Free chapter ยท Read without an account

3-4

by ๐™ฝ๐š˜๐š˜๐š›๐™ธ๐š–๐šŠ๐š— ยท Papi ne!

๐Ÿ‡๐Ÿ‡PAPI NE!๐Ÿ“๐Ÿ“


Written by

Noor Eemaan


Wattpad

@NoorEemaan



Tnx all naga comments dinku da yawa hak'an ya bani k'arfin guiwar typing, Sannan mutane da yawa sun tambayeni cewa menene ma'anar "PAPI NE" toh Papi dai another name ne da diya kan kira uba da shi...


Page 3-4

........" Kai Nu'aymu ka fita idona in rufe fa, bazai yu kullum ka dinga tayar min da hankali ba, dana Ahamadu bai taba sani magana ba, sai kuma tasa k'uka tana cewa Allah ya jikan ka Ahamadu, albasa bata bi halin ruwa ba" ta karasa tana fyato majina...


Kallon ta ya tsaya yi yana mamakin yawan rigimar ta, domin ba wani tsufa mai yawa tayi ba amma dukkanin wata alama na rikicin tsufa ya riga ya gama bayyane kansa.


Runtse idanun sa yayi wanda hak'an ya zame masa tamkar dabi'a, kai kace wani babban saurayi ne.

"Ooh Kaka rigima, nifa ba yaro bane da kullum zaki dinga sa min ido kan lallai sai na dawo gida da wuri, sannan sunana ba Nu'aymu bane, Nu'aym nake!"


"Kai dallah rufamin baki, ina abun yake? Idan kai ba yaro bane toh meye kai dan gidan ku, yaushe ma aka yaye ka?"


Bai kara kula ta ba, saboda baby'n dake tare da shi, cikin lalluma ya fara cewa"haba matar yi haku'ri, in sha Allah zan dinga k'ok'arin dawowa gida da wuri kinji?"


Tabe baki tayi kana tace "toh Allah yasa" Nu'aym na k'ok'arin magana baby'n ta canyare k'uka, wata zabura Kaka tayi ta haye gadonta ta lafe kuriyar dakin kana cikin tsananin tsoron da rudu ta fara cewa "Nu'aymu aljana jaririya cikin gidan mu innalillahi wa innah ilaihi raju'un, mun shiga uku" ta karasa tana zaro ido hadi da sake shigewa jikin gadon.


Wata dariyar mugun ta ya saki, cak! Kaka ta tsaya da k'ukan nata tana cewa "ya rahamanu ka taimake mu, shikenan aljana ta shiga jikin Nu'aymu jikana" jikinta har wani karkarwa yake, yayind'a ta dinga karanto duk add'ua daya zo bak'inta, har add'uar shiga bandaki ta karanto, saboda tsananin rudewa.


sam bata lura da baby'n ba, saboda bata da wani girma hak'an yasa kai tsaye mutum bazai fahimci haka ba.


Gimtse fuskar sa yayi ganin bilhakki da gaske k'uka take, kana a hank'ali ya ciro baby'n daga cik'in jik'in sa, wanna karon kaka ta fi shiga rudu da tsananin firgici...


Bak'in ta rawa yake alamun tana son furta wata kalma, amma ya gagara, kan gadon ya kwantar da baby'n hadi da cewa "relax kaka, baby'n dan Adam ne k'amar mu, kiyi mata wanka ina zuwa" ya karasa yana ficewa domin sanyi sosai yake ji so yake yaje ya sanja kayan jikinsa...


Sai a lokacin bakin Kaka ya bud'e ta fara cewa "wallahi Nu'aymu baka isa ba, kazo ka dauk'e wanna aljanan jaririya daga kan gadona, wanna 'ya karamar diyar da wanna uban madarar kyau kace mutum ce, san...." Kukan da baby'n ta sake sanyawa mai matuk'ar taba zuciya ne ya katse mata tunanin ta.... Take wani tausayin baby'n ya fara ratsa ta, add'ua dauk'e a bak'inta ta dauki baby'n hadi da runtse idanun ta, baby'n sai girgiza take a hannunta, sak'amak'on rawar da hannun ta ke yi...


Ta kai tsawon mintuna goma a haka kana ta bud'e idanunta ganin babu abinda ya sameta, kwantar da baby'n tayi kana ta sauko daga kan gadon tana waiwayon baby'n still cikin tsoron domin gani take tamkar halittar K'yak'yyawar baby'n zai iya sauya wa...


Sif (wardrobe) dinta da ko murfi babu kuma tsahon yayin nan ne ta nufa, wani zanin ta ta dauko ta lullube baby'n da shi kana ta janyo wata tsohuwar stove (risho) ta kunna kana ta dauko wata sabuwar tukunyar ta dake da sauran sabunta ta, saboda tsananin son da take wa tukunyar shiyasa bata dorawa a wuta, cikawa tayi da ruwa ta dora, babu jimawa ya fara tafasa, dan sirkawa tayi da ruwan sanyi kadan, kana ta dauko wani babban roba, hadi da dauko baby'n ta fara yi mata wanka da wani sabulun ta dan saba'in da take ta lallaba saboda sosai take son kamshin sabulun, sosai ta gasa wa baby'n jiki kana ta sake nada ta da zani ta kwantar da ita kan gadon, Sif dinta ta dauko wasu riga da wando masu dan kwari data siyawa diyar kawarta data haihu, kan cewa jibi zata je musu barka, daga kayan tayi tana kallon su kana ta fara cewa "sai ka biya ni kudina, domin naira na gugan naira har dari takwas na cire na siya, atoh" ta karasa Cik'in fad'a tamk'ar Nu'aym din ne a gabanta.


