Free chapter · Read without an account

Chapter 26

by Maryam Umar · HUSNA KO HUZNA

🅿️_26




Alhaji Abdullahi matawalle da matarshi Hajiya Aisha haifaffun garin Kaduna ne sunyi auren saurayi da budurwa bayan dogowar soyayya da suka dad'e suna shimfid'awa , 


Alhaji Abdullahi matawalle shahararren Mai kud'i ne na fad'a aji , Wanda ba Wanda bai San da zamanshi ba a duk fadin Nigeria 'Dan kasuwa ne sannan Kuma gogaggen d'an boko Wanda ya rik'e muk'amai da dama Wanda daga baya yayi ritaya ya rik'i harkan kasuwancinshi , Aiki ne ya dawo dashi Abuja tun shekarun baya ,Wanda ko bayan yayi ritaya sai bai koma kaduna ba yaci gaba da gudanar da harkokinshi anan Abuja ,


Matan shi biyu Hajiya Aisha wadda suke Kira da Ummu itace babba tanada 'ya'ya ukku Abdul Hakeem , Sa'id sai Salma 


Hajiya Raliya itace matarshi ta biyu tanada yara biyu Zainab wadda ta kasance tsarar Salma ce sai auta Mustapha Wanda yake da shekara 7 a halin yanzu, 

 

Gidansu gidane na zaman lafiya da k'aunar juna , rayuwarsu gwanin sha'awa , kasancewar Alhaji Abdullahi matawalle tsayayyen mutum ne , sosai Ummu take Jan girmanta shiyasa suke zaune lafiya ,


Daga Abu har Ummu sun dauki son duniya sun dorawa Abdul Hakeem ,hakama anty Raliya kamar yadda yake kiranta , 


Wata hudu da suka wuce ne ya had'u da Huzna sunje wajan siyayya lokacin baiga su Husna ba don sun zagaya , lokaci d'aya yaji sonta ya daki zuciyarshi , tabbas wannan itace irin matar da ya jima Yana nema , ido kawai ya zuba Mata yana kallon tsantsar kyau da cikar halitta ko k'yaftawa bayayi , 


Lafiyarka Abdul Hakeem ? Tun dazu Ina ta maka magana kayimun banza , cewar wani Abokinshi da suke tare Mai suna Nura , 


Firgigit yayi ya dubi Nura yace " na..am..mi..kace .. kallon mamaki Nura yamashi kamun ya dubi wajan da yake kallo, Saida zuciyar Nura ta buga lokacin da yayi ido biyu da Huzna wadda Sam batasan da wanzuwarsu ba a wajan sai sha'anin gabanta take , 


"Ah lallai doli ka firgice guy irin Wannan Kaya Haka , a fusace Abdul Hakeem ya juyo ya watsa mashi wani irin kallo Mai cike da gargad'i yace karka k'ara yabamun Mata kaji ko yayi maganar cikin hade gira don yasan halin Nura Sarai da shegen son matan tsiya gara ya taka mashi birki,


Wata irin dariya Nura ya kwashe da ita yace ah lallai abun nayi ne daga ganin sarkin fawa sai Miya tayi zak'i ! To Allah ya kyauta , kyale Nura yayi yajuya da nufin Isa gareta Amma mi !

Juyowar da zaiyi sai ganin wajan yayi wayam ba Huzna ba alamarta ,


K'ara ware idonshi yayi da kyau yafara zagaye wajan dasu , ganin ko Mai kama da ita baigani yasa cikin hanzari yafara zagaye a cikin plaza din Yana nemanta Amma Kamar aljana neman duniya yayi ciki da waje babuta Babu alamarta yafi awa biyu Yana zagayen nemanta , Nura kuwa tun abun nabashi dariya har yafara bashi mamaki izuwa yanzu kuwa har yafara tsorata da lamarin ganin yadda gaba Daya namiji Kamar Abdul Hakeem Yana nema yayi mashi Dan k'aramun Hauka akan mace don lokaci Daya ya firgice idonshi sun k'ank'ance sunyi jawur , da k'yar Nura yasamu ya janyeshi suka koma gida , 


