Free chapter · Read without an account
47-48
🍇🍇PAPI NE!🍓🍓
*WATTPAD*
@NoorEemaan
EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌
47-48
.......... *Habib Husain* ta gani a rubuce, unplugging wayar tayi kana ta kara a kunne ta, cikin sweet voice dinta mai cike da kuruciya tace
"Assalama alaykum"
'Wa'alaiki salam, da fatan mai kyau na ta wuni lafiya?"
Dan runtse lumsasun idanun ta yi, kamar yadda papi ke yi kana tace
" lafiya Alhamdulillah"
"Toh haka nake son ji, ina kofar gidan fa"
Dan Jim tayi kana tace "Toh gani nan zuwa"
ware Idanunta tayi ta kalli kaka data kafe ta da ido tace
"kaka ya Habib Husain ne yazo"
"Toh maza je ki sai kin dawo, amma ƙarki ɗaɗe"
Mayar da wayar caji tayi kana ta shiga dakin ta, wani hada'dden abaya pink mai yalwa stone ta saka, tayi rolling da mayafin abayar daya k'asance dark pink. Turare a fesa hadi da body spray, wani uban kyau mai tafiya da hank'ali duk wani lafiyayyen namiji tayi, wani black snicker's ɗa ya kara fito da haske kafar ta ta sanya kana ta fito cikin takun nutsuwar ta....
Tsaye yake jikin motar sa, ya sha k'yau cikin kananun kaya, ga tsadaddiyar wayar sa a hannu yana latsawa, tun kafin ta karaso k'amshin turaren ta ya riga ta isowa, take ya dago k'ansa ya sauke su fess ƙan fusƙar ta, wani mugun kyau yaga tayi masa fiye da na k'ullum, Yayinda soyaayar ta mai zafi ya sake ratsa zuciƴar sa.
Aljihu ya mayar da wayar yana jefan ta da wani lafiyayyen murmushi, martani ta mayar masa, hakan yayi daidai da isowar ta wajen shi.
A kunyace tace "Assalama alaykum"
"Wa'alaiki salam, barka da fitowa kyakyyawa da babu kamar ta a duniya"
Murmushi mai dan sauti ta saki, domin babu wanda baya son a yabe shi...
"Ya kaka take, ya kuma school?" Ƴa sake tambaya a tausashe.
"All fine Alhamdulillah" ta bashi amsa.
"That's Good!" ya faɗa
Shiru wajen ya dauko na tsahon mintuna biyar babu wanda ya kara cewa komai, sai ma Habib Husain daya kafe ta da idanu baya ko kiftawa, Yayinda Nu'aiymah ta kawar da kanta gefe saboda kunyar sa....
Ajiyar zuciya mai tafe da murmushi ya saki, kana yace "na san kin gaji ko? Ko mu shiga mota, domin sam bana so ki wahala"
Murmushi ta saki, domin bayan Papi da kaka shine mutum na uku dake nuna kulawar sa a kanta irin sosai dinan....
Girgiza kai tayi kana tace "A'a ban gaji ba, nan ma yayi thanks"
"Don't mentioned mai kyau nah, kin cancanci fiye da haka"
Wani murmushin dai baby'n Papi tayi, bata ce komai ba.
"Yaushe zaki gama school ne? am eager na ga kin zama matata" Habib Husain ya fada, so yake ya jata ɗa hira domin ta saba dashi sosai...
ciƙin kunƴa tace "Na gaba kadan in Sha Allah" Nu'aiymah ta bashi amsa.
"Good! Mai kyau nah, sosai kika kara kyau fiye da ranar dana zo, na lura kullum sabon kyau kike karawa, gayamin miye siririn? Me kaka ke baki ki ke ci ne?"
Murmushi daya bayyana white teeth d'inta mai dauke da open teeth (wushirya) tayi tace
"babu kome fa?"
"Da gaske ya kara fada?"
"Eh da gaske nake" Nu'aiymah ta bashi amsa.
"Toh yayi kyau, ya maganar mu? Ina son jin amsa na yanzu".....
