Free chapter · Read without an account
Chapter 17
MAIDUGURI:
BOKA DA UMMA LAURE
Boka ya ce, “Yanzu abin da za ki kawo naira 500000 ne.”
Ta da fa kirji ta ce, “Ni Lauratu me ka ce boka?”
Kuɗaɗen da boka ya ambata ya sanya gumi wanke mata fuska, babu shiri ta fara fifita da gyalen da ke jikinta.
"Boka mu talakawa ne gaba da baya a yi mana sassauci.
Cikin ɗaga murya ya ce, “Sassauci shi ne na zayyana miki abubuwan da ake buƙata ku je ƙasar Sin ɗin ku kawo. Kuma ki sani ko na faɗe shi ƙaryar bil'adama ya kawo. Ki kawo kuɗi, idan ba za ki iya ba to a bar aikin ga hanya ki tafi.”
“Yi haƙuri boka, Allah ya huci zuciyarka.”
“Tun farko na faɗa miki buƙatarki babbace, idan wani ne ba ke ba sai ya ajiye mini 2 million kafin na yi masa, ke ba kya hango daɗin da za ku shiga, idan kun mallaki wannan attajiri sai kin mallaki fiye da abin da kika kashe.”
Ta miƙa masa kuɗin da ta zo da shi ta ce, “Ka ga sama da ƙasa abin da na mallaka ke nan, bayan shi ba ni da komai, amma idan aka ɗaga mini ƙafa zan kawo ragowar.”
Boka ya dinga muzurai yana ambatar sunayen aljanu ya dinga shewa. Umma Laure har ta tsorata, ya nuna mata tafin hannunsa ya ce, “Me idonki yake gani a tafin hannuna?”
Jiki na rawa ta ce, “Mus’ab ne ke durkushe a gaban Safinat yana roƙonta.”
“Kin dai gani ko to idan na yi miki aiki haka zai kasance a gare ta, za ta juya shi fiye da tunaninki. Saboda kin zama customer ce zan ba ki sati ki je ki haɗo kan kuɗi ki kawo, wata ya yi yawa buƙata za ta biya.”
“To boka zan yi iya ƙoƙarina, komai zan rasa a rayuwa in har za mu cimma burin mu zanyi shi.”
Umma Laure cikin ɗari-ɗari ta ce, “ Amma yanzu boka ba za a ɗan ba ni wani laƙani da za mu fara jawo hankalin nasa gare mu ba, yanzu haka ɗiya ta na gida a tunaninmu zai zo ya ɗauke ta sun samu saɓani amma shiru ba ɗuriyarsa.”
Boka ya fara gurnani ya ce, “Ke Hajiya sai kin dire kuɗin da aka buƙata za a fara aikinki, ba abin da zan iya yi miki a yanzu haka, juya ki fice na gama da ke.”
Haka Hajiya Laure ta fice, tana fita boka ya fara kuwwa da kururuwa a take shi ma ya ɓace.
TAKAI (Tsintar)
Yagwalgwalar Turai ce a fusace ta dubi Aliyu ta ce, “Da ma ba ku fahimci juna kai da mahaifiyarka ba, kuka sa na shiga cikin lamarin nan?”
Aliyu cikin sanyayyir murya ya ce, “Yagwalgwal ki yi hakuri bisa abin da na yi, ina son ta tuntuɓen harshe ne.”
Ta nuna shi da ya tsaya tare da cewa, “Karya kake, magana dai zarar bunu ce idan ta fito ba ta koma wa. Ka furta shi kuma kowa ya ji shi.”
Tana gama faɗa ta fice Aliyu ya bi ta a baya.
Jama’ar da ke wajen wannan ya kalli wancan, wancan ma ya kalli wannan.
Baffan Ma'u jikinsa ya yi sanyi.
Ma'u da ke ɗaki amma tana sauraro da ganin duk abin da a ke, wannan saɓanin da ta gani shi ya fi mata komai daɗi a ranta, domin lokaci guda annashuwa da walwala suka bayyana a fuskarta.
