Free chapter · Read without an account
Pg 2……
by Fatima Zahrah · ANAYAH
_*ANAYAH*_
_[Heart Touching Story]_
*BY*
_*ZAHRATY* ❤️_
*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*
بسم الله الرحمن الرحيم
*JAN HANKALI:* _*Dan ALLAH in kina karanta littafin kika ji an kira sallah ki tashi kije kiyi,dan ALLAH mu*_ _*rinka kiyayewa Dan gudun fadawa halaka,ALLAH yasa mu dace.*_
*Dedicated to*
_*Queen Lateefat*_
_*Pg 2.....*_
_EDITED_
Salati kawai Dr.Maryam keyi,yanzu kuwa bata san taya zata fara wannan maganar ba,dago kai tayi ta kalli mummy tace "haba mum ANAYAH wannan wani irin magana ne babu dadin ji babu dad in saurare,Dan Allah kiyi hakuri,kisa ma zuciyar ki salama kada kizo kiyi abunda nan gaba zakizo kina dana sani,zama ya kamata kiyi ki bnincika wani dalili ne yake saka mijin ki neman mata saboda wasu m!azan ba haka kawai suke neman mata ba akwai dalili", wani irin murmushi mai ciwo mummy tayi tace" haba Maryam ke me kike tunanin zai saka Sadeeq neman mata,kawai dabbanci ne da akuyanci dake damun sa,Maryam condom fa na tsinta a dakin sa,haba me yake yi da condom,da farko da ace yana da gaskiya zai zaunar dani ne yamun bayani akan abunda na bani,ya wanke kanmsa,amma da yake ance 99days for a thief one day for the owner gama kasa kwanciyar hankali,hankalin sa ya tashi daya tabbatar naa abun, a lokacin sai nayi main uzuri kan cewa kila banashi bane,jiya a nan wata karuwa tazo neman sa,daga nan na dasa alamar tambaya akan shi,na tambaye shi wacece ita,ya kasaa bani ansa,yau kuwa kin San wani abun mamaki,kaya fa ya siya mata,inners da sexy wears na gani a motar sa ,amma a haka kuma ake bani hakuri in cigaba da zama da wanda bai dauki aure da mutunci ba,wanda bansan darajar aure ba,wanda bai san inda ke masa ciwo ba,haka I'm tired wallahi Dr,I can't kawai kind ki same shi ya bani takarda ta,I can't continue living with a man that betrayed me,wallahi Allah sai saka mun,Allah ba zai bar Sadeeq ba sai ya bi mun hakki na",hawaye ne masu zafi suka sauka akan fuskar Dr.Maryam,kallon mummy tayi tace"maza kala kala ne mum ANAYAH,dayawan su akwai abun da yasa suka fara neman mata,akwai namijin da sai bayan da yayi aure ne ya fara neman matan,irin wadannan kuwa sakaci ne daga gurin matan mostly saboda mazan nada kafin sha'awa amma sun kasa kula da wannan sai kiga namiji baya neman mata kafin yayi aure amma bayan auren shi sai kiga ya fara neman mata.Na biyu;akwai wanda yana Neman mata kafin yayi aure amma da zarar yayi aure sai kiga ya bari,wannan kuwa da yawa matan su sun taka babbar rawa gun wannan bar in da yayi saboda kila rashin mata ne yasa yake Neman matan,amma da yayi aure sai kiga ya daina saboda matar shi zata iya gamsar dashi.Na uku;akwai Wanda tun kafin yayui aure yake neman mata,kuma har yayi auren bai dena ma,irin wadannan sai dai ke a matsayinki na matarshi kiyi ta main addua Allah ya shirya shi saboda irin wadannan ma sunfi yawa.Abun dubawa a nan shi ne ke a matsayin ki na matar shi zaki duba me ke kara dilmiya shi a cikin wannan harkar neman matyan,wasu zaki ga yawancvi abokai ne da mutanen dake kusa dasu sosai, sai ki San yadda zakiyui ki rinka janye shji daga abokan da baki gamsu da abokantakar su bana,in Allah yazo sai