Free chapter · Read without an account

Book 1 (Farko)

by Hafsat c Sodangi · AYI DAI MU GANI

AYI DAI MU GANI



Al'amarin ya taso ne tun daga ziyarar da na kai wa Likita don ya kara jaddada in cikar lafiyata kamar yanda ya saba yi min a can baya.

 Sai dai a wannan karon maimakon ya yi min hakan cikin yabawa da nuna gamsuwa da cikar lafiyar tawa sai ya shiga yi min wasu tambayoyi masu tsanani da fadar da gaba har yana bani wasu gwaje-gwaje da ban gane dalilin yinsu ba.

 Karfin hali nayi na danne damuwar dake cikin zuciyata ban bari ya gane tsananin tsoratar da nayi ba na daga ido na kalle shi cikin atsuwa na ce mishi me wannan abin yake nufi Dakta? So kake ka nuna min cewar lafiyar tawa da nake ta tattali tana cikin barazana? Ko kuwa so kake ka fahimtar dani cewar na riga na kamu...." Bai bari na karasa maganar tawa ba ya katse ni ta hanyar cewa, "ba haka nake nufi ba Hajiya, kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki zan yi miki bayanin da zaki gamsu ki kuma dauki komai ya zamo ba komai ba ne.

 Nima ban tsaya sauraron bayanin nashi ba nasa hannu na dauke jakata dake jingine gefen kujerar da nake zaune, na mike tsaye cikin natsuwa na kalle shi

 

12                                                                                                  

 

na ce mishi, "mu bar duk wata magana sai bayan na dawo karbar test din da aka yin, Laraba ka ce ai ko?" Ya gyada kai a hankali don tabbatar da hakan a fuskarshi kuwa ya saki murmushi sannan ya ce, "Laraba za ki dawo Hajiya wacce mutanenmu ke yiwa kirari da tabawa ranar samu, ban saurari murmushin Likitan ba don nasan kokari yake yi wai ya kawar dani daga damuwar da ya riga yayi min dalilin fadawa a cikinta.

A gida rannan zama nayi cikin kunci da damuwa zuciyata takai matuka wajen kuntata saboda nauyin da tayi, naje ziyara don in kara samun kwanciyar hankali abu yana nema ya zama tamfar allura ce take nema ta tono gainma.

Kai kawon da zuciyar tawa take yi shi yai dalilin da na shiga kokarin yin waiwaye wato adon tafiya' kan lamurran nawa don ganin ko zan iya hango wani abin da zai bani haske. Shekaru ashirin baya da suka wuce, shekaru goma ne kacal dani a duniya a wancan loka cin tasowa nayi gaban iyayena biyu wato uwa da uba wadanda suka riga suka manyanta wato shekaru suka yi musu yawa. Ga kuma mas'alar babu, ina kuma da wa mai suna Buhari wanda

 

13

 

 

yake akwai tazarar shekaru har guda bakwai a tsakanina dashi.

Gidanmu wani dan tsukakken gida ne ginin laka 'yan dakunan gidan yan kanana masu dauke da wasu munafukan tagogi da saboda Kankan tarsu ko murfin rufewa ba ayi musu ba, takaici kan kama ni a duk lokacin da zafi ya ishe ni na daga ido can sama na hango su sai in ji ina tambayar kaina ko don me maganin nan yayi tagogin nan oho? Watakila dai keta ce kawai maimakon ya barwa mutane gidan haka kawai babu tagar sai yayi hujin don kawai sauraye su samu wurin shigowa, amma ba don a sha iska ba, gamu da dan kankanin tsakar gida wanda wawakekiyar rijiyar gidan ta cinye daya bias ukunshi abu guda daya dana san bamu taba rashinshi ba tun tasowata a gidanmu shine tsafta, in ban da shi to komai a maneji muke yin shi saboda mafi yawancin al'amuran gidan a wancan loka cin yaya Buhari ne mai tafiyar dasu shi kuma bai kawo karfi ba da dan abin da yake samu a wurin koyon sana'arshi ne yake bayarwa ayi amfani dashi, wannan dalili ya sanya bai zamo dole a gidaninu sai anci abinci sau uku ba mafi yawancin lokaci (1.0.1) wato aci da safe

 

14

 

da rana a hakura sai kuma da daddare, amma duk da haka sai ka ji Baba da Inna suna hirar rufin asirinsu ko ka ji suna cewa wai sun gode Allah kan rufin asirin da ya yi musu ya mallaka musu gidansu na kansu bai barsu suna yawo a gidan haya ba, inda komai kayi ido yana kai koma ace maka don me? Ni kuwa in naji su suna irin wannan hirar takaici ne yake kama ni in ce wannan gidan da mafi yawancinshi ya fadi ko yake gab da faduwa dama sai dashi kuka yi ku ka kama mana hayan gida mai kyau ko da na shekara daya ne in yaso sauran shekarun ma san yanda zamu yi in kudin hayar namu ya kare.

Zan iya cewa ni kadai ce nake yiwa gidan namu irin wannan kallon don kuwa yaya Buha ri ma son shi yake yi don bai gajiya da facinshi musamman ac lokacin damuna yana ganin wani tsaga zai nemi kasa ya hada da suminti ya kwaba ya yabe shi tun daga bandakinmu zuwa tsakar gida har kofar gidan namu kullum fes yake.

A gidanmu ni kadai ce bana ji da gidan nan, har nake ganin abin kunya ne in nunawa kawayena shi in ce shi ne namu don haka ma bana yarda sabuwar kawar da bata san gidan

 

15

 

narmu ba ta biyo ni don kunya nake ji a ganshi musamman da yake a tsakanin tankama- tankaman godaje muke don kuwa unguwar tamu shake talke da tankama-tankaman gidaje na masu hannu da shuni ba sam ba ma ko ganin rashin dacewar dan tsukakken gidan namu a tsakanin tankama-takaman gidajen ne yasa wani makwabcinmu Alhaji sabon kudi ya matsawa Babana kan ya sayar mishi da gidan namu wai zai kara girman harabar ajiye motocinshi shi kuwa Baba ya ce a'a har tayin saya mishi wani gidan yayi a wata unguwar ya tashi ya koma can mu bar mishi namun ya rusa Baba ya ki yarda da hakan duk kuwa da bani ba hatta Inna ma taso ya yarda da hakan ya ki ina jinta tana ce mishi haba Mallam ina amfanin wannan kafiyar can in da zai saya maka din nan ai gida mai kyau ya ce zaka zaba ya sai maka kaga ai mun ci riba tunda mun fita daga cikin barazanar da muke shiga na rushewar gidannan in damuna tazo, nan take Baba ya balbaleta da fada yana fadin ke kike ganin barazana bani ba, wannan gida kuwa komai za a bani a kanshi bana ba yarda shi don kuwa gida ne da kakanmu ya gina da hannunshi mnahaifinmu ya zauna a ciki nima

 

16

 

na ci gadonshi sai kuma haka kawai in rabu dashi? Ya rushen nace yaje ya yi ta rushewa ban fita daga cikinshi, yaya Buhari ya ce haka ne Baba kar ka yarda muyi ta zamanmu a ciki nan Allah ya nufe mu da zama.

Tun ina yarinyayar karama na taso da dabi'a ta shiga gidajen makwabta a lokacin da nake yarinya yar karama babu gidan da bani shiga a unguwarmu, musamman ace an kawo sabuwar amarya inda zaka tarar yara suna taruwa ta sanya musu kallo ko kuma a hadu ana hira, ko da yake a wannan lokacin bana cikin wadanda ake irin wannan hirar dasu saboda kankantata, amma ina son sauraron hirar da za'a tashe ni don a aike ni ma cikin hanzari zan tashi in yi maza in je in dawo don kar a fadi wata maganar ban ji ba, tun a wannan okacin sai na zama babu abin da nake so irin aure nima dai in mallaki dakin kaina ace kuma in yi sa'a ya zamo ina da kayan kallona wanda nima zai sa yara su rinka taruwa min ina basu labarai.

Na fara karatun boko nc a dalılin gajiyar da yaya Buhari yace wai yayi da shiga gidajen mutane da nake yi, Inna. tana kallona ta kasa daukan matakin hana ni vwai daga kawai ya yini

 

17

 

ina cewa Inna su kam gidan Alhaji Sabonkudi da naman kaji ake miyar kukan gidansu, shi ne ka wai ya kama mun kunne ya rike yana ja cikin gargadi da kashedi na kar in sake shiga wani gida in ga abin da ake yi in fito ina ba da labari, duk da ihun da nake yi bai sa ya saki kunnen nawa ba sai da yaga Inna ta taso cikin fusata tana fadin wane irin mugun. hali ne wannan Buhari? Kai kuwa wane irin rashin tausayi ne da kai? In aka barka da Rahina za ka rike ta kuwa?

Bai tanka mata ba ya juya ya fita ya bar gidan ita kuwa tayi ta rarrashina tana bani hakuri har tana shafa min manteleta a kunnen nawa, to wai bayan nanne kuma yaje ya yanko form ya kawo gida da sunan sanya ni a makarantar boko.