Tindaga lokacin Abdul Hakeem yashiga matsananciyar damuwa ya daina cin abunci kullum bashida aiki sai tunani , sannan kullum sai yaje wannan plaza ya dubata ko Allah zaisa wata Rana ya ga Noor dinshi Kamar yadda yake kiranta Wanda kusan kowa nashi Saida yasan da zaman Noor,

Wasa-wasa sai da ciyo ya kwantar da Abdul Hakeem saboda damuwar da ya sawa ranshi , ba k'aramun tashin hankali iyayenshi suka shiga ba ganin suna nema su rasa Dan da yafi soyuwa a zukatansu, gashi basu San inda zasu samo mashi wannan yarinyar ba ,haka suke lallabashi da nuna mashi yayi hakuri insha Allah zai ganta harma ya aureta , da k'yar suka samu suka shawo kanshi ya rage damuwar da yake ciki , Amma fa Noor na nan zaune daram a zuciyarshi , 

Wannan so da yake Mata ne yasa gaba Daya ilahirin yan gidan suke mutuwar sonta, tun basu San wacece ba sun dauki son duniya sun Dora Mata , yau Kuma sai gashi kwatsam Allah ya had'ashi da ita a inda bai ta'ba tsammani ba , Wai duk wannan wahalar da yakeyi yarinyar a makarantar su take karatu, yanzu tunaninshi Daya ta yadda zai shawo kanta don yayi alwashin sai yasamu cikar burinshi kota halin Yaya ne ,


🙄🙄🙄to Malam Abdul Allah yaba Mai rabo sa'a





___________________


Tun daga lokacin Abdul Hakeem yashiga bibiyar Huzna sai da yasan komai akanta dai dai da irin abubuwan da tafiso a rayuwarta sai da ya binciko , yayi bincike sosai akanta ta yadda Saida yasan komai akanta kamun yafara tunkararta , 


A wata safiyar Alhamis ya shirya tsaf cikin wata arniyar gizner anmashi dinkin da samarin yanzu ke yayi ya kafa hularshi wadda ta dace da yanayin jikinshi sai zuba k'amshi yake Kamar anyi 'barin turare a jikinshi , Abdul Hakeem bak'i ne saidai ba sosai ba Wanda hutu da jin dadi suka ratsashi yayin da fatarshi Takoma calculate yanada dogon hanci Wanda ya dace da yanayin tsarin fuskarshi , yanada matsakaitan idanu su ba manya ba Kuma ba kanana ba daidai da zubin fuskarshi  Abdul Hakeem kyakyawane sosai ga iya tsara ado da iya tsara kalamai yanada fara'a sosai ta yadda koda yaushe zakaga murmushi akan fuskarshi Sam bashida fad'a bare fushi Yana tafiyar da komai nashi cikin nutsuwa da sanyin hali, 


Lokacin da ya aika a Kira mashi Huzna batai wata-wata ba tace aje ace bazata je ba , da yake tasaba yiwa samari Hakan duk Wanda yazo wajanta bazata fita ba harsai mama ta lalla'bata akan taje ta sallami koma waye cikin ruwan sanyi ba kyau wulak'anci , 

..........duk a zatonsu saboda maganarta da Mu'azzam ne yasa take korar samari Wanda Sam ba Haka bane tana korarsu ne saboda Sam Babu soyayya a tsarinta a yanzu a cewarta karatu zatayi sai taga karshen biro, 


Wannan karon ma hakan ce ta faro, da kyar mama ta samu ta lalla'bata ta tafi Kiran Abdul Hakeem , 


Fitowa tayi tsakar gidan acan nesa da inda take ta hango motarshi , cikin jin haushi ta k'arasa wajanshi da tunanin irin rashin mutuncin da zata shuka mashi ta yadda gobe ko ance ya dawo bazai dawo ba ,


Tana zuwa tayi tsaye bakin motar kasancewar Yana ciki bai fito ba , a hankali ya bude motar ya fito , kallonta yayin cikin wani irin shauk'i yayi Mata sallama da muryarsa Mai tsananin taushi da dadi , 

