajiya Tanya ta dafe had'i da cewa " Oops ni dai ina ganin rayuwa, yanzu in banda Allah yasa nayi saurin ankara me kike tuninanin zai faru da Ammar ya iske Zaman a d'akin Basmah?
" Hmmmm shiyasa tun farko na fad'a miki wanda kika kawo cikin aikinki, na fad'a miki zai watsa shirin da kikayi shekaru kinayi,
numfashi Hajiya Tanya ta fitar kafin ta bud'e baki zatayi magana, shigowa Zaman yasata yin shiru, da ido suka tsare shi suna jefa mishi kallan tuhuma,
" lafiya dai ko?
Ya fad'a yana kallansu, " daga ina kake?
Shakira tayi maganar tana kunna mitar wutar, " kinfi kowa sanin bana san tambayar renin hankali, ni k'aramin yaro ne da zaki saka ni gaba kina tambayata daga inda nake sai kace d'anki dan renin hankali?
Ya k'arasa maganar yana jefa musu kallan banza, babu wanda yayi magana cikinsu, har Hajiya Tanya da haka nan taji tsoron Zaman ya kamata,
karo na farko a rayuwarta dataji tsoran wani mahaluk'i a iya tsarin rayuwarta, " an abinda Shakira take fad'a bazai zama gaskiya ba, na d'auko ruwan dafa kaina!?
Tayi maganar cikin ranta tana bin bayan Zaman dayake shigewa bedroom da kallo, hasken daya gauraye d'akin ne yasa Ammar zame bakinshi daga nata, juna suka k'urawa ido na d'an lokaci,
kafin Basmah ta kawar da kanta gefe tana sauke ajiyar zuciya me nauyi, shima kan ya kawar gefe yana fad'in " I'm sorry ba nufi na kenan ba,
da mamaki ta kalleshi deep down tana mamakin halayya da d'abi'un Ammar, ta wani b'angaren kuma salan nashi na burgeta, wai I'm ba nufi na kenan ba,
kamar ita d'in ba matarshi bace ta sunna, a gefen Ammar kuma yana yin hakanne danya nuna mata yasha banban da sauran mazan zamani da kamar jira suke akai musu matar,
wasu ko d'aga k'afar kwana d'aya basa iyayi, yana so ya nuna mata ita yake so ba jikinta ko wani abu nata ba, yana san ya tabbatar mata zai iya yin rayuwa da ita koda babu sex, farin cikinta kawai ya isheshi....!
bayyi magana ba ya mik'e ya shiga bathroom ya had'a mata ruwan wanka, " ki shiga kiyi wanka, ya fad'a yana kallanta a tsanake,
kamar zatayi mishi musu sai kuma ta mik'e batare datayi magana ta shiga bathroom, shi kuma ya fita, bai dad'e ba ya dawo d'auke da tray ya aje saman bedside,
da kanshi ya shiryata ya bata tea d'in tasha kana yaja musu bargo, bayan ya rungume ta sosai a jikinshi.
Tunda Shakira taga Ammar na san cikin jikinta ta langwab'e ta shiga amaye-amaye da laulayi, shiko bawan Allah bai san dawar garin ba ya shiga lallab'ata yana nan-nan da ita, nan fa ta samu damar yiwa Basmah iskanci da habaici, Shakira na zaune Basmah tazo zata shiga kitchen, Shakira ta kalli Basmah had'i da kawar da kanta gefe tace,
" juya...! an kasa koda b'atan wata, af ashe fa na manta ba'a tab'a had'a gado ba balle a had'a jiki, har Basmah tasa kai zata wuce wata.zuciyarta tace ta dawo ta mayar mata,
ta tsaya akan Shakira tana k'are mata kallo fuskarta d'auke da murmushi tace " had'a gado bashine ke nufin ana sanka ko ba'a sanka ba,
kayi k'ok'arin saman matsugunni a zuciyar mijin shine abin so,
rashin had'a gado yana nuni da abu biyu ne kodai ana san tabbatar miki ana sanki ba jikinki aso ba, ko kuma ba'a damu dake ba, kada ki manta ranar auranki aka aure ni,
aka banda dake bai k'arabi ta kanki ba, ya tare a asibiti yana jinyar matar so, matar da yayi auren soyaya da ita ba wacce akayi k'arya da k'arairayi aka lik'a mishi ita ba,
ciki kuma ke kanki kin san ni ba juya bace tunda kinga tabbas a inda na baro, kuma da matar so ke d'auke da cikin dake jikinki da sai kinga abinda zai kashe ki saboda bak'in ciki,
banza asararriya wallahi na wuce ki Shakira nayi miki nisan nisan da bazaki iya kamo koda taku na bane, dan mazan dake hauka akaina ke su kike bi,
a fusace Shakira ta d'aga hannu zata kifawa Basmah mari, cikin zafin nama Basmah ta rik'e hannunta ta warb'ar gefe ta sharara mata marin da saida taga taurari,
ta nunata da yatsa tana fad'in " a! a! a! Shakira karki soma nan da can ba d'aya bane, idan kuma kikace zakiyi ke zaki kwashi kashinki a hannu dan nan a gidan Ammar muke ba Zaman ba,
sororo Shakira tayi dafe da kuncinta tana kallan Basmah cike da mamaki, Basmah ta cigaba cewa " wannan marika nayi miki su ne na gargad'i,
gaba idan kika k'ok'arin d'aga hannunki a kaina tayi kwafa had'i da cije lips, tabar wajen, Shakira tabi bayanta da kallo dan babu halin d'aukar mataki akan Basmah tasan muddin tayi mata wani abu Zaman da Ammar ba kyaleta zasuyi ba.
