Free chapter · Read without an account
2
*đ€ME ZAN YI DA ITA?*đ€
NAZEEFAH SABO NASHE
FREEđ
***
-
2
Sumul suka farka innaji ranar ta dâan ji sauâki, har yamma shatu na tare da ita Ta kasa motsawa ko nan da can ranar kam jikinta a sanyaye yake duk tsiwar da masifat ta zubar tana gefen innaji a zaune kan tabarmar karauni. Innajin Ta tsefe mata kanta Ta wanke tas da kanwa da karkashi sai âkyalli gashin yake yasha man kwakwa kasancewar shatu mai gashi na ban mamaki tamkar mutanen âkasar hindu don ma bata son gyarashi da âkyar take barin innajin ta taâba mata kai shima sai tayi mata jan ido.
Har aka gama tana kwance lamo ba mai magana tsakaninsu ita innaji tana karatun suratu maryama ita kuwa shatu ta lula duniyar tunani gaba dâaya ta rasa sukuni.har laâasar tayi kafin ta miâke tayi alwala ta kuma zubawa innajin ruwan alwala innaji ta karâba tana murmushi â Allah yayi miki albarka shatu yasa ki cimma duk burin da nake miki fata a rayuwarki â. âAmeen â shatu ta fadâa murya a shaâke. Suna idarwa innajin ta aiketa gidan modibbo karâbo rubutu.
Duk tsokanar da yara suke mata a hanya ranar banza tayi dasu burinta taje ta dawo ta iske innaji lafiya sumul, don haka take ta sauri kamar zata tashi sama.
Ko mintuna biyu bata yi ba a gidan moddibon ta juyo a sukwane ko saurarar gwaggoji ( salame) da take âkwala mata kira ba tayi ba.
Kamar an cillota haka ta afka tsakargidan da sauri ta saki ajiyar zuciya hadâe da cewa Alhamdulillah Allah innaji na dâauka kafin na dawo kin mutuâ murmushi innaji tayi kafin ta furta âmutuwa ai sai lokaci yayi ayshatuâ da sauri ta dubeta jin sunan da ta kira ta dashi innaji ta waro ido tace âlafiya â ta hau girgiza kai â ji nayi kin kira ni da sunan da baki Taâba kira na ba â dariya kawai tayi tana shan rubutun ta hadâe da kallon shatu kallo mai nuna tsananin âkaunar da take mata.
Cikin dare innaji ta fara jin ciwon naâkuda tun tana daurewa har abin yaci âkarfinta ta miâke da âkyar ta budâe wata adaka ta zaro wasu hotuna da biro ta rubuta address din family house dâinsu ta nadâe a takarda ko bakomai bata san ya ta Allah zata kasance ba.
Da âkarfi ciwon yazo mata har bata san lokacin data fara tashin shatu ba a razane shatu ta tashi saboda wani mummunan mafarki da take a wannan lokacin, ganin innaji cikin wani mawuyacin hali bata san sanda ta zunduma ihu ba tana ruâkunâkumeta â bana so innaaji bana son mafarkin da nayi ya tabbata â. Da kyar innaji taâkaâkalo wani murmushi tana miâka mata takarda â ayshatu ban san ya ta Allah zata kasance ba amma koma dai yayane bayan raina ki nemi dangi na idan mahaifana suna raye ki basu wannan takardar da wannan hoton suna gani sun san ke jini nace Ayshatu idan babanki ya dawo kice masa ya yafe ni Allah ya yanke ganawarmu â. Hawaye take yi sosai na tsananin azabar naâkuda. Ayshatu kuwa ta zama kamar mutum mutumi ta rasa ma mai zatayi abinka daâkanâkantar shekaru. Sai jijjiga innaji take ba bakin magana har zuwa sanda taji innajin ta saki kalmar shahada jikinta gaba dâaya ya saki ji kake dâif lamarin Alhakamu ya tabbata. Ita kuwa a nata tunanin barci innaji tayi bata san mutuwa ba bata san ya ake mutuwa ba gashi ana fadâa musu zafin fitar rai a yanda kuwa ake kwatantawa tabbas wannan ba mutuwa bace barcine ta ayyana hakan a ranta, don haka hankalinta kwance ita ma ta kwanta a gefen innajin barci ya kwasheta barcin da shine ya kaita harâkarfe goma na safe.