kika ga ya bari amma bari in fada miki wani Abu,duk wacce mijinta ke neman mata sai tayi hakuri,zina Nada wahalar dainawa ga mai yinta,amma in Allah ya taimake ki mijin ki ya tuba ya bari tareda alkawarin insha Allah bazai koma mata,shikenan sai ki gode ma Allah",hawaye ne suka zuba akan kuncin mummy tace"mum Munaya wallahi bansan sanda Sadeeq ya fara neman mata ba,I'm trying my possible best inga cewa ban tuye Sadeeq ba a shinfidan shi,mum Munaya abunda ke kara daga mun hankali shi ne Sadeeq fa Zina yake aikatawa da auren sa fah,bai duba mai wannan dabi'ar zaij haifar ma family din nan ba yake aikatawa,mum Munaya kar ki manta cewa Zina bashi ne in har ka aikata sai an aikata maka,in ba'a yi da yar ka ba,za'a yi da matar ka,ko da mahaifiyar ka ko kuma da kanwar ka ko yar ka,ko kuma da katangar gidan ka,mutane da yawa bnasu San mai ake nufi da wannan katangar ba,zai iya yuwa wacce zata gina maka family kenan wato surukarka",hawaye Dr.Maryam ta share tare da cewa"nasan da haka mum ANAYAH amma duk da haka kiyi hakuri ANAYAH bazata iya kula da yaran nan ba in kika tafgi kika bar su,tsaya yara shekara 12yrszata kula dasu,ga Ummusulaim ga Maryam ga Abdallah tsaya zata kula dasu,kin San bazata iya ba",ajiyar zuciya mummy ta saukme sannan tace"shikenan Dr naji zan zauna amma ina mai tabbatar miki da cewa a yanzun duk duniyar nan ba wanda na tsana na tsani gani kamar Sadeeq amma zan yi hakuri in zauna ko dan yarana",cike da farin ciki Dr Maryam tace"masha Allah gaskiya naji dadin yadda kika sauka da wuri haka,kuma ina fatan an sasanta kenan,da izinin Allah ba zai kara shiga cikin lamauran ku ba","ameen ",mummy ta ansa dashi,sannan Dr.Maryam tayi mata sallama ta tafi,har bakin kofa ta rakota sannan ta nufi dakin su ANAYAH ta duba su,Dr.Maryam na fitowa ta tadda daddy a tsaye,kallon sa tayi tace "gaskiya dad ANAYAH banji fadi ba akan abunda ka aikata,baka tunanin wannan abun yana ma rayuwar yaran ka da matsala, its unfair Allah,naji kunya sanda take fada mun abunda ka aikata,haba yanzun ma da kyar ta amince zata cigaba da zama a cikin gidan nan,amma not because of you is just for the sake of her children", kallon ta yayi yace" thank u Dr.Maryam I really appreciate, I know what I'm going to do zata sakko",godiya ya kara ma Dr Maryam sannan ya shige gidan.
Mummy na shiga dakin su ANAYAH kallon su tayi dukka yaran sujka zaune akan bed ta bude storty book din ta mai suna SIGHTING LIGHT IN THE DARK wanda Mr Gambia ya rubuta,gaba daya labarin ya tafi dasu shiyasa ma basu ji shigowan ta ba,kallon su tayi,she's happy yadda taga yaran suna suna cikin farin ciki,kallona tayi tace"Aunty novel like karantawa",dagowadukkan mu muka yi muna kallon ta,ganin fuskar ta da nayi cikin fara'a yasa naji nima zuciya ta cike da farin ciki,cemata nayi"mummy bazaki tafi ba,kin amince zaki zauna damu",gyada mun kai mummy tayi tace"bazan tafgi ba,ina nan tare da yarana abun alfaharina,insha Allahu babnu abnujnda zai raba ni daku zai mutuwa",rungume ta nayi sannan na kalli su Ummu Sulaim nace "hey my dear siblings, come let us jubilate mummy is not going", saka ta saka musu a speaker din dake dakin,rawa muka farayi,babu abunda make jij a dakin sai hayaniyar mu