“Ni Ma'u abin da idanuwana da kunnuwana suka ji a yanzu ya fi a ba ni kujerar Hajji da Umura duk shekara. Yadda kuka tafi ɗin nan Allah ya sa kun tafi tare da manufarku har abada kar ku waiwaye mu.”
Murmushi ta yi sannan ta kuma ce, “Ni dama na san ta Ahmadi ce, haka shi ma ya san ni tasa ce.”
Ta kyalkyale da dariya ta faɗa gado.
Baffan Ma’u wani wuri ya nema ya zauna shi kaɗai ya yi jugum tare da tafka tagumi a ran shi yake cewa, “Kar fa a ce ta leko ta koma. Kar mafarki da nake na idan Ma'u ta ta auri yaron nan za mu fita a ƙangin talauci zai zama ƙarya.” A fili ya furta wannan maganar, “Kai ina hakan ba zai yiwu ba, auren nan sai ya tabbata.”
Miƙe wa ya yi ya ya fice.
MAIDUGURI:
Safinat, tun bayan ficewar Ummanta ta fara aiki ba kakkautawa, ta gaji sosai, sallamar Ummanta ce ya sa ta kai dubanta zuwa bakin kofar, barin abin da take yi ta yi ta je ta rungume Ummanta tana yi mata oyoyo da sannu da zuwa.
“Don Allah sake ni haka kar ki ƙarya ni, ba ki san a gajiye nake ba?”
Ta sake ta suka nufi ɗaki bayan sun zauna, Safinat tun ba ta ji komai ba ta dinga washe baki ta rausayar da kanta ta ce, “Umma ya dai? Ina fatan mun dace?”
Ta harare ta ta ce da ita, “Kin fiye zumuɗi to sai na yi wanka na nutsu zan ba ki labarin komai yanzu fara kai mini ruwan wanka.”
Safinat ta miƙe kai na rawa ta ce, “To Ummana bari na je na haɗa miki ruwan.”
ƘARAMAR HUKUMAR TAKAI (Tsintar)
Aliyu da mahaifiyarsa da yagwalgwalarsa zaune suke dukkaninsu sun yi shiru. Yagwalgwalar Turai ce ta katse shirun da cewa, “A gaskiya abin da ya wakana a idona bai yi mini daɗi ba, hakan zai iya jawo mini abin nuni da faɗa a ƙauyen nan, wallahi da na san lamarin nan haka ne da ban sa kaina ciki ba.”
Mama hamma ta yi sannan ta ce, “Adda (Yaya) ki yi haƙuri an ɓata miki rai kam tabbas, amma na fahimci Aliyu idan har na ce na janye batun shi ya ci riba a kaina ba ni na ci riba a kansa ba, saboda haka sai an ɗaura auren nan a yau, idan ya so ya bi dare ya je ya kashe ni sai ya ji daɗin rayuwa ya kawar da wacce take masa katsalandar a rayuwa, amma muddin ina raye 'ya’yana da zaɓin raina za su dinga gina rayuwarsu ba da gajeruwar tunani irin ta su ba.”
“Amma Hajiya Halima 'ya’yan yanzu ba irin mu na da ba ne, mace ma ba a tursasata ballantana ɗa namiji a bar su da zaɓin ransu, kar a zo a yi abu bai yi daɗi ba..”
Yatsina fuska ta yi a fusace ta ce, “Adda ni 'ya’yana dolen su su bi zaɓina don ni na haife su ba su suka haifan ba. Ina mamakin iyayen da su suke bin ra’ayin 'ya’yansu ba su su bi nasu ba.”
Baffan Ma'u ne ya shiga bayan ya yi musu sannu ya nemi wuri ya zauna ya ce, “Hajiya lamarin yara……..”
Dakatar da shi ta yi ta ce, “Baffa mun riga mun yi solving na komai ka bar maganar.”