Babana ba ma'abocin son bokon ba ne tunda shi da kanshi bai sanya yaya Buhari da yake namiji ba to amma hujjar da yaya Buharin ya bashi na cewar ta hakanne kawai za'a iya raba ni da dabi'ar da nake da ita ta yawan shiga gidajen mutane tasa ya yarda don kuwa shima babu abin da ya tsana irin ya shigo gida bai ganni ba ya tambayi in da nake ya ji ana kame-kamen boye ni don takamaimai ba'a san in da za'ace mishi naje ba.

 

18

 

Na faro karatunne rumu-rumi duk da dai ba sonshi nake yi ba to amma dai ina yi daga makarantar allo har zuwa ta bokon daidai gwargwado ina tabawa ba na cikin 'yan gaba- gaba to amma kuma ba a can baya nake ba, ina cikin yan tsaka-tsaki ne.

Haka nan damar wasanni da nake samu ya rage min yawan kin ta, don haka a kullum gari ya waye zan shirya in tafi ina dawowa gida kuma zan tube kayan maka ranta in sanya na gid ain shiga makwabta musamman in samu Inna bata ajiye min dan wani abu mai dadi ba to ko wanke-wankenta bana kalla balle in tsaya yi, da zata kira ni ma don in yi sai in ce mata na gaji bata da wata damuwa kan hakan balle ta nuna min 6acin ranta sai dai kawai tayi murmushi ta ce ai ko babu laifi na gode.

Kullum yaya Buhari da Inna cikin sabanin ra'ayi suke a kaina, saboda ba ya son yanda take tafiyar da al'amurana na duk abin da nayi tana kallo tana sa ido bata kwaba in kuma nayi fushi tayi ta ban baki tana ba da hakuri tana neme- nemen abin da zata bani don dai taga naji dadi na dan saki raina, ita kuwa gani take ya tsane ni tsananin da yake yi min yayi yawa don komai

 

 

19

na yi sai ya cerdon me? In ya kama na hukunci yayi min ko da kuwa bata so mafi yawancin lokaci kuwa sai bacin rai ya biyo bayan hakan.

Tun farkon sanya ni a makaranta kullum nakan tafi maka ranta ne raina a bace, a dalilin raina kudin makarantar da ake bani da nake yi gashi wani lokaci ma kunu da kosan da nake ka rayawa dashi a raine ba yanda nake son ba bai samuwa sai Inna ta ce in ci dumame in dora ruwan kunu a kai ko da yake dai nasan ba akan son ranta take yin hakan ba, don mafi yawancin lokaci sai ta yi min dogon bayani da ban hakuri kafin ta bani dumamen.

Yaya Buhari kuwa ya asa daurewa ganin irin wadannan abubuwa bai iya jurewa yayi shiru saiu ya ce mata Inna ki rinka baiwa Rahina abin da muke dashi kai tsaye ba sai kin rinka rarra shinta kina wani bata hakuri ba, tun da ke da Baba ku ke ci banga abin da zai sa ita ta kasa yin hakan ba ai ku ne mafi darajar mu ba ita ba. Ki barta kawai ta gane hakan ba ita kuwa sai ta bata fuska ta ce, "a'a barni in rarrashe ta, in kai baka tausayinta ni ina yi, in ta wayi gari bana nan itama ba za ta jira sai wani ya rarrasheta ba." Ya ce mata "to shi kenan."

 

20

A lokacin da na fara wayo a makaranta sai na gano mafi yawancin kawayen da nake tafiya dasu abin da suke ci loka cin break yafi karfin abin da suke zuwa dash1. Sai dai kuma ban san yaya suke yi ba.

Rannan muna hira da wata yarinyar ajinmu da tamu tazo daya Balaraba dan da korafi nake yi mata kan kudin makarantar da nake zuwa dashi nace sule fa ake bani kullum safiya daga sulen nan babu kari.

Nayi-nayi Inna ta kara minn ta ki saboda tana tsoron yayana don shi ke mai bada sulen da ake banin.

Bala raba ta kalle ni cikin yanayin tabewan baki ta ce "Ai ke kin ji dadi, dama ni, kallon yargata nake yi miki." Nayi maza na ce mata "don me ki ka fadi haka? Ta ce "To dubi duk cikin littatafan da ake amfani dasu tun daga na rubutu har na karatu, wato test books, babu wanda ba ki dashi, uniform din ki ma yawa ne dasu na yi maza na ce mata, "a'a kala biyu ne ke dai kullum ana wanke min a ninke a sanya a karkashin matashin kai in na tashi sanyawa sai in dauko su cikin tsabta ta ce to kin gani ai gata ne ya kawo hakan, to gashi kuma har ana ajiye

 

21

 

miki sulen zuwa makaranta kullum ai kin gode Allah.

Na sake zuba mata ido ina kallonta cikin mamaki da kaduwa ni da nake sha'awarta saboda ciye-ciyen da nake ganin tana wuni yi a makarantar sai kuma gashi wai tana ce min ni yar gata ce, to ko dai gatse take so tayi min? Ina cikin shirin yi mata wannan tambayar sai naji ta ce min, "Ni din nan da kike ganina in ban da ina da hikima ai da kashina ya bushe a makarantar nan, to Allah yasa ina da dabara shi yasa asirina yake rufe don ko 'yan iskan kawayen nan namu in suka gane baka da malasa ba harka da kai zasu yi ba." Na sake kallonta na ce mata "menene dabarar taki?" Ta ce min "ke dai kawo sulen naki kawai ki gani gaya min me da me kike son ci lokacin break?" Na tsaya ina kallonta ba tare da na mika mata sulen ba, ta ce "bani mana zan baki biscuit din sisi in baki alalan sisi in baki alawan sisi in baki kunun zakin sisi in mun fita ina ce dai kema kin samu karuwa?

 Na ce eh, amma to mu bari in naga mun fita kin bani sai in baki sulen." Ta ce "au, baki yarda dani ba kenan? Na ce a'a ba haka ba ne, ta ce to shi kenan ki bari sai mun fitan. "

 

22

Mun fita break Balaraba ta tsaida ni a inuwar wata bishiya ta ce in jirata a nan ta tafi da gudu ta shiga tirmitsin yara masu sayen kayan kwalama, jimawa can sai gata ta fito da kayayyakin ciye-ciye iri-iri tazo ta diban mun abin da tayi alkawarin bani tasa hannu ta karbe sulen hannuna ta jefa shi cikin aljihun rigarta tare da cewa, "adashe zan je in shiga da wannan kudin kullum ki ka zo ki rinka ka wo min sullen ki zan rinka baki kayaan break zan yi ta zubin adashe da naki kudin don in samu in tara kafin sallah tazo in sami in yiwa kaina zanin da zan daura.

 Na sake binta da kallo cikin raina na ce ashe yara kan yi tattaki don yiwa kansu zanin sallah?'Ban dai furta mata ba.

Ba mu dauki lokaci mai tsawo da Balaraba muna wannan harka ba na gane hikimar tata shiga cikin tirmutsin yara take yi ta kwashi duk wani, abin da take so tayi tafiyarta ba tare da ta biya ko kobo ba, ko da yake na gane abin da take yin ban daina bata sulen nawa ba don ba zai yiwu nima in yi irin natan ba tunda nasan sata ne, kullum kuwa Inna tana gaya mun cewar komai dan halal yayi a do ne in dai ba sata ba

23

 

ce, sai dai naki yarda da diban mun da take yi muka koma cin komai tare.

A haka muka zauna ni da Balaraba kullum zan bata sulena ita kuma ta shiga ta kawo mana abin da zamu ci, muka kulle sosai kawancenmu yayi karfi ita tana murnan sulen da nake bata nima ina murnar ci gaban da na samu nacin duk wani abin kwalama da nake so in koshi har ma in na tafi gida na samu ba'a ajiye min wani abin da ya gamsar dani ba banci sai kawai in canza kayan jikina in yi ficewata in shiga gidajen sabbin gidajen amaren unguwar in dan taya su  aiki su sanya mana kallo muyi mai kirki daga cikinsu ma sai kaga har da abin motsa baki take bayarwa.

Rannan na dawo gida ban saurari faten tsakin da Inna ke fadin yana nan a dakin dahuwa ba a dalilin ban san yaya Buhari yana nan a gidan ba don da nasan yana nan to da na amsa maganar da take yi min, sai kawai ganinshi nayi ya fito daga dakinshi a fusace yana tambayata ke wacce irin'yar iskar yarinya ce baki ji Inna tana yi miki magana ba ne kika yi shiru? cikin rawar jiki na ce mishi na amsa, ya yi maza ya kara matsowa kusa dani alamar ranshi ya kara baci, yana

 

24

 

tambayata kin amsa kike ce me? Kan in bashi amsa sai ga Innan ta fito daga dakinta cikin sauri tana rike da dankwalinta a hannu tana fadin ya isa haka kar ka ce zaka taba ta. Ya isa yanzun nan ta dawo daga makaranta a cikin zafin ranar nan, ya daga ido ya kalli Inna cikin natsuwa ya ce mata Inna har da wannan rainin da Rahina ke yi miki ba ki ga kamar ya kamata ki bari a ladabtar da ita ba? Tayi maza ta ce "A'a, ni babu wani raini da tayi mun sha'anin ya'yan yau kuma in ma da wani wanda ya raina ni ai kaine.

