Free chapter · Read without an account
Chapter 10
RAN MAZA YA ƁACI.
Mus’ab yana huci zuciyarsa na masa ƙuna ya ce, “Safinat shaitan ya yi fitsari a kanki, kin cuce mu sakayyar da za ki fara nuna mana kenan? Allah shaida ne kullum ƙoƙarin mu ni da Aunt ki shi ne mu ba ki tarbiyya, mu rabu da ke lafiya amma ke kina ƙoƙarin rushe wannan tubalin. To ƙaryanki masu hore miki kunnen ma ƙaryansu, amanar da aka ba ni sai na cika shi ba zan taɓa bari ki lalata rayuwarki ba da yardar Allah da kuma karfin addu'ah.
Ita dai Safinat sai kuka take Mus'ab ya farfasa mata jiki, ga bakinta da ya gwara da bango ma ya yi suntum.
Ya riƙe kunnenta yana ja, "Safinat samarin shaho za ki biye wa ko? To ki yi wa kanki karatun ta nutsu, idan ko ba haka ba za su kai ki su baro ki da zarar sun ci moriyar ganga. Magana ta ƙarshe ba ke ba kuma fita cikin gidan nan idan na kuskura na ganki a bakin gate ba waje ba ma ki yi kuka da kanki, don abin da zai biyo baya sai kin yi nadamar zuwanki duniya. Kina ji na!”
“ Eh yaya.” ta faɗa cikin kuka
“ Idan ina cikin gidan nan, ko inuwarki ban son gani ballantana ke kar ki kuskura mu yi ido biyu duk abin da kike buƙata, ki sanar da Aunty ki ta sanar da ni. Ko da abinci ne ki ci ke kaɗai."
MAIMUNATU DA ALIYU
Maimunat ta leka ta hango Umar na latsa waya.
"Umar, ni fa ba baƙuwa ba ce ka fita waje ka keɓe don Allah shigo daga ciki."
Ya miƙe, " Ba haka ba ne Aunt na yi waya ne."
Bayan ya shigo suka taɓa hira ta duba agogo ta ce, “Dear zan koma, Allah ya ba ka lafiya, Allah ya sa kaffara ce.”
“Amin dear, amma ni a tunanina kin zo don ki kwana a wurin mijinki.”
Ta taɓe baki haɗe da zare ido, "Rufa mini asiri. ”
"Me ye abin rufa asiri kuma, don mata ta zauna ta kula da jinyar mijinta."
"Haka ko? To na damƙa amanar kulawa da kai wurin Umar zai kula da kai sosai sama da ni." Ta dubi Umar, "Ƙanina ka karɓi amanar?"
"Na karɓa Aunt, ki huta gajiya a gaishe da Mummy da Daddy." Ta amsa da za su ji ta fice.
Aliyu na ƙishingiɗe ya dubi Umar ya ce, “Umar don Allah ko da Mama ta zo kar ka sanar da ita da Maimunat ta zo”
“Haba yaya ko ba ka faɗa ba, ba za ta ji ba.”
Yana hamma ya ce, “Yauwa ɗan uwa rabin jiki na gode.”
“Ba komai yaya, ni ma fa na san komai abin da yake tafiya, Mama mahaifiyarmu ce amma halayyarta na ƙin Aunt Maimunat yana daga cikin abin da yake ci mini tuwo a kwarya.”
Aliyu ya ɗan yi miƙa, “Haka ne, Mama addu’a ya kamata muna yi mata don addu’a shi ke maganin komai.”
“Tabbas haka ne yaya. Allah ya fahimtar da ita.”
MU WAIWAYI SAFINAT DA MUS'AB
Mus’ab ya yi mata wani irin matsiyacin kallo ya ce da ita, “Ba ni wayarki, daga yau sai naga abin da za ki yi amfani da shi, don na tabbatar handset ma yana ɗaya daga cikin abin da ya lalatar da rayuwarki.”
Safinat cikin sheshshekar kuka take cewa, “Yaya don Allah ka yi haƙuri ka bar mini wayata, wallahi ba zan kuma yi ba.”
“Za ki ba ni ko sai na gwara kanki da bango.”
Jikinta na rawa cikin tsoro ta miƙa masa.
Yana karɓa ya zare sakatar ɗakin ya fice, Hafsy kai tsaye ta shigo ta rungume ta tana cewa:
“ 'Yar Aunty abin da nake guje miki kenan na hana ki fita amma ke ba ki hango hakan ba.”