Ta juya kan Aliyu ta ce, “Ina ba ka umurni ka je ku fahimci juna da Ma’u, kuma wallahi na ji wani furuci mara daɗi idan aka faɗa a kanka………” daidai gaɓar nan ta yi kwafa da cije laɓɓa ba ta ƙarasa ba.
Ta juya kan Baffa ta ce, “Baffa ka yi masa jagora zuwa wurin ɗiyarka don su samu fahimtar juna, kamar yadda a ka ce bayan sallar juma’a za a ɗaura aure magana na nan, yanzu haka an je cire kuɗin sadaki ne.”
Daɗi kashe ni in ji ɓarawon zuma, Baffan Ma’u sai daɗi yake ji kan shi a sunkuye ke nuna godiyarsa
Aliyu tsimi-tsimi jiki ba kwari ya miƙe ya bi surukinsa gidansa.
Maiduguri:
Umma Laure ta yi wanka kamar yadda ta buƙata, kuma ta samu nutsuwar da take buƙatar samu kamar yadda ta ce.
Gyarar murya ta yi za ta fara magana sai suka ji sallama, suna ɗaga ido Umma Laure da ta ga wacce ke sallamar ta yi tsaki ba ta amsa sallamar ba.
Safinat ita ma na ganin ta ta haɗe rai ta amsa sallamar ciki-ciki.
Bayan ta nemi wuri ta zauna ta gaishe da mahaifiyarta, Safinat ta ba ta haƙuri bisa abin da ta yi mata ta ce ba komai.
Mahaifiyarta ta dube ta, "Amma lafiya kika kuma zuwa?"
"Umma, Yusuf ne ya ƙira ni tafiya ta zo masa ba shiri ya ɗau hanya, shi ne na ce da shi ba zan iya kwana a gidan nan ni kaɗai ba zan taho gida ya ce ba damuwa."
Ta juya ta dubi Safinat ta faɗa mata duk yadda suka yi da boka, sai dai ba ta ambaci sunan Mus’ab da Hafsy ba don ba ta so Rufaida ta san hakan.
Rufaida bayan ta gama ji ta ce, “Umma, duk tunatarwa da na yi a ɗazu a banza, to zan ci gaba da yi wala alla wani lokacin sai a dace kun ɗauka. Umma bokaye mushrikai ne, kuma shirka yana daga cikin manyan ƙaba'irai. Idan har mutum ya riƙi bokaye sune majiɓantan lamarinsa har ya mutu bai tuba ba zai dawwama a wuta a ranar alkiyama. Umma me ya sa idan muna cikin damuwa, ko kuma muna da buƙatu ba za mu roki Allah subhanahu wata'ala ba, a ko'ina kake idan ka roƙe shi yana ji zai kuma amsa mana, sai dai kuma akwai wasu lokuta da addu'a suke saurin karɓuwa kamar yadda nassi ya nuna mana kamar sulusin dare, da yayin sujjada, da tsakanin kiran sallah da iƙama, da kuma lokacin buɗa baki game azumi, da kuma lokacin saukar ruwa. Me zai hana a matsayinmu na bayin Allah mu lazimci roƙon Allah a waɗannan lokutan, har Allah ya biya mana buƙatunmu ba tare da wani ƙaton banza ya ci kuɗinmu kuma ya raba mu da tauhidinmu ba. Shi boka ya ce da ku aikinku sai a ƙasar Sin za a yi tukun a yi galaba, shi kuma Allah subhanahu wata’ala kina cikin ɗakinki kika roke shi zai amsa miki. Allah ne fa ya ce yana jin ƙunyar bawansa da zai ɗaga hannunsa ya roƙe shi ba tare da ya amsa masa ba. Mu watsar da mayaudara maƙaryata mushrikai ɗin nan mu kama Allah mu rabauta duniya da lahira.”
Umma Laure miƙe wa ta yi tana miƙa ta ce, “Safinat zan je na ƙishingiɗa.”
Ta ba su wuri, Safinat ta ce, “Yaya ki yi haƙuri ni ma kaina ciwo yake ina so na je na kwanta.”
Rufaida murmushin ƙarfin hali ta yi haɗe da girgiza kai don ta san dalilin su na yin hakan.
