Free chapter · Read without an account

6&7

by Rabiatu bashir · JAMILA

*_🍇🤍JÁMÉÉLÉR🤍🍇_*



💎Labarin Jamila🖌️




   *Na💖*

*RABI'ATU BASHIR ABDULLAHI*

(Ummu Maher)Miss green💚☘️


 *MATAR BASH💎*






*Shãfî nã🟨6&7*



.......Kallonta Abu ta yi sannan ta tsuke bakinta alamar tana san ta yi dariya kuma babu halin yin hakan,Janyo hannunta Safiyya Abu ta yi sannan suka Zauna.



 

 Safiyya sai kallon Kafirin Bokan ta ke yi tana k'en k'eminshi don duk hak'uransa sunyi wani irin yellow shar, kamar yasha d'orawa ga wani irin yawu da ke dalala a bakinshi,Uwa uba wani irin wari da ke fitowa daga Bakinsa har ma da jikinsa.

  

 Wata muguwar dariya boka ya yi sannan ya kalli Abu ya ce,Shegiya Abu da alama kina samun kud'i sosai don jiya ma kin kawo wata nan, d'anya sharaf da ita ga ta da wani maik'o da alama Amarya ce ko?koda na ji don yarinyar akwai abin harka,zanso a ce wannan ma haka ta ke don da alama ta yau har ta fi ta jiya dank'o. 

     

 Bokan ya fad'i hakan yana bushewa da dariya kamar tsohon Mahaukaci,yana wangale k'azamin bakinsa.



Koda Abu ta ji doguwar maganar tasa ta yi yawa sai ta fara sharhi kamar yadda ta sa ba"Boka wannan yarinyar da ka ke gani wani saurayi ta ke so ta Aura,shi kuma Saurayin k'anwarta ya ke son ya Aura,ita kuma yanzu tana son arabashi da yarinyar a Aura mishi wannan yayarta ta,ayi musu farrak'u yadda bazai k'ara kallon fuskarta ba.




 ......"Hhhhhhh" 

 

ya bushe da wata irin dariya sannan ya d'auko wani k'aton abu kamar jelar zalb'e Ya ajje a dai dai saitin Guiwar Safiyya sannan ya k'ara bushewa da dariya irin ta basawa d'innan.




 "A yadda naga al'amarin yaron yana son waccen k'anwar taki sosai don idan aka rabasu komai zai iya faruwa don bayan son da ya ke mata yana matuk'ar Sha'awar yarinyar sosai,don haka ina ganin sai dai a b'atar da ita kinga idan aka b'atar da ita shikkenan kin huta,kin yada kwallon mangoro".




 Da k'er Safiyya ta aro dauriya ta aza akanta jin ance Yaya Deen yana matuk'ar son K'anwarta harma da sha'awar ta,wani kishi mai zafi ya tokare mata a k'irjinta.



 " Boka yanzu kawai ayi musu farrak'un saboda idan an b'atar da ita wataran kuma idan suka hyi'u fa don muddin hakan ta faru to babu abinda ba zaisa in kashe Jamila ba,Amman yanzu kawai ayi musu farrak'u."





 Dariya ya k'ara bugawa sannan ya ce"Muguwa wato sai ki kashe ta?har kin tunomin d'an uwana dana luma mai wuk'a saboda kawai yaci bashi na bai bani kud'ina ba shine kawai na yanke shawarar kaishi bar zahu."



 Abu kuwa kallon Safiyya ta ke yi tana kallon boka,don bata tab'a zata Safiyya zata iya kashe mutum ba ballan tana ma ace y'ar uwarta uwa d'aya uba d'aya.




 "Yarinya kisha kuruminki yau yau d'innan za'a yi musu farrak'u ya ji idan bai Aureki ba zai iya mutuwa don haka ya zama lallai ya Aureki,Kuma inason yanzu ba anjima ba indai kinason burinki ya cika na zama matar waccen masoyin na ki?to sai na yi amfani da ke na d'an d'ani abinda angonki bai fara d'an d'ana ba."




