Free chapter · Read without an account
7~8
by Khadija · D'A NA KOWA NE
ƊA NA KOWA NE
[RAYUWAR SAMHA]
MALLAKAR..
Maman Amatullah(Sarauniyar Jarumai👑)
JARUMAI WRITERS ASSOCIATION💪🏻📚
YA HAYYU YA ƘAYYUM.
Tallah! Tallah!! Tallah!!!
TAURARI BIYU MASU HASKE✨✨
Albishirinku masoya littafan Haziƙar Marubuciyar nan MAMAN AMATULLAH dana Fasihiyar nan wato KYAUTA DAGA ALLAH wa innan taurari biyun sun shirya tsaf domin nishaɗantar da masoyansu da daddaɗan littafinsu mai suna KAICO! Labari ne mai ɗauke sa kiyayya soyayya yana ɗauke da ƙalubale na rayuwa yana tafe da tarin darissa na rayuwa ku biyomu 30 ga watan September akan kuɗi naira 300 kacal👌🏻 domin neman ƙarin bayani ku tun tuɓemu ta wa ɗannan lambobin *** ko ***
Tallah!
Inakuke masu San burge maza jensu Ina Me son ta Zama ƴar lelen mijinta kuma ƴar gaban goshi, to maza ku garzo ga kayan mata ƴan SOKOTO na musamman muna siyar da ɗaya muna bayar da sari, sannan muna da maganin sanyi sadidan karfa ki manta sanyi mugun ciwo ne duk gyaranki idan kina ɗauke da sanyi to barin gyaran shi yafi dominkuwa baze yi miki amfaniba domin Neman ƙarin bayani ku tun tuɓi wannan lambar ***..
SHAFI NA 7~8
*WANENE FARUQ??*
FARUQ ALIYU AHMAD,shine cikakken sunansa wan da akafi sa ni da (AA Faruq) ɗa ne guda ɗaya tillo agurin Alhaja Aliyu wato Abba da Hajiya Maryam (Mama) su na zaune a cikin garin gwambe.
FARUƘ kyakkyawa ne ajin farko, ya haɗu ta ko ina.
Alhaji Aliyu, shararran ɗan kasuwa ne,wan da ya yi suna sosai ajahohin dake ƙasar nan har ma da ƙasashen da ke maƙotaka dasu, Alhaji Aliyu ya tara abin duniya fiye da yan da ku ke tinani..
Sai dai duk yawan tarin dukiyarsa ɗa ɗaya Allah ya azurtashi da
shi ɗan da yataso cikin so da ƙauna daga iyayen sa.
Amma duk da irin son da suke nuna masa hakan besa,sun kasa ba shi tarbiya mai kyauba..
FARUQ ya samu,tarbiya mai kyau daga mahaifansa duk da cewar FARUQ ya taso cikin arziki,da wadata hakan besa ya kyamaci talakaba,sai ma son mutane da yake da shi,ga girmama manya Sam baya raina na sama da shi kokuma dan kai talaka ne ya kyamaceka FARUQ ga sakin fuska tare da faran-faran da muta ne. duk da hakan ya samo asaline daga irin tarbiyar da yasamu daga gida..
FARUQ yana da kyakkyawar Alaƙa da muta ne kowa nasa ne duk da ƙarancin shekarunsa, amman yana da alaƙa da mutane daban-daban sabi kyakkyawan halinsa.
Zuwa yanzu FARUQ yana level 1 a university, in da yake karanta business dan yana da burin ya tallafawa mahaifinsa a kan harkokin kasuwancinsa.
Haka ɓangaran ilimin addini,nan ma FARUQ ba'a barshi a baya ba dan yana da hadda akansa sannan ya haddace,littattafai da dama..
*CIGABAN LABARI*
Amatukar gigice ta tashi tana,"yan dube-dube ba komai yasa ta hakan ba sai saukar ruwa mai sanyi da taji ajikinta tana tsaka da bacci gashi dama yau suntashi da muku mukun sanyi
Kamar daga sama tatsinkayi muryar Inna mari tana cewa "Nicenan dan ubanki,wato sabi da tsabagen kin raina mutane shine kikazo nan ki ka naɗe kina bacci to uban waye zaiyi miki,duk wancan aikin gidan?
"To wallahi karki sake na rigaki fita daga ɗakinnan,idan kuma ba haka ba to wallahi jikin ki ya fada miki Shegiya mai mugun hali"
Cikin kuka mai ban tausayin,samha,,tace "Dan Allah inna kiyi haƙuri kibarni na sake kaya kinga sanyi ake" ta ƙarasa maganar cikin rawar murya.