Fizgar jikinta ta yi ta ce, “Ki bar ni Aunt ba na so.”
Cikin sanyin jiki ta bar ta.
Tsaki Feenah ta yi ta ce, “Duk abin da ya same ni ke ce sila, yaya kawai kare ki yake amma ni na san komai haka za a ganni a bar ni.”
“ Feenah kin san da wa kike magana kuwa? Kuma kin san abin da bakinki ke furtawa?”
“ Nasan me nake furtawa tun da ba a cikin maye nake ba, ke ɗin ce dai ban sani ba ko kin sha cordian, da Hafsat Abdullahi nake magana, kin tabbatar garau nake ko.”
Ta zaro mata idanuwanta tana dalla mata harara da murguɗa baki
“A kaina za ki huce haushinki ko, ba laifin ki ba laifina ne, ni kike jefa da muggan kalamai ko.”
“ Waye ke da ba za a faɗa miki magana ba?”
“Hafsat kai tsaye babu ko sakayawa na gode.”
“To, ikon Allah, waye ke da ba za a ambaci sunanki ba uwata ce ke da zan yi shayin faɗa, na faɗa Hafsat Abdullahi sai ki kira mijinki ki shaida masa ina faɗin sunanki sai ya yi gunduwa-gunduwa da ni saboda an taɓa Shalelensa juya wacce bata haihuwa kin mallake yayan mu, to ta Allah ba naki ba.”
“An zo wajen yanzu na fara fahimtar inda kika dosa. Ke ma sai ki samo mijin ki yi ƙoƙarin zama Shalelensa in za ki iya kuma ki mallake shi, ai sai mace ta isa mace take zama shalele kuma ta mallake amma ballagaza ba ta isa ta yi haka ba.
“ Ni ce ballagaza ko?”
“Yep.”
“ To koma mene ne alhamdulillah ke ma da boka da Malam kika mallake yayan mu, kuma sihirce-sihircenki yana gab da wargajewa.
“ Ya isa haka Safinat, ni ba sa'ar yin ki ba ce.”
Ta miƙe tsaye ta riƙe kugu “Kin san da haka kika shiga abin da bai shafe ki ba. Mijinki ya sani ko zai kashe ni sai na yi abin da raina ke so.”
“Me ya sa ba ki faɗa masa a gabansa ba, yana gidan bi shi ki faɗa masa. A nan zan tabbatar ke cikakkiyar fitsararriya ce ba hargagi a bayan idon sa ba. Ba ni na kar zomon ba, ni ma rataya a ka ba ni. Shashasha ban san dalilin da ya kai ni ma yin musayar yawu da ke ba."
Ta fice tana mai buga kyauren da ƙarfi.
Bayan ficewar ta Feenah ta zuba tagumi ta fara maganar zuci, tana cewa, “Amma yaya ka cuce ni, raba ni da waya da ka yi ya fi yi mini ciwo fiye da dukan da ka yi mini, amma ba komai akwai ranar da zan yi mulki ni ma a kanka.”
Hafsy da ta koma falo ta zauna bisa duguwar kujerarta ƙwalla suka cika idanuwanta saboda takaicin kalaman Feenah a kanta ba kalmar da ta yi mata ciwo kamar ta juya mara haihuwa da na ta mallake yayanta ta hanyar boka.
Miƙe wa ta yi tana mai kallon silin tana maganar zuci tana cewa, “Me ya sa na biye wa yarinyar nan muka dinga musayar yawu? Yarinyar da ba sa'ar yi na, in sha Allah ba zan kuma sa'insa da ita ba.”
Bathroom ta nufa ta watsa ruwa ta je ɗakinta ta yi ƙwalliya.
Ta shafe ilahirin jikinta da turarurruka daban-daban ta nufi site na Mus'ab ta shiga tana mai yi masa sallamah ya amsa mata sallamar amma fuskar shi babu fara'a.
Durkusa wa ta yi a gaban shi, ta shafi kasumbar shi ta ce da shi, “Mijin mace ɗaya, nawa ni kaɗai wa ya taɓa mini kai?”
“Au haka ma za ki ce ba ki san dalilin fushi na ba ko? How many minutes ina zaman jiranki an taɓa ɗiyarki kin je kina rarrashinta ko?”
“ Wallahi nasan Safinat ba ta kyauta ba amma zuciyata na tausayinta sai isa na shiga na ba ta haƙuri tare da nutsar da ita. Allah ya huci zuciyar my hero kaina a ƙasa ina neman afuwa. "
Jawo ta ya yi jikinsa yana shafarta ita kuwa tana lumshe ido, ya ce, “Ba afuwa yau kam na fatar baki, abu ɗaya za ki yi mini a daren yau na yafe miki.”
