Free chapter Β· Read without an account
27-28
ππPAPI NE!ππ
*Written by*
Noor iman
*wattpad*
@NoorEemaan
EDITING IS NOT ALLOWEDβββ
(Pls sister'sπ vote and follow me on wattpad @NoorEemaan)
27-28
(Not edited)
............ Ζayan yaje kantin ya siyo sanitary pad mai suna MOLPED. Ζ³a dawo gidan yaga har yanzu bata fito ba, sai kukan ta dake tashi kadan_kadan a bandakin.
Dakin kaka ya shige yana mamakin ina taje haka, pant din Nu'aiymah ya dauko ya ajiye kan gadon kaka kana ya zauna yana jiran shigowar ta...
Bayan kamar mintuna goma da zaman nasa ta fito idanunta jajur, tana tafiya a hankali tamkar mai koyan tafiya, kafe ta yayi da ido, tausayin ta fall zuciyar sa, kawar da kansa yayi hadi da cewa "gashi ki kimtsa jikin ki..." Ya karasa ya nufi hanyar waje
"Papi nah!" Ta kira sunan shi a raunane
Cak! Ya tsaya batare da ya juyo ba.
Ganin ya juya yasa tace "Papi kaga jinin har yanzu yana zuba da yawa ko kuma ni mezan yi da wanna abun" tace tana nuna sanitary pad din.
Tausayin ta mai yawa ne ya darsu a ransa, hakika ita din karamar yarinya ce bata san kan abun ba.
A hankali ya juyo yace "Baby ki saka pad din a jikin ki, ina waje"
"Papi ni ban iya sawa ba"
"Ooh God! Baby nima ban iya ba, ki..." Sai kuma yayi shiru ya dawo gadon ya zauna.
Pad din ya dauko ya kurawa ledar ido yana karanta bayanin da suka yi hadi da hoton da aka zana mai d'auke da yanda mutum zai saita pad din a jikin pant, tare da awanin daya dace mutum ya cire Saboda kiyayye lafiya.
Bayan ya gama saita mata, ya bata yace "saka shi, ki saka kaya, ina waje"
"Toh papi" tace tana kokarin cire zanin data d'aura.
Zanin gadon sa daya baci da jini ya cire hadi da kayan ta. Amo ya jika da ruwa cikin babban roba, kana ya daga zanin gadon da nufin fara wankewa, hakan yayi daidai da sallamar kaka....
Salati ta sanya ganin jini a jiki zanin gado, cikin tsoro tace "dan nan ina ka samu jini? Ciwo ko kaza ka yanka mana?" Ta fada tana dube_dube, idanun ta suka hango mata kayan fadeelah a kasa, take ta fahimci abinda ya faru. Cikin sauri ta nufi daki ta hango Fadeel na kokarin sanya wando.
_"ya rasulillahi manzon Allah, Ohh duniya"_
Kaka tace cikin mamaki tana kallon Nu'aiymah.
Da gudu Nu'aiymah ta fito ta rungume Nu'aym ta baya tana cewa "Papi kana jin kaka ko? Kace ta daina, tana sani kunya" ta fada cikin iyakar gaskiyar ta tana boye fuskarta, yayinda take kuka.
Juyo da ita yayi ya rungume, yana bubbuga bayanta alamun rarrashi, cikin son kwantar mata da hankali yace "yi shiru kinji, daina kuka you see jikin ki ya yi zafi"
Hannunta ya riko suka dawo kan tabarma yace ta zauna kana ya cigaba da wankin sa, batare da ya kula kaka dake ta salallami ba.
Bayan ya gama ya shanya kayan hadi wanke hannunsa ya dawo kan tabarma ya zauna hadi da dora kan baby Nu'aiymah kan cinyar sa yana dan bubbuga bayanta...
"Yayi muku kyau uba da 'ya, gabadaya kun share ni"
"Ohh! Kaka a enough please, kin tafi ki bar min Baby cikin mayuwancin hali, da ban dawo ba fa?"
'Kaga malam karka isheni da wani turacin karyan ka, har da wani enop(enough) unguwa naje dubiya, kafin na tafi kuma lafiya lau na barta, gata gabanka ka tambayeta, Nu'aiymahtou ba lafiya lau na tafi na barki ba, har kika ce na siyo miki cakulat(chocolate)? " ta dawo da maganar kan Nu'aiymah cikin tsigar tambaya.
