Free chapter · Read without an account
1️⃣5️⃣
ABIN DA YA BAKA TSORO
Mai_Dambu
EWF
Top-notch
1️⃣5️⃣
*Abari ya hucce...*
Last page
-----------
Yadda yake taune bakin shi yayi, yana me kara jin damuwa sama da koda yaushe. Shi kan sa Mansur yasan Mehd yana cikin matsanancin damuwa.
"Kayi hakuri shine abin da zan kara fada maka, amma har ga Allah kayi kuskure." Buɗe ido yayi ya juya ga Mansur.
Gyada kai Mansur yayi yana murmushi sannan ya gyara zaman shi.
"Auren ka da Meryam yana da alaka da mutuwar Innah Isa, kuma da ka aure ta amadadin ka gyara zaman ku da adalci sai ka ɗauki dabi'ar babu ruwan ka da ita, nasan all dreams dinka kai da Innah Isa ce, amma da ja samu Meryam sai ka rike ta hannu bibiyu, wani babban laifi da kayi wofantar da ita, wannan shi ya bata damar saka maka kwaya har ka bukace ta, da taso sai tayi ta bin mazan waje tana lalata dasu, kuma tayi ta kawo maka yaran cikin gidan ka. Sai ta gwammace koda bala'i sai ka haɗa shimfida da ita. Mehd tabbas bahaushe yayi gaskiya da yace haihu da makiyi ba a bin ka dauka ka bawa masoyin ka ba. Kar ka kuma haka"
"Is too late" ya fada a kasar makoshin sa.
"Ko daya ba a makara ba, asalima gyara ya kamata kayi domin shine hanyar da zaka gyara goben ka!"
Tashi yayi zaune ya kurawa Aminin shi da bai da wani sama da shi a duniya ya riko hannun shi.
"Ko na gyara Meryam 95% na lafiyar ta ya raunana. Kasar jini gare ta." Ya furta a hankali, yana sauke numfashi me nauyin gaske.
"Zaka iya gyarawa! Mutuwa kuwa ta Allah ce."
Yake yayi wanda yafi kuka ciwo, ya ce mishi.
"No way! A koda yaushe zata iya mutuwa"
"Sabida shine wishing dinka? Shine burin ka? Shine fatar ka ta mutu ko zaka sake kayi yadda kake so what about your kid's?"
Ware oily eye's din shi yayi a kan mamaye.
"She deserved happiness? Ko min kashin sa tana buƙatar farin ciki, tana bukatar adalci daga gare ka, domin ta haka ne zata rayu sama da yadda ake hasashen lafiyar ta, idan har kaso zaka yi farin cikin da baka yi ba da can baya."
Murmusa mishi yayi domin Mansur bai san yadda yake ji bane.
"Ba kasan So ba?"
Dariya Mansur yayi yana faɗin.
"Amma nasan kiyayya, kasan yadda kiyayya take kuwa? Haka shima soyayyar haka yake. Maina ka lalata gidan ka tunda gashi yaran ka har farin ciki suke dan sun ga kayi dariya. Maina wallahi kaji tsoron Allah. Duk haukar da xaka yi ka daina saka Yara domin su babu laifin su ban da ma dan iska irin ka ina ruwan yara da matsalar ku, matar ka ta lakato ka ba yara ba dan banza"
Karshe haka Mansur ya gama gaya mishi abinda ran shi yayi mishi kafin suka nufi kamfanin shi na nan Ingila.
A can gidan kowa yana dakin shi, kasa hakuri Nuratu tayi ta mike tana faɗin.
"Innar mu zan tafi cikin gidan wallahi ba zan iya barci ban ga yadda cikin gidan yake ba!"
"Hm" ta fada tana zaune akan abin sallah, bata jira amsar ta ba ta yi waje abin ta. Sai da ta fara leka katafaren kitchen din gidan wanda tsanani kyanshi sai idanun ta suka kawo kwalla.