Ya juya zai koma dakinshi ban san kuma me ya tuna ba sai naga ya juyo ya kalle ta cikin natsuwa ya ce mata amma dai da zaki yarda da kin binciki inda Rahinan take samun kudin da take saye-sayen kayaiyakin ciye-ciyen da na gani a dakinta. Tayi maz ata ce yau to ba gashi ba baga irin rainin naka ba? Ya sake cewa kiyi hakuri kan irin mu'amallar dake tsakanina da yaya Buhari da hana shi sakat da Inna tayi a kaina sai da Babana yasa baki yayi wa Innar ba dadi kan yanda take yi din shine ma har ya dan samu damar ya ganni nayi.

 Laifi yayi mun fada.

 

25

 

Ana cikin haka rannan Balaraba bata zo Makaranta ba hankalina yayi matukar tashi ban san abin da ya hana ta zuwa ba tunda ita ba mai fushin Makaranta bace wani karin tashin hankalin kuma shi ne yau bani da mai debo mun abin break don haka da aka fita break din nima na nufi tirmutsin jama'a don sayen abin da zanci amma ba don in diba ba.

 Ina isa wurin na mikawa Maman guda-guda sulena na debi gwangwani biyu naja gefe na tsaya ina jiran ta bani canjina ba? Ina fadin haka ta waiwayo cikin sauri ta kaile ni maimakon in ga ta miko min canjin nawa da nake jira sai kawai naji ta fara tuhumata yaushe ku ka bani kudin da kike cewa in baki canjin? Kan in ce mata komai tuni tasa hannu ta fige yan gongonayen alalan dake hannuna ta mayar cikin kwanon kayanta.

 Nan take kuma ta shiga yi min kwalala ke wannan yarinyar dama ina mar kin dinki kina cikin yaran dake jagorantar yaran dake zuwa nan suna daka mun warwaro akan kayana, na yi maza na ce ni? Tayi maza ta zaro mun ido tare da buga mun dakinta akan goshina da sunan zunguri tace ke fa, na ce ke kece ko an ce miki bana lura dake ne? kullum ba'a rufe ni a kama rufe ni da

 

26

 

sowa a rudani a wawashe mun kayana ayi ta karbar mun canjin karya sai kin iso kan kayana tukuna, to yau Allah ya kama mun ke ban rude ba tukunna balle ki cuce ni, kin wani coge a gefe kina jiran in rude ki karbe mun 'yan kudina saboda rashin imani da rashin tausayi tun asuba nake tashi in kama aikin abin sana'ar nan amma sai in zo ku warwashe mun in naje gida in rasa yanda zanyi da mutanen da nake karbar kayansu, ja'irar yarinya kawai data maida kanta barauniyar da gangan, ina jin ta fadi na kama kuka mai tsanani.

Saboda ni dai nasan ban ta6a daukan mata wani abu da sunan sata ba, ban da haka ma a wurina sata shi ne mafi munin abin da nake ganin bazan taba yin shi ba a duniya saboda jin da nake yi Inna tana cewa komai dan halal zai iyayi ya zame mishi ado amma ba sata ba.

Na bude baki da niyyar yi mata bayanin da zai gamsar da ita ta fahimci bana cikin yaraan dake yi mata hakan amma ba wai don ta bani sule na ba, sai kawai naji tace mun kance ni ki bani wuri da wannan kukan naki na munarfurci zaginki nayi ko kuwa dukanki? Munafukan yara kawai da tun basu isa komai ba suke koyon cuta

27

 

in baki matsana daina ganinki kusa dani ba sai na kai ki gaban headmastem kun an fito dake gaban assembly tulkuna, da sauri na kauce na bar wurin don nasan wannan shi ne mafi munin wulakancin da zan fuskanta a makarantar.

Na fito daga cikin cincirindon yaran da suka zuba min ido suna kallona na dawo gindin bishiya na tsaya ina ta faman kuka saboda bakin ciki da takaicin lankaya min sata da tayi, ina cikin kukan sai ga wata yarinya tazo wucewa yara sa'o' inta sun rufa mata baya.

 Tana ganina ta taho in da nake tsaye gindin bishiya ina kuka.

Tana isowa wurin nawa ta saki murmushi ke kam da ganinki shagwaba tayi miki yawa, in ba haka ba me zai sa da girmanki ki tsaya kina wannan kukan ido hawaye hanci majina baki kuma a bude? Wani Malami ne ya ci zalinki?

Nayi maza na ce mata, a'a, ta ce to menene?

Nayi shiru ta sake tambayata dalilin kukan nawa kulawar da ta nuna yasa na gaya mata abin da Maman guda-guda tayi mun, ta dan ta6a baki kafin ta ce to babu dadi dai kam abin da baka yi ba ace kayi to amma sai me? Don maman guda- guda ta ce kayi mata sata? Azzalumar matar da tun bamu shigo makarantar nan ba take cutar

 

28

 

yara alalen kwabo-kwabo a gari tazo makaranta tana sayarwa yara da shi kwabo bibiyu? ai in yara sun wawashe mata kaya ma rage cutar da take yi musu suka yi ba haram suka ci ba share hawaye kije kiyi break dinki kin ji? Ungo wannan hannu biyu na kar6i sule biyan da take bani bata jira nayi mata godiya ba ta wuce ta tafi sauran yaran suka bi bayanta, nima na bisu da kallo cikin mamaki sule biyu ta bani haka siyan ko a jikinta bata damu ba ina jin dai 'yar masu kudi ce abin da zuciyata take gaya mun kenan.

Rannan a gida babu wanda bai tambaye ni abin da ya same ni nayi irin wannan kukan ba don kuwa idanuwana duk sun kunbura sai dai ban yarda na fada ba ban ma ce komai ba don ba dabi'ata ba ce yin karya don haka ban yarda nayi wata magana ba har aka gaji aka kyale ni da tambayoyin Balaraba ta dawo zuwa makaranta amma ban yarda na koma bata sule sulena tana debo mana kayaiyaki, mutane ba don kuwa abin da maman guda-guda tayi mun yafi yi mun kama da alhalin kayan mutane da nake yarda ina ci ne ya jawo mun hakan don haka na koma hakuri da abin da nake dashi sai kuma hakan

 

29

 

yayi dalilin raguwar dasawar dake tsakanina da Balaraba.

Kwanaki hudu bayan faruwar wannan abin ina ajinmu ina kuka a dalilin abin takaici biya daya same ni na farko dai ina zumudin zuwa makaranta da sule biyu yau a karo na farko da yaya Buhari ya nishadu ya bani sule biyu don zuwa makaranta sai kuma akayi rashin dace kudin suka zube a filin wasa na tsaya ina nemansu yara suka dawo suka barni ina shigowa Malaminmu ya sani na durkusa na daga hannu a dalilin wai in gama wasan ni ban shigo ba bai burin aje na zauna ya bini da bulala.

 Ina cikin kukan wannan abin takaicin sai ga yarinyar nan ta leko cikin ajin namu yau ma yara suna biye da ita tana ganina tayi murmushi ta ce yau ma kuka kike yi ni in ce ko kece 'yar auta ne a gidanku? ban kula ba balle in amsa, ta dan tsuke fuska kafin tace mun gaskiya in na sake zuwa wurinki na same ki kina kuka zamu 6ata dake wannan ai dabi'ar kananan yara ce nan fa aji uku bane na makarantar secondary amma har yanzu bakya jin kunyar wage baki a cikin mutane kiyi kuka? To ni yaushe rabona da inyi kuka ta dan yi shiru cikin nazari nuna alamar

 

30

 

tunani take yi. Jimawa kadan sai naji ta ce "a'a babu babu zan kai shekaru goma, nayi maz ana dago kai na dube ta zuciyata cike da mamakin yanda za'ayi mutum ya shekara goma bai yi kuka ba, sai naga ta sake kallona cikin yanayin tabe baki ta ce wai ma menene amfanin yin kuka ne? Ai kuka dabi'ace ta ragwayen mutane ai ni ko abu yana cina a raina ban zubar mishi da hawaye, bana yarda barinshi kawai nake yi yayi ta cin nawa muna fafatawa dashi, ko sanda nake yarinya karama kuwa da Innata ta nemi maidani jaka kullum sai ta buge ni barinta nake yi tayi ta jibgar nawa sai ta gaji ta bari don kanta amma ba zan yarda in zubar mata da hawaye ba balle inje in wage baki mutane suna jina, na kara zaro ido cikin wani mamakin ina kallonta, cakulet ta miko min da ta debo daga aljihun jakarta cikin tafin hannunta nasa hannu biyu na karba ina shirin yi mata godiya sai kuma ta biyo bayan cakulet din da naira biyar wai duk nawva ne bata kurma jira godiyartawa ba tasa kai ta tafi na sake bin yan rakiyartata da kallo cikin zuciyata ina tunanin tabbas wannan in ba 'yar gidan sarauta bace to tabbas 'yar masu kudin gaske ne nan da nan na shiga kwatanta yanda

 

31

 

girman gidansu ya kamata ya zamo da kyan tsarinshi da wasu daga cikin gidajen unguwarmu, wani lokacin ma in ce kai ya kamata ace nasu yafi haka.