dasiblings dina,kallon mu mummy kawai take yi zuciyar ta cike da farin ciki,tambayar kanta ta farayi" wai dama haka yaran nan suke kaina na,kai daace na tafi na tabbata Dana bar family na cikin tsaka mai wuya da tashin hankali mai tsanani........katsewa tunanin ta yayi jin daddy ya shigo yana cewa"kai Baku da hankali ne kun cikawa mutane kunne da ihu sai kacewasu mahaukata",kallon sa SULAIMY tayi tace"daddy we are jubilating, our mummy is not going anywhere, she will stay with us",kallon yarinyar yayi sannan ya kalli mummy,MARYAM ce tace, "daddy we love mummy,we don't want her to leave us", kallon yaran yake yi,a hankali idanun sa suka fada kaina,Wanda tun daya shigo name na zauna a bakin gado,kallona yayi yace"ANAYAH ke bakya farin ciki da kin tafiyar mummyn taki ne", mikewa nayi ina cewa" daddy ai ba wanda ya kaini farin ciki da hakan tunda ita din Mahaifiyata kuma abun alfahari na,bani da kamar ta,kuma bani da wanda zan maida a maimakon ta",ina gama fadin hakan ta fada cikin bathroom din dake dakin, kamar yadda kuka sani daddy irin mutanen nan ne !ask saurin fushi da fusata,abun kadan sai ya fusata,haka kuwa akayi wannan maganar ba karamin fusata shi yayui ba,wanda ni kaina bansan main yga fusata shi ba a cikin maganar yawa,fada ya farfa yi kamar yadda ya saba"Fatima kinga abun da kika kawo ko,wai kamar ni wannan yar yarinyar ke fada mun abujn da yazo bnakin ta koh,toh wallah yau sai daij ta kwana a bayin amma ijn har ta fito na lahira sai ya fita jin dadi Dan naga har yanzun bata gama sanijn wanene force bna,zan nuna mata real colour din na",kallon sa mummy tayi cike da sabon mamaki cike da al'ajabi tace"yanzu Sadeeq ni make blaming akan wannan abunm,toh bari kaji wallahi baka isa ka taba mun yarinya ba,Allah sai dai muyi duk abunda zamuyi da kai amma kayi kadan daka taba mun yarinya",kallon ta yayi yace"shikenan you are joking with me",yana gama fadin hakan ya juya a fusace ya bar dakin,kallon yaran mummy tayi yanda sukayi tsuru tsuru,tausayi suka bata sosai yanda sukayi,bakin toilet din ta nufa,bubbuga kofan tayi tana cewa"ANAYAH my baby bude ya taf",kuka na fashe dashi saboda yadda naji kirgina yayi nauyi ga kuma zafi da yake mun sannan nace"mummy tsoron daddy nae zai dake ni",a hankali mummy tace"sorry dear babu abunda zai miki,fito mana",a hankali na bude toilet din na fito cike da sanda saboda bana son inga daddy a cikin dakin,kallo na mummy tayi tace"ki rage wannan tsoron in ba haka ba zaki rinka cutar da kanki ne,yanzu ku zok muke kuci abinci",mikewa sukayi dukkan mu mujka yi muka nufi dinning room din mu,mummy da kanta tayi serving din mu muka ci,muna gamawa muka tsaya mummy clearing gurin da wanke dishes din,sai da ta tabbatar mun gama kafin muka nufi parlour muka kunna TV,wani file muke farakallo mai suna The seven dwarfs wanda ya dauke hankalin mu daga duk wani damuwar da muka tsinci kan mu a ciki a yau din nan,mun Dade muna kallon film din kafin muka tashi,mummy da kanta ta shirya Abdallah ta kai shi dakin sa,muma sai da ta tabbatar da cewa mun chanza kayan mu zuwa night wear,addu'an bacci tayi mana sannan muka kwanta,sauke mana mosquito net din dake gadon tayi sannan ta mana sai da safe ta tafi zuwa dakin ta.......