Ina ma ace zata iya daukar kasadar nan yadda ta ga gidan Yar uwanta yake, yanzu ta gane ita tafi dacewa da Mehd ba Yar Uwarta ba, kuma tsaf zata iya cika muradinta akan. Ai itama Mehd kwacen shi tayi a hannun wata so ba wani abu bane dan itama ta kwaci Mehd a hannun ta. But irin wannan yanayin yana bukatar shiri na musamman.
Bata kuma razana ba, sai da ta shiga dakin Nadiah da Emaan, mafarkin future din yaranta ita fa tama fi yar Uwarta kyau da sura me kyau, akan me yar Uwarta zata dauke kaso dari na dari na farin cikin ta? Kwalla ne ya zubo mata ta goge, tsabar Hassada domin sun mai da Mehd dan babyn robar wasan Yara ko?
Haka ta gama zaga side din yar Uwarta sannan tayi nasarar isa bangaren Mehd Junaid, idanu ta lumshe tana kallon bata kudi da barnan dukiya, duk wannan daular na .mijin yar uwar ta? Duk wannan duniyar na mijin Meryam? Tasan Mehd yana da Arziki bata san likafar taci Uban na da ba.
Kamar ta saka hannu a kan ta, yayi kuka haka ta shigo falon, Ashe Ayyah ta ga shigowar ta. Dan haka ta biyo ta tana faɗin.
"Hajiya nan part ba a shigowa yallabai da iyalin shi kawai suke shigowa"
Juyawa tayi tana kallon Ayyah, ganin ta cikin wata irin kaya kamar uniform yasa ta mata kallon kaskanci ta ce mata.
"Amma kin san dai mijin yar uwata ce? Sannan."
"Kiyi hakuri akan aikina nake" Ayyah ta fada mata.
"Toh ba zan fita ba,"
Ta nime wuri ta zauna tana faɗin.
"Hala baki san kusancin mu da shi ba!"
Hayaniyar su Fahmidah taji ta fito hannun ta rike da towel, ganin Nuratu ne yasa bata mata magana ba, ta juya abin ta.
"Mtsew an auri mai kudi an goge har da nuna mana iyayi da kinibibi. Toh Arzikin da mijin ki yake takama da shi na mijin Yar uwata ce"
Fahmidah tasan da ita take dan haka bata wani damu ba, domin ai ba wannan bane karon farko ba,.ita dai a sanin ta, sune suka ki Mansur sabida abin duniya. Murmushi tayi abin ta ta shige.
"Ke ki fita ba zan bar nan ba, a hada min abinci zan ci"
"Ayyah lafiya?" Hajiya Mama ta tambaye ta.
"Lafiya Hajiya tun kafin Ku zo yallabai ya sanar da ni cewa iya kune anan, su kuma su zauna a can side din Mammy, kuma itama Mammyn ta gaya min haka, jiya da muka je shine nace ta koma nasu bangaren."
"A'a ta zauna ai ko ina ma duk zata iya zama."
"Toh Hajiya"
Cikin rashin kunya ta ce.
"Yawwa abinci na ki saka a kawo min nan. " Juyawa tayi tana faɗin.
"Hajiya Mama Nagode haka kawai wai sai na fita, bayan nice Amaryan Ya Maina" ita kan Hajiya Mama bata wani biye mata ba, ta shige daki. Ta kwanta abin ta,.sam idan ka cire Meryam ga baki daya yaran Zubaida basu da hankali. Meryam ce kawai tafi ta Zakka a cikin su. Fatan shiriya ta musu.
Da yamma likis suka shirya Selim yazo ya kai su asibitin, ganin halin da take ciki sai da yasa jikin su yayi sanyi.
"Sannu Hajiyar mu, ya hanya Hajiyar mu na d'ago ki ko?" Ta fada hawaye na zuba mata.
"Allah ya baki lafiya Meryam, cuta ba mutuwa bane ai."