Bayan tafiyarsu na zauna ina shan cakulet din nan ina sosa kunnena don dadi tare da tunanin ko sunan ta ban sani ba nan gaba dai duk inda na sake ganinta zan tambaye ta sunanta da kuma ajin da ta fito, rannan na fito daga cikin ajinmu sai gata zata wuce yamma da yara a bayanta na karasa wurin da taja ta tsaya na kale ta cikin murmushi na gaisheta ta ce a to ke ba kya neman mutane sai dai kullum a neme ki, na dan yi murmushi nace mata ai ban san a jinki bane dama sunanki, 'yan bayanta suka barke da alati tare da tafa hannu yanzu, nan baki san sunan Lari baby ba? to waye bai santa ba a makarantar nan? Ta yi murmushi ta ce a'a bai zama dole sai kowa ya san ni ba tunda ga Rahina ma nina san sunaki duk da baki gaya min ba tun ranar da na fara ganinki na ji ina sonki saboda ni mai dabi'ar son kyawawan yara ne balle kuma kyau irin naki ina nufin boyaiyen kyau wanda ba farat daya ake gane shi ba da zanyi sa'a uwarki ta yarda tace ta bani ke da tavi

 

32

mamakin yanda zan gyara mata ke don kuwa ina sonki. Yaya ke fa kina sona? ban taba gamuwa da wanda yayi min irin wannan tambayar ba ajinshin mata ko maza don haka zuba mata ido nayi ina kallonta cikin nazari da tunanin dalilan da zasu sa in sota din ko kuma in kita, bata barni na kai karshen tunanin nawa ba sai naji ta ce any way zo muje kayi break ba yanzu za ki bani amsar ba.

Ina cikin yaran da suka rufa mata baya zuwa shagon wata mai masa dake can wajen makarantar tamu gaba daya muka hau kan bencina muka zauna muna jiran a zuba mana gabana sai faduwa yake yi, yana dakan uku-uku ban taba shiga shago irin wannan ba balle har inn dare kan benci in zauna ina jiran a bani abin da zanci allhalin ga wasu kartin mutane a ciki da ban hada komai dasu ba, kunya ado ne wurin 'ya mace, kalmar Inna da ta fado cikin raina kenan, nan da nan na shiga waige-waige ina zazzare ido ina kallon mutanen wurin nan tare tunanin yanda za'ayi in iya buda baki a gaban sa ina lomar abinci? Ke fa guda nawa za'a zuba miki?

Mai masa ce take tambayata, lokacinne na gane ashe tuni ta gama sallamar sauran yaran da

 

33

 

muka shigo tare saurari, nayi maza na ce mata daya da sauri ta ce daya? gaba daya mutanen wurin suka kwashe da dariya. A'a ba ci zaki yi ba, ta sake fadi.

Lari baby ta kalle ni cikin murmushi ta ce kici abinci muna Rahina a baki biyar, nayi maza na ce a'a dayar ta ishen ta ce to a bata daya a bata nama biyar, aka zuba aka miko mun na karba na rasa yanda zan yi in gutsura in kai bakina saboda gani nake tamfar ba mutanen da nake tare dasu a cikin shagon ne kawai suke kallona ba hatta masu wucewa ma idon su a kaina yake, gaba daya sauran 'yanmatan sun gama cinye nasu sai sakuce suke yi wasu suna ta faman gyatsa yayin da Lari ke shan maltina a dalilin tace wai malt kawai zata sha to kiyi kici mana mu tafi Rahina ke fa muke jira don kar kuyi lattin komawa aji ko? tunda naga alamar bakya so a taba miki jikin nan naki, maimasaa tayi murmushi ta ce hala bata son duka? da sauri Lari ta ce mata ko kadan ta sake wani murmushi ta ce tana gaskiyarta, loman masa daya nayi na hadiye ta dakyar saboda na kasa jin dadinta ga wani uban yajin da ya kidimani nayi nufin barin masar in cinye naman dake ciki tunda ni dai

 

34

nasan ko kura bata fini son cin nama ba, sai dai ina jefa naman baki na naji ba zan iya cinshi ba da kyar nake iya motsa bakin nawa, na faki idonsu na fito dashi na rike a hannuna na kalli Larin na ce mata "na koshi." ba tare da ta 6ata rai ba ta ce to mu tafi, muna fitowa ta danka min sule biyar tsaye ga wannan ki samu wani abin kici na karonda nayi mata godiya muka kamo hanya muna lafiya yaran sai hirar dadin masar suke yi ni kina jinsu ban ce komai ba haka nan itama Larin sai da taji hirar tayi yawa ne ta ce musu kai ku kam babu abinci mai dadi a gidajenku in ba haka ba menene na wannan santin? Rahina ko tsoka daya bata hadiye ba balle aje ga cin masar suna jin haka suka kama adin a'a Larin caf, ita kuwa sai ta kwashe da dariya.

Yau da gobe hausawa suka ce wai ita ce maimaida tsohuwa yarinya ban san yanda aka yi ba ban ankara ba sai kawai ganina nayi na kware a cin masar mai masan nan har nima ina gane dadinta ina yin santinta ashe rannan kunya ce ta takura ni ta hana ni gane dadin nata saboda takurar da nayi, kan kace meye wannan sai na sulle na zama ba masar mai masa ba kawai duk

 

35

 

wani wurin sai da abinci da muka shiga ina iya zagewa in bude bakina in cika cikina sai naji na koshi in dora kwalbar lemo akai har ma in zauna in yi sakuce yau da gobe mai sawa a daki amarya in ji Hausawa a hankali sai muka yi wata irin shakuwa da Lari shakuwar da ba zan iya kwatantawa ba, Lari tana sona wani irin matsanancin son da ba zan iya tsayawa ina badaa labarinshi ba, komai yi min take yi komai kawo mun take yi in muna tare da sauran kawaye hirata ita ce tata zancena shi ne abin sauraronta shawarata kuma ita ce abin dauka.

A hankali sai na gane ita Lari ta shigo Makarantar ne kai tsaye ta fara daga S.S.2 ina ganin wannan shi ne dalilin da ya sanya ban santa ba a tsawon zamana a makarantar sai a wannan lokaci.

Rannan muna hira ni da Larí ita tazo kofarajinmu ta same ni sai na kalle ta na ce mata yanzu saura shekara daya ki gama karatun nan Lari, ta dago ido cikin natsuwa.ta kalle ni ta ce- mun har kema Lari zakí kira ni? Bani da mutuncin da zaki ce mun Antin ma? Na ce mata to kiyi hakuri daga anti zan rinka kiranki ta ce vauwa to ko kefa? Menene maganarki nace a'a

 

36

 

 

gani nayi saura shekara daya ki gama ki tafi jami'a abinki, ta kalle ni cikin natsuwa ta ce mun in kina so ai sai in yi zamana in jira ki kawai mu gama tare, da sauri na kalle.ta ina dariya nace kiyi ta zama a' makaranta kina jirana? ta ce yo to menene? wannan al'amari ai duk sana'ace kawai ta jawo haka in ba haka ba abin da ya wuce ka ai ya wuce ka ban gane wannan bayani na Lari ba ban kuma nemi karin bayanin ba balle in fahimta.

Shakuwata da Lari a wannan lokacin ba karamin amfani yayi mun ba don kuwa a gidanmu al'amura sun kara cakudewa dan abin da Babana yake kawowa wanda saboda raina shi da muke yi har bama sanya shi a lissafi babu, saboda ya kwanta jinya a wannan lokacin ne muka gane komai kankantar akwai gara shi din da babu, komai yaya Buhari ne mai yi har da neman magani sai ko kanwar Baba dana ci sunanta Baba Rahina itama tana iyakacin  kokarinta, gaba daya hankalin gidan ya koma kan rashin lafiyar Babana don haka dan abin da ake samun mafi yawancinshi kan maganar magani yake Inna kanyi hikimominta ne kawai ta samnan wa mutanee abincin da zasu ci bata

 

37

 

 

damuwa da cewar sai mai dadi ba, sa'a ta kawai dawowa gida nake yi cikina a cike, don haka in

na dawo na tabe sai in shiga cikin ayyukan da ake yi na hidimar gida saboda nima ciwon na abana ya takura ni ban saba ganinshi a kwance ba duk da dai shi din mai yawan lalurare amma ba mai kwanciya ba duk da halin da ake ciki na jinya a gidanmu da kai kawon yaya Buhari, cikin rashin kwanciyar hankali wai ya riga inna gane bana cin abincin gidan nan rannan ya dawo da rana wasu magunguna da Likita ya rubuta ya sayo ya kawo sai muka gamu dashi a zauren gidanmu ina shirin fita shi kuma zai shigo, na danja da baya nace mishi da zuwa a hankali don nasan shima bai cika damuwa da amsa gaisuwata ba saboda mafi yawancin mu'amular dake tsakanina dashi ta muzurance ja yayi da baya ya tsaya yana kallo har zaki fita ne? Nayi maza na ce mishi ba inda zani, ya ce to, to koma ciki ki hakura ki zauna a can tunda dai ke darma ba ayi ki don ki, rinka zaman waje ba, ban bata lokaci ba na juya daga cikin shi kuma ya biyo ni, tare da tambayata ni a ina kike cin abinci ne kwanan nan? bakya cin abincin da ake ajiye miki, nayi maza nace mishi ina ci mana saboda

 

38

 

nasan bana barin abincin a kwanon da ake zubawa, har yayi kamar zai wuce sai ya juyo manafa naji kamar kin ce min? Ban yi musu ba nan take kuma nayi hanzarin tsuke fuskata ina muzurai tare wurwurga idanuwa ko'ina alamar dai rashin mutunci saboda in fahimtar dashi cewar yanzu ba da bane don na ji Lari tana cewa ai wani fadan ma kai kake bada damnar ayi maka amma mutum yana farawa kayi maza ka tsuke fuska ya gane ba wasa tuni da. shima zai shiga taitayinshi yayi harkarshi kaima kayi taka.