Sosai yarinyar tayi kyau cikin kayan, wani zanin ta sake dauk'owa ta lullube dukkanin jikinta, kana ta cigaba da mitar Nu'aymu zai d'awo ya same ta, kawai ya dire mata 'ya ba tare da yace komai ba ya fice...


Kwantar da baby'n tayi kana ta shiga goge ruwan daya zuba a kasa, fitar da robar ruwan wank'an waje tayi ta zubar kana ta fara juye ruwan saman data tara cikin robobi cikin wata tsohuwar duro dinta, tsakar gidan ta fara sharcewa, kana ta nufi wajen rariya ta fara dauraye kafarta, wanda yayi d'aidai da sallamar da ya yi.


Amsawa kasa kasa tayi, ita ala dole fushi take dashi, bai kulata ba ya nufi dakin kakan, hak'an ya kara bak'anta ranta "wato Nu'aymu saboda ka raina ni shiyasa kayi ficewar ka batare da ka ce min komai ba, saboda ga marainiyar wayon ka ko?" Tun daga tsakar gidan take wanna maganar har ta cimmasa a daki"


"Wato ga sabuwar kamu ko, ina maka magana kayi min shiru?"


"Dan Allah kaka kiyi Shiru, zan yi miki bayani komai"


D'aidai gaban sa ta tsaya ta rike kugu tana cewa "bazan yi shiru ba, nace bazan yi shiru ba dan gidan ku, tukunna ma yar waye kace ka dauko babu ko riga a jikinta, ga ta sabuwar haihuwa"


"Zanyi miki bayanin komai kamar yadda nace, ga madara irin na yara na siyo mata sachet daya ki bata da karamin feeder na siya, ga kuma awarar ki cikin ledan nan, sai da safe" ya karasa yana ficewa...


'Ka dawo ka dauk'e wanna yarinyar daga kan gadona, kana nufin a nan zata kwana ban san wacece ba" ta karasa tana binsa har kofar dak'in sa, sai dai ya rufe dakin nasa, kwankwatsa dakin ta shiga yi yayi shiru a dakin yana dariyar hadi da cin tuwon sa miyar kuka hankali kwance...

Bayan ta gaji da buga kofar ta koma dak'in ta tana sababi...


Ruwan zafin daya yi ragowa ta hada mata madarar da shi, sanya wa baby'n feeder'n tayi a baki ta bata fusk'a taki sha, ciga'ba da bata tayi har ta fara tsotsan... Tas baby'n ta shanye feeder'n, ga wani gumi daya tsatsafo mata saman goshi, tausayin baby'n ya kama kaka d'omin yanzu hank'alin ta ya dan kwanta saboda babu wata alama daya nuna cewa wanna baby'n aljana ce...


Bayan ta kwantar da ita ta janyo ledar awarar ta ta fara ci tana tunanin rashin mutuncin da zata yi wa Nu'aym go'be bayan ta gama ta fita hadi da dauro alwala, kan gadon ta kwanta tana karanto add'uar kwanciya bacci, domin kaka akwai ibada...Babu jimawa bacci ya d'auke ta


2:30am

Baccin su suke hankali kwance, sai kawai k'uk'an baby'n ya karade dukkanin ila'irin gidan, yamutsa fuska kaka ta yi domin ba kadan ba take jin dadin baccin ta, tashi tayi zaune ta fara lallaba baby'n, sai dai ina tamk'ar kara cewa cigaba da k'uka take...


Yana cikin baccin sa yaji tamk'ar cikin kunnen sa take yinsa, mik'ewa yayi ya bud'e kofar dak'in sa ya fita, yana zuwa ya dauk'e ta izuwa dak'in sa ba tare da ya sake cewa komai ba, jijigata yake sai dai taki yin shiru, labb'ansa na kasa ya sanya mata a baki, take ta kama ta fara tsotsa, wani zafi-zafi ke ratsa kwanyar sa a sak'amak'on tsotsan da take yiwa labb'ansa, k'ok'arin zarewa yayi saboda zafi da ya ishe shi, ta tsalla k'uka, saurin mayar mata yayi, ya ciga'ba da jure zafin har tayi bacci, sauki ajiyar zuciya yayi kana ya kwantar da ita kan gadon sa da bai fiye girma da taushi ba, kwanciya yayi shima, yana add'uar Allah yasa kar ta tashi kafin safiya...



Har yanzu bamu shiga cikin labarin ba, just bear with me habeebt's, sannan Ku yi manage wallahi nayi typing ya goge, raina a bace yake๐Ÿ˜”



SHAREโœ”

COMMENโœ”

VOTEโœ”

EDITโŒ

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.