Mummy na shiga dakin ta ta tadda daddy a zaune a gefen gado,kallon sa tayi ta dauke kai ba tare da tace komai ba,bin ta shima yayi da kallo har ta gama dukkan abunda take yi,zuwa tayi ta kwanta,kallon ta yayi yace"Fatima wai me na miki ne haka kike shareni,me na miki ne haka da zafi",kallon sa tayi cikin mamaki tace"yanzu Sadeeq har kana da bakin tambaya na me kayi mun nake fushi da kai,toh bari kaji in har kana tunanin bazan iya kallon ka ba in fada maka dalilin da yasa nake fushi da kai ba,toh tabbas ka yaudari kan ka,bari kaji abunda yasa nake fushi dashi shine ka yaudarew ni,ka aikata zina da auren ka da yaran ka,kai kana tunanin Allah zai bar ka ne,toh tabbas kayi ma kanka karya,kuma kasa ba ranka bashi kaci kuma sai an biyaka har da gyara in baka yi hankali ba",wani wawan kallo ya mata kafin ya fara magana cikin fushi"Fatima ni kike wa wannan mugun fatan saboda rashin sanin darajar kai",wanij murmushi mai ciao mummy ta saki tare da cewa"ai wannan maganar da make ganin ina fada maka kana dauka a matsayin mugun fata, toh ka tabbata ya zama gaske,sai da ni ina rokon Allah ya duba mu,ya duba halin da muke ciki nida yaya na,Allah kasa kasa rayuwar su ta wulakanta",wannan maganar ba karamin yima daddy zafi tayi ba,nan da nan ya fara hayaniya da fada wanda har haka yayi sanadiyar tashin mu daga bacci,fitowa parlour muka yi dukkan mu zuwa bedroom din mummy muna kuka,kallon mu mummy take yi kawai,ita kuka mu kuka,wannan wacce irin masifa ce da bala'i ace babu sauran kwanciyar hankali,kallon mu take yi tace"meyesa kuka fito,zo muke Ku koma bacci",rike hannun SULAIMY tayi da MARYAM ni kuma na bisu a baya,sai da tabbatar mujn kwanta sannan ta juya,riko hannunta nayi ina kuka,kallona tayi muryan ta na rawa tace"ANAYAH kwanta kiyi bacci kinji,ki bar sa damuwa a cikin zuciyar ki ",kuka na fashe dashi nace" mummy wai meyesa daddy baya son ki ne,kullum yayhi ta azabtar dake,baya tausayin ki",gogew hawayenta mummy tayui tace"kiyi bacci,in Allah ya kaimu gobe zamuyi magana",daga haka muka koma baccin mun ita kuma mummy ta tafi dakin ta.
Tana shiga bayi ta nufa,ablution tayi sannan tazo ta shinfida praying mat ta fara gabatar da sallahn nafila,sai da ta gabatar da raka'o'i takwas sannan ta fara azkar kamar haka saboda kauda quncin dake cikin zuciyar ta;
لا إله إلا ﷲ العظيم الحليم,لا إله إلا ﷲ رب العرش العظيم,لا إله إلا ﷲ رب السموات ورب الارض ورب العرش الكريم
_La'ilaha illallahul azimul haleem,la'ilaha illallahu rabbul arshil azim,la'ilaha illallahu rabbus samawati wa rabbul ardi wa rabbul arshil kareem._
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,mai girma(wanda babu abin da yake girmama a gareshi),mai hakuri (mai jinkirin azaba tare da cikakken ikon aiwatar da ita).Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,Ubangijin Al'arshi,mai girma.Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah,Ubangijin sammai,Ubangijin kasa,Ubangijin Al'arshi mai yawan baiwa.
اللهم رحمتك أرخو فلا تكلني إلى نفسي طرفة عين وأصلح لي شأني كله,لا إله إلا أنت.
_Allahumma rahmataka arjuw fala takilniy ila nafsiy darfata ain wa aslihliy sha'ni kullahu,la'ilaha illa anta._
Ya Allah!Rahamar ka nake kauna,don haka kar ka kyale ni da kaina ko da kiftawar ido ne,kuma ka kyautata mini sha'anina dukkansa,babu abin bautawa da gaskiya sai kai.
لا إله إلا أنت سبحانك إني كنت من الظالمين
_La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzwalimin_
Babu abin bautawa da gaskiya sai kai.Tsarki ya tabbata gare ka,lallai ni na kasance daga cikin azzalumai
ﷲ ﷲ ربي لا أشرك به شيأ
_Allahu,Allahu rabbi la ushriku bihi shai'an_
Allah!Allah ne ubangiji na,bana yin tarayya da shi da wani abu acikin bauta.