"Kayya Hajiyar mu, ba irin wannan cutar ba. Fahmidah Yasu little Innah Isa?" Hàdiye kukan ta tayi tana faɗin.
"Na barta a wurin Ammah"
"Me yasa baki kawo min ita ba?"
"Allah sarki bafa zuwan nutsawa bane muka yi akan me zan tawo da ita Inna Isa shekara goma sha daya, ai ta girma"
"Muga hotonta"
Ciro wayar tayi ta shiga gallary ta dauko mata hoton Yar budurwan yarinyar.
Murmusa mata tayi, tana faɗin.
"Allah sarki! Inna Isa na, na tuna ranar da aka haife ta. Ba zata Mansur ya kira Mehd yake ce mishi Alhamdulillahi an samu Innah Isa, wallahi ban tab'a ganin rikicewar shiri irin ranar ba dan bai fahimci haihuwa aka yi ba, sai da yayi sujjadul shukuriya. Na Tambaye shi lafiya? Ya ce min An samu Innah Isa. Abin mamaki nasan wanda ya mutu baya dawowa, sai na kuma ɗaukar wayar na kira Mansur naji me yake nufi aikuwa ya ce min Fahmidah ce ta haihu. Tun daga ranar ban kuma ganin dariyar shi ba, har sai dazun zuwan Mansur. Allah ya mata albarka ita kuma me sunan Ubangiji ya gafarta mata yasa mutuwa Hutu ne a gare ta. Nayi laifi kuma nayi rashi." Ta fashe da kuka, tana faɗin.
"Son zuciya bacin zuciya, bawa baya wuce ƙaddaran shi amma ni na kasa fahimtar haka, toh ina zan kai wannan rabon? Ina zan zuba su? Hajiyar mu, wallahi laifin da nayiwa Mehd na rantse da Allah, babu namijin da xai zauna dani a cikin irin wannan yanayin, da ciwo da zafi laifina babba ne, nayi kokarin ganin na nime .."
Shigowa dakin yayi fuskar shi a kame.
"Ya Maina barka da shigowa, kaga matar ka sai wani magana take hala ciwon ne ya tab'a kanta ko?"
Yadda tayi maganar yasa shi kurawa Meryam idanu tana kuka sosai.
"Kin san matsalar ki ko? Ko kin manta da yanayin condition ɗinki ne?"
Ya tambaye ta, yana riko hannun Junaid.
"Maina ya jikin ta? Me ke damun ta?" Kamar bai ji tambayar Innar su ba, sai jin Muryan Meryam yayi tana faɗin.
"Innar mu cutar daji ce ta jini. Kuma yaci karfina zuwa wannan lokacin sai abin da hali yayi "
"Yummmm" wani irin abu yaji yana yawo a jikin shi bai tab'a sanin zata iya fadar ciwon da bakin ta ba, sai yaga ita ko a jikin ta sai ma kara musu bayani take.
"Ai na jima da ciwon tun haihuwan Junaid, ina shan magani yanzu kuwa ya isa matakin da ba zan iya dakatar da shi ba, kuma babu abin da muka iya domin ciwon ya samu karfi a jini na sosai, ga cikin sati goma sha shida. Da babu cikin zan iya nisan kwana na shekara guda toh yanayin cikin ya kara ta'azzara ciwon ban sani ba ko zan haifi cikin ko kuma zasu min wata hikima idan rai yayi halin shi. Amma nasan hakkin Innah Isa ce yake Bibiyata."
Mikewa Innar su tayi ta bar dakin tana kuka, wallahi bata tab'a danasanin aikata abin da ya dame ta ba sai yanzu cutar daji fa? Innalillahi wa'inna illahi raju'un. Ta fada cike da nadamar abin da suka aikata tsawon shekaru ashirin..
Sai magariba suka bar asibitin, tare da Yaran, har shima Mehd din.