Turo baki Nu'aiymah tayi hadi da cewa "Eh"
"Toh kaji dai da kunnenka, da za ka fara min wani kumbure_kumburen ka na banza, wai kai mai 'ya ko"
"Toh naji, ya isa kakus" ya fada cikin gajiyawa da maganar ta.
"Yawwa 'yar nan bud'e kunnen ki, ki ji abinda zan gaya miki, daga yau kin girma fa, babu ke babu wasa da namiji ko kula wani namiji, idan kika bari namiji ya taba ko da yatsan ki ne, shikenan zaki samu ciki, ki nutsi ki daina tsalle_tsalle, ki kula da gyara jikin ki idan ba haka ba wari zaki na yi, da kin shiga mutane zasu fara gudun ki idan bakya kula da tsaftar jikin ki..."
Kukan Nu'aiymah ne ya katse Mata sauran maganar ta, ita babu abinda yafi sa ta kuka kamar cewa da kaka tayi za a dinga gudun ta.
Runtse idanun sa yayi kana ya ware su kan kaka yace "kaka! kaka!! kaka!!! Please ya isa, tayaya baby zata iya daukan duka wadannan kalaman naki? Sun yi mata tsauri dayawa, domin har yanzu yarinya ce karama, kin sani cewa bata zuwa ko ina, daga makaranta sai gida, ni ki daina sa min ta kuka"
"Toh ka fini son ta ne? nace ka fini son ta ne? nima ina son ta ai, shiyasa ma na zauna ina gaya mata abinda ya dace, tunda kai uban zamani ne baka gaya mata ba, kuma da kake cewa ba ta zuwa ko ina, ai na fika sanin Nu'aiymahtou mai nutsuwa ce, amma dan yau ne ka haife shi baka haifi halin sa ba, a toh ka barni in gaya mata, kina jina Nu'aiymahtou ko? rabu da Papi'n ki....." Haka dai kaka ta cigaba da yiwa Nu'aiymah nasiha, Nu'aym kuwa tagumi ya buga yana kallon kaka...
*** *** *** ***
*BAYAN KWANA HUDU*
A yau jinin Nu'aiymah ya d'auke, tayi wanka, kasancewar ta san yanda ake wakan jinin haila domin a islamiyya ana koya musu.
Bayan tayi wanka ta fito ta sanya kaya, kaka tace ta zauna ayi mata kitso ko hudu ne yayi bushe da wuri kasancewar tana da cikar gashi hadi da tsayi. Ai ana fara taje gashin ta fara matso hawaye, kaka sai mita take "dole ki so kitso yarinya, tunda kin zo a mace, idan kuma ba haka ba sai a aske gashin kowa ya huta"
Ana haka Nu'aym ya dawo daga gareji, kasancewar bai samu aiki har yanzu ba, ya sanyi shi ke zuwa garejin.
Tun kafin ya karaso Nu'aiymah ta kara sautin k'ukan ta, zama yayi ya shiga lallashin ta, amma inaa sai juya kai take, jikin sa ya sanya ta ya shiga lallaba ta, har aka yi kitso zane guda hudu...
Ana gama wa kuma ta shiga nunawa Papi kitson daga sauka har wajen mazaunan ta, shafa kan yayi yace "kitson yayi kyau Sosai Baby na"
Washegari da misalin shida da rabi na sanyin safiya, Nu'aymah ke tsugunne cikin kitchen gaban murhu sanye da kayan Nu'aym na bautar kasar sa da aka rubuta NYSC da manyan haruffa sai hula p-cap, kana ta d'aura zani, ita ala dole tasa kayan Papi, domin sosai take son kayan, ita bata ki kullum ta sa kayan ba, Nu'aym har dariya yake mata idan ta saka, domin kayan yayi mata yawa.
Doya hadi da kwai da Nu'aym ya kawo jiya, wanda yau kaka zata yi musu karin kumallo dashi ta d'auko, dakyar take iya fere doyan domin rinjayar ta yake, haka ta fere wani wajen har da bawon doyan a jiki, ga jikin ta daya fara yi mata kaikaiyi sak'amak'on taba jikin ta da ta yi da hannu da take fere doyar, still dai bata hakur'a ba, ta fara datsa doyar, kasancewar wukar mai kaifi ce yasa bata sha wahalar datsar ba.