Baki Inna mari ta dafe tare da cewa "Iyeeee to uwata,, kinsan Allah ko za ki mutu sabi da sanyi baza ki canza kayaba haka za ki fita za ki wuce ko sai na kwaɗa miki mari,shashasha"...
Haka samha tanaji tana gani tafita ,tana ɗigan ruwa gawasu hawaye masu zafi da suke bin kuncinta wani nabin wani ,azuciyarta,kuma tana addu'ar Allah ya kawo mata karshen,wannan rayuwa da take ciki, mai cike da ƙunci..
Tana rawar sanyi hak'oranta nakaro da juna,, sabi da tsananin sanyin da takeji haka ta fara aikace ai kace,,har kayan suka bushe a jikinta,,,
kafin tagama zazzabi mai zaifu ya rufeta..
In da agefen mari,tana ɗaki ita da yaranta ta kaimusu,garwashi sunajin ,ɗumi,suna shan kokon safe..
Cike sa ƙarfin hali take ta aikin sakamakon matsanancin zazzaɓin da ya rufeta...Amma zuwa yanzu tana ganin juriyarta tazo karshe,dan ita kaɗai tasan irin yunwar da takeji,ga zazzabin ya kara rufeta,fiye da ɗazu dan har wani duhu-duhu,ta fara gani..
Adaddafe ta nufi ɗakin innah mari sallama tayi, cikin wata iriyar murya wacce mai sauraro daga yajita ya san me ita ba kalau yake ba.
Cikin fada inna mari tace "Lafiya ki kazo kina cikamin kunne da sallamar muna furci" cikin rawar murya samha,tace "inna Dan Allah kisammin kokon,ko babu yawa nasha wallahi jinake kamar zan faɗi" ya ƙarasa maganar tana lumshe ido "inye samun guri waima in tambayeki kingama aikin da na sakaki?
Kai ta girgiza tare da cewa "Wallahi inna zanyi idan na karya" "Eh lallai wuyanki ya isa yanka to bari kiji yau ko mutuwa za kiyi,sai kingama duk wani aiki da na sakaki sannan za ki karya kinji na faɗa miki, Za ki wuce ki bani guri ko saina ,kwaɗa miki mari" Ta ƙarasa maganar tana huci..
Samha baiwar Allah babu yan da ta iya haka taja ƙafafunta,tabar gurin,tana ganin,duhu yana yimata,yawo..
Tana zuwa tsakar,gida jiri ya ɗebeta,jikake ta faɗi yeeff,,nan take numfashinta,ya tsaya chakkk...
Cike da matsanancin tashin hankali,mlm habu da ke shigowa gidan yanzu ya ƙaraso in da take,kwance da sauri yasa hannu ya ɗa gota,, yana kwala mata kira,,ƴar baba ƴar Baba amma Sam ko alamun tamotsa babu,,
Jiki,na rawa ya ɗauketa ya nufi ɗakinta da ita kwantar da ita ya yi gaba ɗaya ya ruɗe ya ma rasa me,zeyisai faman,girgizata yake,cike da tashin hankali waje ya fita da sauri ruwa ya ɗebo ya dawo shafa mata ya farayi,yana cigaba da girgizata ciki, sa'a yamu ta fara nisawa
Wani Dogon numfashi taja da karfi Alhmdllh malam habu yake iya furtawa yana sauke ajiyar zuciya.
"Sannu ƴar baba me yake damunki inane yake yimiki,ciwo haka yake ta jero mata tambayoyi, ita kuwa ina bakin magana dan,bazata iya ba sai ido nuni tayi masa da hannu alamun sanyi takeji jiki na rawa ya ɗauko za ni ya lilliɓeta..Jikinta ya kara taɓawa yaji zafin ya haura,na ɗazu subahanallah! ya furta cike da damuwa kinci abinci kuwa? Ya tambayeta kai kawai ta iya girgiza masa, rai ɓace ya girgiza kai tare da ficewa..
Bewani jima baa ya dawo ɗauke da,madarar shanu wacce ya tatso, yanzu da ɗuminta ɗagota ya yi ya samata, 'ko'kon a bakinta,yan da takeshan madarar ,baƙaramin tau saya mata ya yiba kai da gani kasan tana cikin yinwa mai tsanani, kwallah ya share sabi da tsananin tausayawa.