Safinat bayan ta kwanta ta ce, "Ban san dalilin da ya sa Yaya take shiga abin da bai shafe ta ba, dole na faɗa wa Umma mu yi taka-tsan-tsan da ke don idan kika fahimci inda muka dosa sai sai kin ɓata mana tafiya.”
TAKAI (TSINTAR)
Ma'u da Aliyu zaune suke bisa tabarma a sauron gida yayin da Ma'u ta juya masa ƙeya tana cika tana batse wa sai harare harare da murguɗa baki da take tamƙar Aliyu na ganinta.
Aliyu ya sauke numfashi ya ce, “Na fahimci da ni da ke babu wanda ke muradin juna amma sai ga shi ƙaddara a dole tana so ta haɗa mu.”
Miƙe wa ta yi a fusace ta kalle shi ta ce, “Dakata Malam a yanzu ma ƙaddarar ba ta haɗa ba, sai dai idan ka kuskure nan da wasu awanni ƙaddarar za ta iya haɗawa, saboda haka ina mai ja maka kunne kar ka yi sake wannan ƙaddarar ta tabbata idan ko ya tabbata shi ne nadama mafi muni da za ka yi a rayuwarka."
Aliyu girgiza kai ya yi ya ce, “Ita ƙaddara ba a hannun bayi yake ba a hannun Allah yake, ba mu isa mu hana ƙaddarar da ya so zartarwa ba kasancewa ba. Da ƙaddara a hannun bayi yake da kowa sai ya zaɓi wanda yake so. Ni dai na karɓi wannan ƙaddara kasancewa na musulmi mai gudun ɓacin ran iyaye, ke ma ya kamata ki karɓi ƙaddarar saboda yadda da ƙaddara tana daga cikin shika-shikan imani.”
Ta harare shi ta kalle shi a tsiya ce ta ce, “Idan har ƙaddara na aurenka ne ba zan karɓe shi ba, wallahi sai na gasa wa duk waɗanda suka yi wannan haɗin aya a hannu.”
Wani irin ɗaci ya ji tun daga zuciyarsa har zuwa bakinsa saboda yarinya ƙarama wacce ko kallo ba ta ishe shi ba ta tsaya tana faɗa masa maganganu son ranta.
Ta ci gaba da cewa, "Idan ka aure ni ka sayi fitina, da masifa da rashin kwanciyar hankali ma kanka da mahaifiyarka, kai dama zurriyarku ba ki ɗaya. Ba na sonka ba na kaunarka, na tsane ka, tsanar da nake maka ya fi tsanar da nake yi wa shaitan da fir'auna saboda su ba su yi yunkurin raba ni da muradin zuciyata ba. Da na rayu da kai a matsayin miji gwamma na ƙare rayuwata a gidan yari.”
Tana gama furta hakan da gudu ta shiga cikin gida ɗakinta ta nufa kai tsaye, ta bankaɗe kofa ta zauna turus a ƙasa, zuciyarta sai faman bugawa take numfashinta kuwa na ƙoƙarin ɗauke wa, a hankali kuma ta fara ƙoƙarin saita numfashinta da take barazanar ɗaukewar, sai wani zafafan ƙwalla suka fara zirya a kuncinta. “Na ga ta kaina ni Ma'u.” Abin da ta ce kenan ta kuma fara kurma ihun kuka tamƙar wacce a ka yi wa mutuwa, don ko lokacin da mahaifiyarta ta rasu ba ta yi shi ba saboda a lokacin ba ta mallaki hankalin kanta ba.
Saif ya miƙa wa Mama kuɗi da ATM card.
Ta karɓa ta yi godiya. A ranta ta ce, “Na fahimci mahaifin yarinyar nan yana da idon cin naira, to ka makara ba ka san da su wa Allah ya haɗa ka ba , 100k zan ba ku shi ne sadaki da kayan lefe a hakan ma nasan na yi ƙoƙari kaf ƙauyen nan ba wacce ta yi sa'an samun irin haka.”