......a hankali ta d'ago da kanta don ganin mamallakin wannan murya Mai matukar dadi da nutsuwa , a hankali idonsu ya sark'e Dana juna , wani irin bugu zuciyoyinsu sukayi a tare , lokaci Daya Huzna taji ta daburce sai mutsu-mutsu take don ba k'aramun kwarjini wannan guy yayi Mata ba , 

Cikin nutsuwa ta gayar dashi ,

  Amsawa yayi fuskarshi fal farinciki yau gashi ga Noor dinshi , Nan suka Dan ta'ba fira kadan inda ya gabatar Mata da kanshi a matsayin masoyi a gareta , Babu wani haufi ta nuna mashi amincewarta don harga Allah yayi bala'in burgeta Kuma ya kwanta Mata a Rai tanajin zata iya rayuwa dashi ta har abada , 


Ba k'aramun mamaki yayi ba ganin yadda lokaci Daya ta karbi soyayyar shi batare da tasan koshi waye ba , shida ya d'auka sai yasha matukar wahala kamun ya samu wannan zukekeyar yarinyar ,! Tabbas ba abunda addu'a ta Bari ya tabbatar k'arfin addu'a ne kawai ,Nan sukaci gaba da firansu cikin shauk'i don ba k'aramun dadin firan Huzna ke ji ba bare Kuma uban tafiya,


Tun daga lokacin suka kulle soyayya suke zubawa Kamar me matsala Daya Huzna tak'i bashi dama yaje ga iyayenta mafi yawan firansu ma a waya ne gashi ko su Husna taki Basu damar da zasu sani yarasa miyasa take Haka Amma yanzu ya yanke shawarar karshen watan nan zai tura Iyayenshi suyi magana da iyayenta tunda Allah yasa akwai sanayya sosai tsakanin Abu da mahaifinta Alhaji Hussain,



___________________________




Yau gidan a cike yake sai hayaniyar yara ke tashi duk inda ka duba zakaga Yana walwali da tashin wani irin k'amshi Mai sanyaya zuciya , Haka duk fuskar Wanda ka ka kalla zaka ganshi cikin tsananin farinciki mussaman ma Inna tafi kowa murna da wannan Rana , Ranar da d'an lelenta Ibrahim Mu'azzam zai dawo k'asarsa bayan kamalla karatunsa , 


Su anty Harira da anty Safiya duk sunzo hakama anty Fatima tuni ta iso sai fama shiri suke don zuwa tarbonsa ,


Husna da Hussaina kamar zasu taka rawa tsabar farinciki sai zumud'in shiryawa suke , Haka suka dandasa ado kamar wasu Amare sunci kyau har sun gaji sai tashin k'amshi suke komai iri Daya suka sa ,

Duk wannan bidirin da sukeyi Huzna na kwance sai faman chart take da Sahibinta tana murmushi alamar tanajin dadin firan da yake Mata , sanye take da riga da wando na bacci yau ko wankan safe batayi ba bare ta canza Kaya sai hidiman gabanta takeyi ,duk wannan bidirin da sukeyi Sam basa gabanta hasalima ko kallo Basu isheta ba , 


Hussaina tace "kefa Yar mulki bazakije tarbon Yayan bane ,? Juyowa tayi ta k'are masu kallo sannan tace " banajin Zan iya fita ko nan da bakin get ne saboda kawai wannan masifaffen zai dawo, 

Kallonta Hussaina tayi da kyau tace Yayan ne masifaffe ? ....zata k'ara magana Husna ta daka Mata tsawa da cewa ......"ke don Allah kizo muje kar Allah yasa taje din banza kawai , a fusace Huzna ta taso tace wa kikecewa banza ? Yo akwai banza irinki ne Mai shegen shishshigin tsiya Allah ma yasa tun daga can yafara nuna maki halin nashi in yaso sai Naga ta yawar k'afa


"To sarakan fada ubanmi kukema fad'a kuma tunda kudai bazaku girma ba cewar Mamah da zuwanta kenan , maganarta ta mak'aleni ganin Huzna sanye da kayan bacci ba alamar ma tayi wanka bare ta shirya , 

Kallonta Mamah tayi tace " ke mi ya Hana maki shiryawa ne Zaki 'bata mana lokaci ?