A cikin motar babu wanda ya iya magana asalima shiru kowa yayi har suka isa gida. Yaran shi suka biyo shi falon shi, a gida suka yi sallah magariba da isha, Nadiah kan dawowa tayi jikin Uban ta fashe da kuka ta ce.
"Daada Mammy na" shima Junaid haka, Emaan itama tazo ta kwanta a jikin shi. Idanun shi ne yayi jajjur.
"Ubana ina ga zamu mai da yaran nan gida kawai muje can su cigaba da zama"
"Don Allah Hajiya, ki bar min su kar maraicin yayi musu yawa Insha Allah kome zai dawo Daidai"
Bata tsawala ba, sai dai daga shi har yaran kusan babu wanda ya saka abincin a bakin sa. Ko da dare yayi Nadiah sai da aka kira family Doctor din shi ya duba ta, domin zazzaɓi ya dame ta sosai, a dakin shi suka kwana shi kuma ya koma saman kujeran dakin ya kwanta.
★
Two weeks ago.
Ya shigo Nijar Amma yadda zai samu damar shiga birnin Beyaro ya faskara, sai da kyar da sodin goshi ya shiga garin inda yayi mugun danasanin halin da yaga Meriama, ya kuma ji rasuwar Malam. Bayan isha yana zaune a tsakar gidan su Babba, tana sanye da wani riga da wando me suna Maharaja, sai dan kwalin shi da ta rufe kanta.
"Rabe ina ga zata koma makaranta babu amfanin zaman ta a cikin gidan nan haka. "
"Anya kuwa? Kawai a bar maganar makarantar nan kawai tayi saukar ta saura wata shida, tunda ta iya Alqur'ani babu abin da ya rage, muna jiran Allah ya kawo miji na gari ne kawai, amma makarantar boko bana ta bane*
"Baaba don Allah rayuwar ta zaki duba da ta Yarinye?"
"Aliyu babu abin da ya gagari Allah, kasan ba dan ta auna arziki ba da yarinyar nan bata raye? Don Allah ka kyale ta. "
Duk yadda yaso ya mai da ita makaranta Baaba taki kuma koda ya samu Rabe da maganar shima goyan bayan Baaba yayi ya ce kai ne baka da matsala amma mutanen da suke kewaye da mu kamar su kashe meriama suke ji don Allah aboki a bar maganar nan domin sai ta tayi sati biyu bata iya tsayawa da kafarta.
Dan dukar da tasha a hannun yara." Ganin haka yasa shi Binta har islamiyya, yasa aka kira ta.
Tana durkushe kanta a ƙasa.
"Meramu nace zan mai dake makaranta sun ki"
"Ba mamaki karatun boko baya cikin ƙaddarata ne! Watakila kuma yana cikin amma ba zan riske shi ba nan kusa sai nayi tafiya dubu bisa zanen ƙaddara ta kafin na cimma shi"
Wani irin yarrrr yake jiki a jikin shi ya rasa abin da zai ce maganar ta ce me muhimmanci ko muryan ta ne? Ikon Allah.
"Meramu!" Ya kira sunan ta.
"Kina da saurayi?"
D"ago kai tayi ta zuba mishi kyawawan idanun ta. Kafin ta sunkuyar da kai kasa tana wasa da tsinken hannun ta.
"Sayyid kenan, waye zai yarda dan shi ya tawo inda nake bayan tagwayen tawayar da nake da su? Ko ka manta Mamma Mahaukaciya ce da bamu san asalinta ba. Sannan ni kuma shegiya ce mara uba yar da aka ɗauki cikin ta cikin kasuwa."
Wani irin bugawa kan shi yayi cikin wani irin yanayi.
"Idan wani yazo toh tabbas irina ne shi domin nasan iyaye na gari ba zasu tab'a amincewa da mace mara nasaba ba"
"Waye yake gaya miki waɗannan batuttuwar ne?"
Murmushi ta sannan ta ce mishi.
