Free chapter · Read without an account
5~6
by Khadija · D'A NA KOWA NE
ƊA NA KOWA NE
(RAYUWAR SAMHA)
MALLAKAR...
Mmn Amatullah (Sarauniyar Jarumai👑)
JARUMAI WRITERS ASSOCIATION💪🏻📚
FALYAKUL KHAIRAN AULIYASMUT🙊
Tallah! Tallah!! Tallah!!!
TAURARI BIYU MASU HASKE✨✨
Albishirinku masoya littafan Haziƙar Marubuciyar nan MAMAN AMATULLAH dana Fasihiyar nan wato KYAUTA DAGA ALLAH wa innan taurari biyun sun shirya tsaf domin nishaɗantar da masoyansu da daddaɗan littafinsu mai suna KAICO! Labari ne mai ɗauke sa kiyayya soyayya yana ɗauke da ƙalubale na rayuwa yana tafe da tarin darissa na rayuwa ku biyomu 30 ga watan September akan kuɗi naira 300 kacal👌🏻 domin neman ƙarin bayani ku tun tuɓemu ta wa ɗannan lambobin *** ko ***
Tallah!
Inakuke masu San burge maza jensu Ina Me son ta Zama ƴar lelen mijinta kuma ƴar gaban goshi, to maza ku garzo ga kayan mata ƴan SOKOTO na musamman muna siyar da ɗaya muna bayar da sari, sannan muna da maganin sanyi sadidan karfa ki manta sanyi mugun ciwo ne duk gyaranki idan kina ɗauke da sanyi to barin gyaran shi yafi dominkuwa baze yi miki amfaniba domin Neman ƙarin bayani ku tun tuɓi wannan lambar ***..
Shafi na 5~6
Haka Rayuwar Samha tacigaba da tafiya babu wani sauyi daga mari sai ma abin da ya yi gaba..
Kamar kowanne lokaci Samha zaune a gaban mahaifinta tana ɗaukan darasi dayake bata da wani Malami sama da mahaifinta,tin daga kan Alkur'ani mai girma zuwa su hadis fikihu tauheed nahawu,mandiq da dai sairan littattafai na addini duk mahaifinta ke biya mata...
Sannan duk da halin da take fiskanta a gidan hakan besa tayi wasaba gurin ɗaukan abin da yake koya mata zuwa yan zu samha,ta sauke Alkur'ani,da wasu lattattafai masu dama...
Dubanta ya yi,sosai tare da cewa,, "ƴar baba ina Alfahari dake a rayuwa sabi da jajircewarki,da haƙurinki,,kicigaba da yinsu dan zasu amfaneki,arayuwar ki ta nan gaba,ƴar baba zankuma faɗa miki,abin da kullum nake faɗa miki,kiyita haƙuri da innarku duk da nasan kinayi,sannan tin da kika taso,agidannan baki taɓa,jin daɗin zama da itaba,to kisa a ranki komai mai wucewa ne watarana sai labari.Dan inaji ajikina za ki samu rayuwa mai kyau a nan gaba har ki zama abin Alfahari gakowa.Sannan kicigaba da yimata biyayya kamar yan da kikeyi,mata karki fasa kinji ƴar baba" ya ƙarasa maganar yana shafa sumar kanta kai ta ɗaga tare da faɗin "To Babana insha Allah zanyi duk abin da kace".
"Yawwa ƴar Albarka Allah ya Albarkaci rayuwarki" "amin babana"
"Yanzu maza tashi kije,kici abinci,ki kwanta sai da safe" da to ta amsa tare da yimasa sai da safe.
*Bayan wasu kwanaki*
Samha zaune tana wanke-wanke wan da taɗauki kusan Awa ɗaya tanayinsa,sakamakon,dawo mata dasu da akeyi da gan-gan,sabi da tsabar mugunta Maryam ce ta sake dawowa hannun ta ɗauke da ƙoƙuna da ludai,ko da ta ƙaraso mai makon ta ajiye sai ta jefawa,samha cikin rashin sa'a ta kwaɗa mata a goshi,sakin soson hannun ta tayi tare da saurin dafe wani a zababban zafi ne yaratsata kai ta ɗago ta dubi Maryam, sake mayar da kanta ƙasa tayi batare da tace komaiba ta cigaba da abin da takeyi..
Sabi da tasan gara tayi shiru da dai ta tanka,dan tasan me zai biyo baya,,dan duk wata rashin kunya da Sadi da Maryan suke mata,bata tankamusu,sabi da gudun abin da ze biyo baya...