Cikin murya mai cike da rauni yace "Ƴar baba kisha a hankali mana karki kwara,,idanma baki ƙoshiba ai sai na ƙaro miki" ya faɗa cikin murya mai rauni tas, ta shanye "Akaro" kai ta girgiza alamar Aa "To madallah kwanta ina zuwa ,mlm ya faɗa tare da ficewa,,
Kai tsaye ɗakinsa ya wuce,magani ya haɗa mata,,sannan ya dawo,ɗakinta bata ya yi tasha tare da cewa "Maza ki kwanta ki huta insha Allah kafin ki tashi zazzaɓin zesauka" ,kai ta daga tare da kwanciya gyara mata rufa ya yi,bata jima ba bacci ya ɗauketa ya jima zaune,yana kallonta yana kumah tausayawa rayuwarta ya zamah dole na kara saka ido akan rayuwar ta,sai da ya tabbatar baccinta ya yi nisah kafin ya fice ya nufi dakin mari,,rai bace,,
Tin kafin y karasa ya fara kwaɗa mata kira mari! mari!! mari!!! "Aa wai lafiya Malam ka ke kwaɗamin kira haka? ,wani mugun kallo ya watsa mata,,tare da cewa,"Au ke har tambayar lafiya ma kikeyi to bari,kiji na faɗa miki,abin da kikeyiwa yarin yar nan SAMHA yafara isahta,,kewai Dan Allah ko kunyar kishi da ƙan ƙanuwar yarinya ba kyaji wannan ai rashin hankaline da jahilci to bari kiji na faɗa miki daga yau karki kara hana ta abinci tin da dai bakece ki ke nemowaba ai kin gida da takeyi wannan bazan hanata ba,Dan nasan ze temaketa agaba,,ammah abin da bazan iya cigaba da ɗaukaba shine horon yunwa,da duka Sam,kisake tinani,a wannan gefen idan ba haka ba to zakiga abin da bakyaso kuma bakiyi tinani ba kinji na faɗa miki" ya ƙarasa maganar yana nunata da yatsa.
"Ai dama nasan,akan wannan ƴar takane kazo kawani rufeni da faɗa babu dama ayimata Abu kalilan sai kazo kaitawani kumfar baki,,to in dai akan wannan ne ni bani da lokacin ka",daga haka taja tsaki tare da shigewa daki,, ..
"Oh haka ki kace to muzuba ni dake,,,naga wan da ya'ajiye,wani tsakanin ni dake".
*Bayan sati ɗaya*
Alhmdllh SAMHA tasamu sauki sosai, har taci gaba da harkokinta,na yau da kullum,,
Malam Habu ya tsaya sosai a kan inna,zuwa yanzu SAMHA ta ɗan samu sauki,kaɗan dan ana bata, abinci a kanlokaci,sai dai bangaran hantara da kyara da duka babu abin da ya sauya sai dai shima batayi a gaban Malam habu,sai dai a bayan idonsa..
**************
"A'a wai har kafito kenan Abba ya tambaya "Eh wlh Abba na fito kasan tafiyar ta motace,,gara mutafi da wuri dan Adamawa da nisa," "Eh haka ne" ,nan faruƙ ya durkusa ya gaishesu,,,mama wacce tin da yafito batace 'kalaba sai yanzu tace "Amma ka zauna kakarya ko kafin katafi?
"Eh mama zansha ko Dan Ruwan lipton ne,dan kinsan bana iya cin abinci idan zanyi tafiya" "Haka ne" nan ya zauna yakarya,,yana gamawa wayansa ta fara ƙara,dubawa ya yi yaga abokan tafiyarsa ne suke kira..
"Tom Abba mama ni zanwuce dan harsun fara kirana ina ji sun,karaso,Addu'o'i sosai sukayi masa tare da fatan Alkairi cike da farin ciki yace "To ngd IYAYE nagari,ni natafi saiminyi waya",,
Har yakai bakin kofa ,mama takirasa,FARUQ,, sai da gabansa ya faɗi dan tin da yake da mamansa betaba ji ta kirasa da FARUQ ba,jiki a sanyaye yajuwo,,tare da amsawa "na'am mama,,ahankali ta tako har zuwa in da yake,hannunsa ta kamo tare,da cewa "FARUQ ɗina Allah yakaiku lafiya ya dawo daku lafiya, tafiyar nan ta kwana,2 amma sai nakejin kamar,mun rabu kenan" murmushi,ya yi wan da ya kara,bayyanar da ainihin kyawunsa ,,tare da cewa,,mamana ki kwantar da hankalinki,tafiya ai bamutuwaceba,kedai kawai kitayimin addu'a" "shikenan my son Allah ya dawo min da kai lafiya" "Amin" ya amsa,rungumarsa tayi sosai,,yana jin faɗuwar gaba maitsanani,Kiran da ake sake,yiwa wayansane yasa ta sakesa,tare da sake yimasa fatan Alkairi..
