Free chapter · Read without an account

57-58

by 𝙽𝚘𝚘𝚛𝙸𝚖𝚊𝚗 · Papi ne!

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓





*WATTPAD*

@NoorEemaan








EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌




57-58





....... Turus mama tayi cikin zallan mamaki ganin Raliya kwance tana bacci babu jaririn yaron ta ƙusa ɗa ita kamar ɗazu.



Ɗa sauri ta hau ƙan gaɗon ta shiga tashin Raliya saboda tsananin rudewa da firgicewa ta manta cewa Raliya bata da ciƙaƙiyyar hankali...




"Ke! Raliya ina yaron ƴake? Yana ina? Ina kika kai shi? Tambayar ki nake yana ina nace miki?" Mama ta karasa cikin damuwa da tsoro yayinda abin da ya faru shekaru goma sha shida suka shiga dawo mata...





Raliya kuwa kallon mama take tamkar ta samu TV. Can ta fashe da dariya har da dukan cinyar mama.




Hannu mama ta dora a kai ta shiga furta "_innalillahi wa innah ilaihi raju'un_"




Ɗomin jiƙinta na bata cewa kamar yadda ta rasa jikar ta na farko hakan ce ta sake kasance da su.


Shin waye yake bibiyar yarta da jikokin t? hawaye sosai ke fita a idanun dattijuwar matar(mama)....




Wayarta ta ɗauƙa cikin tashin hankali ta shiga Kiran y'ay'an ta dama Al'ameen din ta sanar dasu kana ta fito haraban gidan...




Hakan yayi daidai da shigowar malam baba da mai gadi wanda da alama daga masallaci suke.




Cikin sauri ta nufi wajen su tace "malam an sake dauke jaririn Raliya fa, mun sake rasa jika a karo na biyu malam, wanna masifar har inaa? daga na shiga dakina inyi sallah, ƙawai na fito babu jariri" mama ta karasa cikin kuka gwanin tausayi.





Malam baba dattijan arziki sai da hawaye masu zafi suka zubo masa, nan fa mai gadi ya fita waje hankali a tashi ko zai ga wanda ya dauki jaririn..




Yayinda malam baba da mama suka shiga bud'e ko wani kuzurwa a dakin, kai da har da toilet sun bud'e amma basu ga komai ba, duk da sun san cewa baza su gan yaron ba , amma basu hakura ba domin jariri ba kafa gare shi ba, balle a ce zai tafi wani wajen, amma duk da haka sai da suka bincika ko ina na gidan....





Bangaren Al'ameen kuwa a lokacin da mama ta kira shi fitowar sa daga wanka kenan, ɓa karamin faduwar gaba ne ya riske shi ɓa, take wayar ƴa tarwatse a kasan tiles...




Ƙuka ya fashe dashi tamk'ar k'aramin yaro, ya rasa meyasa y'ay'an sa basu jimawa tare dashi, a lokacin daya fi bukatar su ake raba su....



Shin waye yake masa wanna tsantsar mugunta? ya sani cewa a duniya ɓaɓu wanɗa bashi ɗa maƙiƴi, amma taɓɓas zai iƴa cewa ɗuƙ wanɗa ƴaƙe tare dasu masoyan sa ne, toh waye yaƙe masa wanna cutarwan?




Ya jima sosai yana kuka kana daga karshe ya mike cikin sanyin jiki ya zura jallabiya, ko mai bai shafa ba, ba tare da ya leka dakin Mariya ba, ya fice a motar sa zuwa gidan su Raliya.




Ikon Allah kadai ne ya kai shi gidan lafiya, tsaye ya tarar dasu a farfajiyar gidan, kowannensu fusk'ar sa dauke da damuwa.



Rungume juna suka yi da yaya Auwal daya k'asance aminin sa, sosai Al'ameen ke kuka tamkar k'aramin yaro, ya Auwal ma ta maza yayi amma idanun nan sunyi jajur tamkar gauta.




ga Raliya cikin halin hauka bata ma san abinda yake faruwa ba, balle ta gaya musu komai, nan fa malam baba duk ya umarcesu kan su shiga cikin gidan, babu musu duk suka shiga sai mai gadi da suka bari a bakin aikin sa.




Bayan duk sun zauna. Malam baba yayi musu wa'azi kan yarda da kaddara sannan ya ƙara da cewa su fawwalawa Allah lamarin su, nan suka jinjina kai cikin gamsuwa duk da hakan damuwa na shimfud'e a fusk'ar su.



Bayan nan malam baba yayi gyaran murya, ciƙin murƴar ɗamuwa yace " A da bana son yarda cewa wani na jikin mu ke mana zagon kasa, amma yanzu dole ne mu dage da add'ua da saukar qur'ani, in sha Allah ko waye ke mana wanna abin Allah ya gagauta tona masa asiri, in sha Allah komai zai zo karshe, sannan dole mu fara dagewa kan cutar Raliya, tabbas wanna yake sata mata yara, ba shakka yana da nasaba da cutar ta, basan waye ba, ba kuma na zargin kowa, amma Allah zai tona asirin duk wanda yake mana wanna abin, Al'ameen kayi haku'ri kaji ko? hakika mutuwar yaro yafi sauki, akan ace ɓata yayi, domin idan da mutuwa yayi zamu san cewa 'babu shi a duniya, amma yanzu bamu san a wani hali yake ciƙi ba" nan dai suka cigaba da maganar.

Ɗaga karshe dai suka nufi police station, suka bada report, yayinda aka sanar a gidan radio, basu suka dawo gida ba sai karfe 4 na asuba...






*************




Wanna matar da ta saci jariri kuwa, hotel ta nufa ta kwana domin dare yayi... Duk da uban kukan yunwar da jaririn ke yi haka ta dinga bubbuga bayan shi a gari ya waye, sai misalin karfe 7:00am baccin wahala ya dauki jaririn...




Da misalin karfe 4:40 na yamma ta dauki jaririn daya gama galabaita ta rike shi a hannu, kana ta kura masa ido, tamkar babban mutum ne ta fara yi masa magana kamar haka "A yau kai ma zaka yi nesa da iyayenka. A garin da kuma inda na cillar ɗa yayar ka, toh a wajen ɗaiɗai zan yar da kai, ka ci sa'a yanzu ba lokacin damuna bane, da cikin ruwa sama zan yar da kai kamar yadda na yi wa yayar ka. Taɓɓas hanƙalina yafi kwanciya da in yar da kai a garin dana jefar da yayar ka, a kuma daidai wajen, domin gashi yau shekaru sha shida kenan babu ita babu labarin ta hhhhh" ta karasa tana sakin dariyar mugunta, kana ta sabe shi a baya ta goya shi, tsabanin jiya da take sanye da blue din hijab, yau kuma orange color ta sanya kana ta sanya nikab ta fice daga dakin hotel din.





*SOKOTO STATE*



Isar ta garin yayi daidai da karfe 8:20pm na dare waige² ta shiga yi, ganin babu yalwar jama'a ya sanya ta nufi daidai wajen ɗa ta yar da Nu'aiymah lokacin tana jaririya...



Hakika duk uban shekarun nan da suka shude wajen bai bace mata ɗaga ƙwaƙwalwa ba, a hankali ta kunce yaron d'aga bayan ta, gaɓaɗaƴa ƴayi laushi, gwanin tausaƴi ɗomin tsananin yunwar ɗata ci shi, a hanƙali ta shiga ajiye shi a kasa......





MU HADU RANAR ALHAMIS




SHARE✅


COMMENT✅



Noor iman💖

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.