Free chapter · Read without an account
Chapter 24
🅿️_24
Ba k'aramun Hauka Ammi tayiba Wanda gaba daya gidan ya harmutse masu jimami nayi masu dariya nayi kasancewar har lokacin gidan a cike yake da yan biki , Babu shiri aka sanarma da Abee halin da ake ciki ,aikuwa bai 'bata lokaci ba sai gashi ya bayyana a gidan , nan take ya sa aka kiramashi Ammi da wasu daga cikin yan uwanta , yasa akayi Kiran Inna da Abba sai sauran matanshi , Fada yarink'ayi sosai Kamar zai Ari baki kamun yakare dayi masu kashedi , ya dubi Yayyun Ammi Wanda sun kasance uwa 'Daya uba 'Daya ,yace " wallahi kuzama shaida duk lokacin da ta yarda ta kashe auren 'Yar ta to abakin aurenta!! Sannan itama safiyar sai ta nema Mata wani uban Amma wallahi ba a gidan nan ba kinji na gayamaki za'bi ya rage naku ,
Kallonshi yamaida ga Umma datake raku'be duk tayi sanyi kamar ba itaba , yace kema inaso kisani wallahi duk kika kuskura kikayi sanadin da naki yaran sukak'i zaman aure wallahi kema abakin aurenki sannan suma bazasu zaunamun a gida ba.haka kawai bazaku mayar Dani wani mutumin banza ba , Allah ya tamakeni nasamu na aurar dasu to wallahi in suka balle auren ba'a gidana ba kunji na gaya maku , daga haka ya tashi ya bar falon Abba ma tashi yayi yabar wajan don haushin su yakeji sosai akan yadda suke d'agama Dan uwanshi hankali , Sam sun hanashi sukuni kullum da sabuwar fitinar da suke tsirowa ,shiyasa Sam baya sha'awar Tara Mata da yawa wallahi mace d'aya ta isheshi rayuwa ,
Sosai yan uwan Ammi suka lalla'bata tare da Bata baki , itama tuni jikinta yayi sanyi jin hukuncin da Abee ya yanke masu ,inya saketa ai tashiga ukku iyayenta sunjima da rasuwa sai 'yan uwa wad'anda da yawansu ba wani shiri take dasu ba saboda ita idan bakada kudi Sam Bata kallonka da gashi , Haka doli ba yadda ta iya ta Kira safiya wadda har lokacin kuka take ta rink'a Bata baki bayan ta gayamata hukuncin da Abee ya yanke ,
*Agurguje*😏
Haka rayuwarsu taci gaba da tafiya da dadi ba badi , Saudat tanashan wahalar Salim sosai don duk lokacin Da ya shawo kwayarshi haka zai kamata ya jibgeta Kamar yasamu jaka haka nan take hakuri dashi saboda yadda take matukar kaunarshi , yanzu yaransu biyu Mata Ihsan da Salima
Anty Harira kuwa kullum acikin matsin kishiyoyi take ga uban Gori da suke Mata ga shi haihuwa shiru tun Bata damuwa har tazo tafara damuwa ganin yan uwanta duk sun haihu Amma ita Babu wani labari nan suka shiga yawon asibiti duk inda sukaje maganar Daya ce cewa k'wayoyin Hana haihuwa da tarinka amfani dasu Babu k'aIda ya lalata Mata mahaifa ita da haihuwa saidai wani ikon Allah kawai , tashiga damuwa da tashin hankali sosai , sauk'in ta 'Daya mijinta na sonta sosai yake tausayinta kullum cikin kwantar Mata da hankali yake akan tayi hakuri ai haihuwa ta Allah ce ,
Safiya kuwa kullum cikin tashin hankali suke da miji saboda yadda take fama dashi akan yan matanshi , har yanzu halinshi Yana nan na shegiyar k'aryar tsiya da nuna shi wanine ahaka yan Mata keta Kara kaina akanshi idan suna zaune ak'alla ya amsa Kiran mace 4 ko 5 ba dare ba Rana wannan yasa kullum suke cikin fada da tashin hankali yanzu haihuwar safiya Daya Dan ta namiji Mai suna Sulaiman ,
_____________________
Wash Allah wallahi nagaji aka fad'a cikin wata daddadar murya Mai cike da sanyi da nutsuwa , *Huzna* kenan kefa muguwar raguwa ce wannan yar tafiyar ne kika gaji , k'yaleta Husna dad'i ne yamata yawa Abee yariga ya sangartata da yawa shiyasa take ta'bara yanda taga dama, dariya Huzna tayi tace to 'yan bak'in ciki kanku akeji dai ,