Bayan ta gama ta karanta ikhlas,Falaq da nasi,sannan tayi ayatul qursiyyu da amanar rasulu,salatin annabi tayi sannan ta shafa a fuskar ta,Quran ta dakko ta fara karantawa wani sanyi taji zuciyar ta ta mata duk qunci da nauyin kirjin da take ji taji ya kau,sai karfe uku da rabi ta tashi ta kwanta,wani bacci ne mai dadi ya kwashe ta wanda rabon da tayi makamancin sa tun ranar da baraka ta auku tsakanin ta da Sadeeq.Ana kiran sallahr asuba ta farka,sai da tayi nafila sannan ta nufi dakin mu,tada mu tayi,sai da ta tsaya ta tabbatar da munyi alola kafin taja mu muka nufi dakin ta,sallahr asubah muka gabatar tare,sannan mukayi azkar din safe,juyawa nayi ina kallon mummy da mamaki saboda jin sheshekan kukan ta,kallon ta nayi zuciyata a raunane nace"mummy dan Allah ki bar kuka,bana son ganin hawayen ki ",juyowa mummy tayi ta kalleni hawaye na cigaba da zuba daga idanunta,kamo hannaye na tayi duka a cikin nata sannan tace "ANAYAH baki san kalan radadin danake ciki bane da baki ce in bar wannan kukan ba,ji nake kamar zuciya ta zata fito waje saboda radadin da yake mun,ANAYAH mahaifin ku ya goga mun tabon da bazai iya goguwa a cikin zuciyata ba,mutumin da naba ma amanar rayuwata,zuciya ta,gangar jikina soyayyata da kuma duk wani yarda da nake dashi shi ne wai yake yaudara ta",fashewa da wani irin kuka tayi mai tsuma zuciya da gangar jikin mai sauraro sannan ta cigaba da cewa "ANAYAH a rayuwa ta ba wanda nake mutuntawa,nake darajawa nake ganin qimar sa kamar Sadeeq amma daga shekaranjiya babu wanda nafi tsana,naki jini,bana son ganin sa,bana son rayuwa dashi kamar Sadeeq ",kuka na saki nima kamar yadda mummy take yi kafin nace "dan Allah mummy kiyi hakuri,kisa ma zuciyar ki salaama,nasan abinda daddy ya aikata bai kamata ba,amma dan Allah kiyi hakuri kar ki saka abun a ranki ya hana miki kwanciyar hankali ",girgiza kai mummy tayi tana wani irin dariya kafin tace "ANAYAH har yanzun ke yarinya ce,baki san me rayuwa take ciki ba,bazan taba iya manta abinda Sadeeq ya aikata ba,he betrayed me,yaci amanar kauna da soyayyar da nake mishi,kuma ina tabbatar miki da cewa Allah sai ya saka mun",bude baki na kumayi zan fara magana,hannu Mummy tasa ta toshe mun bakina tana cewa "bana son ki rinka saka irin wannan abin a cikin zuciyar ki zata jawo miki matsala babba,kuma zai taba rayuwar ki,bana son in ga halin dana shiga ko ta sanadina ahalina sun shiga matsala,dan haka ki kiyaye ",gyada kai kawai nayi ba tare da nace komai ba,juyawa nayi na kalli su Sulaimy,suna zaune akan gadon mummy suna kallon wani film mai suna ENCANTO,juyowa Sulaimy tayi tana kallona sannan tace"hi twiny wani kuma zancen ake da mummy come and join us mana",dariya na saki ganin yan uwana cikin farin ciki da kwanciyar hankali,tasowa nayi na hawo gadon dan duk cikin yan uwana babu wacce muka shaku da ita kamar SULAIMY dan tun muna kananu sosai muke matukar son junan mu da kaunar juna,haka nayi joining din su muka cigaba da kallon mu cike da farin ciki da kwanciyar hankali.
Sai da muka gama kallon mu cike da farin ciki kafin muka bita kitchen muka taya ta girki,sai da muka shirya a dining table sannan taja mu muka nufi dakin mu,da kanta tayi ma Maryam da Abdallah wanka,mukuma ni da SULAIMY da kanmu mukayi,shiryawa mukayi ciki riga da wando English wears masu kyan gaske,sai da muka jira mummy itama tayi wanka ta shirya sannan muka zauna a dining muka fara cin abincin mu,har santi muke yi saboda yadda abincin yayi dadi dan Mummy ba dai iya girki ba,muna gamawa muka taya ta kwashe plates din muka wanke,muka dawo parlour muna cigaba da kallon mu.
Mummy zaune take akan gadon ta tana duba wasu takardu,karan shigowan message ne ya jawo hankalin ta zuwa ga wayan nata dake kan bedside drawer,message ne ya shigo wayan ta da wata sabuwar no,da mamaki ta bude message din,abin data gani ne yasa taji kamar bugun zuciyar ta ta tsaya,ji tayi kamar zuciyar ta zata fito,a hankali ta kara karanta message din kamar haka;
"Wawiya ,sokuwa,wacce bata san me ke damunta ba,kin zauna a gida kin saki baki kina kishi mijin ki yana nan tare dani muna more rayuwar mun,in kina so ki tabbatar da gaskiya kizo wannan adireshin,ina tabbatar miki sai kingan mu nida mijin ki turmi da tabarya..........
Yawan comment,yawan typing
SHARE FISABILILLAH
Zahraty
***