“Ka faɗa idan har bai fi ƙarfina ba zan yi shi mijina aljannata.”
“To ‘yar aljanna ba ni kunnenki in miki raɗa.”
Ta miƙa masa bayan ta gama jin abubuwan da ya faɗa ta kyalkyale da dariya ta ce, “Mijin mace ɗaya, nawa ni kaɗai, wannan kawai shi ne muradinka, to ka samu ka sha kuriminka.”
A kan gadonsa ya kwantar da ita yana shafarta ya kashe lantarki duhu ya mamaye ɗakin.
ALIYU LAFIYA TA SAMU
WASHE GARI:
Aliyu zaune yake a gefen gado fuskarsa na ɗauke da fara'a.
Mama da Umar na zaune a kan kujeru daga gefe, sai likita da ke tsaye da fayil a hannunsa ya ce, “Su Aliyu manya a ka ce labarin zuciya a tambayi fuska. Shin yau me ya faru ne haka ake fara'a?”
Murmushi ya yi ya ce, “Doctor murnar zan samu sallama ne.”
“Kai dai faɗi gaskiya, akwai wani reason bayan wannan.”
Yana murmushi ya ce, “Gaskiyar kenan likita, wa ke son zaman asibiti idan ba ya zama dole ba.”
“Wannan haka yake, dama abin da muke so daga gare ka shi ne; kullum ka kasance cikin walwala, Aliyu kana cikin kuruciyarka, don Allah ka daina jefa kanka cikin damuwa da tunani, sannan kana ci kana sha a kan lokaci. Yin haka shi zai sa ka dawwama cikin lafiya.”
Ya juya kan Mama ya ce, “Mama don Allah ki kula da ɗan ki, idan har kin san abin da yake jefa shi cikin damuwa da yawan tunani to a magance masa gudun kar rayuwar shi ta faɗa cikin hatsari.”
“Ba komai likita, zan yi iya ƙoƙarina.”
“To masha Allah.”
Ya miƙa musu takardar sallama ya ce, “Aliyu bayan sati biyu, ka ƙara zuwa don duba lafiyarka.”
“Okay Doctor, na gode.”
“Yawwa, Allah ya ƙara lafiya.”
Ya sa kai ya fice.
GIDAN MUS'AB
Hafsy yau ma dai ita kaɗai ta kammala breakfast, ta zuba ma Safinat nata, ta shiga ɗakinta ta yi mata sallama ba ta amsa ba ballantana ta ɗaga ido ta kalle ta. Ita ma kuwa tana ajewa ta fice.
Zaune suke a gaban dining table suna cin abinci Mus’ab ya ce,
“An gaishe da matar da ba ta tsufa a kullum ganinta nake 'yar 18.”
Mumushi ta yi tare da kashe masa ido ta ce, “ Mijina kenan, ai kai kake mayar da ni 'yar 18 a kullum.”
“Ni kuma ga shi kina mayar da ni ɗan 100 ko.”
Dariya ta yi “Ai gwamma na mayar da kai haka, don na hana sauran 'yan mata mallakarka don ka san ba macen da za ta so tsoho, amma idan na mayar da ka irin 25 or 30 'yan mata su dinga kai maka farmaki sun ga handsome guy, su ce ga new catch, ba da ni ba.”
Da dariya ya tuntsire,. “Au dariya ma na ba ka ko! To bari ka ji koko zan fara damawa, wannan sajen naka idan za ka fita duk na shafe shi da koko sai a ga kamar furfura ana yi maka kallon tsoho ana girmamaka.”
“Ai ko, da kin kyauta kuwa sai ki haɗa da sanda ke ki zama ‘yar jagora ina tafiya ina sunkuyar da kai.”
Ta sheke da dariya ta ce, “Har na fa hararo yadda za ka koma, gaskiya zai yi maka kyau, ka ga duk inda aka ganka sai dai a yi kiranka da kaka a dinga taimaka maka.”
“Mus’ab a ko ya yake shi mijin mace ɗaya ne Hafsat, wannan alƙawari ne da na ɗaukar wa kaina, ke ce abokiyar rayuwar Mus'ab, idanuwana da kunnuwana ba sa ji kuma ba sa kallon wasu mata a doron duniya face ke ɗaya. Zan rayu da ke zan mutu da ke abadan da ni da ke zamu zauna. Cewar Umar M Sheriff. To haka za mu kasance.”