"Mu'amalar yau da kullum, shawagi cikin duniyoyi mabanbanta yasa ni sayan littafi da alkalami domin rubutu da sanin halayyar wasu dangin al'ajabi "
"Ya ilahi" ya furta yana kallon Baby face dinta, wannan yarinyar zata kashe shi. Ya fada yana kallon yadda take wasa da tsinke.
Tsintar kan shi yayi yana fada mata.
"Idan na samo miki miji zaki aure shi?"
"Hmm!" Ta furta tana murmushi sannan ta ce.
"Bani da matsala duk abin da na samu zan amsa amma irin kallon da duniyar shi zata yiwa shegiya yar Mahaukaciya nake hangowa, idan Aka bawar Allah ikon shi baya barci kuma baya mantawa yana sane da kome tun daga ranar da ya shirya har zuwa ranar da zai isar da ikon shi da buwayar shi."
"Kenan Sayyidah bata maraba da saurayin da zan mata kenan?"
Mikewa tayi tana faɗin.
"Allah shi yafi mu sanin daidai da rashin sa"
"Ina fatan idan ni na kawo shi ba za a ki kula shi ba?" Fita tayi tana ji a ranta no way da wani zsi shigo inda take domin duniyar ta a gurbace take.
Tun daga ranar Sayyid ya saka kafar kafa gwamnatin shi amma ya kasa fitowa ya fada mata, kuma duk zuwan shi a makaranta ake zancen tun malamai basu d'ago shi ba har aka d'ago yadda yake rawan kai da jiki akanta.
Kashe kudi kuwa kamar bai san ciwon su ba, hidima yake mata wanda har Rabe da Baaba suka daura qyar tambyar su akan shi, itama Meriama ba karya tana jin wani abu akan abubuwan shi sai dai sanin linzamin yafi karfin bakin kaza yasa ta rufawa kanta asiri, amma tabbas motsi kadan zaka fahimci she fall in love. Irin mahaukacin soyayyar nan, kamar jiran Sayyid ake ya fara takalarta da batun kusancin soyayya sai ga samarika gabas da yamma kudu da Arewa. Abin har ya fara bata tsoro domin a kalla sau uku zuwa hudu a rana. Haka yasa baki daya ta kasa sakewa da su, duk wanda ya kira ta, ta fita abu daya take fada mishi.
"Kayi hakuri ka bincika wacece ni, idan ka samu labari saka iya dawowa" da haka take sallamar su.
Basu kuma dawowa dama su zo su latsa ne suji, Allah ya taimaka Aliyu ya tsare mata kome , yar waya me kyau ya saya mata . Ranar an ga shirme da shiririta, domin kuwa minti biyar za a saka wayar a Charge. Baaba me kosai me zata yi ban da dariya. Dake Rabe ya koma dakin Malam da zama tsaki yayi ya gaji da shiririta ya ce.
"Zan kwace wayar wallahi idan baki barta ba"
Wannan yasa wayar ta samu kan ta . Itama ta samu kanta.
Haka lokaci yayi ta gudu, kafin ayi bikin yaye su Aliyu ya mata dinkuna na fitar hankali, wasu shadoddi da ya sayo musu tare aka musu dinkin iri daya, haka hijabai kuwa ita kanta bata san iya adadin su ba, idan zai zo weekend yake zuwa mata, musamman ya saya mata wani mai me kyau wanda ya kuma glowing skin dinta. Bata damu da kwalliya ba, amma idanun baya rabuwa da tozali.
Saura kwanaki uku saukar yau dai ta fito kasuwa dan tunda ya dawo ya haramta fitar ta kasuwa, sannan ta kawo musu katin saukar ta ne, da ta buga aka kawo mata shi zai zo ana gobe saukar.
Shirin Aliyu zai gabatar da kan shi ne ranar saukar shine shirin sa, sai dai kwatsam aka kira shi a Mali ya koma gida da gaggawa.
Dan haka ya bada duk wani abin da zata bukata kafin yazo aka kawo mata akan zai zo daga baya.
