Free chapter · Read without an account

47&48

by Rabiatu bashir · JAMILA

Wata uwar ashar maryam ta buga jin wai mijinta ya yi aure,ta ɗauki waya ta kirawo Ameera wato Hafsat,abu ɗaya ta faɗa mata shine wallahi ba za ayi mata kishiya a zauna lfy ba,ta jira ta gobe zata zo.

 Su kuwa mazajen nasu ko ajikinsu ƙarshe ma suka nuna musu ba ta su suke ba,,mlm mahaifinsu yasha zagi sosai wai duk shine munafukin da ya saka akai musu kishiya.



 Sassafe HAFSAT tazo ta samu MARYAM sai kuka ta ke ta kalleta sheƙeƙe sannan ta ce yanzu zan zamuje wani waje da za ayi mana maganin ƴan banza,sai kallonta maryam ta ke jikinta duk ya yi sanyi suka tafi a motar hafsat Ɗin.



 Wani daji suka shiga MARYAM sai ɗari-ɗari ta ke saboda tsoro,ita kuwa Hafsat sai kusa kai ta ke da alama ta saba zuwa wajen.



 Wani kango sukaje duk sai haƙi ne ya ke tashi acikin kangon Hafsat ta shiga tana kallon ogan nasa,ogan ya jefar da tabar wiwin da ya ke sha ya ce"shegiyar ƙwana biyu kin manta dani".


dariya ta yi sannan ta ce buƙata nazo da ita jamble inaso a kashe min wasu mutane guda biyu.



Da sauri Marym ta kalleta idanunta a warwaje,bata san sanda suka gama maganarsu ba har suka fito daga cikin dajin,tsoro fal a zuciyar maryam.





Contact


Ummu maher

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.