Nayan, Zaman da Hajiya Tanya na zaune Basmah da Ammar suka shigo part d'in gaida Hajiya Tanya, hakan al'adarsu ce kullum sai sun shigo gaida ita,
hannun Basmah rik'e gam cikin na Ammar, cikin nutsuwa suka zauna saman sofa suna fuskartar Hajiya Tanya, " ina kwana?
Suka fad'a a tare fuskarta cike da fara'a ta amsa da " lafiya lau yaran kirki, kun tashi lafiya?
"Alhamdulillah, Ammar yace, tunda Basmah ta shigo idon Zaman da Nayan ke kafe a kanta basu ko blinking, " ina kwananku?
Ammar ya fad'a yana kallan Nayan, bai amsa ba kasancewar baya cikin hayyacinshi, bazai iya tuna lokacin da fara sha'awar Basmah ba, ya dad'e da tsintar kanshi cikin tafkin sha'awarta,
babu abinda yafi so a halin yanzu kamar ya kasance da ita, kullum cikin mafarkinta yake harta kai ko sex yake da karuwanshi baya iya samun nutsuwa sai rink'a hango Basmah,
lamo yayi yana jiran su auna Ammar k'iyama shi kuma ya auna Zaman ya mallake Basmah, jin bai amsa ba yasa Hajiya Tanya da Zaman kallanshi,
had'i da bin inda yake kallo da kallo ganin yadda ya kafe Basmah da ido idonshi har ruwa-ruwa sukeyi saboda jaraba ba k'aramin d'aga hankalin Hajiya Tanya yayi ba,
Zaman kam ji yayi kamar ya kama wuyan Nayan ya tsinke ya rabashi da kanshi, a dururuce tana kame-kame ta d'an mangari Nayan had'i da cewa " ana gaida kai,
tayi maganar tana murmushin yak'e had'i da satar kallan Zaman, wutar data hango cikin idon Zaman yasata rufe idonta cikin ranta tana fad'in,
" na shiga uku, yaron nan baiji kashedin danayi mishi akan Basmah ba kenan, nema yake ya jefa kanshi a bala'i, ya jawo min masifa,
d'an firgigit Nayan yayi kakar wanda ya tashi daga bacci yana fad'in " na'am, murmushi Ammar yayi a karo biyu kana ya gaida shi,
su Ammar na fita Zaman ya mik'e had'i da damk'ar wuyan Nayan ya d'agashi sama yana fad'in " ka nisanci Basmah matuk'ar kana san cigaba da rayuwa,
idan kana san zaman lafiyarka da ranka kayi k'ok'arin nisanta kanka da ita, ka bata tazarar taku saba'in inba haka ba wallahi zan tsinke maka kanka,
sosai Nayan ya soma kakari da k'ok'arin kwace kanshi amma ya kasa, idanuwanshi sukayi jajir kamar gauta, jikin Hajiya Tanya na kerrrrma ta mik'e ta rik'e hannun Zaman,
ta shiga bashi hak'uri, sai da ya tabbatar Nayan yaji k'anshin mutuwa kana ya sakeshi ya zube k'asa yana kakari, cikin fushi ya nuna Hajiya Tanya da yatsa yana fad'in,
" kijawa d'anki kunne dan muddin ya kuskura yayi wani gigi akan Basmah wallahi Allah saina yanke masa mazantakarshi,
idan ya saba neman matan wasu yana cin lalai kija masa kunne akan Bamsah dan daga kanta ya dena iskanci, ya dena haik'ewa kowacce maace, kinji dai na rantse,
bai jira abinda zasu ce ya fice, Shakira ta kalli Hajiya Tanya tace " kin gani ko?