Murmushi jin daɗi ta yi “Mijina farin cikina, ina godiya bisa wannan jihadi da ka yi na mallaka kanka ga mace ɗaya tilo wato ni, ina tsananin son ka ba zan iya raba ka biyu in ba wa wata ba, daidai da turaren da ke jikinka ba zan so wata ɗiya mace ta ji ƙamshinsa ba in har za ta ji daɗi a ranta game da kai, balle kai da kanka mijina, ɗumin jikinka a jikina kawai nake so ya dinga kasancewa har abada. Ban son wata ɗiya mace ta ji shi, ina yi wa kowacce mace fatan samun mijin aure amma ban da my one and only, saboda don ni kaɗai a ka yi shi ni ma kuma don shi kaɗai a ka yi ni.”
Mus’ab, miƙe wa ya yi yana cewa, “Matata kin rufe kofa, babu wata ɗiya mace da take da wannan mukullin da za ta iya buɗe wannan kofar ta ki ballantana ta shigo. Saboda haka kwantar da hankalinki.”
Ita ma miƙe wa ta yi ta ce, “Ina godiya mijina ai ni hankalina ya daɗe da kwanciya tun ranar da Allah ya mallaka mini kai a matsayin miji. Dear tabbas babu mukullin da zai iya buɗe wannan taskar taka, domin ina kulle wa na jefa a kogin Nilu, kuma Mamiyota ta haɗiye.”
Suna hira da raha ta raka shi har zuwa motar shi ta buɗe ya shiga ta yi masa fata na alheri. Ya ja mota ya tafi.
UMAR DA MAHAIFIYARSA
A hankali ya ɗago fuskarsa sai ya ga Mama hankalinta nakan telebijin tana kallo. Ya ajiye cokalin cikin plate da yake cin abincin ya tura gefe yana me cewa alhamdulillah.
Juyo wa ta yi ta kalle shi ta ce da shi, “Har ka koshi?”
Bayan ya sauke ajiyar zuciya ya amsa mata da “Eh Mama."
Ya ɗan sosa ƙeyarsa, "Yauwa Mama idan har ba za ki damu ba ina so mu yi wata magana.”
Ta rage sautin telebijin ɗin ta ce da shi, “Ina sauraronka.”
“Mama ke a ganinki mene ne musabbabin da ya jefa Yaya Aliyu cikin tunani da damuwa?”
Taune lips ɗinta ta yi kana ta ce, “Oho ban sani ba, wannan ba ni ya kamata ka tambaya ba shi za ka tambaya sai ka samu amsar.”
“Amma Mama ni a ganina kamar rabuwa da matar shi ne musabbabin haka.”
A faɗace ta ce da shi, “To dama ka san amsar tambayar taka kake tambayata.”
“Mama don a samu mafita ne na tambaye ki.”
Cikin fushi haɗe da murtuke fuska ta ce, “Umar! Umar! Umar! Na kira sunanka sau uku to ka kiyaye ne, ka daina shiga cikin abin da bai shafe ka ba.”
“Mama………” Sallamar Aliyu ce ta katse maganar da yake son faɗa.
Bayan sun amsa masa sallamarsa, ya nemi wuri ya zauna cikin girmama wa ya gaishe ta, ta amsa masa tare da yi masa ya jiki ya ce da ita da sauki.
Umar shi ma ya gaishe shi tare da yi masa ya jiki.
Mahaifiyarsa ta dube shi, “Ɗan uwanka nata jiran ka ku ci abinci shiru ba ka zo ba na ce maybe ba ci za ka yi ba, na ce da shi ya ci.”
“Gwamma da ya ci Umma, ni yanzu a koshe nake sai dai ko zuwa an jima.”
“Dama nasan haka za ka ce.”
Umar ya girgiza kai ya dubi mahaifiyar ta su ya ce, “Mama idan har kina so Aliyu ya koma kamar yadda yake sai……..”
Ta ɗaga hannu “Dakata Umar ban yi maka kashedi da ka daina yi mini wannan maganar ba, to wahainiyarka ta kiyayi rama ta.”
Ta miƙe ta bar musu ɗakin.
Aliyu ya dubi Umar “Umar, akan lamarina kuke magana ko?’’
“Eh yaya.”
“Ai tun da Baffa ya Musa ya mata magana ta ƙeƙashe ba na tunanin akwai wanda za ta ji na shi, saboda haka rabu da ita ka daina wahalar da kanka, mu fauwala Allah komai.”