Turo baki tayi tace "Mamah nifa bana jin dad'i bazansamu zuwa ba , 

"Eh Naga alama ai bakida lafiya Amma shine kike tsaye kina masifa , ...narai-narai tayi da ido Kamar zatayi kuka tace "wallahi mamah ......hannu mamah ta d'aga Mata tace maza kije ki shirya nabaki 5mnt ki samemu a falo daga Haka ta juya tayi tafiyarta , 

Fuuuuu Husna ta juya tabar d'akin kamar zata fashe don taji haushi sosai da akace da Huzna za'aje , da tana murna Huzna bazataje ba Amma yanzu Mamah tazo ta wargaza Mata shirinta, 


Ta jima tsaye Kamar zata rusa ihu kamun yafad'a bayi wanka tayi ta fito ko Mai Bata shafa ba ta dauko wata dogowar Riga bak'a ta Sanya sai d'an k'aramun hijab da ta Sanya shima bak'i ta d'auko wani makeken glass bak'i ta Sanya kamun ta dauki wayarta ta nufi falon fuskar nan tata Kamar anmata mutuwa , ita kanta tana mamakin irin kiyayyar da takewa Yayan nasu Allah ya sani ko maganarsa bataso amata wani irin k'unci takeji idan ta ganshi ko da kuwa a photo ne ,



Ke mi Zan gani Haka sai kace wadda take bak'inciki inba hakaba akanmi Zaki bimu da wannan shigar oya maza ki koma ki canza Kaya tunkan na Sa'ba maki harda sa wani makeken tabarau duk ya rufe maki fuska kamar wata 'yar daba cewar Inna cikin masifa , 

Gaba Daya falon suka fashe da dariya , Huzna kuwa cikin turo baki tace "eh ai 'yar dabar ce bakisani ba? , Filon dake kusa da ita Inna ta dauka ta jefeta dashi tace ja'irar yarinya kawai ni kike mayar wa da magana , aguje Huzna ta fita daga falon jin muryar Abee tayi inda yake don tasan yanzu in ta biyewa Inna sai tayi sanadin da akasa ta canza kayan nan ,



Husna kuwa tana d'aki sai cika take tana batsewa kanta take k'arewa kallo ta madubi tana mamakin to mi Huzna tafita dashi da har Yaya Mu'azzam zai sota ita ya k'yaleta , mutumin da tun tana yarinya yake matuk'ar burgeta tayi iya yinta don ganin cewa ta ture soyayyar da yake yiwa 'yar uwarta ya maye gurbi da tata soyayyar Amma abun yaci tura duk da ita wadda yakeyi don ta Sam baya gabanta , Amma tabbas doli zata dauki mataki akan hakan tun kamun amata sakkiyar da Babu ruwa daga Haka ta figi gyalenta jin zasu tafi ,



Mota biyar sukayi suka nufi filin jirgin ,Basu jima da zuwa ba jirginsu ya sauka , akan idon su Yaya Mu'azzam da Abokinshi suka fito , suna sanye da wata d'anyar shadda VOWA Fara tass sai wani maik'o take hular kansu bak'a ce hakama takalmansu da agogo komai nasu iri Daya kamar ka sacesu ka gudu kallo Daya zaka masu kasan tabbas sun amsa sunansu na zaratan maza , suman tsaye Husna tayi yayinda ta zuba mashi ido ba ko k'yaftawa yayin da shikuma idonshi yake kan Huzna Yana fitowa da ita yafara tozali wani sanyin dadine yaji Yana shiga kowane lungu da sak'o na zuciyarshi , Yana jin zuciyarshi wasai Kamar San sauke mashi wasu Kaya masu nauyi ,har yagama saukowa daga jirgin idonshi na kanta baya ko k'yaftawa , yayinda Huzna ke mak'ale da waya tana sauraren daddadan kalaman Sahibinta Abdul inda take zuba wani sihirtaccen murmushi Wanda yayi bala'in fito da tsananin kyawunta , ganin wannan tsadadden murmushin yasa Mu'azzam Jan wani irin numfashi .....Wanda hakan yayi dai dai da k'arasowar Husna da Hussaina wajanshi aguje sukaje suka rungumeshi..............✍

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.