Free chapter · Read without an account

CHAPTER 4

by Khadeejah Bint Ismail · WANI RABON........

WANI RABON.................🦋🦋🦋


Khadeejah Bint Ismail (Deejasmah)


Elegant Verified Writers (E.V.W)


In dedication to all single ladies out there...............




CHAPTER FOUR (it wasn't my choice either )


Kukana nayi ma'ishi na share hawayena tuno alk'awarin da naiwa kaina cewa na dena kuka insha allah tunda dai Allah ya gani ba laifina bane na d'auki hakan a matsayin k'addaran da bazan iya kufce mawa ba kwanciyata nai a d'akin dan banso in koma ciki a yanayin da nake ciki don nasan bestie zata iya zargin halin da nake ciki which I don't like 


Tundaga ranar nake d'an rage shigewa hidimar sosai musamman a sabgan da nasan zan iya had'uwa da Mama gudun abunda zaije ya dawo nakeyi ita kuwa creating scene ba wata damuwa bace a wurinta sannan ma banson abinda zaisa ana aibata Mamie this woman has done alot for us in baza mui abinda zaisa a yabeta ba to bai kamata mu aikata abinda zaisa a aibata ta ko a fad'i bak'ar magana akanta 


Sannan duk wanda zai hana d'anshi ya aureka saboda wani dalili marar tushe toh ba k'aramin mak'iyinka bane though bata gabana ko kad'an don na riga na cireshi a rayuwata saidai shi d'in ya gagara cireni daga tashi rayuwar hakan yasa Mama tsanata fiye da baya haka zalika matarshi ma duk inda ta ganni kallon banza ne da habaici but i never care because I'm far better than this abubuwan da suke gabana sunfi k'arfina 


Janye jikin da nai da hidimar yasa bestie jin babu dad'i har tai tunanin maganar da mukayi ne ta janyo hakan saida taji ainihin musabbabin hakan wanda bansan daga ina taji zancen ba hak'uri ta bani sosai nikuma na nuna mata babu komai don na manta waccan maganar ma kuma banso ta sani ba don banson ta shiga damuwa akaina


Hakan yasa na sake ba sosai ba aka cigaba da hidima dani duk dama rabin taron a gidanmu akayishi hakan yasa ban cika had'uwa da 'yan gidansu ba duk wani abinda zai had'ani da zuwa gidan ina kiyayeshi a wannan lokacin don zaman lafiyar zuciya da ruhina 


Events mukayi Kala-Kala tundaga bridal shower henna party sai hausa day sannan Kamu tsarin bikin ya k'ayatar sosai domin abin anyishi akan tsari natsuwa da kuma wayewa sai sam barka 


Ranar Asabar da misalin 2:30 aka d'aura auren Noosrah Abdullah Maikwanoni da mijinta Sahal Mukhtar Maikwanoni a mafi kyawun sadaki bikin ya samu halartar mutane da yawa inda da dare muka wuce ASAA Pyramid hotels inda acan ne akai gagarumar dinner ta masu hannu da shuni a gaskiya an zubda kud'i iya kud'i don su d'in dukansu 'yan dangi ne kuma masu abun hannunsu danma wai a hakan babban gwaskan bai zoba wai da ba k'aramar b'arna zaai ba sai fatan zaman lafiya da soyayya a tsakanin ma'auratan


Koda aka kaita mun zauna muna jiran ango da abokanshi ne saiga Mama ta shigo d'akin tunda ta shigo nasan babu alkhairi a abinda zatai don har sun fita kafin ta dawo daidai kanmu ta tsaya " da fatan kinji kashedin da akai miki akan barin wainda suka kasa samun miji suyita jelar zuwa gidanki har sai sunyi miki k'ullin da zaisa nakin ya tsinke?" 


Kallonta duka 'yanmatan d'akin sukayi yayinda nikam na sadda kaina k'asa ina maijin wani zafi a zuciyata da sauri bestie tace " haba Mama miye haka kuma.....? " da sauri ta katse ta da "miye kike tambayana ? Zaki amsan tambayata ko kuwa ?" da sauri tace "eh mama naji " 


Kai ta gyad'a tareda cewa "very good sauran miki aiki dashi karki yarda ko da wasa inji ko inga hakan........ke kuma !!" tana mai juya akalar magananta kaina "..........tashi mu tafi tunda ba gidan ubanki bane........wuce mu gani sauran kuma inji kin dawo gidannan ......"