 Kad'anne ya rage Safiyya bata kurma uban ihu a wajen ba, don jin furucin arnan bokan,Amman sanin a inda ta ke sai ta maze,Tana had'o kalamai da k'er kamar zata had'iyi zuciya ta mutu ta ce"Na amince in dai zan samu biyan buk'ata ."



Ta ajje mai kud'in da ya buk'ata,shi kuwa sai murmushi ya ke yi


 A ta k'aice dai Boka shi ya fara sanin Safiyya a matsayin Mace,Sannan ya barbad'a mata wani abu a wajen wanda shi kad'ai ne yasan manufar hakan.



 Safiyya ta yi mamakin yadda har ya yi ya gama bata ta shi daga dogon baccin da ta yi ba,don yana kirawota ta nemi hankalinta tarasa,ta kalli jikinta yadda ya yi mata kaca² da jini kamar an yanka rago,da k'er ta tashi tana had'a hanya, tana kuka har ta fiyo daga cikin bukkar d'akin,ba ta ga Abu ba sai ta fara waiwaye ko zata ganta.


 Ganin abu ta yi ta fito daga wata bukka tana gyara d'aurin zaninta,Mamaki da furgici yasa Safiyya zubewa a wajen don k'afa funta sun kasa d'aukarta,Abu ta taho da gudu ta d'ago Safiyya suka kama ta fiya babu alamar boka babu dalilinsa a haka suka tafi har titi Safiyya tana uban tangad'i kamar y'ar maye nan kuwa tsabar wahala ce tsantsagwaro.




 Yanke shawarar kai Safiyya gidanta ta yi duba da yadda boka ya yi wa Safiyya fata²,Sannan ta kirawo su Umma ta shaida musu ce wa Safiyya tana gidanta wai mai mashin ne ya kad'e ta ta suma.


 Sun yadda sosai da Abu don shekara kusan Bakwai tana musu Aiki ba'a tab'a samun matsala ba har ta yi Aure,don haka suka d'unguma zuwa gidan Abu don duba d'iyar tasu.




 Ni kuwa a lokacin muna d'aki nida Fatima Umma ta shigo tana fad'a mana da hanzari muka bisu, abun mamaki har da Yaya Deen shi da basu tab'a wata doguwar magana bq don jininsu bai had'u ba,don Aunty Safiyya bata da kunya ga turb'une fuska.



 B'oye mamaki na na yi har muka shiga mota muka tafi dubota,Yaya Deen kuwa sai rawae jiki ya ke yi ba tare da ya kalleni ba tun da muka shiga motar,idan kuwa ada ne muddin muka fita unguwa koda dasu Umma ne haka zai juya glass d'in motar ya yi ta b'ingira dariya yana tsokana ta.




Da rawar jiki ya shiga d'akin tun kafin a yi mishi iso,Ita kuwa Abu k'ara k'arfafa mishi guiwa ta ke yi wajen ce wa"Ka shi ga can ciki tana k'urya saboda iska shiyyasa da aka shigo da ita na ce a kaita cen".



 Wani malulun bak'in ciki ne ya ya tokareni alokacin dana ga Yaya Deen yana rik'e hannun Aunty Safiyya yana mata sannu ita kuwa sai wani kukan shagwab'a ta ke yi.


 Fatima kuwa kallon Aunty Safiyya ta yi ganin duk k'afar ta jini ne,Ai kuwa da sauri Abu ta rufe k'afar Safiyyar don gudun kada asirinsu ya tonu,basu san tuni Fatima ta dad'e da gano abinda ya faru Da Safiyyar ba,don Allah ya yi wa Fatima baiwar gane duk wani mutun mara gaskiya don tana shigowa ta gane don baiwar Fatima tana da yawa.


 Sai kuwa Yaya Deen ya ce"Umma mu tafi da ita gida don ta samu kulawa sosai don nan akwai zafi Sosai don bana son Matata ta shiga wani hali.





*Kuyi hakuri kunsan bani da lfy ne na samu Miscariage so shiyyasa na yi typing kad'an*.





*Ummu Maher*

Miss green ce.



Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.