"Dama na fad'a miki, duk abinda kikaji Zaman ya rantse to babba ne dan haka ku kuka da kanku, ta k'arasa maganar tana barin wajen,
abinda Zaman yayiwa Nayan ba k'aramin hasalashi yayi ba, zuciyarshi ta shiga tafasa tana suya, ya k'udurce a ranshi komai zai faru yau sayya kusanci Basmah,
bayyi magana ba ya mik'e ya shige d'aki, bai jima ba fito ya fice yana rik'e da wuyanshi, Hajiya Tanya tabi bayanshi tana yi mishi magana baiko juyo ya kalleta ba ya shige motarshi.
K'arfe 11 saura na dare Nayan ya shigo gidan kallo d'aya zakayi mishi kasan a buge yake tatul, yana tangad'i ya nufi part d'insu ya shige bedroom d'inshi,
saman gadonshi ya fad'a had'i da sakin murmushi yana juya wayar Ammar daya sata d'azu, sai da saita kanshi kana ya kira layinta,
bata d'aga a kiran farko ba sai da ya k'ara shima sai da ta kusa tsinkewa kana ta d'aga cikin bacci, kwaikwayon muryar Ammar yayi yace " kizo part d'in Mom ba lafiya, ina d'akin Nayan,
kasancewar cikin bacci Basmah take kuma Nayan yayi k'ok'arin kwaikwayon muryar Ammar yadda ya kamata yasa Basmah bata gane ba Ammar d'in bane,
" me ya faru!?
Tace tana wartsakewa, " idan kinzo kyaji, bai jira abinda zatace ba ya kashe wayar, daga ita sai rigar bacci iya cinya, ta mik'e jikinta na rawa ta d'aura zani had'i da zumbula hijabi,
cikin siririyar muryarta tayi sallama daga bakin k'ofar d'akin, " shigo....! akace a tak'aice batayi tunanin komai ba ta shiga d'akin,
tana shiga ya rufe k'ofar dama yana lab'e a bayan k'ofar, cike da mamaki ta kalleshi tana fad'in " Na.....Nayan lafiya?
Baya yaja had'i da rik'e hab'a yana kallanta had'i da cije lips irin na gogaggun 'yan bariki, " meke faruwa ne?
"Ina Ammar....!?
Basmah tayi maganar tana kallan Nayan, " ba Ammar bane ya kiraki nine, ya fad'a had'i da nuna mata wayar Ammar dake rik'e a hannunshi,
cikin rashin fahimta tace " lafiya?
"Lafiya lau Basmah, taimako nake nema daga gareki, " taimako kuma?
"Wanne irin taimako?
Ta tambayeshi dan kwata-kwata hankalinta bai bata abinda Nayan ke nufi ba, matsowa yayi gaf da ita zai rik'eta tayi saurin ja baya,
" meye haka?
"Shine taimakon da zakiyi min, ki taimake ni ki mallaka kanki na daren yau kad'ai, duk abinda kike so nayi alk'awarin zan mallaka miki shi,
na dad'e da k'ishirwarki cikin raina ki taimakeni mu raya daren yau, na dad'e da sanin babu abinda ya shiga tsakaninki da Ammar,
asalima ko shinfid'a baku tab a had'awa, ya k'arasa maganar yana rik'ota, had'i da k'ok'arin mannata da jikinshi, kyakkyawan mari ta kifa mishi,
had'i da ture shi ta fashe da kuka mai sosai zuciya tana fad'in " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
na shiya me nayi da nake fuskantar hukunci ta fuskoki da dama, wanne irin laifi nayi da rayuwata ke garairaita tana wulak'anta,
a gidan miji gidan aure na ban tsari daga sharrin fasik'an maza ba, bazance ka bani mamaki ba, dan wannan kad'an ne daga cikin abinda mutum zai iyayi,
musamman mutane masu san zuciya wad'anda duniya ke rud'a, na dad'e da sanin shaid'an yayi maka fitsari aka, duniya ta kad'a maka gangar ma'azu,
in banda kai gafalalle ne tab'abb'e ne ya za'ayi ka nemi matar k'aninka da kuka fito tsatso d'aya, ina baka shawarar ka tuba tun kafin duniya tayi maka atishawar tsaki,
dariya ya sanya had'i da sake nufarta yana lasar leb'e yace " ki fara gusar min da k'ishirwata kafin kiyi kin wa'azin, juyawa tayi da nufin fita daga d'akin,
ya rik'eta yana fad'in " haba 'yan mata ina zaki baki biyamin buk'ata ta ba, yayi maganar yana k'ok'arin had'e bakinsu,
kokawar kwace kanta Basmah ta somayi shi kuma yana san jefata saman gado, nan fa kokowa ta kaure a tsakaninsu,