Bayan ta gama ta wanke doyar, sai ta fasa kwai nan guda shida, a wani kwano karami, dama wuta ya huru har ya gaji da ci, domin shine abu na farko data fara yi.
Wata tukunya da kaka ke suya akai ta dora a wuta, hadi da zambada mai da suke tattalawa cikin tukunyar, doyar nan a danyar sa haka ta tsoma shi cikin kwan da ko Maggi mai samu ba, ta sanya cikin man daya dau zafi, ganin kwan yana kama jikin doyar yasa ta saki yar karar murnan a fili ta furta "yau papi da kaka zasu ci girkina, Papi zai ji girkina yafi na kaka dadi"
Haka dai ta gama suyar da ko wani wajen mai bai taba doyar ba, ta kwashe a wani faranti mai murfi tana jin wani dadi na ratsa ta, gamawar ta keda wuya kaka ta fito Salati sauke a bakin ta, ganin har rana ta fito bata dora musu karin kumallo ba...
"Amma 'yar nan baki da kirki, dama kin tashi baki tashi ni ba, in dora mana girki"
murmushi murna tayi hadi da cewa "ai na yi mana girki kaka" tace tana nuna farantin da hannun ta
"Kinyi me?" Kaka tace cikin daga murya yayinda ta kwalalo ido.
"Na soya mana doya da kwai" ta kara fada murmushi d'auke a fuskar ta.
"Innalillahi wa innah ilaihi raju'un" shikenan kinyi mana bakin cikin cin kayan dadi, kika san yanda nake ta zumudi gari ya waye kin soya mana, wa ya aike ki ni zainabu?"
Nu'aym dake tsaye bakin kofar dakin sa, sai gimtse dariyar sa yake, domin kaka ta bashi dariya.
"Toh kaka ki ci d'aya kiji akwai dadi, wallahi na fika iya girki" Nu'aiymah tace tana kara sakin murmushi irin na alfahari da kanta dinnan
Gaban Nu'aiymah kaka taje, daya ta dauko ta sanya a baki, furzar wa tayi sak'amak'on wani karnin kwai, ga doyar danye.
"Amma kin gama da mu wallahi, dan nan, dandana kaci ko tafasa doyar bata yi ba" kaka ta fada tana ansar faranti daga hannun Nu'aiymah ta mikawa Nu'aym.
Wani murmushi ya saki, kana ya dauki daya, idanunsa kafe kan na Nu'aiymah dake ta sakar masa murmushi, ita tasan ubanta zai yabi girkin ta, haka ta aiyana aranta.
Tauna daya yayi ya kasa hadiye wa, Saboda wani dandano mara dadi daya ziyarce harshen sa, dan bata fusk'a yayi ya furzar da doyar a bakin rariya ya kuskure bakinsa ya dawo gaban Nu'aiymah data fara matso hawaye, kaka sai cewa take "kaji abinda naji ko nu'aymu, abu salam ba armashi" amma bai kulata ba.
kafadun baby'n sa ya riko yace "My baby ta girma har ta ita girki, kinyi kokari sosai kinji"
Turo baki tayi tace "toh meyasa ba ka ci ba Papi?"
Dan murmushi ya sakar mata yana share mata hawayen yace "ki bari anjima zan gaya miki kuskuren ki, sai ki gyara nan gaba kinji ko"
Murmushi ta sakar masa tace "Papi jikina kaikaiyi yake min"
"Ai dole baby, doya fa kika fere, bari na zuba miki ruwa kiyi Wanka"
Kaka data saki baki tana kallon su tace "amma baka yi ba, ina jira kayi wa 'ya fada, amma ka kama wani iyayi wai kai nunawa 'ya soyaayya ko? Ai shikenan sai mu zauna ba karin safe"
Bayan Nu'aiymah ta fito ta sanya kayanta, har lokacin kaka mita take, Allah yasa yana da dan kudi a hannun sa, ya siyo musu biredi(bread) dan dari biyu da hamshi, sai kayan shayi na dari biyu da ya siyo musu sukayi karin safe(breakfast) amma inaa har yanzu mitar kaka bai kare ba, fadi take Nu'aymah tayi musu asara da bakincikin cin kwai da doya...
(Gobe ma zan yi kokarin yi muku update, am so sorry habibtie's, wutar mu ce ta lalace, sai jiya da magrib aka gyara. Nagode sosai da kauna
Noor loves you too)
#Share
#Comment