Free chapter · Read without an account

37-38

by 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗 · Papi ne!

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓








Written by

Noor eemaan









Wattpad

@NoorEemaan






EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌





(Pls do vote and follow me at wattpad @NoorEemaan)





(Kila kuga typing error🤒)





37-38



.................. Haka suƙa cigaɓa da rayuwar su ciƙin farinciƙi da annushuwa, Nu'aiymah ta dage da jinyar Papi'nta bama ta bari kaka tayi. Nan fa kaka zata shiga fada wai Nu'aiymah ta hanata samun lada, da dai sauran su, kaka rikici kenan abinda bakai fada bama yi take...









*** *** *** ***






Nu'aiymah ce sanye da uniform farare kal hadi da ratsin blue, Yayinda hijab ɗin ta ya kasance medium(maɗaiɗaici) shima fari, idanunta sanye farin glass daya yi matuk'ar amsar ta, kafarta sanye da canvass farare. Kasancewar Nu'aym ya sanja mata makaranta zuwa na private (ta kudi).













Jakar goyo ce a bayanta baka, hannun ta rike da wani bakin Leda data yiwa Papi tsaraban aya, biscuit, alawa, egg roll da spring rolls sai zobo da har yanzu da sauran sanyin sa, domin mutum zai iya hango hakan ta ledar.









Sosai ake rana, daga yanda take tafiya a hankali tamkar mai tausayin kasa zaka dauka bata jin zafin ranan, sai dai ba haka bane tsananin gajiya ne, domin yau ko break ba a bari sun fita ba, Saboda karatu daya ɗau zafi...










Zumudi take, burinta taje giɗa tayi tozali da Papi'nta, tayi kewar sa tun safe, dama da kyar taje makarantar, taki tafiya sai faman kuka taƙe, wai bazata tafi ta bar shi ba, sai ɗata ga ɓacin ransa sannan ta tafi

domin har yanzu bai koma aiki ba, Saboda jikin sa bai gama warware ba, ya kuma sanar, har an turo mutane biyar ɗa suka zo duba jikin sa daga company'n nasu....













Ta sha ƙwanar layin gida ƙenan taji ana ta danna horn a bayanta, tafiyar ta ta cigaba da yi batare da ta juyo ba, sallama taji wata had'add'iyar murya tayi ta basar bata juyo ba, amma ta amsa a ranta, saɓoɗa muhimmancin ta.









Ta danyi nisa taga ansha gabanta da wata motar hummer jeep, kaucewa tayi ta cigaba da tafiya, ganin da gaske bazata tsaya ba ya sanya mamanllaƙin motar fitowa daga ciƙin motar sa.....








Hada'dden saurayi ne mai kyau hadi da kuruciya ya sha wasu had'add'un English wears, cikin sauri ya tari gabanta yace "haba mai kyau, yanayin ki ya nuna ke mai tarbiyya ce, sannan ya nuna cewa daga gidan mutunci kika fito, an kuma san duk wani mai tarbiyya da girmamawa dan Adam, tunda Allah subhana wata ala ya karrama dan Adam, ko ba komai ai kya masa mun sallama, duk da ba mutuncin mace bane a tare ta a titi, am sorry for that, amma ki bani mintuna biyar dan Allah, I know kin gaji daga school kike please mai kyau" ya karasa cikin wani salo.








"Afuwan, ina sauri ne please" Nu'aiymah ta amsa tana kokarin wucewa.





Kara shan gabanta yayi yace "dan Allah ki saurare ni, bazan bata miki lokaci ba, ni kaina ina saurin ne, amma ganin ki ya sa bazan iya barin ki ba, ba tare ɗa nayi miƙi magana ba"






Dan yamutsa fuska baby'n Papi tayi ita ala dole yanmmata(😹😜) tace "alright ina jinka"






"Nagode mai kyau da wanna damar, da farko dai sunana Habib Husain ni dan nan garin sokoto ne, ina aiki a company'n MTN, sannan ina zaune tare da iyayena ɗuka ɗai anan sokoton, ko zan iya sanin sunan ki?"





Habib ya fada yana jifan Nu'aiymah da wani kallo mai kashe sassan jiki.




Dan turo baki tayi domin ba kadan take jin ranar ba, a taikace tace " SUNANA NU'AIYMAHTOU NU'AYM AHMAD "





"Wow! Nice name, ina son sunan ki, but it seems kin gaji da yawa bani number'n ki ma yi waya"






Dan waro ido tayi kana cikin yarinta tace "Papi na baya bari na rike waya, dana kaka ma nake yin game"







Shagala yayi da kallonta, sosai yarintar ta ta tafi da hankalin sa, murmushi ya saki kana ya sanya hannunsa a aljihun wandonsa ya ciro wayar iPhone 11promax yace "ga wanna ki fara maleji(manage) kafin na sanja miki sabo, domin kin girmi wanna wayar mai kyau nah"








"Sake waro lumsasun idanunta tayi tace " a'a Papi zai yi fushi da ni bana so, ƴace ƙaɗa na ƙarbi aɓin ƙowa"










wow! irin macen da naƙe fata da muradi kenan wato mai tarbiƴa ya aiyana a ransa amma a fili "Sai kice sirikin sa ne ya baki" Husain ya fada yana son ta karbi wayar.