Sai dai ni kam nawa muzuran basu sanya yaya Buhari shiga taitayinshi ya kama harkar gabanashi ba don kuwa sauri yayi ya karasa dakin Inna ya bayar da magungunan da yazo dasu yana gama bayanin yanda za'ayi dasu ya biyo ni dakin a dana shiga ina jiran ficewarshi kafin nima in fita ina cikin tunanin daga yanzu irin muzuran da zan rinka yi mishi kenan in ya ce zai yi min fada sai gashi ya fado dakin yana shigowa ya rufe ni da duka tare da tambayar ni kike yiwa irin wannan kallon? duka yake yi babu kakkautawa babu saurarawa ni kuma ihu nake yi ina karawa amna ban ga alamar mai ceto ba tamfar dai babu kowa a gidan, da kyar

39

na samu na sabuto na yiwo tsakar gida da gudu nayi nufin fadawa dakin Innata Baba Rahina ce tsaye a bakin kofar tayi maza ta dakatar dani ta hanyar nuna min hannunta kar kiyo nan koma can kiyi ihun naki ja'ira kawai mara mutunci ai Buharinne maganinki in ban da dashi din a gidan nan da ban san iyakacin sakarcin da kika yi ba.

Yaya Buhari ya fito da zabgegiyar dorinarshi a hannu yana huci alamar in so samune banki ace ya kara min dukan ba ni kuma nayi maza na kara kaucewa daga gare shi, kayi hakuri Buha ri kayi hakuri ka rinka yi mata addu'a kana yi mata nasiha maimakon duka akowane lokaaci cikin natsuwaa tayi mishi wadannan kalaman.

Inna ta ce ai shi bai san ana wannan ba sai gwada karfi da sauri baba Rahina ta ce mata uh'uh Maude kar ki fara kar kice zaki shiga tsakaninsu in har kika yarda kika taimaki Rahina ta raina wanta to kema ba kwashewva kalau zaki yi a wurinta ba, wannan yaro ai a tsaye yake kan komai shi din jaruma ne in kika taimaka mishi akanta sai ya zame mata uba amma ba ki ce zai yi gini ki rushe ba, a hankali

 

40

 

Baba ya buda baki ya ce mata kullum abin da nake kokarin fahimtar da ita kenan.

Kwana biyu a jere banje makaranta ba saboda ba dukan wasa yaya Buharin yayi min ba, gashi kuma ya dakatar dani daga fita gaba daya ya ce wai sai ya gama binciken da yake yi a kaina tukuna da taimakon Baba Rahina ko leka kofar gida bana yi saboda a wurin ta komai yaya Buhari yayi daidai ne duk wani motsi da zai yi a kusa da ita albarka zaka ji tana sanya

mishi, gaba daya na takura ga yunwa dakekwakwulata na saba wuni ina ciye-ciyen abubuwa makaranta har ma in makalo wasu a jakata in dawo dasu gida in na shige dakina in rinka ci to gashi ba zato ba tsammani an hana ni zuwa makarantar balle in je in dan samu da kamar nasan za'ayi hakan nema to da na yiwa kaina dan tanadi, dana tsunduma cikin tunani mai zurfi sai naga babu abin da ya dace dani irin yin addu'ar Allah dai yasa ba gaba daya ne yake nufin ya cire ni a makarantar ba tunda in yayi hakan babu mai cewa don me? dama shi yaga dama ya sani yake kuma daukan dawainiya komai don hatta kudin makarantata shine mai bani, to balle kuma kayan karatun da kudin

 

41

 

break yanzu in ya ce ya cire ni yaya zan yi nayi maza na kawar da wannan tambayar don bana  Son jin amsar da zuciyata take shirin bani.

A kwana na hudu ne naje makaranta bayan an wuce asabar da lahadi wato litinin kenan, ina isa makarantar ajin su Lari na dosa don in sanar da ita nazo, rike baki tayi da hannayenta duka biyu wai alamar mamakin nata ya tsananta, ke baiwar Allah kar dai ki ce min lafiyarki kalau kika yi min wannan lalatar? Yo to lalata mana zan ce ai kin san in banganki ba bani da kwanciyar hankali ko kin san jiya ko bacci banyi bana kalle ta cikin kaduwa saboda ban aba samin ana kasa bacci don wani dalili ba, haba dai bacci? ta ce uhun kin maida son da nake miki wasa shi yasa bani da mutunci a wurinki zakiyi fashin makaranta ba za ki gaya min ba ganin yanda ta dauki abin da tsanani yasa na ce mata Babana ne bai da lafiya don kar taga rashin kirkin nawa da yawa, ina fadin haka

ce, waiyooo, ki ce muna da dalili mai karfi mana ni fa nasan banza ba zai sa kiyi mun irin wannan wulakancin ba, to bari maje in gaishe shi.

 Gabana ya rigigigigi! dana ji ta ce zata fadi mata nayi don in wanke kaina a wurinta ba don

 

42

ta ce zata ba bakina ya jawo min abin da zuciyata ta fadi kenan.

Muna tashi daga makaranta rannan sai ga Lari a kofar ajinmu wai zata ta gaida Babana na ce mata mu bari sai gobe nufina in ta yarda da hakan goben sai in ki zuwa, sai naji ta ce "a'a, a'a ai ba ayin haka shi mara lafiya gaggawan zuwa gaishe shi ake yi don a samu alherin dake cikin ziyarar, muje kawai muje ai dama tuni nake tunanin ya dace musan gidajen juna don un riga mun zama daya."

Kan dole Lari ta taso ni a gaba muka kamo hanyar gidanmu muna tafiya tana cewa, "ashe dai ba karamar tafiya kike sha ba kan ki zo makarantar kullum bari na rinka baki kudin mashin kina hawa." Ban tanka mata ba saboda da damuwar da take zuciyata tayi yawa, farko dai ban son Lari taje gidanmu don nasan idan suka yi ido biyu da yaya Buhari abin ba zai mun dadi ba, dama ya tasa ni a gaba da tashin hankali kan yawan kawayena to maimakon yaga ina ragewa zai kara ganina da wacce bai taba sani ba na biyu kuma bana son Lari tasan gidanmu saboda bana so taga dan tsukakkeen gidanmu ginin laka don kar ta raina ni tunda ita kam ko

43

 

da gani nasan Babanta hamshakin mai kudi ne, ko daga irin kashe-kashentama ba sai ta tsaya yin bayani ba, ina ganin ma wannan gamsuwar da tayi ne yasa bata maganar iyaye ko ana hirarsu kuwa bata tsoma baki, sai dai tayi ta bin ku da kallo tana tayaku dariya in har taji kun yi abin dariyar.

Har muka iso unguwarmu ban ce mata komai ba ita kadai take ta zancenta, itama kuma bata nuna matsawa kan sai na amsa mata ba, ni dai tafiya kawai nake yi ji nake kamar in zabi wani tabkeken gida cikin gidajen unguwar tamu in shiga ina mata shine namu sai dai kuma babu hali, akan dole na wuce tabka-tabkan gidajen na dai shigar da ita namun.