Kafinma ta kai k'arshen maganar ni nakai k'ofa Ina jiyo bestie tana cewa " Mama ya zaki min haka dan Allah " ita kuma tana cewa "ki cigaba da tambaya ta dan ubanki ki bar ganin ke amarya ce hakan bazai hanani in zaneki ba in yaso shi Sahal d'in yayi jinyarki tunda ke sakarai ce" Sauri na na k'ara jin tana tahowa a baya na tana b'ab'atu 


Mutanen waje ne suka fara tambayata ko lafiya na fito saidai jiyo muryan Mama yasa kowa yai shiru daga tambayata wasu suka fara tausarta suna nuna mata illar hakan wasu kuma goyon bayanta suka farayi da sauri na nufi gate d'in gidan ina mai hawaye d'an tafiya na fara sai naji horn a bayana hakan yasa na tsaya Anty Nafeesah ce ta fito tareda umartana da in shigo motarta 


Banda zab'i sai na shiga har k'ofar gidanmu ta kaini tana mai lallashina Niko ban daina kukan da nakeba haba cin mutuncin yai yawa abin har ya wuce daga mu sai ita ya koma har cikin mutane ina ganin kiran bestie nak'i d'auka har aka sauke ni godiya nai mata sannan na kira Fadeel ya bud'e min gida ba shige bayan na d'an saita kaina kad'an d'akinmu na nufa nai kwanciyata ina mai jin zafi a raina 


Wani kiran ya k'ara shigowa na sake ignoring gajiya tai da kiran ta hak'ura ba dan taso ba message d'in ban hak'uri da lallashi dubawa kawai nayi ban mata reply ba ina mai jin tausayin mu mu biyun dan nasan abinnan sai ya sakata a damuwa fiye dani kaina don soyayyar ta gareni mai matuk'ar girma ne da kuma kima rashin abin fad'i gareta ne yasa nak'i d'aukar kiran 


2 days later 


Tunda abunnan ya faru nak'i zuwa gidan nak'i kuma kiranta a waya har Mamie ta kira aka ci sa'a tana office ta kira Areepha itama tana school fav ma hakan rasa yanda zatai tayi da yamma ina parlor a zaune saiga kiran waya bak'uwar number ce hakan yasa na d'an jinkirta kafin na d'auka muryan namiji na jiyo yana cewa " haba bestien mu mai yai zafi har haka .........." 


Kafin ince wani abu na jiyo muryarta tana cewa "tunda anci sa'a ta d'auka ma ai an gode babe bani wayar " cewa yayi " ba wani angode fushi nakeyi da ita tunda tak'i barinki ki huta sai wahala take saki da kuka......." Fisge wayar tayi tareda cewa " baby mana............" Murmushi nayi jin muryanta cikin shagwab'a a hankali na furta " I've missed this soul "


"kin kyauta !! ......" Ta fad'a a hankali I can imagine her rolling her eyes " da nayi mene kuma " nima na fad'a ina k'umshe dariyar da tazo min " ai ba laifi kika yi ba kyautawa kikayi " ta bani amsa kunya ce ta rufe ni jin yacce tai maganar nima nasan ban kyauta ba ko kad'an dan haka nace"I'm sorry babe........kunyar reaction d'ina na ranar ne ya hanani picking kiranki " 


" Hmmmmmm.......sai kuma kika kasa min message ko kuma kizo tunda kinsan ina buk'atar ki kusa dani ko ....." ta fad'a itama shiru nayi kafin na sake cewa "I'm really sorry habibtie " ajiyar zuciya ta sauke kana tace " ba zanyi ba har sai kinzo inda nake" daganan muka shiga hirar yaushe gamo har Sahal saida yace "yau dai an manta dani tunda an samu bestie ko is okayyyy " da sauri nace "bestie sai anjima kinji we'll chat " 


sallama mukayi na ajiye wayar ina mai cewa "ya rabb ka sanya yalwataccen zaman lafiya da walwala a rayuwar auren wannan baiwa taka......."


Awnnnnnn.......friendship like this


Deejasmah 🦋❤🥀


Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.