Fita ya yi yanajin,duk jikinsa ya yi sanyi jiyake inama,ba bikin saddiƙ ba ne,da ya fasa wannan tafiyar,ko Dan mamansa.
Yana fita da gudu ta faɗa jikin Abba tana kuka,,,cikin murya mai taushi,yace,"Haba maryam,,kiyi haƙuri mana tafiya ai ba mutuwa ce" cikin kuka tace, "Baza ka gane ba Alhaji ni kaɗai nasan yan da nakeji,,tin da yarannan ya tsiri tafiyar nan nakejin,kamar wani Abu yana shirin faruwa,,kullun cikin faɗuwar gaba nake daga natuna,zeyi tafiya,yanzu kuma,jinake kamar mun rabu kenan" takarasa maganar tana kara fashewa,,da kuka "kinga kiyi haƙuri,babu abin da zefaru da shi,insha Allah zedawo lafiya ki kwantar da hankalinki,,kiyita addu'a" da kyar Abba ya ɗan rarrasheta,har ta dan kwantar da hankalinta...
Tafiya suke, sunata fira, abinsu,,su 5 ne masu tafiyar,,2 agaba 3 abaya
Tafiya tayinisa sosai,dan zan iyacewa ma zuwa yanzu har sunshiga jahar Adamawa,dan Faisal ba daga bayaba yana taka motar sosai,,kai kace,sama, ze tashi,sannan tin da suka taho,sallah,ce kawai ta tsayar,dasu.
" Ya kamatafa mukira,saddiq ya ƙara yimana,kwatancen,gurin dan karmu,ɓata" "Eh,gaskiya ne,wannan, amma kabari,nina kirasa tin da kai kaga tuƙi,ka ke,karka,raba hankalika biyu saura sukace,maganarka,haka take.Jamil kar ya yi wasa da rayukanmu ga hanyar,naga tana da kwana sosai,ga manyan motoci,dariy a Faisal ya yi tare da cewa,, "Wallahi kun bani dariya amman,dai kunsan waye Faisal,in dai agurin sarrafa motane? "Eh munsani amma dai kabari, akirasa...
"Kunga dai ni ne nake tuki,to ni yakamata,kubari,na kira yana yimin kwatance,inabi" "kai ɗinnan akwai kafiya,tomunji kirasa" cewar,FARUQ, dariya Faisal ya yi tare da cewa,, yawwa kokufa...
Waya ya Ciro ya fara kiran, saddiq "kai ango gamu agarinsu Amarya,nan ya yi masa kwatancen in da suke a nan saddiq,ya yi masa nasa watan cen,in da zasu,je.Faisal yace "To ango mungode sai dai munkaraso" ",idan bakuganeba kuyi tambaya"
"OK"
Mai makon ya ajiye waya sai ya fara tsokanar ango nanfa fira, ta ɓarke. Manner ne yace kai "Malam,bafa awaki ka ɗaukoba,ya kamata ka ajiye wayannan ka kula da tukin ka"
Ai ina hankalin Faisal ya tafi gurin Fira ,kawai bai ankaraba,ya tsinci katuwar mota,,a gaban,su,gaba ɗaya salati,suka ɗauka shikuma Faisal,, ya shiga ƙokarin kauce mata,,,cikin rashin sa'a motar ta kwace masa tayi cikin daji,,,
Babu abin da ketashi a cikin,motar, sai salati,,sosai motar,,take Shiga,cikin daji,Faisal duk ya rude,ya kasa tsai da ita,
Bangaran,saddiq han Kali tashe,yake kiran,lafiya amman babu amsa dan duk yanajin abin da yake faruwa,,,
Wata katuwar bishi,motar, ta daka take motar ta koma da wuta...
Dai-dai lokacin,Mama ta d'auko,plet,tana kokarin fitowa daga kitchen,jitayi,gabanta ya yi wani,mummunan faɗuwa wan da yasata sakin,plet,ɗin ya tar watse,hannu bibbiyu tasa ta dafe kirjinta tana.....
Comments
Share plz
UMMU AMSAD CE😍