*********
Nu'aym daya taho tun daga nesa ya hango kamar baby'n sa ce ke tsaya, domin bai yarda ita din bace, yana kara kusanto shi yana kara ganin fusk'ar Nu'aiymah d'insa na sakin murmushi da wani saurayi da baya iya ganin kamanin sa sosai, domin ya dan bashi baya...
Fadin tashin hankali d'aya fara riskan K'anshi aciki ba mai sauki bane, duk saurin da yake yi, gani yake tamkar ba sauri yake ba...
Gaba daya jikinsa tafasa yake Saboda zallan tashin hankali da bacin rai, idanun sa sun sanja launi sosai cikin seconds kalilan...
Yana daf da isowa kofar gidan, a daidai lokacin ne Nu'aiymah ta budi baki zata bashi amsar sa, sai dai hango papi ya sanya ta fasa, kana murmushin fusk'ar ta ya yawaita, ba tare da ta bashi amsar ba tace " kaga Papi nah!" Ta fada a hankali
"Ban fahimta ba, kina nufin ƴaƴanki?" Shima ya furta a hankali, idanun sa ƙan Nu'aym daƙe tahowa.
"A'a faaa ba ƴaƴa na ba ne, Papi nah nace, ubana mahaifi da ya haife ni" Nu'aiymah ta bashi amsa.
Dan waro ido Habib Husain yayi, cikin madaukakin mamaki.
Ta ya ya wanna saurayin da baya ko tamtama ya san zai girme shi ya haifi Nu'aiymah, abin da mamaki matuk'a kana da d'aure kai.
Dauke idanun sa yayi daga kan Nu'aym da bai riga ya karaso ba yace " What! are you serious? Kina nufin wanna shine mahaifin ki, I mean you biological father?"
"Wallahi Allah shine" Nu'aymah ta kara fada tana murmushi ita kam bata kawo komai a ranta ba, daidai lokacin Nu'aym ya karo sa wajen...
"Papi nah! Ka dawo?"
Nu'aiymah ta fada tana nufar wajen sa, sai dai inaaaa bacin ran ɗa ƴaƙe ciƙi bai sa ya ji abinda take cewa.
Duk da habib Husain yasan cewa ya girmewa NU'AYM amma dole ya nuna girmamawa a gare shi tunda yana son 'yarsa, duk da har yanzu yana cikin mamak'i ganin wanna matashin saurayin ya haifi kamar Nu'aiymah.
Rissinawa yayi cikin girmamawa yace "ina wuni Papi ka dawo lafiya?"
Wani sabon tak'aici ne ya kara kama Nu'aym babu abinda yake sai faman murza yatsun sa yake, shagwa'ba fuska Nu'aymah tayi tace
"Papi! ya Habib Husain na gaishe ka faaaaa"
Idanunsa masu fidda zallan tashin hankali ya kafawa Nu'aiymah yana hararar ta, yana mamakin nawa take ta har ta fara zance? Sosai yayi controlling temper d'insa (fushi) yace
"baby go inside"
Kara shagwa'be fusk'a tayi tace " Papiiiiii......"
Cikin fushi da murya mai sautin amo yace
"I said ki shiga ciki, before I lose my temper"
Tabe baki tayi irin na shagwa'ba, hawaye har sun ciƙa Idanunta ta shige gidan da gudu....
Dawo da kallonsa kan habib Husain yayi, da har yanzu bai Mike ba kamar wanɗa aƙa ɗasa, rage tsahon sa yayi, ya dora hannunwansa duka biyun kan guiwowinsa, Yayinda ya kafa masa jajayen idanunsa, ga jijiyoyin kansa da suka mike suka fito radu² Saboda tashin hankali har wani ruwan hawaye na zallan bacin rai ya taru a gefen idanun sa.
Cikin wani irin murya yace "Habibu ko what so ever sunan ƙa yake, ina maka gargadi da babban murya, daga yau sai yau kada na kara ganinka kusa da 'YATA! domin bazan mata aure yanzu ba, yata karatu take...."
Share fisabilillah
Comment
Vote
Thank you for reading my novel Papi ne!
NoorEemaan ce🔥