Muna shiga ta zube a kasa tana gaida Baba Rahina cikin mutunci da girmamawa tare da tambayarta yaya mai jiki? Ta ce a'a jiki da sauki an gode Allah, gashi nan ma yau ya samu sauki, suka kunma gaisa da Innata itama da fara'a ta amsa mata shiga ki kawo muku abinci ta bani umarni babu halin in ce a'a saboda Baba Rahina naje na dauko naja Lari zuwa dan tsukakken dakina na ajiye mana abincin tuwon dawa ne miyar zogala bacin wasa Lari tayi mishi har naji

 

44

 

mamaki ta gama shanye miyar tana lashe hannu ta kalle ni ta ce mun "Kai Rahina mutánen gidnaku sun iya miya na kalle ta kawai nayi murmushi na kwaso kwanikan na fitar da su itama ta biyo ni ta wanke hannunta sannan taje tayi sallama dasu Inna ta kawo kudi masu yawa ta basu wai a sayawa Baba lemo da ayaba, na biyo ta zuwa zaure muka yi sallama na dawo Baba Rahina ta kalle ni cikin fara'a ta ce aiya wannan Malamar kune? Ni kuwa saboda in kara burgewa don naga amin kudin da ta ajiye musu da sunan sayen lemo da ayaba sai na ce mata a'a daliba ce kamar ni ai ma kawata ce, ina fadin haka ta kama salati "kawarki Rahina? wannan ai ta haife ki." Inna tayi dariya, ta ce "haihuwa gaba daya? Baba Rahina ta ce eh kwarai kuwa ai wadannan mazaunai nata bana yara ba ne na dubi bayanta ai da zata fita, ko da yake kana iya kawance da sa'ar uwarka amma ke da ita kawancen naku bai dace ba, wannan lokaci da zata sai dake ta kar6e kudinki kina ina?" Yaya Buhari ya shigo fuskarshi a daure baba wacce mata ce wannan na gamu da ita a kofar gidannan?" Ta ce mishi kawar Rahina ce tazo gaida Mallam gama kudi ta bayar ta ce a saya

 

 

45

mishi lemo da ayaba, ranshi a bade sosai ya ce to kuma Baba sai a karba? Me za'ayi da kudinta? wannan ai karuwa ce ba ki ga yanda ta maida kanta ba? Fuska ta zama kala biyu, yanzu ke wannan ba abin kunya ba ne a ganki d aita ba? wannan bata kusan yin jika dake ba? Baba Rahina tayi dariya ta ce, a'a bata yi jika ba dai kam amma ko shale ka bana yi ta haife ta, wannan kan ko tantama bana yi, gama kudi ta bayar ta ce a sai wa mai jiki lemo yayi maza ya ce to baba sai kuma ku ka karba? ta ce, to ai an ce ne ba'a maida hannun kyauta baya, yayi maza ya ce, a'a Baba ban da irin kyautar wadanan su duk abin da kaga sunyi suna da dalilin yinshi zai yi wuya kuma ka samu Allah kadai suke nufi don haka a bata gobe ta mayar mata kar a yiwa Baba amfani dasu, ta ce a'a ban da mayarwa kam kai dai tunda kace kai dashi ba kwa so to bari ni da Mande mu raba ko kuwa me ki ka ce Mande? Inna ta ce kwarai kuwa."

Washe gari a makaranta Lari ta tambaye ni wannan da muka gamu dashi a waje shi ne yayan naki? Na ce mata eh, ta dan yi shiru cikin nazari kafin jimawa kadan bakinta ya furta kyakkyawan saurayi sai dai ban sani ba ko ba

 

46

 

ason ranta bakin nata ye fadi hakan ba, ta sake kallona cikin natsuwa ta ce mun da ya shigo gida ya ce? na shiga inda-inda ina cewa bai ce komai ba, tayi murmushi ta ce gaya min kawai raina ba zai baci ba zan dai san matakin dauka ne kawai ai na riga naga irin kallon da yayi min, tana fadin haka na gaya mata gaskiyar abin daya fadi duka, ta tsaya kawai tana kallona kafin daga bisani tayi wani munafukin murmushin ba bai kai murmushi ba ban kuma gane me hakan yake nufi ba ta dai bude baki kawai ta ce min hakuri kawai zan yi don ba zai yiwu ya raba mu ba, ko kin goyi bayan ya rabamun? tun bai kai ga bata amsa ba sai ta ci gaba, "yana sonki ina Sonki, yana da dalilanshi na sonki kamar yanda nima nake da nawa dalilan, kowa kuma yana da irin tashi manufar akanki, abin da nake so dake kawai shi ne ki gane ki kuma yarda da cewar ina Sonki, nayi kamar in tambaye ta to don me kike Sona sai na kasa na dai ja bakina kawai na yi shiru.

Kwana biyu bayan zuwan Lari gidanmu ta nemi nima in je nasa gidan sanin da na yi yaya Buhari ya yi alkawarin kara sa ido a kaina yasa ban yarda da tayin d atayi min na zuwa gidan

 

47

 

nasu ba, na ce mata ba yanzu ba, ta ce sai yaushe? na ce sai Babana ya ji sauki tayi maza ta ce, eh ai kuwa kina da gaskiya kinga har da cewar da yayanki yake yi na haife ki gashi kinyi aiki da hankali fiye dani shi yasa baka raina aboki komai girman da kayi mishi in kuka yi mu'amalla tare baka rasa abin da kake samu na karuwa daga gare shi ba.

Mun ci gaba da mu'amalla da Lari a makaranta, mu'amalla mai dadi duk da kashedin da kullum yaya Buharin yake yi min a kanta sai dai na dauki matakin zuba ido wai don in hango cutarwar da yake cewa zata yi min.

A gida Baban ya ji sauki har ma ya fara fitowa waje yayi hira tare da abokanshi in ban da ma yaya Buhari ya ki yarda ya koma zuwa kasuwar shi da yanzu ya fara fita amma ban yarda na gayawa Lari ba don kar ta ce mun sai na je gidan su a gidan rannan yaya Buhari da Baba sun dawo daga sallar juma'a yaya Buharin yana biye dashi a baya ya rike musu dardumar da suka yi sallar akai suna tafe kuma suna hirarsu ina jin Baban yana ce mishi to in daina fita kasuwa in zauna gida in yi me? Kuma

 

48

 

hidimomin gidan fa? ai baka kawo karfin da zaka dauke nauyin komai ba.

Yaya Buhari ya ce eh, baba amma da ka kwanta jinya ai an hakura da fitan dole don haka yanzu ma a ci gaba da hakurin kawai zuwa lokacin da Ubangiji zai warware mana komai amma ba zai yiwu ka sake komawa cikin wannan wahalar ba kullum wuni a rana wataran ma aje a dawo ba'a samo komai ba, ga kuma shekarun girma ai ka kai lokacin da ya kamata ace ka huta.

 Da sauri Baba ya ce, "a huce nake bani da wata wahala na kuma gode ma Allah da ya bani kai ya kuma yi wo ka mai kokari ina rokonshi ya yi wa kokarin naka albarka.

" Suka ci gaba da hirarsuu daga ni har Inna dai babu wanda yaso hana Baba fita kasuwa da yaya Buhari ya yi ni dai na 6ata fuska nayi shiru yayin da Inna taja tsaki ta ce "wannan yaro da dorawa kai wahala yake ai sai yayi tayi in mutum yaga zai iya hadiyan gatari ai sai a sakan masa kota hirar tasu tayi tsawo har yaya Buhari ya shiga tambayar Baba izini don yana son barin wurin maigidanshi.

 Da sauri naji Baba ya tambaye shi dalili, ya ce ketar mutumin ne tayi yawa. Baba, dubi irin wahalar da nake yi mishi

49

 

 

amma bai san in na tashi zan tafi ya kawo wani abu ya bani ba ya kuma san na iya aikin nan ba wai ban iya ba ne tunda ko bana nan aka kawo aikin ba zai yi ba ba kuma zai sa wasu suyi ba sai ya ce a bari sai nazo, amma bai san ya kyautata min ba har makwabtanmu nan sun gane nine mai aikin nashi in kuma na bar wurin zai iya jin jiki don suna cewa in dawo wurinsu za su biya ni ladan da na nema.

 Baba ya yi maza ya katse shi ta hanyar jan tsaki mai karfi ya ce, "yanzu naji batu kace an zugo ka ne kazo in mara maka baya ka yi wa maigidanka tawaye don anga ka iya aiki za'a rabaka dashi don har yaci amfaninka to ni ba'a wannan rashin mutuncin dani ban yarda ba yanda ya wahala ya koyar da kai haka zaka zauna ya ci amfanin alherin da yayi don kuwa bai yi maka mugunta da ba ka iya ba ina laifinn wanda ya yi maka dalilin iya sana'ar da zaka rike kanka har ka amfani wani naka, mahakurci ai shi ne mawadaci kana nan din sai kaga watarana ya sallame ka don kanshi ya ce kaima kaje ka bude naka wurin kuyi rabuwar girma da arziki ai yafi ace batawa kuka yi kar ka yarda ku bata ubanka

 

50

 

ne kaji ko baka ji ba? Yaya Buhari ya ce mishi naji Baba.

Hana Baba fita kasuwa da yaya Buhari yayi sai yasa ya koma hidimar masallacinn unguwarmu da hantsi lokacin da maza suka fita wuraren harkokinsu shi kuma, sai ya fito ya shiga Masallaci ya share ya goge abin da yake bukatar gogewa ya feshe shi da turare yaja ruwa ya cika durom-durom da ruwa ya kuma dura a butoci ya ar'ajiye in an zo alwala sai dai kawai a dauka.

 Wannan hidima da Baba ya dauka taa yiwa kwamitin masallaci dadi don har turowa suka yi da albishir na sun sanya mishi albashin da zasu rinka bashi kowanne wata, shi kuma ya ce a'a ba don albashi yake yin aikin ba don haka bashi da bukatar karbarsu.