"A'a nagode sai anjima" inji Nu'aiymah.




"To tsaya, bani number'n kaka zan kira ki, karki ce a'a please na roke ki da Allah"








Dan Jim tayi Kana ta amsa ta sanya masa, saboda kada ya sake tsayar da ita yasa tayi gaba abinta, bata ma tsaya sauraran abinda yake cewa ba.....







Zaune ta tarar da kaka da Nu'aym suna hira jefi_jefi ɗuƙ ɗa yawancin maganar kaka ce take yin sa, domin Nu'aym hankalin sa naga baby'n sa ganin har karfe biyu bata dawo ba....







Sallamar tace ta katse masa tunani, wani sanyin dadi ya ratsa zuciyar sa, a fili sai ya balla mata hararan wasa, tabe baki tayi irin na shagwa'ba kamar zata saki kuka tace "Papi nayi laifi ne?"





"Eh mana tun d'azu ina jiran dawowar ki, amma har after 2 baki dawo ba?"




"Am sorry Papi kajiiiiiiiii"


"Toh na hakura 'yar albarka"



"Ke dai gadon bakin hali kika yi wurin ubanki, ace ki dawo daga makaranta ba zaki gaishe ni ba, ni ba mutum bace, wato nayi kankanta baki ganni ba ko, ƙo kuma ban isa ki gaishe ni ba, uhm yar ganin ɗama?"






Dafe kai Nu'aym yayi, ko yaushe baby'n ta ɗawo da zata ce bata gaisheta ba? kallon Nu'aiymah yayi yace "baby please talk to kaka, if not she won't allow us to receive fresh air" Nu'aiym ya fada da turanci gudun magana amma bai tsira ba, suka ji tace "toh meye na kiran sunan kaka a karyar Singlishi(English) idan ba tsoro ba ka fada da yaren hausa mana, gabadaya kun aro karya turancin ku, toh bari kaji baka birge ni ba ehe!, ina alfahari da yarena dama al'ada ta, amma ku yaran zamani sai kayar turanci wai ƙu boko ko...?"









"Kaka sorry kinji, ina wuni na sameku lafiya" inji Nu'aiymah ta na kumshe dariyar ta.






"Lafiya nake ras kuwa, yar ganin dama sai yanzu zaki gaishe ni?"





Nu'aiymah bata kula ta ɓa, ta kalli Nu'aym tace "Papi I bought kayan dadi for you daga school ɗinmu"





Kaka jin an kira *kayan dadi* domin shine kadai abinda ta fahimta a turancin, babu abinda take sai zube ido take taga me a ciki leɗar.........





"Really baby? Thanks 'yar gidan papi'nta" inji Nu'aym.





Murmushi Nu'aiymah tayi ta fara fito da duka kayan ta zube su gaban sa, dariya ce ta taho wa Nu'aym "ooh baby rigima ina zan kai duka tarkacen nan?"





Cikin shagwa'ba ta fara dire kafafu tace "Allah papi ka cinye duka kai na siyowa faaaaaa"




Rike kafafun da take ta buga wa a kasa ƴayi, kana yace "it's alright baby, amma ki min haku'ri ba duka zan ci ba, like this ones..." Ya nuna aya, biscuit, da alawan.


"Su ki cinye na yafe, tunɗa dama kece gwanar zaki"





"Toh Papi nah" ta fada cikin murna domin ba komai yake yarda yaci ba, musamman idan ya bai san waye ya girka ko ya hada abin ba, egg roll din ta sanya masa a baki ya gutsira, lumshe ido yayi yana girgiza kai alamun yayi dadi domin sanya ta farinciki....





Dariyar farinciki Nu'aiymah ta kyalkyalle dashi tace "da dadi ko Papi?".


" sosai ma 'yar Papi, Amma idan da ke kika yi, nasan sai na cinye leɓena Saboda tsabar dadi, I know my daughter is a good cook"





Murmushin jin dadi ta saki ganin an ƴaɓe ta.






"Uhmmmmm duniya" Kaka tace tana tafa hannu, daman ta jima tana kallon su kamar taga TV, bazata iya yin shiru ba hakan yasa tace "wato yarinyar nan ban taɓa sanin cewa bakya sona ba sai yau, ki siyawa wa ubanki abin tabawa amma ni da nake siya miki abu in naje unguwa ki kasa siyo min koda yar aya nan ce, kin manta ranan naira na gugan naira har dubu d'aya na siya miki wani dan kunne na yanmmata Saboda nasan zai miki ƙƴau, Saboda kin mai da ni gantalalliya bansan ciwon kai na ba, shine bazaki iya taho min da komai ba, ai shikenan kuma wallahi sai na dauka na ci, ɗama bakincikin ɗanɗanawa kuke min" tana gama fadin haka ta wawuro springs rolls hadi da zobon ta nufi dakin ta harda saka key kana ta dan daga murya yanɗa zasu ji tace "marasa kirki, kuma sai na cinye duka zan fito"..........



(Am so sorry habibtie's for keeping you waiting, ina busy ne kwana nan, wanna ma a tsatsaye na muku shi💖)









Thank you for reading Papi ne!💞







Share

Vote

Comment



Nooreemaan

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.