Ta je ta samu yagwalgwalar Turai ta faɗa mata yadda ta tsara.
Saboda sanin halinta ta ce, “Ba damuwa Allah ya sanya alheri, bari na sanar da Liman tun da amini yake ga mahaifinmu sai ya zama alwalin Aliyu.”
Ta amsa da hakan ya yi suka fice.
Mama da yagwalgwalar Turai da mahaifin Ma'u da alwalin Aliyu suna zaune suna tattaunawa, alwalin Aliyu ya ce,
“Baffan Ma’u ga kuɗin auren ɗiyarka sadaki da kayan lefe da duk wani al'ada da a ke za mu bayar da kuɗi a dunkule, saboda yadda kuka buƙaci a yi auren a gaggauce.”
Ya ƙarɓa jiki na rawa ya ce, “Ba komai za mu yi duk abin da ya sawwaka.”
Yagwalgwalar Turai ta ce, “A yi hakuri dubu ɗari ce, muna fatan za a ba mu yarinya ɗana da mahaifiyarsa ba na ƙoƙonto a kansu za su riƙe muku 'ya bisa gaskiya da amana, Allah ya sa ta kasance mai biyayya.”
Baffan Ma’u na jin dubu ɗari jiki ya yi la'asar.
Mama ta ce, “Ana ɗaura aure za mu tafi da amaryarmu, amma ku tabbatar kun haɗa mu da kayan gara don yaro ba zai yiwu ana gama hidimar biki ya fara cefa ne ba.”
Yagwalgwalar Turai ta dube ta ta ce, “Haba Hajiya wannan maganar bai dace a ji ta daga bakinki daga yanzu ba. Ku ta shi mu tafi.”
Ta miƙe tana cewa, “Ita fa gaskiya ɗaya ce dole a faɗe ta.”
Bayan sun tafi ne Baffan Ma’u ya dinga juya kuɗin ya ce, “Wannan kuɗi me zai yi a hidimar aure, dama ashe cika baki ne kawai kike, babu wani kayan gara da zan yi, taki zan je na saya na yi amfani a aikin gona. Yarinya haka zan ba ku babu ko cokali.” Kwafa ya yi ya nufi wurin matarsa.
Bayan sallar juma’a a ka ɗaura auren Ma'u da Aliyu.
Ma'u tana ɗaki ta dulmiya cikin kogin tunanin Ahmadinta ta ji ana guɗa ana faɗin Allah ya sanya alheri.
Miƙe wa ta yi ta zauna daram ta ce, “Guɗan me ye ne haka? Ni dai na san a cikin wannan satin babu wani aure a layinmun nan.”
Ta buɗe labulen taga sai ta ga jama’a ana ta raba musu goro da alawa suna dariya suna shewa.
“Ikon Allah!” Abin da ta ce kenan, sai ta ji an tura kofar ɗakinta an shigo ta yi maza ta waiwaya.
Wacce ta shigon ne ta ce, “Ashe dai ana son auren tun da har leke ake ana ganin abubuwan da suke wakana a waje. Ai ni da ma na san ba za ki taɓa guje wa rayuwar birni ba.”
Ma'u miƙe wa ta yi tana tambayar matar Baffanta, “Dada, ban fahimci maganarki ba, kalaman da kika furta sun sa kaina ya ɗore, me ke faruwa ne? Me kuma kike nufi?"
Shewa ta yi ta ce da ita, “Abin da ke faruwa shi ne aurenki aka ɗaura da Aliyu, kuma a yau za su tafi da ke ina fatan kin fahimci abin da nake nufi..”
Ma'u dafa kanta ta yi sai ta ji ɗakin na juya wa ba ta san lokacin da ta zube a ƙasa sumammiya ba.
Dada na ganin haka ta fice a guje tana cewa, “Jama’a ku zo ku taimaka Ma'u ta faɗi.”
Jama’a suka shiga ɗakin domin taimakawa suna ta salati.