Tafiya sukeyi cike da aji da wata irin yanga Kamar bazasu taka k'asa ba ,kallo d'aya idan ka masu zakaji sun bala'in tafiya da imaninka , mace ma burgeta suke bare Kuma namiji , abunda zai Kara baka mamaki dadu shine tsananin Kamar da sukeyi su ukku kamar su Daya Sam idan ba Wanda yasani ba zai dauka sud'in yan ukku ne sanye suke da uniform din makarantarsu sky blue Wanda yak'ara fito da asalin kyansu , duk da suna sanye da hijab hakan bai Hana ganin shape dinsu ba da yadda hips dinsu ya bayyana cif-cif gwanin sha'awa , gasu da cikar k'irji kowace kamar ita tayi kanta , Huzna tana sanye da wani siririn farin glass Wanda yak'ara fito da sirrin kyaun fuskarta , rike suke da wasu littafai zasu shiga aji kasancewar suna kan zana jarabawarsu ta karshe ne ,
Kaikaikai Brother kaga wasu masu zafi , yafad'a Yana cire bak'in glass din fuskarshi yayinda ya saki baki da hanci Yana k'are masu kallo , gefenshi wani had'ad'd'en guy ne zaune akan wata arniyar mota Wanda ga dukkan alamu da shi wannan Mai maganar yake , ko kallon Mai maganar baiyi ba haka zalika Kuma bai tankamashi ba sai faman duba wasu takardu yake ,
Kallonshi na tsayen yayi yace "wallahi Brother in baka ga wadan nan kyawawan babys din ba to anbarka a baya wallahi ko shakka banayi in ka Gansu doli ka za'ba aciki , don irin kalar matan da kakeso ne , Kai nifa wallahi harma narasa wadda Zan za'ba maka aciki , don wadan nan zafafan sai Kai nikam sunfi k'arfina ,
Wani tsadadden murmushine ya su'bucewa guy d'in jin bayanin Sa'id , yarasa wane irin mutum ne da Sam baya gajiya da surutu , d'agowa yayi da nufin yiwa Sa'id magana ......charaf idanunshi suka fad'a kansu , zaro ido yayi da sauri Yana k'are masu kallo jikinshi har rawa yakeyi , wani irin rud'ani ya shiga lokaci d'aya yafara fad'in " itace wallahi itace wadda nake baku labari Sa'id , Amma ya akayi ta koma mun ukku kodai ido nane ke mun gizo Yana maganar cikin sauri da hard'ewar harshe ,don ya bala'in shiga rud'ani ganin yarinyar da yake mutuwar so yake kwana da ita yake tashi da ita yarinyar da saboda ita yakasa yiwa kowace mace kallon mace yarinyar da a kullum yake da muradin gani ,yau gata a gabanshi Amma yakasa gane wacece ita acikin su ukkun , tunda yafara magana Sa'id ke kallonshi da mamaki kamun yace " kana nufin *Noor* dinka da kake bamu labari???
Yes Sa'id ita nake nufi saidai Ina cikin rud'ani nakasa tantance wacece ita acikin su ukkun nan ,
Indai wannan ne karka samu damuwa muje kawai mu tunkaresu insha Allah bazaka rasa wata alama da zatasa kagane wacece Noor dinka ba ,
Jin hakan yasa ya sauko da sauri suka nufi wajan da su Husna suke
alokacin sukuma Husna da Huzna Suna dariyar maganar da Hussaina keyi , cak ya tsaya Yana k'are masu kallo kamun yaja wata dogowar ajiyar zuciya tareda d'aura hannunshi akan k'irjinshi , lumshe idonshi yayi sannan ya bude a hankali ya Nuna Huzna da hannu yace "gata can Sa'id saboda bazan ta'ba mantawa da wannan dimple din nata ba don suna Daya daga cikin abunda yafara jan ra'ayina akanta ita kuwa waccan batada dimple saidai tana da wushirya inaga wannan shine bambancinsu da badon hakan ba da tabbas bazan iya ganeta ba ,
"To ai ta kwana gidan sauk'i Bro kawai kazo muje mu tunkaresu ,
"Kai bakada hankakine a makaranta suke fa sannan Ni malaminsu ne Kuma shugaban wannan makaranta so kake mutuncina ya zube , zanyi bincike akanta a hankali , insha Allah Noor tawace Ni kadai yayi maganar Yana wani lumshe idonshi cike da wani irin shauk'i.............✍🏼