Duk cikin kasuwar sai da ta kai musu katin saukar, Fatah Alkhairi kuwa tana shan shi a wurin al'umma a gajiye ta dawo wurin Baaba ta zauna bayan ta d'aga nikkab din fuskar ta tace musu.
"Kawu Mudan da alamu garin za ayi ruwa ko?"
"Eh Meriama muma fatan haka muke"
"Raguwa dan zaga kasuwar ce kike gumi haka?" Baaba me kosai ta faɗa.
"Kawu Ghali kaji Baaba ko?"
"Kyale ta Uwata matsalar Baaba a bayyane take, bamu kulata."
Wata kyakyawar bakar land cruiser ce tayi parking a gefen rumfar babba.
Alhaji Ahmed Marwan ya fito tare da driven shi, suka nufi rumfar Mudansiru.
Matsawa tayi ta koma wurin Baaba tana tura baki.
"Ni wallahi Baaba ki bar kirana raguwa"
"Tafi can. Mummunan baka me dogon hanci"
"Kawu Rabi'u kana jin ta ba?" Ta fada idanun ta yana kawo ruwa, ta tsani Baaba tace mata baka mummuna.
Murmushi Alhaji Ahmed Marwan yayi ya ce mata.
"Naga Iv din hannun ta. Bakar mace azurfa" murmushi mishi tayi, har hakoran ta suka bayyana.
"Alhaji me za a hada muku?"
"Coffee da madara, sai soyayen kwai, iro me kake bukata su hada maka " ya tambaye shi yana amsar takardan hannun ta.
"Masha Allah, sauka zaki yi?"
"Eh"
"Allah ya sanya albarka "
"Amin" ta fada a hankali.
"Toh a bani nima ko ba a gayyace Ni bane?"
Cire mishi tayi ta mika mishi.
"Nagode " ya fada.
Murmushi tayi tana faɗin.
"Baaba zan koma kar Mamma ta fito waje "
"Zoki amshi namar ki."
"Kawu azumi nake "
"Toh kaiwa Yarinye tunda kina azumi "
"Hmm! Ina ga wallahi idan baku daina bata me dogon hancin nan ba ko" Baaba tayi kwafa.
"Haba Hajiya kishin ki yayi yawa tunda nazo nan kike kushe hancin Sajidah "
"Hm Alhaji kenan bata ka feleke take min ba" amsar kayan da suka bata tayi sannan tayi musu sai anjima.
Bata san ya suka karkare ba.
Shima Alhaji Ahmed Marwan yana gamawa ya musu sallama.
---
Shiri sosai ake ɓangaren su Baaba domin tun ana gobe saukar basu je kasuwa ba, da safe aka kawo musu katon rago da masu aikin shi, dama kuma Aliyu ya saya mata, Baaba Jumalo tazo dan an kirata ta wayar salula.
Kusan kwana aka yi ana aiki dan ma matar Ghali da Mudan sun zo, washi gari ranar saukar masar gero da ta shinkafa da sinasir, cincin da zobo aka yi ana fita da shi sadaka, kafin ta fito cikin wata danyen shadda fari kal, ta daura hijab dinta a kan shi, sai farin jaka na kamfanin Channel da takalmin shi.
Sannan suka nufi makarantar ita da Masa'udah babbar yar Ghali da Jamil babban dan Mudan tun suna yara suka nuna musu darajar ta, shi yasa koda saukar yazo sune kawayen ta, har shima Jamil din. Baaba tasha wanka cikin kayan alfarma, haka Itama Yarinye English me zanen ganyen albasa ta saka, tayi kyau sai ka zata irin yayar Meriama ce amma taki fita dan.tsoron mutane take ji.
Ana can ana sauka su babba sun fita Baaba Jumalo aka bari a gida toh tana jin kome.