"Amma dai har ga Allah Mama ba ta kyauta ba, haka kawai ma'aurata na son junansu a raba su, ni kam idan ni ne ko sama da ƙasa za ta haɗu ina son matata ba zan sake ta ba."
Aliyu murmushi ya yi kawai game da kalaman ƙanin nasa.
MU LEKA GIDAN UMMA LAURE
Umma Laure zaune take ta miƙa ƙafafuwa ana ja tana cewa, “Don Allah ɗana ka ja a hankali akwai azaba fa.”
“Mama, sai haƙuri haka sha'anin gyara yake, zafi shi yake fitar da ciwo." Ya wani haɗa ƙashi sai da ya yi ƙara kas
Umma Laure ta zambaɗa ƙara, "Yaro ka kashe ni, dama ai ku Maɗora mugaye ne ba ku da tausayi ko na anini.Ta haɗa gumi haiƙan, “Wayyo ni Lauratu na ga ta kaina.”
“Sannu Mama, idan muka sa tausayi a aikinmu ai mun ɓata." Ya daddana ya buɗe wata 'yar leda ya ciro wata kwalba da magani a ciki kamar mai ya dinga shafawa yana dannawa tana wayyo, kana ya yi tofi ya ce, "Shi ke nan ma, ya haɗu kina ƙoƙarin takawa kina zagaye gidan a hankali, Allah ya ƙara lafiya.”
Ba ta ce da shi kanzil ba, sai nishi da take zufa na sauka a goshinta.
Rufaida ce ta amsa da amin, ya ciro ƙullin magani leda uku ya yi bayanin yadda za a yi amfani da su.
Miƙe wa ya yi, sai Rufaida da ke zaune tana yi wa Umma Lauratu fifita ta ce da shi, “Sannu, mun gode sosai, Ka tsimaye ni a kofar sauro.”
Ya amsa mata da ba damuwa.
Ta miƙe ta bi shi, bayan sun tsaya ta ce da shi, “Don Allah nawa za a ba ka?”
“Hajiya, mu ba ma yanke kuɗi duk abin da mutum ya bayar to Allah ya sa albarka.”
Ta ce da shi, "To shi kenan, ta zaro kuɗi ta ba shi ya yi godiya ya ce, “Don Allah maganin nan a yi shi bisa ƙa'ida kar a saɓa ko a ki yi.”
“In sha Allah za mu yi kamar yadda a ka buƙata.”
“ To Allah ya ba ta lafiya, Allah ya kiyaye gaba.” Ta amsa masa da amin ya sa kai ya fice.
“Rufaida ɗan ɗaga ni na jingina da bango.”
“To Umma.” Abin da ta amsa mata kenan ta tallafa mata ta jingina da bango.
ALIYU A GIDANSU MAIMUNATU
Aliyu zaune yake ya sunƙuyar da idanuwansa ƙasa domin jin abin da zai fito daga bakin surinkin shi.
“Aliyu ya kuma ƙarfin jiki?”
“Alhamdulillahi Abba.”
“Masha Allah, haka ake so, Allah ya sa kaffara ce.”
“Amin Abba.”
Gyarar murya ya yi, sannan ya sauke hular da ke bisa kansa ya ajeye a gefe, ya gutsire goro bayan ya taune ya ce, “Aliyu me kake shiryawa game da matarka?"
“Abba ni shawarar da na yanke shi ne; zan haƙura har Allah ya sauki Maimunat lafiya, bayan hidimar suna da kwanaki sai na ɗauki matata mu yi rayuwa a can. Amma ku a matsayin iyaye me kuke gani.”
Ya sauke ajiyar zuciya, “Hakan ya yi amma ina da sharaɗi.”
“Abba ina sauraronka.”
Abban Maimunat ya dubi Aliyu ya ce da shi “Aliyu na yarda da batunka na Maimunat ta haifu, amma ka sani dole ka karɓi Fatima a wajen mahaifiyarka ka ba wa Maimunat ta riƙe ɗiyarta idan za ku tare.”
Wayar Abban Maimunat ne ya fara ruri da ya duba ya ga mai kiran ya ce da Aliyu, “Yi hakuri bari na amsa waya.” Ya fice.
“Tirƙashi!” Abin da Aliyu ya ce kenan, ya kuma cewa, “Anya Mama za ta amince na karɓi Teema na ce da ita zan kai ta wurin mahaifiyarta?”
Zufan da ke goshin sha ya goge da handikcheif ya fara tuna yadda suka yi da mahaifiyarsa akan Teema sa'ilin da ya saki matarsa.