Bayan wani lokaci ta farfaɗo, tun da ta farfaɗo take gunjin kuka masu rarrashi na yi amma kamar zugo ta ake, Baffanta ya tunzura ya fara jibgarta da kyar aka kwato ta a hannunsa ta yi lilis.
Da misalin karfe biyar na yamma aka ɗauki amarya, suna tafiya a mota Ma'u na kukan zuci, yayin da shi ma Aliyu zuciyarsa na cike da begen matarsa da tunaninta. A haka har suka isa birnin Kano unguwar Tal'udu.
MAIDUGURI BIRNIN SHEHU
Safinat da mahaifiyarta Bayan sun idar da sallar magariba, sun ci tuwo suka nemi wani wuri can suka keɓe saboda Rufaida.
Umma Laure ta dubi ƴarta ta ce, “Safinat aikinki kin san na buƙatar kuɗi sai kin dage ki nemo mana, alhazawanki da kika ajeye a gefe ma ba kya kula su dole a yanzu ki waiwaye su don mu cimma burinmu.”
Safinat bayan ta saki wawan hamma ta ce, “Umma wannan makudan kuɗaɗen a ina muke da hanyar samun su.”
Ta kalle ta ta wutsiyar ido ta ce, “Akwai mana cikin wasu 'yan sa'o’i kaɗan fa kika samo man 100k ballantana wannan da mako guda fa za ki yi, yadda kike santaleliya ai za ki haɗa 1 million ma a sati.”
Gauron numfashi ta sauke ta ce, “ Umma kenan mazan yanzu fa suna da matsala kuɗi baya fita a hannunsu haka siddan.”
Bayan ta gutsiri goron da ke kusa da ita ta tauna ta ce, “Safinat a baya ba ki taɓa kawo mini irin ƙorafin nan ba sai yau, ke fa nake ginawa rayuwa ba kaina ba, idan kin ga za ki iya haƙura ki rasa Mus'ab damuwarki ba damuwa ta ba.”
Shiru ta yi saboda Safinat babu abin da ba ta son ji kamar a ce ta rasa Mus'ab, amma kuma da ta tuna hanyar da ta samu 100k yanzu ma idan har tana so ta daɗa samun sama da hakan sai ta wannan hanyar da ta yi da farko sai ta ji zuciyarta ba ta so. Take ƙwaƙwalwarta ta nemo mata wata hanyar sai kuma ta ji ta gamsu.
Ta langaɓe wuya tana wasa da yatsun hannunta ta ce, “ Umma shawarata shi ne hanya mafi saukin mallakar kuɗaɗen nan, a sayar da gidan nan, sai mu nemi gidan haya mu zauna na ɗan lokaci idan buƙatar ta biya abin da ya fi gidan nan zan gina miki.”
Ta dubi 'yar ta ce, “Cinikin biri a sama. Ba da ni ba wannan gangacin.”
“Haba Umma kenan kina shaƙƙu game da aikin bokan ma, kuma bayan ke kika ce aikinsa kamar yankar wuka ne.”
Umma Laure ta yarda da aikin boka ɗari bisa ɗari. Amma batun sayar da gidan hankalinta bai ɗauka ba, daɗin da ɗawa takardun gidan ba a hannunta suke ba, ko ta nema sai an san me za ta yi da shi kuma sauran 'ya'yan ma sai sun kawo mata cikas musamman Rufaida.
Jijjiga ƙafarta ta yi wanda ya kasance ɗaya akan ɗaya ta ce, "Ki ajeye gurguwar tunaninki ki yi abin da na ce, ki bibiyi dukkanin samarinki da alhazawanki ki haɗo mana kan kuɗi nan da sati a samu abin da ake buƙata ko sama da hakan. Fakat!”
Gumi ne ya yanko mata a goshi, “ Amma Umma……”
Tsawa ta daka mata kafin ta ƙarasa furta abin da take son faɗa, “Safinat, na fa gama magana zaɓi ya rage naki."