Hakan yabawa Maryam da Sadi dama suka rainata,tamkar ba itace gaba da suba..
Ganin tayi shiru ne yasa maryam ta kwashe da dariya tare da cewa "Da kitanka mana,dakinga yan da zan had'amiki sharrin da inna sai tayi miki dan banzan duka a gidannan"
Itadai SAMHA ko Ƙala bata ceba..
Sam idan sunayi mata Abu bata tanka musu amma duk da haka wani lokacin bata tsira..
Kamar DG sama,sukaji muryar Babayana cewa "Ashe ke Maryam bakyajin magana ko wannan ba yayar ki bace,ko bance karna sake ganin ko jin wan da ya yi mata rashin kunyaba?...
Jiki narawa Maryam,tace "wallahi baba banyi mata komaiba" wata gigitatciyar tsawa ya daka mata,tare da cewa,me ki ka mayar dani iyi,yarinya ƙanƙanuwa dake kin iya ƙarya,to duk abin da kikayi a kan idona kikayi mata" kara ya ɗauko tare da cewa "zonan"
Tini jikin maryam y fara rawa,,hawaye suka fara zarya a kumatunta,haƙuri ta fara basa "Baba kayi haƙuri wallahi ba zan sakeba" ta kai ƙarshen maganar tana ƙara fashewa da kuka,karan ya ɗaga kamar zai zuba mata,wata razananniyar ƙara ta saki tare da cewa "Dan Allah Baba kayi. haƙuri wallahi nadena"
"To naji idan kika karafa? "
"Wallahi Baba kazaneni" "Tom naji na haƙura yanzu maza jeki ki bata haƙuri"
Karar da maryam tayice ta tayar da inna mari daga baccin da takeyi agigice tafito,,tana tambayar lafiya,ganin maryam tayi durkushe tana bawa samha haƙuri,in da Malam habu ketsaye da kara ta duba tare da cewa "Haba Malamya za ka kama yarinya da duka da wannan danyan karan" ta kai ƙarshen maganar tana hura hanci wai ita masu ƴan..
Duban ta ya yi tare da cewa "Akanme za kizo ki titsiyeni,akan ina gyara tarbiyar yarana to banason haka idan za ki iya saka ido ki kalla to ki saka idankuma baza ki iya ba to ki koma ta in da ki ka fito" ya ƙarasa maganar yana nuna mata ƙofa.
Cikin hasala tace "Eh ai dama kafaɗi haka mana tin da antaɓa ƴar gwal to gaskiya ni bazan ɗauki wannan rashin Adalcin da ka ke yiba" ta kai ƙarshen maganar tana turo ɗan kwalinta gaban goshi.
Baki sake Malam Habu yake kallonta wai kokunya Mari da kanta take faɗar haka, kafin yace "ke yanzu abin da kikeyiwa samha a gidannan adalcine ko akasin haka? ko dan ita bakece kika haifeta ba? to bari kiji n faɗa miki zan kuma mai-mai ta abin da ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba,nasha faɗa,daga yau karna sake gani ko jin yarannan sunayiwa samha rashin kunya,,idan kuma na sake gani ko ji to rai zebaci,na faɗa miki"..
Yana kaiwanan,,ya wuce ya barta nan tsaye..Sake da baki..
In da samha ke zaune ta kalla tare dazabga mata wata uwar harara,,tare dayin kwafa t hannun maryam takama sukayi ɗaki,nan sukabar samha,tana cigaba da sharar kwalla tare da tausayawa rayuwar ta.
Maryam da sadi sune yaran mari,wan da duka duka shekarun maryam bewuce 10 baamma idan kunga irin abin da takeyi zakuyi mamaki haka sadi me shekaru,7,,duk inna mari ta ɓatasu da rashin kunya kala kala,sai dai FATAN shiriya....
INNALLAHA'MAH'ASSABIRIN☺
Wani matashin,saurayi ne,yake tako matattakalar benan sannu a hankali yake saukowa kai kace,yana tausayin step's ɗin ne matashin saurayi na wan da shekarunsa basuwuce 21zuwa22 ba sanye yake cikin kananan kaya wa in da sukayi matukar karɓar jikinsa,kai kace dan shi akayi su,kannan nasa kuwa yasha gyara,
Ahankali ya ƙaraso cikin palon bakinsa ɗauke da sallama, wata matashiyar mata ce ta amas ,Dan bana kirata da dattijuwaba,Dan shekarunta bazasu wuce 37zuwa38 ba..