Teema yarinya ce da shekarunta ba za su haura huɗu ba, sanye take da uniform na makaranta a jikinta ta ce, “Daddy ina Mummyna ne? Tun da na dawo fa ban gan ta ba.”
Aliyu a tsugunne yake yana haɗa wa Teema kayanta a 'yar ƙaramar akwati ya ce, “Mummynki ta je unguwa, matso na cire miki uniform naki sai na kai ki wurin ta.”
Tana jin za a fita ta fara tsallen daɗi.
Mama dama tun da ta ji shigowar Aliyu tare da Teema bayan ya ɗauko ta a makaranta suna shiga sashinsu ta bi bayansu ta raƙaɓe domin sauraron abin da za a ce.
Buɗe labulen ta yi ta shigo kai tsaye ba sallama tana cewa, “Ba inda za ka kai Fatima ni ce nan zan riƙe jikata, ka kai yarinya kullum tana jera maka matsaloli ta tsiyatar da kai ba, to karyanta, cikin da ke jikinta ma tana haifa idan aka yanke cibiya su ba ni zan raine shi.”
Cike da kaɗuwa da razana bisa furucin Mama ya dube ta yana ƙoƙarin motsa laɓɓansa da ya yi masa nauyi ta ce:
“Rufe mini baki ka ji na rantse Fatima ba za ta taɓa zama a hannun matsiyaciyar matarka ba muddin ina numfashi.”
Ta suri Teema, ita ko Teema tana zamewa tana cewa, “Ni ki bar ni na tafi wurin Daddyna ya kai ni wurin Mummyna”
“Wurin uwar Mummynki za a kai ki ba wurin Mummy ba.”
Teema dai sai fizge wa take ala dole sai ta sauka.
“Ke yarinyar nan ban son shegantaka yanzu sai na yi ƙasa-ƙasa da ke.”
Ta ɗauke ta caɗak ta nufi sashinta da ita.
Aliyu haɗa kai da guiwa ya yi na taƙaici.
“Aliyu! Aliyu!! Kai Aliyu tunanin me kake ne haka? Na yi sallama shiru, na zo na zauna na kai daƙiƙa ɗaya ina zaune a gabanka amma ba ka sani ba.” cewar Abban Maimunatu
Firgigit ya yi ya ce, “Abba, na zurfafa da tunanin wani abokina ne, da muke aiki a wuri ɗaya jiya ya rasu sudden death, muna hira fa ya ce kan shi na ciwo, a ka ba shi paracetamol ya sha, ya dafa kan shi a table muna ta hirarmu baya tankawa da muka tashi tafiya, na taɓa shi ina cewa Bello ciwon kan ne har yanzu, shiru, da na girgiza shi, shi ke nan sai ga shi wanwar a ƙasa babu rai ya yi halinsa, to wannan mutuwar ke tsuma ni ke sani tunani.”
Abban Maimunatu ya jinjina kai, “Allah sarki, Allah ya ji ƙansa, mutuwar da ake kenan yanzu sudden deaths Allah dai ya kyautata ƙarshenmu, dole mutuwar ta tsuma ka.”
Ya amsa masa da amin yana sosa ƙeyarsa.
Abban Maimunat ya ce, “Ina sauraron amsarka.”
Shiru ya yi da ba zai wuce second biyar ba ya ce, “Ba damuwa Abba wannan mai sauƙi ne.”
“To shi ke nan Aliyu, Allah dai ya yi maka albarka.”
Ya amsa da amin ya yi godiya ya fice.
Bayan ya shiga motar shi ya zauna ya dafa sitiyarin yana cewa, “Na amsa wa Abba buƙatar shi alhalin ba ni da tabbacin yiwuwar hakan. To idan ma hakan ya tabbata wataran idan Mama ta ce za ta zo ta ga jikarta idan ba ta ga jikar ba ya kenan?"
Wani sashi na zuciyarsa ta ce da shi, "Mahaifiyarka yadda take ji da kanta sai dai ta ce a kawo mata 'yar ba dai ita taka ta je ba." Tagumi ya yi, "Shin Abba yana nufin idan har ban cika wannan sharaɗin ba zai iya warware abin da muka tsaya a kai? Ina sam ba zai yiwu ba, Maimunat sai ta dawo gare ni rayuwa babu ita tamƙar raba hanta da jini ne.”
Ɗago fuskarsa ya yi yana jinjina wa lamarin ya ja motar shi ya yi gaba.