Safinat hamma ta yi tare da miƙa idon duk sun yi ƙanana alamar bacci.“Umma bara naje na kwanta, aikin da na yi yau a gidan nan, duk jikina ciwo suke yanzu haka.”
“Ai aiki ko kin kama hannu da shi, sai dai kawai zan ɗaga miki kafa ne don za ki dinga fita nemo mana kuɗi.”
Ita dai Feenah ba ta ce uffan ba ta nufi ɗaki.
Number Mus'ab Hajiya Laure ta yi dialing kamar ba zai yi picking ba don ya jima ya na ringing sai kuma ya ɗaga ya mata sallama, sannan ya gaishe ta bayan ta amsa masa ne ta fara magana kamar haka:
“Mus’ab ina so gobe ka kawo wa Safinat wayarta.”
Mus’ab goge goshinsa ya yi da handikcheif da ke kusa da shi ya ce, “ Umma amma ina ga Safinat ta zauna ba waya shi ya fi alheri a gare ta, riƙe waya akwai hatsari.”
Wani irin tsaki ta ja cikin tsawa tamƙar tana ganin shi a gabanta ta ce, “Dakata Malam! Ba na son wani ƙabli da ba'adi umurni nake ba ka gobe na ga wayar Safinat. Idan ka haifi 'yar cikinka sai ka ajeye mata irin wannan dokar amma ba a kan 'ya’yan wasu ba.”
Ta tuntsire da dariya ta ce, “Au na manta ashe da juya kake tare idan da ita za ka gama rayuwa ba kai ba haihuwa sai dai ka ga wasu na hayayyafa ba dai kai ba.”
Mus’ab maganar ta daki zuciyasa sosai domin sai da fuskarsa ta nuna haka, ya cija laɓɓansa ya ce, “Umma wannan maganar ba girmanki ba ne bai kamata a ce ya fito daga bakinki ba, ko wasu ki ka ji suna faɗa ke mai hana su ne, Umma kina uwa a gare ni kina min gorin haihuwa. Na gode duk wanda ya yi min gorin rashin haihuwa ba zan ji haushinsa ba tunda na ji a bakin da ban taɓa tsammanin ji ba. Waya kuma gobe zai zo hannunki zan kai gidan Abba yara za su kawo.”
“Abin da nake son ji a bakinka kenan, sannan a haɗo mata da kayayyakin na sawanta. Sai ta katse wayar.
Musab bayan ya gama wayar ya dafe ƙahon zuciyarsa saboda wani irin masifaffen harbawa da take da azabar ƙarfi sanadiyyar kalaman Umma Laure.
“Ya salam!” Shi ne abin da ya furta a zuciyarsa.
Hafsy ce ta shigo ɗakin riƙe da cup a hannunta da ke cike da lemo yanayin da ta ga mijinta a ciki ne ya sa ta kiɗime nan take ta jefar da cup ta isa wurin sa.
Zuba guiwowinta biyu ta yi a gaban shi, ta sa hannayenta biyu ta tallaɓe fuskarsa kana ta kalle shi cike da damuwa ta ce, “*Mijin mace ɗaya,* what's happen? Ni dai na san na fita na bar ka cikin annashuwa.”
Mus’ab wani irin sake wa ya ji jijiyoyin ƙan shi zuwa zuciyarsa suke yi suna ba da sautin ras! Ras! Yayin da sassan jikinsa take suka fara rawa tamƙar mai jin sanyi kunnuwarsa kuwa suka dinga amsa amon muryar Umma Laure da take cewa, “*Au na manta ashe da juya kake tare, idan har da ita za ka gama rayuwa sai dai ka ji wasu na hayayyafa ba dai kai ba.*”
“Wayyo zuciyata!” Abin da ya ce kenan numfashinsa ya fara harba wa.
Hafsy ganin yanayin da Mus’ab ya shiga lokaci guda ta shiga ɗimuwa hantar cikinta ne ya kaɗa ji kake kuuuuuuu “Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!” Shi ne abin da laɓɓanta ke furta wa ta fita cikin hanzari ta sanar da maigadi suka nufi asibiti da Mus’ab.