Yaya Buhari mai okari ne kwarai ko daga fitarshi ya samu yan kudi zaka ganshi da sauri ya dawo gida ya kawowa Inna don a hanzarta ayi mana wani abin in kuwa da auki ya samu ma to zaka ga yayiwo cefanen da kanshi koma yayiwo awun hatsi, wadannan hidimomi da suke kanshi kuwa basu sawa in ance mishi kudin break dina sun kusa karewa ya bata rai sai dai ya himmatu wajen ganin ya kara su amma duk da haka bana ganin

 

51

 

 

kokarinshi na kuma tsane shi saboda ganin da nake yi ya matsa min lamba sa'arshi guda daya ita ce tsoron da nake yi mishi mai yawa ne ba don haka ba da bai ji dadina ba don haka kawai nakan zauna a daki in yi ta kwatantawa kaina irin rashin kunyar da ya kamata in yi mishi a duk loka cin da ya yi mun irin titsiyewar da ya saba sai dai bai yiwuwa ina zuwa gabanshi nake shiga hankalina don kuwa nasan yamutsa fuska kawai in nayi ba kalau zan kwashe ba a wurinshi.

Ban san yanda akayi Lari ta gane Babana ya ji sauki ba sai kawai naji ta rannan tana ce mun yau kam duk tsiyarki sai kinje gidanmu ko yayanki ya ce miki muna cin mutane ne? ban tanka mata ba ban kuma yi muusu da maganar tafiyar ba saboda yanda ta sha mur.

Mashin biyu ta tare mana muka hau, ta ce tafiya har muka isa wata unguwa daidai wasu manyan gidaje muka tsaya a zuciyata na ce dama nasan gidansu Lari dole ya zamo babban gida tana biyan mai mashin kudinshi tana gaya min wanda yasan gidanku ai shi ne ya sanka, amma sanin titi shekara kusan biyu muna tare amma baki san gidanmu ba to in mutanen da

 

52

suke ganinmu tare suka zo nemana a wurinki me zaki ce musu? Ai ba'a yin haka ita yarda da kike ganinta daya ce ta kuma fi komai dadi kamar yanda amana ma take guda daya, ban ce komai ba nabi bayanta muka nufi wadannan manyan gidajen da nake zaton nan zamu sbiga sai kawai naga mun bi ta cikin wani lungu muna tafiya sai da muka dan yi nisa kadan kafin muka sake karya kwana zuwa cikin wani lungun mai yawan kazanta don sai kayi taka tsan-tsan kwarai kafin ka samu dutsen da ka dora kafarka bata nitse cikin kwata ba, sai dai ita kam Lari dab-dab ta jefa kafarta cikin hanzari ta wuce ta barni ina ta fama.

Wani dan tsukakken gida da fuskarshi take kallo cikin lungun muka shiga a zuciyata.... wadannan basu iya tsaida kofar gida ba yaya za'ace kofar gidanka kwata tana malale? Muna shiga ciki na soma ganin abin mamaki babban gida sosai gini irin na da kamar dai namu wani wurin ma ya rushe sai dai wannan cike yake da jama'a saboda sashi-sashi ne sai dai yawan mutanen dake cikin bai anfanawa gidan komai ba don kuwa ko arzikin shara bai samu kazantar dake cikinshi takai mutuka wajen yawa ta

 

53

 

buwaya, kana daga labulen gidan kudaje zasu taso yuuuu su mamaye ka, ga rijiyar gidan a bude babu murfi bakinta ba'a gyara ba daga inda jibgin wanke-wanken gidan ke tare kudaje suna gada a kansu babu abin da zai hana ruwan dattin gangarawa ya koma cikin rijiyar, na dan kauda idona daga gare su sai kuma na hango wata shara tsibi guda tudunta ya kai tsawon dakunan gidan, na ce a'a Allah mai mutane, wai jaba taga bakin mijinta ana kokarin raba muhalli da kazanta su kuma a cikin nasu gidan suke jibge tasu kazantar sannan wani abin takaicin shi ne gaba daya matan gidan daga tsofaffinsu zuwa yaran babu mai riga a jiki babu kuma mai yin wani aiki an hadu ne kawai ana zaune ana hira wuri-wuri kuma wai har suna iya kwashewa da dariya babu kuma abin da yafi komai bani mamaki irin yanda Lari ta keta cikin gidan nan ba tare da cewa kOwa uffan ba, balle ta samu lokacin gaishe su.

Ni kam sai da na bisu da dai-dai na gaishe su kafin na karasa na shiga dakin da naga ta shiga a same ta kan wata dindimemiyar katifa tana rike da rimot tana kokarin daidaita firm din  datake son sanyawa.

 

54

 

Ina shiga ta daga ido ta kalle ni da alamar wani abu ya sosa mata rai ta ce kin tsaya gaida wadannan munafukan mutanen ko? gabana yayi mummunan faduwa ban taba jin inda karami ya zagi babba ba na zaro ido ina kallonta na ce mata har da tsofaffin ma muna fukai ne? ta

gatsina fuska ta ce to sai me? don an cewa tsohon da bai kama kanshi ba munafuki har wani laifi ne yin hakan? na zaro ido na saki baki galala ina kallonta, ta zuba min ido cikin  natsuwa ta ce hala baki taba ganin lalataccen tsoho ba? nayi maza na girgiza kaina nuna alamar a'a, ta gyada kai nuna alamar yarda da maganata ta ce naga alamar hakan ai ke baki san komai ba Rahina kinyi sa'a iyayen da suka haife ki masu tsafta ne don haka zaki dade baki san wahalar duniya ba balle ki san kazantar dake cikinta, sai mu nan ta sake girgiza kai nuna alamar jaddada zancenta, ta sake kallona ta ce to amma ai kin san ana samun tsohon dan daudu ko? na kalle ta cikin natsuwa na ce mata menene dan daudu?

Ta ji? "uhn mu bar wannan zancen Rahina kin j ungo nama kici jawo wannan kwanon na kusa dake kiyi taci sai kin įi kin koshi, ga ruwan

 

55

lemo can na ce mata to ina cin naman tana sake bani wani labarin bayan ta ce mu bar zancen ai nan gidan da kike gani duk yan iska ne a cikinshi kowa nan da kike gani gadararshi bata wuce'yan dakunan da yake ciki nashi ne ba ya ci gadonsu babu mai iya tashinshi don haka sai kowa ya ci karenshi babu babbaka, na ce "au ashe duk mutanen gidan 'yan uwane? ta ce 'yan uwane mana ai wadannan tsofaffin masu dan mul din bakin nan wadanda basu da aikin yi sai gulma dasa ido yan uwan Babana ne yayunshi

ne da kannenshi." cikina ya bada wani irin sauti mai tsananin karfi kulululu! saboda tsoratar da nayi da jin zancen Lari ita kuwa ko a jikinta sai tauna cingam dinta take yi tana kus-karai ras kas in gaya miki tunda suka kyalla ido suka ga babu ubana gidan nan suka bar aikin zumunci suka koma na gulma da sa ido.

Muna cikin haka sai ga wata tsohuwa ta shigo dakin babu sallama amma bata karasa tsufan wadannan can da muka wuce ba, Lari tana ganinta ta hada girar sama da ta kasa ta tsuke fuskarta tsohuwa tana haka ta shiga natsuwar ta tana fadin dama na ce bari in duba in gani waye yake taba miki kofar? bata kalle ta

56

 

ba ta ce uhun nice na dawo, har ta juya zata fita sai kuma naga ta dawo tana cewa, "uh na ce ba, na ce kar ki gaji dai zan samu wani abu ne ko zaki yi girki dani ne? tayi maza ta ce "uh'uh ga wannan." ta mika mata takardar sule biyar ta karba ta fita tana godiya, na kalli Lari cikin natsuwa mai cike da mamaki na ce mata wacece wannan Anti? ta dan yi murmushi ta ce "lah baki gane taba Mamana ne," na ce mahaifiyarki kenan? ta yi maza ta ce eh, ai itama nan da kike aninta bata da dadi ne kafin in koyi dabarar zama da ita ba karamar wahala ta bani ba, fitinanniya ce ta kin karawa babu halin wai taga na fita na dawo sai tazo ta tasa ni a gaba sai nna bata wani abu wani lokacin ma in bata ta raina, to haka ake yi ai ba a kasa nake fita in debo ban kuma fitan da nake yi din abu ne mai sauki itama ta fita mana.

Tana maganar tana kokarin girka mana abin da zamu ci akan dan risho din ta komai na kayan abinci akwai shi a đakin Lari abin har abin mamaki.

Ni dai ina kwance ne kawai kamar ruwa ya Cinye ni, yau ga abin mamaki abin da nake jin yana ta famar fitowa daga cikin zuciyata kenan

 

57

 

shiru kawai nayi ina kallon allon talabijin amma takamaimai da za'a tambaye ni bazan iya fadin komai game da kallon da nake yi ba, saboda hankalina baya wurin.