suka soma tik'ar dambe tititir-tititir, Allah ya bawa Nayan nasarar cire mata hijab, ya fisge zanin jikinta, ya rage daga ita sai guntuwar rigar bacci, ganin yana neman kaita k'asa ta dage iya k'arfinta, aiko ya kasa gayar da ita,
haushin mace na neman gagararshi yasashi kifa mata marin da saida taga wuta, ya damk'i gashinta ya jefata saman gado,
ya tsaya kanta yana cire wandonshi, mik'ewa tayi sauri had'i da fasa ihu, ganin yana neman keta mata haddi yasa zuciya ta kawota wuya,
ta wawuri kwalta giyar dayasha zata buga mishi yayi saurin rik'e hannunta,
nan fa tambe ya sake kaurewa dayafi na farko kafin kace me sun fashe duk wani abu me glass a d'akin, har TV while Basmah na cigaba da ihu,
bibbiyu Ammar ke taka k'afar benen sakamakon ikon Basmah da yake jiyowa, kicib'us yayi dasu Hajiya Tanya, Zaman da Shakira a parlour tsayawa sukayi suna kallan juna,
dan duk ihuun Basmah da k'arar fashe-fashen da akeyi ne ya fito dasu, ihuuun data k'arayi ne yasasu rige-rigen nufar d'akin Nayan,
bak'aramin tashin hankali Hajiya Tanya ta tsinci kanta a ciki ba ganin Nayan na neman ketawa Basmah haddi, tasan komai ya lalace yau,
tasan komai yazo k'arshe, Nayan ya gama lalata komai mussaman data lura a buge yake baya cikin hayyacinshi, yana iya fad'ar duk abinda yazo bakinshi, tasan koda Ammar yayi shi ya kyale tasan Zaman bazai tab'a kyaleshi ba.....!
idanuwan Zaman rufewa sukayi da har ya manta da wani Ammar, ya manta da batun dukiya balle gargad'in Hajiya Tanya...!
da iya k'arfinshi ya damk'i Nayan ya kai mishi naushi a fuska bakinshi ya fashi...!, jikin Basmah na rawa ta fad'a jikin Ammar tana kuka da iya k'arfinta take fad'in " nace maka ka d'auke ni daga nan kak'.......!
kalaman Nayan ne suka sakata sakin jikin Ammar ta zuba mishi dayake fad'in " akan me kake duka na, bayan ita kawo kanta?
"Ita ta kawo kin tallar kanta da buk'atarta, ta dad'e tana rok'ona akan na kusanceta nak'i, wai Ammar yak'i kwanciya da ita,
yaki biya mata buk'atarta dana k'i shine fa yau tazo har d'akina ta tsare ni, wai idan ban biya mata buk'atarta na kwanta da ita sai tayi min sharri, shine dana k'i ta fasa komai ta hau ihuuu,
idan kukayiwa kallan basira zakuga idan da nine me laifi me zai kawota dak'i na....!?
"Da ni zan nemeta da nine wanda zaije d'akinta, Basmah da tunda ya fara magana take girgiza kanta, babu inda baya rawa a jikinta,
Hajiya Tanya tayi caraf ta amshe da cewa " k'arya kike yi munafuka d'ana ba d'an iska bane ke kike san lalatamin shi, shekaran jiya ina jinki a kitchen kina rok'onshi,
nayi miki nasiha ashe baki d'auka ba, inda shine kwarton ai da shine zaije inda kike, gunjin kuka sosai Basmah take yi, ta fita daga hayyacinta,
jikinta na kerrrrma ta shiga jijjiga Ammar tana fad'in " wallahi k'arya suke yi sharri zasuyi min, ka yarda ni, wallahi ban nemeshi ba, ganin Ammar yak'i motsi yasa Basmah haukacewa ta d'imauci tana wani irin kuka da wanda ke cikin halin rai ko mutuwa ke yinshi,
ta rungume Ammar tana maimaita " ka yarda dani wallahi ban nemeshi ba, shine yaso keta min haddi, a hankali Ammar ya kawar da kanshi tare da raba Basmah da jikinshi batare daya kalleta ba,
cak ta tsayar da kukanta ta kalleshi had'i da kallan hannunshi dake tureta daga jikinshi, kasa magana tayi illa kanta datake girgiza mishi,
lips d'inta na rawa alamar magana take sanyi amma tashin hankali ya hanata,
murmushi Hajiya Tanya tana kallan gefe kana ta fisgo Basmah had'i da d'aga hannu zata kifa mata mari,
caraf taji da rik'e hannunta gam kamar za'a karyata da mamaki bayyane a fuskarta ta juyo...........
*Ku k'ara hak'uri dani an kusa hamawa da izin Allah, nagode sosai da addu'o'inku......*