Fuskarta ɗauke da murmushi,take kallonsa kamar yan da shima yake kallonta cike da so.
Kafin tace "my son,harkafito yau da wuri haka? ta ƙarasa maganar ta sigar tambaya tare da mayar da hankalinta kansa, har ƙasa ya durkusa ya gaisheta, tare da cewa "Wallahi Mama,yau jinayi gaba ɗaya nagaji da baccin shiyasa nafito dan nasan dama kina zaune ke kadai babu abokin fira..Dan nasan war Abba yajima da fita" ya ƙarasa maganar yana zama a gefenta duban sa tayi fuskarta ɗauke da annuri ta ce "To yazanyi my son ai har na saba idan katafi makaranta,abbanka yafita kaga abokin firata" tafaɗa tana nuna masa Alkur'ani mai garma,dake ajiye a gefenta ,murmushi ya yi wan da yaƙara bayyanar da ainishin kyawunsa..
Kafin yace "To yau kina da abokin fira,Dan yau babu in da zanje,,ina tare da mama na" ,yakarasa maganar yana kwantar da kansah,a gefen kafadarta dubansa tayi tare da cewa,, "katayani fira kokuwa,ka isheni da shagwaba,kamarwani yaron goye,,yanzu daga zuwanka,zakafara daddanneni,da wannan kannaka"
Cike da shagwaba yake kallonta,tare da cewa,,to mama idan banyi mikiba towa zanyiwa Kuma ina kaina yake da nauyi,ai da yana da nauyi,da bazan dorawa mamana ba dan banaso ta wahala"
Yakarasah maganar yana dry itama dariya'r tayi,,tare da cewa "wayafada maka haka cewa wannan kan babu nauyi" taƙarasa maganar cike da zolaya
"Kai mama dan Allah kidena cewa haka,yan da ya yi maganar kamar wanj ƙarami yaro,yanaso,yayi kuka "Dubarkafa kai kokunya bakaji,,,kadinga shagwaba kamarwani boy".
"To ai boy ɗin ne a wajan mama na"..
Yan da suke raha,tsakanin uwa da ɗanta,abin gwanin birgewa..
"Yawwa mama,yakukayi da Abba akan maganar tafiyar da zamuyi? "Ai tini mungama magana,amma ni,sai nake ganin da zaka haƙura,da maganar tafiyannan,,Dan duk na tuno da tafiyar nan sai naji gabana ya faɗi,sai nake ganin da ka haƙura"
Zamansa ya gyara sosai,tare da kamo hannunta ya riƙe kafin yace "Haba Mama dan Allah kikwantar da hankalinki,,insha Allah babu abin da zai faru,,Addu'arki ka ɗai nake,bukata..Mama, kinsan,dai yan da nake,da saddiq,,basai na fada ba,duk da saddiq yagirmeni,,amma muna da kyakkyawar alaka,atsakaninmu...Ayan da Mike da shi ace aurensa ya tashi amma naki zuwa,,kumah lpia'ta kalau,,ai kinga ban kyautaba..Mama nasan baza ki manta da irin dawainiyar da saddiq ya yi ba lokacin da aka,kwantar da Abba a Asibiti"
Hmmm,nisawa tayi tare da cewa, "kwarai ba zan ta ɓa manta wannan lokacin ba da kuma irin temakon da ya yi mana to shikenan Allah y kaiku lafiya ya dawo daku lafiya" "amin mama na harkinsah naji dadi"
Dariya tayi tare da cewa "Yaushene tafiyarnn?
"Sai wani sati" ya bata amsa ",to Allah ya nuna mana" "Amin mama na
" Amma dai ba zaku da ɗeba dan kasan bazan iya dadewa banga boy ɗina ba",,
Dariya ya yi,tare da cewa "Insha Allah kwana 2 kachal zamuyi,,nima bakaramin missing ɗinku zanyiba ,ke da Abba dan wannan itace tafiyata tafarko wacce zanyi batare da Kuban...Amma mama karki damu ,ai gawaya,zamu dinga gaisawa" "To ai shikenan,amma jirgi zakubi,ko? "Aa mama mota,zamubi kinsan tafiyar bata mutin 1 bace kuma a cikinmu a kwai wa'in da basu da ƙarfin biyan titin sama ba shi yasa gara mubi mota,,duk dayane"
"To hakanma yana da kyau,,fatana dai,Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, ya kaɗe. Dukkan wata fitina ta hanya",
Ya amsa da "Amin mamana...
Comments
Share
UMMU AMSAD CE😍