Bayan ayi nasiha da fadakarwa, sannan aka kira Meriama Rabi'u Umar. Ta musu karatu daga suratul Yusif. Lokacin da da ta fara karatun. Sai da mutane dayawa suka yi shiru gashi an yi gayyata sosai manyan malamai hat Sheikh Aboubakar Yayan Sadi da kan shi ya zo saukar dan girmama da'awa.
A lokacin da yaji muryan yayi mishi kama da na Yar shi Juhainah, kasa dauke idanu yayi a kanta, har ta gama karatun.
Haka aka bata kyautattuka, shi kuma ya biya mata umra ita da iyayenta.
Sai da Baaba tayi kuka tana tuna batun Malam tabbas bata san Arzikin abincin yarinye ba sai yau.
--
A can kasuwa kuwa yau Alhaji Ahmed Marwan ya dawo daga Niamey dan ya tsaya ya ci abinci ya manta yau saukar meriam, ya ga babu mutane anan yake tambayar su.
"Iro muje makarantar na manta amma ban manta da yarinyar ba, haka kawai nake son yarinyar cikin gidana"
"Alhaji zaka kara aure kenan?"
"A'a Fu'ad zan nimawa auren ta"
"Masha Allah ai ko Allah ya tabbatar" haka suka nufi wurin saukar, sun samu ana ta bawa Meriama kyauta, dan haka ya kusa ciki har wurin kyautar, yana tsaye bayan an gama yaga yadda take ta kuka kamar ranta zai fita kowa a wurin ta bashi tausayi sai waige-waige take, a wurin ya nime shugaban makarantar da limamin unguwar, ya mika bukatar shi ga Baaba me kosai. Ita kuwa bata yi kasa a gwiwa ba, ta kira Rabe da su Ghali.
Aka yi magana, Alhaji Ahmed ya samu karban ban mamaki domin a wurin Sheikh Aboubakar ya tsaya a matsayin waliyin Meroh dan sun gayawa Alhaji Ahmed Marwan yar su bata da Uba ga ... Murmushi yayi sannan ya ce.
"Nima ina neman Allah ya rufa min nawa asirin ne ba zan iya jira ba, a bari ya huce shi ke kawo da rabon wani ga shi na biya sadakin Meriama. A wurin aka daura auren Meriama Rabi'u Umar da Fu'ad Ahmed Marwan ranar da ba zata tab'a mantawa ba. Bayan yi sallah azahar....
*_Wacece Innah Isa? Waye Mehd Junaid Maina? Wacce irin Cin Amana Meryam tayi? Me yasa Nuratu take son akan Mehd? Shin da gaske Inna Isa mutuwa tayi? Me yasa Aliyu ya tafi? Ya makomar Soyayyar Aliyu da ya kasa Confess din shi! Ina Sadi da iyalin shi suke? Shin Fu'ad Ahmed Marwan zai amshi Meriama? Me yasa Alhaji Ahmed Marwan yayi tunanin bawa Fu'ad Meriama? Shin Yarinye tana lafiya kuwa ina Danginta suke? Da gaske Abin da ya baka tsoro wata rana zai baka tausayi? Lallai tafiyar ba ta wasa bace*
Da 1000 zaku mallaki Books Uku Insha Allah!biyu 700, daya 350....
Anan muka ajiye Free pages...
_Books din da zasu zo kamar haka_
1- Sahla A Paris
2-Bani Da Laifi
3-Abin Da Ya baka tsoro.
Dukkan su Uku 1k
_Guda daya_ 350₦
_Guda Biyu_700₦
_Guda Uku_ 1k
_Zaku iya payment ta to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria_
_and send evidence to does number_
*****
Or
**** or ****
_Dukka zaku iya tura shaidar biya_
_Ga masu turo katin MTN zasu iya turawa Zahrahn Addah Ramlat da kuma Yan Nijar zasu turawa Nana A'ishah_
**** a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah
*+22784506476*
_Welcome ta Top-notch Team_
fatan alkhairi da zaben Top-notch..