Tana farkawa ta tashi a razane tana kallon hasken dâakin tare da tunanin me yasa innaji yau bata tashesu sallahr asuba ba. dubanta ta kai inda innajin take da sauri ta zare ido ganin idonta a kakkafe ya kalli sama ai bata san sanda ta hau jijjigata ba jin bata motsi yasa ta runtuma waje a guje tana Kiran jamaâa âkuzo ku duba min innata tayi barcin zomo na tasheta taâki tashi â maâkota suka shiga gidan sai gani tayi suna fitowa jiki a saluâbe ga kallon tausayi suna mata . Kalmar da taji wata ta fadâa ne Allah yajiâkanki maryamu halinki na gari ya biki yasa ta farka daga tunanin da take na cewa innaji barci take.aiko zuba hannu aka ta âkwallaâkara sai ganinta a kayi a zube ba numfashi.
Allahu akbar kabeeran Ubangiji kenan mai yin yarda yaso a lokacin da yaga dama Allah yajiâkan iyayenmu.
A safiyar jumaâar misalin âkarfe sha dâaya na safe aka sada innaji zuwa gidanta na gaskiya hawaye sai zarya yake a fuskar abokan arziki kowa ya shaida innaji bata da abokin rigima to ita maganar ma bata dameta ba balle har ta samu abokin rigima. Shatu zube a cinyar gwaggoji sai mayar da ajiyar zuciya take da razana har sai da moddibo ya sake mata rubutu aka bata. To haka dama rayuwa take.
A hankali shatu ta fara sabawa da rashin innaji kullum kuwa maâkale da takarda da hotunannan take kwana tayi alâkawarin sai ta sadu da dangin mahaifinta. Gidansu gwaggoji ta koma ta daina wanka ta daina komai wai ita ta gama jin dadâin duniya tunda innaji ta tafi ta barta. Yaran mutane kuwa a lokacin ta âkara takura musu musammam masu uwa raye shatu bata da âkiba sam amma sai âkarfi ta gallabi mutanen garin tun ana dâaga mataâkafa saboda rashin uwa har tausayin ya kau aka fara kawo âkararta wajen gwaggoji. Gwaggoji bata da fadâa sam don haka shatu takeâkara sangarcewa kullum da rashin jin da zata rakito ta kai yanzu har manya shiga shirginsu take musamman masu gonaki da suke kuka da ita.
Makaranta kuwa tuni tayi sallama da ita ta allo kawai take yi itama don moddibo yana cin gidansu ne da batayi ba. Gashi yanzu shi bashi da cikakkiyar lafiya yau fari gobe tsumma.
BAYAN WATA SHIDDA
Da rasuwar innaji jikin moddibo ya âkara tsananta, hakan yasa shi fara hadâa komatsansa baya so ya mutu anan ya fito ya mutu cikin ahalinsa da suke garin yola. Itama gwaggoji hankalinta yafi kwanciya su tafi musamman saboda shatu ko bakomai a can dangi da yawa zaâa samu mai tayasu kula da ita.
Safiyar wata asabar suka fito da âyan âkullin kayansu suka fara sallama da mutanen garin da suka yi dandazo a âkofar gida, duk jikinsu yayi sanyi musamman yara da suke kallon shatu Idanunsu fal âkwalla. Shatun ma kuka take ta kalli yaran tana murmushi âkuyi min tsokanarâkarshe don Allah ko bakomai zan dinga tuna ku.â Shiru su kayi mata, murya na rawa ta fara binsu dâaya bayan dâaya tana cewa âku fadâa mujiya mai idonta a loko....â Ai kuwa yara suka fara har ita suna kuka kuka, dariya- dariya a haka suka rakasu har inda mai amalanke yazo ya dâebesu tana dâaga musu hannu suna bin amalanke , rayuwa kenan ba mamaki shikkenan tayi sallama da garin nijar. Amma taâkudirce insha Allah zata dawo.
Kwanansu kusan biyu suna tafiya, kafin Allah ya kawo su garin yola nan suka hau motar garinsu demsa, daga demsa suka shiga wataâkurâkura ta isar dasu cikin âkauyensu gwamba. Ai kuwa mutanen garin suna ganinsu suka shiga fitowa ana murnar ganinsu.