Tuni na tsinke da al'amarin Lari ita da iyayenta masu abin mamaki iri-iri. Nan take kuma naji ina gasgata kalmomin yaya Buhari da na dade ina karyatawa cewar Lari tafi karfina a dalilin ita din ba sa'ata bace ta girme ni matsanancin girman da ba zan iya ganewa ba saboda kullum tana kokarin maida kanta yarinya, na biyu kuma ni da ita tsarin  rayuwarmu ba daya ba ne abin nufi kowa dairin iyayen da suka haife shi sannan kuma dalilinshi na uku shi ne Lari tana kashe duk wani kwabo ne a kaina cikin lissafi don tana tunanin ta inda zata fanshe abinta ba asara zata yi ba, yau na tabbatar da wadannan duka don kuwa in tausayi ke sata tana yi mun alherin da take yi min to ga wacce ya kamata ta tausaya wa fiye dani ita ce mahaifiyarta d atayi dalilin zuwanta cikin duniyar wacce girma da babu suka mamaye ta in kuma so ne kamar yanda take yawan fada to ita ya kamata taso fiye dani, ina gama wannan tunanin na kudurawa zuciyata rabuwa da Lari ba

58

 

zai yiwu muci gaba da mu'amulla ba tafi karfina. Ko ba komai dai nasan iyayena mutane ne masu mutunci, sun fi karfin ayi musu irin wannan iyashegen ba talauci ba kuwa kome suke fama dashi nasan ba zai yiwu su daga ido su kalli abin da ke çikin hannun 'yarsu budurwa ba balle su nemi ta basu suyi amfani dasi, su mutane ne masu kamewa ban taba ganin Babana a tsayea kofar daya daga cikin tankama- tankaman gidajen unguwarmu yana jiran maigidan ya fito ya yi mishi maula ba ko ya gaya mishi wata damuwar shi kullum wanda yake nufa da bukatar shi shi ne Makadaici,

Mabuwayi wanda in baka rokonshi yake fushi da kai saboda shi ne mai abin bayarwa, bias wadannan halaye nashi sai ya zamo abin girmamawa a unguwar tamu duk da takaicinshi saboda yawan shekarunshi.

Na daga ido na kalli Lari dake ta faman aikace-aikacenta tana kuma bani labarin wai nifa da kike ganina Rahina tun ban fi shekara goma sha hudu ba nake ciyar da kaina in yiwa kaina duk wata hidima ko ciwo nake yi kuwa to ranta mun kudin magani ake yi daga baya inna warke in biya, to menene ni ban gani ba a

 

59

 

duniyar nan? na yi maza na mike tare da ce mata babu, ta yi maza itama ta kalle ni yaya naga kin mike? na ce gida zani don yanzu an kusa tashi Makaranta ke kuma kin san in har aka tashin banje gid aba abin da zai biyo baya ba mai kyau ba ne, ta kale ni tayi murmushi ta ce ai komai zai biyo baya sai kin ci abincin nan da nake girkawa domin ki baga agogo can ba amma haka kawai in yi ta hankolo dominki kice mun ba zaki ci ba to me aka yi kenan? Kallon agogon da nayi naga lokaci yasa na koma na zauna in jira girkin na Lari tunda ya kusa kammala.

Nan da nan ta zubo min a faranti ta iko min gashi nan ban zuba miki da yawa ba don nasan irin cin naki ta koma ta kara jawob wani kwanon wani abin take son bani, tana bude kwanon ta tsaya tana kallonshi cikin takaici gaskiya anayi mun sata a dakinnan nan da nan tana daga tsayen ta kwala wa Mamanta kira sia gata ta shigo cikin sauri tana shigowa Lari ta kalle ta gefen fuskarta ba tare da ta waiwaya ba ta ce mata Mama ana yi min sata a dakin nan ni kuma ina yin kashedin a daina domin ko aljanu ne masu yi min satan in na kama su...ta gyada kai kafin ta ce shi kenan."

 

60

 

Maman Lari ta rasa abin cewa jimawa can ta dan yi kokarin cewa to ko beraye ne? Lari tayi maza ta kalle ta ta ce beraye? gafiyoyi, ta juya ta fita jin abin da 'yartata ta fada mata.

Lari ta dawo kusa dani ta zauna a gefena ta dora tattausan hannunta kan kafadata tana kallona cikin natsuwa ta ce min Rahina ki kwana mana nayi maza na dago ido na kalle ta na ce in kwana? ta ce eh mu kwana abin mu bana son rabuwa dake in dare yayi akwai abin da zan nuna miki ke baki da sakin jiki da mutane yanzu dubi Jamila kwana kwanan nan nake dan yi mata abu amma gashi yanzu har kwana take zuwa tana yi a gidannan, amma ke baki ma taba zuwa ba sai yau saboda bakya sona baki damu dani ba."

Damuwar da ta bayyana a fuskarta tasa na ce, "ba haka bane Anti Lari, mutanen gidan mu ne iyayena ba zasu yarda ba da hakan, musamman yaya Buhari ai duk in da na shiga sai ya nemo ni."

Ta ce, "ke dai kawai Rahina bakya sona amma ni ina ruwana da wannan yayan naki tashen balaga ke damunshi yake ganin kamar shima nan wani abu ne ai kin kwana babu mai ganewa don ba zuwa gida zaki

 

61

 

yi akan kin kwana kin koma ba, a'a tunda ga irin iyayen da kike dasu da irin hikimar da zamu yi musu kin san kowane mutum da irin yanda kake tafiyar dashi bari zamu yi sai kinyi kwana uku ko hudu sunyi nema har sun gaji tun suna jiran dawowanki don su miki hukunci har sun koma addu'ar ki dawo kawai su ganki a raye sai ka wai in sa wasu su madia ke gidan naku akan tsintanki suka yi a bakin titi barayin mutane ne suka sace ki kika kubuto in lokacin yayi zan shirya miki hikimomin da zaki yi babu mnai ganewa mu sai kiga maimakon fada da duka sun koma murna da farin cikin kin dawo gida lafiya a raye."

Ina jin karshen maganarta, Lari ban tsaya bata amsa ba mikewa kawai nayi na tsallake abincin da ta ajiye mun din na fita daga dakin ina jinta tana cewa ina zaki? Ban tanka mata ba, da sauri na fito daga gidan cikin mummunan faduwar gaba saboda na gane agogon dakin Lari ba dai dai yake aiki ba, ina gama ficewa daga kazamin lungun su na kama gudu ina jin Lari tana cewa tsaya in baki kudin mashin ki hau ya kai ki don duk saurinki ba zaki kaishi ba ban kula ta ba.

 

62

 

Gidanmu kawai na dosa don nasan an riga an tashi daga Makaranta tuni, gudu nayi na kusan mintoci ashirin da biyar kafin na isa ko far gidanmu.

Yaya Buhari na fara gani yana zaune shi kadai kan dakalin kofar gidanmu da gwiwowina duka biyu na durkusa a gabanshi a gabanshi.

 "Ina kika tsaya, me ya tsaid ake sai yanzu kika dawo? Ko yau ma kun tsaya diban laka da ginin tukwane ne?" Nayi kamar in ce mishi eh, don yasan muna yin hakan sai kawai na fasa nace mishi a'a gidan su Lari naje ammna kayi hakuri."

 Jikinshi ya dan yi sanyi saboda gaskiyar da ya ji na fadi, me kika je yi? Ban 6oye mishi gaskiya ba ita na gaya mishi duka sai dai ban bashi labarin abin da idona ya gani a gidna ba da tayin da tayi min na in kwana ba.

Ya kalle ni cikin natsuwa ya ce min, "kinyi sa'a da kika fadi gaskiya don yanzu dinnan da kike ganina daga Makarantarku nake na kuma dade da dawowa ga jakar makarantarki can a gida an kuma gaya mun an ganki tare da ita kun hau mashin darajar gaskiyar da kika gaya min ba zan yi miki wani hukunci ba amma zan jaddada miki ki fita hanyarta, cutarki zata yi in ma zuwa yanzu bata nuna miki wani abu ba to

 

63

 

can cikin ranta tana 6oye da wani abu kin san ana saida mutane ko? "

Shawararta ta fado mun na in kwana a gidanta daga baya ta dawo dani gida akan an sace ni ne na kubuto, ki fita hanyarta bake ba ita kin ji na gaya miki nace mishi to na tashi na shiga gida daga Inna har Baba babu wanda bai yi mun magana ba kan fita harkar Lari na ce musu to.

Rannan da daddare ina kwance a dakina ba bacci nake yi ba tunanin al'amuran Lari da abin da na gani a gidansu nake yi, na kara takura kan 'yar katifata na gyara rufana cikin zuciyata kuwa na yarda na gamsu da yawan godiyar da nake jin su Baba suna yiwa Ubangiji kan rufin asirin da suke cewa yayi musu in ma da can bana gane rufin asirin da suke magana a kai to yau na hango shi nima na gane a cikin rufin asiri nake rayuwa don kuwa Allah ya ni'imtani da iyaye masu addini da mutunci gidanmu akwai tsabta da kwanciyar hankali da kuma tarbiya daidai gwargwado.

Washegari na tafí Makaranta da niyyar babu abin da zai hada ni da Lari saboda nima na tsorata da al'amuranta na gane tana da wata manufa akaina don haka na shirya rabuwa da ita

 

64

gaba daya rannan ko sule biyun da nazo da ita daga gida ban fita na kashe ba don yaya Buhari yayi mun karin kudin Makaranta a safiyar ina zaune a aji a lokacin break ban yarda na fito ba sai ga Lari ta shigo ajin namu cikin murmushi zuwa na yi in tambaye ki yaya gajiyar gudu?

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.