Free chapter · Read without an account

Trailer I

by Azizat Hamza · SAHLA a Paris

TOP -NOTCH ....the touch of excellence, just for you

Trailer! Trailer! Trailer!

"Bad luck! Bad luck! Bad luck everywhere Sahla"

Shhhh

"Ba ki da sa'a ko kaɗan a rayuwarki Sahla"


"Dan Allah kar ku bari Sahla ta shiga min kitchen dan na san tana shiga yau abincin gidan nan ba zai ciwu ba"


Hmm

"Ni fa ko addu'a na yi sai dai a samu akasin abinda na tambaya. Kar ku ce ina da raunin imani fa, kawai dai abinda na lura shine wasu rayuwarsu yadda take tafiya tamkar su suka ɗau alƙalami suka rubuta ƙaddarar rayuwarsu, komai sai ka ga ya tafi daidai da jin daɗinsu. Amma irinsu Sahla kam tamkar da ƙafar hagu suka faɗo duniya"


***


Wato sha'anin Bature sai a hankali. In dai batun soyayya da kare ne sai dai a shafa musu Fatiha kawai. To ma ni miye ruwana tunda kuɗi ake biyana.

Amma Allah ya isan talauci. Karen Mrs Julie fa abinda yake ci a kuɗin Nigeria a kullum ya kai naira dubu ɗari biyu da hamsin. Wani shegen kwayyane, au kwainane. Mtsw kwaimane, kai dole sai na yi Hausa ne ma. Nan fa Paris ne, Babban birnin ƙasar Faransa. To ni Sahla idan ban yi Hausa ba Uban me na iya a yaren farasancin? Na san dai Mrs Julie na yawan cewa karanta Le mo ( L'amour)


Shi kuma Mr Dodo idan yana faransanci ba ji nake ba, kallon bakinsa nake da hanci dan gani nake shaƙewa zai yi, ina ankare inji ya shaƙe na kawo masa ruwa.


Aff! Kar ku gaya masa ina kiransa da Mr Dodo fa. Dan Wallahi idan ya ji labari Nigeria zai mai da ni. Duka-duka yaushe na zo Paris ɗinma balle ace za a maidani wata ƙasa wai Nigeria, a'a Lanjeria. Walle ni da Lanjeria sai dai a mafarki. Taɓ! Irin azabar da na sha a Lanjeria.


Ai, ashe ina maganar karen Mrs Julie ne ko? Barin faɗa muku gaskiya ba kare ɗaya nake kula da shi ba. A sati sau uku zan kwashi karnuka guda biyar na tafi yawo da su na tsawon awa biyu, sannan na dawo da su gida. Amma shegen karen Mrs Julie ne ya fi bani haushi, matar nan har wanka take masa a cikin bath tube ɗin ta. Ni wa ya sani ma ko auren karen ta yi tunda mun sha jin labarin Bature na auren kare, ko kuma ya barwa kare gado, shiyasa na ce muku al'amarin Bature mai jan kunne da kare sai dai a shafa Fatiha.


To dai sunan Karen Mrs Julie Sky, eh nace Sky kamar sararin samaniya kenan da Hausa. Amma kun san me? Wallahi Titiɓiri na ke kiransa idan na fita da shi park.

Sauran karnukan ma duk na chanja musu suna daga Bingo, Kubuwa, Sakadale ( karen yana da tudun mazauna. Opps, Allah ya shiryeki Sahla)

Ta ƙarshen wata 'yar ficila da ita wai sunanta Princess amma Tsillirilli na saka mata.


Na ga sai wani hararana kuke, wai na baro Lanjeria na zo Paris ina aikin Dog walking. To kun sanni ne? Kun san ma daga ina na fito ne? A 'a haka kawai kuna wani ƙananan maganganu a kaina saboda tsabar gulma da tsugudidi. To in gulmar kuke so ku biyo bayan Topnotch writers mana, sai na ji daɗin baku labarina da dalili.


Aisha Faridan Sir Najib tana gaishe ku (Sakatariya ta)


Asiya Shahidar Gwamna SS Kachallah ma tace kar ku manta ku bibiyi marubutan Top-Notch (Matar Gwamna)


Zaytoonan Justice Yunus-Zannoon ma ta ce ku bi Sahla a Paris, kar ayi ban da ku (Chronicles of Zaitoonah)


Coming soon...


Littattafan Top-Notch za su faso a October 2022 Insha Allah


Abinda ya baka tsoro - Mai_dambu


Bani da laifi- Shatuu


Sahla a Paris- Azi_zat


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.