Bayan sun shiga cikin gidan mai girman gaske gininâkasa suka fara yiwa juna gaisuwa anan suke jin labarin mutuwar muji mahaifin shatu. Ashe da ya taho hatsari yayi a garin yola hakan yasa ya bada address din family house dâinsu na nan kafin a kawo shi kuma rai yayi halinsa. Su kuma basu san inda zasu samesu ba. hankalin shatu ya tashi ta zube wajen har iskokanta suka ziyarceta, kowa a wajen ya tausaya mata musamman da suka ji labarin rasuwar maryamu ma. Moddibo kuwa innalillahi wa inna ilaihir rajiâuna yake ja kansa yana juyawa sai gani a kayi shima luuuuu ya kifa. Ai ko ana dâago shi aka ga rai yayi halinsa. Nan kuwa koke- koke ya âkaru shatu kuwa kuka take aljannun Na sake bugeta. Gwaggoji kuwa kasa magana tayi tana taajjabin lamarin Ubangiji ashe haka mutuwa take lokaci dâaya taji mutuwar dâanta âkwaya guda da rage bata dawo daga razanin ba shima mijin ya mutu, ai ji tayi ina ma ita ma ubangiji ya dâau ranta.
Moddibo kam ya dace ya mutu ranar jumaâa aka sadashi da gidansa Na gaskiya. Haka rayuwa take Allah yasa mu cika da imani .
Gwaggoji daga ranar bata sake samun lafiya ba. sai dai a kwantar a tayar, hankalin shatu ya matuâkar tashi duk ta sake firgai firgai ko wanka batayi, bata so ta rasa gwaggoji a karo na hudâu Ta san idan ta rasa gwaggoji gatanta ya gama zubewa warwas. Mutanen nan taga basu da zumunci ko a yanzu haka ita take yiwa gwaggojin komai hatta da gyara jiki idan taâbata. Iyakacinsu da su abinci shima ko yaroâkarami zai iya cinyeshi.
Ranar wata jumaâa da yayi dai-dai da rasuwar malam sati takwas, suna kwance gwaggoji na nishi sans-sama tace â shatu ko bayan raina kada ki zauna ana tunda kince maryamu ta gaya miki inda magaifiyarki take kiyi tafiyarki can, wadannan mutanen kowa kansa ya sani, ga âyan ubanci da suka a kansu ba zasu riâke ki da gaskiya ba , ina jin tsoron in mutu in barki anan don haka na dadâe da tanada miki kudâin mota.â Ta fadâa tana lalube a cikin bujenta dubu goma cif ta ciro ta miâka mata. âKiâboye shatu ki adana su Allah yayiwa rayuwarki albarka ya kareki daga sharrin dukkan abin âki, baki da wani gata sai dangin mahaifiyarki saboda haka ki tafi can ni na san lokaci na yayi, mutanennan mugaye ne duk âyan uba suke da malam dalilin gallazawar da suke mana da saran âboye yasa muka gudu muka barsu yaranmu ta dalilin azabarsu su uku muka rasa don haka kema ba zasu barki ba....â tari ne ya fara sarâketa tuni ta fara aman jini, zuciyar shatu ta bushe Ta riga ta saba da mutuwa ta san ita dâinma mutuwar zata yi.
A Jikinta kuwa gwaggoji ta saki kalmat shahada ta mutu, ko alamar hawaye babu a idon shatu sai zuciyarta data ke wani tuâkuâkin baâkin ciki. Ta ja mayafi ta rufe mata fuska taja gefe tana jan wani numfashi mai huci ta tabbata yanzu bata da wani gata........
Sai asuba ta sanar da mutanen gidan mutuwar gwaggoji. Ba tare da wani nuna jimami ba su kayi janaâizarta aka kaita gidanta na gaskiya.
Bayan kwana bakwai rayuwa ta canjawa shatu zancen gwaggoji ya fara tabbata, ko abinci basa bata sai tayi musu aikatau. Karshe suka ce zata fara fita tallan nono bayan ga âyaâyansu mata basu dâora musu ba.
Cikin dare taji jatau suna shawara da dâan uwansa wai su hadâa ta aure da liti yaron da kowa ya shaida dâan Taâaddane, ai kuwa shatu a daren ta miâke Ta hau shiri tabbas lokacin barinta garin yayi a yau zata tafi dangin uwarta.
Cikin duhun daren ta fito sai dai kafin ta kai ga dâarewaâkaramar katangar jatau ya hasketa. Waye nan.......